0
MISKILIN DARE MISKILIN DARE

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya   Sunana Hajara daga kauyen Sambisa Allah ya hore mini kyau na gani a fada, tun ina yarinya...

0
TSAKA MAI WUYA TSAKA MAI WUYA

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya   Auren soyayya mu ka yi da mai gidana. Yana sona nima ina son sa muna zaman soyayya bama b...

0
Photo Album Photo Album

0
IN BISHIYA TA GIGA..... IN BISHIYA TA GIGA.....

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya Kyakkyawace ajin farko,kallo daya zaka mata ka gane cewa bata son raini, tafiyarta kawai abin kallo ce domi...

MISKILIN DARE

Daga
Rabiu Muhammad Abu Hidaya
 
Sunana Hajara daga kauyen Sambisa Allah ya hore mini kyau na gani a fada, tun ina yarinya na taso cikin gata karkashin kulawar iyaye da yan'uwana, duk abinda nace ina so, kafin wani dan lokaci an bani.
Mun shaku da mahaifina matukar shakuwa Allah ya yi ni da jarabar tsokana, amma tsoran kada a taba ni mahaifina ya yi fada haka ake kyaleni lokacin dana kammala makarantar Firamare sai aka kaini wata sakandiren mata ta kwana da ke gabas da garinmu, babu abinda ya dameni a makarantar sai dai kadaicin iyayena, har so nake a ce lokacin hutu ya yi don kawai na dawo gida na ga mahaifina da yan'uwana Allah ya yi ni yarinya mai kokari wannan ce tasa na zama fitacciya a makarantar, domin duk gasannin da ake sawa ni nake cinyewa, haka ni ce na ke yin ta daya ajinmu.
A kwana a tashi yanzu saura shekara daya in kammala makaranta, yanzu kuma kewar kawayena nake ba gida ba, domin mun saba sosai musamman babbar kawata Mufeedah muna son juna ni da ita lokaci-lokaci takan bani labarin birni da irin abubuwan birgewar da suke can don ita yar wata gari ce a birnin Mambil mai suna santanbul, tun ina jin maganarta a matsayin labari har na soma marmarin zuwa birni sakamakon yadda take gaya min garin.
Watarana muna hira da ita sai na ce mata Mufeedah ni fa duk kin sa min sha'awar zuwa garin nan naku. Sai dai babanmu ba zai yadda ba.
Sai Mufeedah ta ce kinga kuwa da zai yadda sai ki cigaba da karatunki a can birni tunda akwai makaranta a can kinga ni ma idan na gama wannan wata za'a sama min in cigaba da yi a can garinmu,
tun ranar da muka yi wannan hirar da Mufeeda na kuduri aniyar duk yadda za'a yi ni ma sai na cigaba da karatu.
Komai ya yi farko yana da karshe yau makarantarmu cike take makil, da mutane ana ta dibar dalibai domin rana ce da muka kammala jarabawar mu ta karshe cikin shesshekar kuka muka rabu da mafi yawa daga cikin kawaye na saboda shakuwa, musamman Mufeeda duk da ta bani kwatancen gidansu amma da kyar muka rabu cikin kuka.
Wata sabuwa wai in ji yan caca, bayan komawata gida sai wani dan kanen babata ya fito wai yana so na ya kuwa ci sa'a kowa a gidan yana sonsa, dan haka babana ya ce ya bashi ni, kawai sai a zo a yi biki, haba ni kuwa sai na yi tsalle na dire na ce bana son shi, wannan abin ba karamin mamaki ya ba mutanen gidanmu ba, domin basu taba tsammanin haka daga gareni ba.
Cikin tsanani yayyuna suka hayayyako min da zagi da masifa wai lalle sai na aure shi, ni kuwa na tubure ganin haka sai Mahaifina shi da Mahaifiyata suka kira ni, bayan na gama cin abinci sai na nufi turakarsa, na same su zaune suna Hira Mahaifina ya ce Hajara me yasa baki son auren dan'uwanki?
Kaina a kasa na ce, baba ba son sa ne bana yi ba, kawai ina so na cigaba da karatu ne, saboda so nake na zama likita.
Zancen banza zancen wofi! Mahaifiyata ta fada yanzu ke akan wannan banzan tunanin naki kike kin aure?
To wallahi tun wuri ki fita idona in rufe tun muna sheda juna, ku ji mu da yarinyar zamani, an gaya miki karatun likita sauki ne dashi a yadda kike din nan kafin ki kammala kin tsofe kuma ba me aurenki,
ke bari ta wannan ma a gidan ubanki za'a samo wannan kudin karatun da kike magana?
Duk wannan maganar da Mahafiyata take Mahaifine bai ce kanzil ba, sai bayan ta dan tsahirta sai ya dube ta, ya ce haba Hajjo! me yasa kike haka ne? Ki bita a sannu mana, kin san yarinya ce karama, ke Hajara tashi je ki, zan neme ki mahaifina ya bani umarni.
Ina jiyo lokacin da mahaifiya ta haushi da fada tana cewa daman ai kai kake goyon bayanta shi yasa take abinda ta ga dama a gidan nan.
Bayan kamar mako guda da faruwar wannan abin cikin ikon Allah sai jarabawarmu ta fito na kuwa yi sa'a ina ciki mutum uku da muka fi kowa cin jarabawar, dan haka gwamnati ta dauki nauyin karatunmu mu uku wadanda muka fi nuna kwazo a makaranta, ana dara ga dare ya yi, kowa a gidanmu sai da ya nuna baya son wannan karatun nawa, mahaifiyata ma cewa idan na tafi birni lalacewa zan yi.
Da kyar mahaifina ya shawo kanta ta hakura ta barni, ranar da zan bar gida Mahafina ya kusan kwashe awa biyu yana mini Nasiha game da kula da kaina da kuma yin karatu tukuru.
Hajara nasanki kina da kokari, to ki kara akan wanda na sanki dashi, sannan ki sani zaman birni daban yake dana kauye ki kula sosai da kanki kada ki zubar da mutuncinki, ki mai da hankali sosai akan karatunki, Allah ya taimaka Allah ya bada sa'a, idanuna na zubar da kwallah na ce amin, a haka muka rabu dashi.
BIRNIN MAMBIL JAMI'AR SANTABUL.
Kwanci tashi kwana nesa yau wata na biyu da sati daya a makaranta babu abinda ke damuna sai zulumi gaskiya zaman kauye ya fi na birni dadi, domin birni ta cika cunkoso sannan ga hayaniya kamar ana yaki, uwa uba kuma zaman kadaichi ya dameni duk da tare muke da Mufeedah amma ina jin kewar gida da yawa.
Duk karshen mako lokacin da ba karatu ran juma'a mukan ta fi gidansu Mufeeda mu kwana, sai litinin da sassafe mu dawo, gaskiya gidansu Mufeedah mutane ne domin sun rike ni tamkar yarsu, mun shaku da yan gidan sosai, dan haka duk lokacin dana aka mana hutu na koma gida nakan bawa Mahafina labarin gidansu Mufeedah da irin karamcin su gareni, shi kuma yakan ce dama haka rayuwa take, Allah ke hada jinin mutane ke dai ki dinga kula sosai musamman kan abinda kika je yi.
Lalle kwanaki suna gudu yau saura shekara biyu mu kammala karatunmu
A cikin wannna hali ne soyayya mai karfi ta kullu tsakanina da wani wan Mufeeda mai suna Yasir, duk da bana son yin soyayya a wannan hali amma ba zan iya juyar da soyayyar da yasir ya min ta yi ba, musamman idan aka yi la'akari da yadda gidansu suka nuna min kauna, a haka muka cigaba da gudanar da soyayyarmu da shi yawanci idan muna makaranta har can yake binmu ya shiga lacca in mun fito mu yi ta hira sai wajen yamma zai koma gida, washe gari kuma ya dawo.
Gaskiya Yasir ya iya soyayya domin duk ya sanya min son sa cikin jini na yanzu ta kai idan ban ganshi ba har wani dan zazzabi nake ji, ranar da bamu da karatu Yasir yakan dauke mu a mota mu shiga kasuwa ya yi mana siyayya.
Watarana mu biyu kawai mu ke fita kasuwa, wani sa'in Yasir yakan tafi dani wajen shakatawa mu yi kalle-kalle, sannan mu dawo gida na lura Mahaifiyarsa bata son haka dan haka na ce masa Yasir yakamata fa mu dena fita mu biyun nan na lura mama bata son haka?
Daga wannan rana Yasir ya dena daukata mu fita idan ina gidansu sai in ina makaranta, ita ma Mufeeda na lura bata son fitar da muke kawai shiru ta yi.
Tashin Hankali ba'a sa masa rana a cikin wannan fita da muke da Yasir ne ya yi amfani da son da nake masa yace na raka shi gidan wani abokinsa da ya yi aure za mu gaisa da matarsa, ashe gidan ba kowa dakin wani abokinsa ne, da daddare ya keta mutuncina ranar na ci kuka kamar raina zai fita, amma da yake Yasir mai wayo ne sai ya shawo kaina, tun daga wannan rana muka shiga yin abinda mu kaga dama dashi sai da ta kai Yasir ya mai da ni tamkar matarsa.
Bana taba mantawa da wata ranar laraba da rana mun tashi daga lacca, sai na ji yanayin garin ya canja mini a hankali kuma sai jiri ya soma dibita cikin yan dakiku kadan sai idanuna suka rufe, ban tashi bude ido ba sai ganina na yi a asibiti, da yake asibitin a shashen da muke karatu yake kowa ya san ni kuma malamanmu ne likitocin, yanayin kallon da naga malamin yana min shi ya tsorata ni, bayan kamar minti uku haka da bude ido na, sai ya ce dani Hajara kina da aure ne?
Ras! gabana ya fadi bakina na karkarwa na bashi amsa a'a.
To ina kika samu ciki?
Cikin fargici na mike tare da dafe kirji na shiga uku! malam ciki fa ka ce?
Eh ciki ne dake kin kuma san dokar wannan makaranta ba'a yarda mace ta yi ciki ba dan haka hukumar makaranta ta kore ki, yana gama fadin haka sai ya miko min takarda ya fita abinsa.
Tabbas ciki ne dani abinda sakamako ya nuna kenan, wayyo! Allah na, yau ina zansa kaina? cikin karaji na fashe da kuka duk wannan abin da ake Mufeedah na gefe ta zuba uban tagumi, sai da taga kukan nawa yaki karewa sannan ta taso ta matso inda nake ki yi hakuri Hajara ki dauki kaddara, sai hakuri daga nan ita ma ta fashe da kuka.
A ranar na hada kayana bamu zame ko ina ba sai gidansu su Mufeeda Muka kwashe labari tsaf muka gayawa mahaifiyarta, mahaifiyar su Mufeedah ta nuna tausayi sosai a fuskarta ta ce daman sai da zuciyata ta bani wani abu game da fitar da kuke, bari Ya zo ya sameni ki yi hakuri kin ji Hajara zan san yadda zan bullowa al'amarin, zuwa can dare sai ga Yasir ya shigo ina ji Mahaifiyarsa ta kira shi suka shiga daki, zuwan can sai gata ta fito, ta zo inda muke zaune ta tsaya, a yanayin dana ganta sai da gabana ya fadi, ke Hajara yanzu da abinda zaki saka mana kenan?
Ki rasa wa zaki yi wa sharri sai dan cikina yanzu duk irin gatan da muka nuna miki da wannan zaki mana sakayya? lalle kin cika yarinyar kauye, to tun muna shaida juna ki kwashe komatsanki ki bar gidan nan.
Babu irin lallashin da Mufeeda bata yi wa Mahaifiyarsu ba akan ta fahimtar da ita gaskiyar al'amari amma sam, ta rufe ta kore ni.
Ko sallama bata bari mun yi da Mufeeda ba, ta turo ni ni da kaya na waje, wayyo Allah Duniya yanzu ina zansa kaina? Yanzu wace duniya zan nufa?
A cikin wannan hali ne na dawo kauyenmu, tunda na bayyana musu abinda ya faru kowa a gidanmu ya tsanane ni ba mai shiga harkata, mahafiyata ta dena yi min magana gaba daya, tunda nake da mahaifina ban taba ganin fushinsa ba, kamar na wannan rana ba.
Cikin zafin rai yake magana yana cewa:
"Hajara me ya dawo dake gida? Yanzu abinda zaki saka mini dashi kenan, Hajara me na yi miki a rayuwa dana cancanci wannan tukwicin daga gareki?
Yanzu ina kike so in sa kaina da wannan abin kunya da kika debo kika kawo mana gida... Kuka ne, ya kwace masa, tuni zuciyata ta gama karyewa.
Hakuri na dinga bashi, tsakanin Mahaifi da sai Allah bayan dogon lallashin dana yi ta masa sai samu ya sauko, duk gidan ba wanda yake shiga harkata sai kusan kullum ina dakinsa.
Kwanci tashi kwana nesa ranar wata juma'a da safe da safe na tashi da nakuda ban dau wani dogon lokaci ba na haihu, na haifi santalelen yaron sai dai wani ikon Allah yaron ba rai ya zo, amma duk da haka mutanen gidanmu basu hakura ba, har yau ba wanda yake shiga harkata.
ganin abin yana neman ya wuce makadi da rawa sai mahafina ya tara duk yan gidanmu ya yi musu nasiha akan yadda suka kyamace ni, bai da ce ba Allah yana iya jarabtar kowa a cikinsu, dan haka daga ranar kada ya kara ganin wani ya min kallon banza.
Daga wannan rana rayuwata ta dawo sabuwa a cikin gidanmu, bayan kamar wata bakwai da faruwar wannan al'amari sai ga yan gidan su Mufeeda sun zo gidanmu sun bada hakuri tare da neman aure na gashi Yasir din, mahaifina bai yi musu ba ya ba su aure na cikin sati biyu aka yi biki.
Yaushe shakararmu goma kenan da aure yaranmu uku kuma muna zaune lafiya da miji na.
Babu abinda ke damuna sai tunanin Mahaifina da ya rasu a yan kwanakin nan.
KARSHE.

TSAKA MAI WUYA




Daga
Rabiu Muhammad Abu Hidaya
 

Auren soyayya mu ka yi da mai gidana.
Yana sona nima ina son sa muna zaman soyayya bama bukatar duk wani abu da zai bata mana rai, yawanci nasan abinda yake so da abinda baya so kuma na kiyaye su sosai dan haka yau shekarunmu uku dashi amma bamu taba samun wani sabani ba na azo a gani, tsawon wannan lokaci ban taba ko batan wata ba.

Kwatsam watarana ina zaune a gida sai naga ya dawo gida yana ta fara'a na tambaye shi me ya faru naga ya shigo yana ta fara'a haka?

Sai yace taransafa ya samu zuwa gida (garinmu na asali) kin ga yanzu sai mu dinga zumunci sosai tunda dama Hajiya(Mahaifiyarsa) tana korafin bama zuwa ganin gida sosai.
Duk wannan maganar da yake ni gaba daya jikina ya yi sanyi domin nasan yanzu duk inda farin cikina yake yana dab da samun matsala.
Ya naga kamar bakya murna da wannan abin farin cikin daya same mu?
Maganar sa ce ta dawo da ni hayyacina.
Hmm! Ina murna mana me ka gani kace haka?
Gani na yi kamar kin shiga tunani.
Eh ina tunanin yadda zan bar kawaye na nan garin ne.
Mata kenan yanzu dan dan wannan abin shine kike damuwa kamar kin rabu dasu gaba daya? Ai zamu dinga zuwa ganinsu.
Bayan kamar sati biyu da wannan taransafa sai muka shiga shirye-shiryen dawowa gida, cikin makon muka dawo garinmu da aiki.
Da yake gidansu babban gidane Nan cikin gidansu ya samu daki muka zauna.
Tunda muka dawo garin nan kusan kullum sai kannensa sun gaya min magana wai yayansu ya auro juyo kuma ta mallakeshi.
Ni ba abinda kannensa ke gaya min bane yake bata min rai ba illa irin yadda mahafiyarsa ta dena cin ko abincina wai na mallake mata Da. kai yanzu dai ta kai ko gaisheta na yi sama-sama take amsawa.

Tun ina kokarin boye halin da nake ciki har takai rama ta fara bayyana a jikina gashi kuma mijina bashi da halin da zai iya cewa zai fita daga gidan kasancewar mahaifiyarsa ta fi son zamansa a kusa da ita.

Kullum cikin bani hakuri yake yana fadin ki yi hakuri komai mai wucewa ne.

Ni kam nakan yi kokari in nuna masa rashin damuwata a fili. Duk da cewa ina ina jin jiki a gidan.

Muna cikin wannan hali sai kawai mahafiyarsa rana tsaka ta fito tace dole sai ya sake ni saboda bata ga dalilin zama dani ba duk na bi na mallaki shi na hana shi ganin ya'yansa a duniya.

Duk irin hanyoyin da yakamata ya bi don ganin ya shawo kanta sam taki ya nemi ta bari zai kara aure in yaso ya zauna da mata biyu amma sam ta ki yarda tace ya yi karami ya rike mata biyu,

dan haka tilas ya hakura ya ba ni takardar saki daya tare da kudi naira dubu dari biyu.

Ranar nasha kuka kamar raina zai fita.

Yanzu haka tasa ya kara aure kuma har yau basu haihu da matar ba.

Lokaci-lokaci yakan bullo mu dade muna hira ganin haka sai iyaye na suka takura min akan na sake aure amma na kasa saboda gani nake kamar ba zan samu soyayya irin ta mijina ba.
Zuciya bata da kashi a hankali sai shedan ya shiga tsakanina dashi muka shiga aikata barna.
Kai in takaice muku batu yanzu haka ciki ya bulla gareni kuma tunda na fada masa ya dena zuwa inda nake idan na kira wayarsa baya dauka na shiga tsaka mai wuya dan Allah ku bani shawara ya zan yi?

Photo Album



IN BISHIYA TA GIGA.....


Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya

Kyakkyawace ajin farko,kallo daya zaka mata ka gane cewa bata son raini, tafiyarta kawai abin kallo ce domin tamkar dawisu haka take tafiya.
Amina kenan budurwar da kowa ke shakkar kulawa. Bayan Amina da ake kiranta tana da sunaye kala-kala da ake kiranta da dasu tsabar jin kan da take dashi.
Wasu na kiranta Shu'uma, wasu ko Hatsabibiya, kai wasu ma Miskila ke kiranta tsabar nuna isarta.
Cikin nutsuwa ta kwankwasa kofar ofishin mutumin da ta zo nema tana tsaye tana cin cingam a bakinta ji kake kas-kas! karar sautin cin cingam din yana fitowa daga bakinta, kamar dakika biyu da buga kofar sai aka bude wani dan kakkauran mutumne baki ya bude kofar yana ganinta sai kawai ya wangame bakinsa yana fadin ashe yau muna da manyan baki a ofis  din namu? Bismillah shigo ciki mana, guri ta samu ta zauna, shi kuwa Mutumin ya rasa inda ma zai zauna tsabar zumudi, me za'a kawo miki ruwa ko lemu? Wani irin murmushi Amina ta sakar masa gami da lumshe idanu tace nafi son ruwan, cikin hanzari ya bude firji ya dauko mata ruwan roba ya aje a gabanta.
Bayan Amina ta gama shan ruwan sai ta juyo da kallonta gareshi Alhaji Mati kenan kuna sha'aninku tana magana tana cizon lebe da alamu akwai abinda Amina ta kullo a ranta.
Wata mika Alhaji Mati ya yi yana wangale baki kamar mai yin ihu ga duk alamu nufinsa dariya yake, duniya kenan Amina wai ina kika shige shekaru da yawa haka?
Kisan yau rabona da inganki wajen shekaru biyu kenan?
Amma ko a ina kike lalle kina jin dadi kinga yadda fatar nan taki take ta sheki kamar wata sabuwar Amarya?
Hala ta samu ne dan nasan ke ungulu ce bakya jewar banza.
Wani irin kallo Amina take yi wa Alhaji Mati a lokacin da yake maganarsa.
Hmm! Alh.Mati kenan kai dai baka rabo da tsokana, ba wata samuwa kawai na zo mu gaisa ne ganin mun dade bamu hadu ba.
Kin kuwa kyauta Yan mata, kinga kuwa yanzu zan tashi daga ofis a wani otal kika sauka ne?
Amina tace Banma kama otal ba saukata kenan.
Ok to bari yanzu sai muje awarwasa otal sai in kama miki daki, Kinga sai mu yi hirar yaushe gamo ko?
Murmushi Amina ta yi sannan tace kai dai baka da dama to godiya nake.
Sannu a hankali motar kirar Honda Sienna ta samu guri a harabar otal din wurin da aka tanada dan ajiye motoci ta yi fakin. Amina da Alh. Mati suka fito daga mator suna tafe suna dariya da alamu sun tuna da tsohuwar soyayyarsu ne .
Bayan karbar tikitin dakin da zasu zauna kai tsaye dakin suka nufa.
A ranar kusan kwana suka yi suna aikata barna dama kuma al'adarsu ce haka duk lokacin da suka hadu kamar tumaki haka suke kasancewa tsabar saukin juna.
Hasken rana ya keto ta tagar dakin da Alhaji Mati ke kwance wanda yake nuna alamun gari ya waye, cikin mikar gajiya ya mika hannu dan kamo Amina Ga mamakinsa sai ya ji wayam! ya kama iska, cikin hanzari ya karasa bude idanunsa domin ganin ko ta sauya bigiren kwanciya babu ita babu alamunta sai wata doguwar takarda a wurin da take kwance...