0
Siffofi 20 Na Mace Tagari Siffofi 20 Na Mace Tagari

Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali, shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wacce t...

Siffofi 20 Na Mace Tagari


Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali, shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wacce take tattare da siffofi abin koyi da za su taimaka mata wajen tafiyar da gidan yadda ya kamata. Siffofin sun hada da:

1. Ta kasance mai riko da addini, ba mai saka ci da shi ba.
2. Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a kodayaushe.
3. Ta sanya Allah a ranta a duk al'amuranta na yau da
kullum
4. Ta zama mai shigar mutunci, misali sanya hijabin da zai
rufe mata jikinta yayin da ta fita zuwa unguwa.
5. Ta kasance mai kamanta iyaye da 'yan uwa da abokan
mijinta.
6. Ta kasance mai yawan kwalliya da ado ga mijinta
7. Ta kasance kwararriya wajen iya girki.
8. Ta kasance mai godiya ga abin da mijinta zai kawo mata,
kada ta rika rena abin da mijinta zai kawo mata .
9. Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da maigida ya
kira ta zuwa shimfidarsa.
10. Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu
kayayyaki da yake amfani da su.
11. Ta kasance mai rufa wa mijinta asiri, ba mai watsa
sirrinsa ba.
12. Ta kasance mai ba shi hakuri cikin lalama yayin da ta yi
masa laifi.
13. Ta kasance mai nuna farin ciki idan abin farin ciki ya
same shi, da nuna bakin ciki idan abin bakin ciki ya same
shi.
14. Kada ta yabi mijin wata alhali tana tare da mijinta.
15. Ta kasance mai kwantarwa mijinta hankali yayin da
yake cikin damuwa.
16. Kada ta ba wata ko wani dama ya ji sirrinsu (ita da
mijinta).
17. Ta kasance mai kokarin neman ilimi da aiki da shi.
18. Ta kasance mai nisantar abin da ba ya so, ta kuma rika
kusantar abin da yake so.
19. Ta kasance mai bin umarnin yi ko bari wajen nuna masa
so da kauna a fili, ba a boye ba.
20. Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa bukatun da ba zai iya biya mata ba.

Babu shakka da bincike na tsanaki ne ake samun mace mai siffofi nagari abin koyi, gaggawa da kwadayi kuwa a harkar neman aure, babu abin da suke jawowa face da na sani, ita
kuwa da na sani aka ce keya ce. Allah Ya agaza mana.

Ibrahim Hamisu ya rubuto daga Kano.

Za a iya samun sa a adireshin Imel: ibnkhamis2@mail.com
ko ta lambar waya: 08060651676