0
TASIRI DA GUDUMMUWAR SARAKUNAN KASAR NIJAR WAJEN BUNKASAR AL'ADU DA ZAMAN LAFIYA A KASAR NIJAR TASIRI DA GUDUMMUWAR SARAKUNAN KASAR NIJAR WAJEN BUNKASAR AL'ADU DA ZAMAN LAFIYA A KASAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) Wannan rubutu ya samo asali ne daga wani kira da wani dan dan'uwa marubuci Usman Mani Kusumawa Karg...

0
AN GUDANAR DA TARON NUNA AL'ADUN HAUSAWA A KASAR BURKINA FASO AN GUDANAR DA TARON NUNA AL'ADUN HAUSAWA A KASAR BURKINA FASO

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya) Gmail:abuhidya3@gmail.com +2348065025820 A ranar Juma'a 14 ga watan Afrilu 2017 hukumar a...

TASIRI DA GUDUMMUWAR SARAKUNAN KASAR NIJAR WAJEN BUNKASAR AL'ADU DA ZAMAN LAFIYA A KASAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya)

Wannan rubutu ya samo asali ne daga wani kira da wani dan dan'uwa
marubuci Usman Mani Kusumawa Kargeri, yayi min game da cewa yakamata
na yi dan rubutu game da sarakunan kasarsu ta Nijar game da hibbarsu
da kuma adalcinsu ga duk wanda ya kusance su, sakamakon yadda wasu
mutane suke ganin cewa Masarautar Agadez ba ta kyauta ba don ta hana
'yan fim din Hausa(Kannywood) zuwa kasarta da sunan shirin fim, saboda
wani Fim da kamfanin 2Effect Empire suka shirya mai suna DAN SARKIN
AGADEZ fim din da ya gaza cimma manufar sakon da ake son nunawa
jama'a, hasalima fim din tozarci ne ga masarautar da al'adunta.

Babu Shakka masarautun kasar Nijar kaffatanninsu masarautu ne masu
cike da haiba da kuma dimbin tarihi kuma masu adalci ga al'ummar da
suke shugabanta.
Duk mutumin da ya kasance mai bibiyar tarihi zai yarda kuma har ma ya
aminta cewa sarakunan kasar Nijar ba su da kyashi ko baiken jin cewa
sun taimake ka wajen samar da tarihi da kuma labarin da abin da ya
shafe su, kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba kamar yadda hausawa ke
azancin magana da cewa wai "Gani Ya Kori Ji".
Bari na fara da Masarautar Sultan ta Damagaran a shekarar 2014 na
ziyarci fadarsa a wani rangadin bincike da nake yi wanda zai kai ni
har gaba da Agadez, Sultan Abubakar Sanda wanda yake mulkin kasar
Zinder yayi matukar farin ciki da zuwa na ya kuma bani masauki tare da
bani cikakken lokacin da muka zanta da shi na wani dogon lokaci, har
ya gayyace ni zuwa tarbar Ministan cikin gidan kasar wanda zai kawo
ziyarar aiki a jihar, amma rashin lokacin da ba ni da shi ban samu
damar amsa gayyatar ba, don a daidai lokacin yakamata a ce na isa
Agadez akan lokaci, bai damu ba ya yi min wannan uzuri sannan ya bani
sakon gaisuwa zuwa ga takwaransa na Agadez wato Sultan Ouamar Ibrahim
Oumar na Agadez mun yi bankwana da fatan idan na dawo na sake biyawa
fada na sanar da shi, hakan kuwa aka yi bayan na dawo na biya masa
abin mamaki sha tara arziki aka min a wannan fada cikin barkwanci da
raha sosai mu ka yi bankwana da shi da duk mutanen fadar.
Har ila yau daga cikin karamcin wannan sarki shi ne ya dauki nauyi
taron kaddamar da kungiyar hadaka ta kasashen Afrika mai suna
GIDAUNIYAR ZUMUNCI tare da bikin al'adun hausawa na duniya a jihar
Zinder a wannan shekara ta 2018.

Haka ma jihar Agadez bayan na isa masarautar na sanar da sultan zuwana
sai na wuce zuwa masaukina don hutawa saboda gajiyar hanya, bayan
kwana daya da zuwana,ina bacci da rana sultan ya aiko yana son za mu
gana ta hanyar Yariman Agadez Malam Ousseini dan Abbo, Sultan na
Agadez mutum ne mai cike da kwarjini da haiba ga izza wadda za ta nuna
maka shi cikakken sarki ne mai daraja ta farko, duk da cewa mu hudu ne
a fadar ta shi amma baya magana da ni kai tsaye hasalima bana jin abin
da yake fada sai idan ya yi magana a gaya min abin da ya ce, a haka
muka tattauna muhimman batutuwa, wani abin burgewa da wannan sarki shi
ne son jama'ar kasarsa da kyautata musu, mun yi tafiya da shi zuwa
dazuka (idan aka je daji a kasar Nijar ana nufin wasu garuruwa da suke
cikin duwatsu da sahara) don halartar taron addu'a na karshen shekara
da ake a kasar don neman zaman lafiya da wanzuwar arziki a kasar,
motarmu tana gaba ta sultan tana bayanmu sai muka wuce wasu mata da
kananan yara a hanya ga dukkan alamu wani garin da ke gaba da su za su
je, a cikin motarmu sai sakataren Malaman Jihar Agadez Malam Namadina
Alhaji Ousseini ya ce "Zai wahala Sultan bai tsaya yasa a dauko
mutanen nan ba", haka kuwa aka yi ba mu yi nisa ba sai muka ga ana
alamta mana cewa mu dakata, bayan mun tsaya muka dawo baya sai muka ga
Sultan ya sauko da kansa ya sanya an ba wadannan mutane mota guda
wadda ta dauke su tare da kayansu ta kai su garin da za su je.
Wannan abin ya matukar burgeni na kuma ji na kara kaunar wannan sarki.
A tsawon kwana uku da muka yi a dajin nan wallahi kusan ko yaushe duk
abin da aka kaiwa Sultan sai ya sanya an kawo mana da yake masaukanmu
suna dab da juna. Bayan an kammala wadannan addu'o'i ba fadarsa ya
dawo ba sai da ya wuce zuwa wasu garuruwa don ya gansu ya kuma
tattauna da su, bincikena ya gano cewa wannan sarki kusan koyaushe
yana cikin wadannan ayyuka na ziyarar mutanensa da kuma gabatar da
ayyukan da suka shafi ci gaban kasarsa duk da cewa akwai sarkin da aka
sanya don lura da wadannan garuruwa da ake kira A'ir mai suna Muhammad
Suleyman Anastafident, bayan mun dawo sarkin ya sake tambayata akwai
wani abu da nake bukata wanda ban samu ba? Na amsa da babu duk wani
aiki da ya kai ni na kammala shi har da ma ribar kafa.
A bangaren mutanen Agadez da Nijar kuwa babu wani abu da zan bayyana
su da shi sai dai na ce su mutane ne masu son jama'a da kuma girmama
baki da kaunar junansa, wani abu da ya sa nake kara yaba musu shi ne
yadda suka rike al'adunsu da kuma girmama tarihinsu.

A shekarar 2016 ma na ziyarci fadar sarkin Maradi tare da wani babban
dan kasuwa da ke Nijeriya don bude reshen harkar kasuwancinsa garin
Maradin babban abin da ya burge ni shi ne yadda mutanen fadar suka
karbe mu da karamci tare nuna jin dadinsu game da wannan abin alheri
da zai zo kasarsu, haka ma mahukunta jihar su ma sun nuna jin dadinsu
don har wakilin gunduma ya ba mu gayyata ta musamman zuwa gidansa amma
da yake muna sauri za mu wuce zuwa Niamey ne, ba mu samu zuwa ba, a
wannan bangare ma na yaba musu kwarai.

A saboda a haka a matsayina na Marubuci kuma Dan Jarida nake rokon duk
wani marubuci ko dan Jarida kai har ma da masu shirya fim su kasance
masu bibiyar tarihi da bincike tare da bibiyar masana kafin yin duk
wani aiki wanda zai shiga hannun jama'a saboda gudun irin abin da ya
faru a baya game da Fim din Dan Sarkin Agadez, da ma wasu daga cikin
rubuce-rubucenmu, Allah Ya jikan marigayi Gambu mijin Kulum mai wakar
barayi mun taba hadu da shi a jami'ar jihar Kaduna muna zantawa yake
nuna min rashin jin dadinsa da abin da wani marubuci yayi masa na
rashin adalci, ya ce marubucin ya rubuta karya game da shi da sunan
tarihinsa ba tare da kyakkyawan bincike ba.
Bana mantawa lokacin dana ziyarci wata fada a kasar Nijar din dai ta
sarki Ahmad Aghali Ibbah sarkin Tanhiya sun sanar da ni tarihinsu
tare da cewa duk abin da suka gaya min haka zan rubuta kar na rage kar
na kara, kun ga wannan ai shi ne adalci, wani abu da ya sake burgeni
da mutanen kasar shi ne lokacin da na je shan ruwa wajensu an samu
matsala, amma da na bayyana musu cewa ni bakon sarki ne sai suka kyale
ni na tafi abina.(Cikakken rahoton yana cikin labarin ziyararmu birnin
Tanhiya) A nan ma ya nuna cewa wannan sarki zaune yake da al'ummarsa
lafiya suna kaunarsa yana kaunarsu.
Da fatan wannan tsokaci zai sanya mu amfana wajen yin abin da zai zama
karbabbe a kan komai da za mu yi.

AN GUDANAR DA TARON NUNA AL'ADUN HAUSAWA A KASAR BURKINA FASO

Daga

Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)
Gmail:abuhidya3@gmail.com
+2348065025820

A ranar Juma'a 14 ga watan Afrilu 2017 hukumar adana kayan tarihi da
al'adu tare da hadin gwiwar kungiyar Makarantar Hausa ta kasar Burkina
Faso suka gudanar da taron ranar bajakolin al'adun Hausawa na duniya
tare da gabatar
da taron karawa juna sani a babban birnin kasar Wagadugu(Ouagadougou),
taron dai wanda ya samu halartar kasashe da dama kamar:
Nijeriya (Nigeria)
Nijer (Niger)
Togo (Togo)
Sanigal (Senegal)
Kodebuwa (Ivory'Cost)
Chadi (Chad)
Mali da sauransu. An fara gabatar da shi da misalin karfe goma na
safiyar ranar juma'a, an soma da gabatar da takardu cikin harshen
Turanci da Faranci karkashin
jagorancin uban kungiyar makarantar Hausa, Alhaji Sani Dan
Tule. wadanda suka gabatar da
takarda a ranar akwai:
Sarkin Askar Yariman Safana
Dakta Bashir Aliyu Sallau da kuma Yusif Nuhu Inuwa.
Bayan sun kammala sai aka yi musu tambayoyi suka bayar da
amsoshidaga nan aka tafi
masallacin juma'a.
Da misalin karfe hudu na yammacin ranar dai aka ci
gaba da gabatar da taron,
ministan al'adun kasar ne ya bude taron a madadin shugaban kasar
Burkina Faso Roch Mark Cristian Kabore ya yi jawabi a
matsayinsa na babban bako inda
ya nuna cewa Hausa tana da girman da yanzu ba iya Afrika kawai take
ba, za a kira ta ne da harshen duniya ya kuma jinjinawa
wadanda suka shirya taron
musamman shugaban kungiyar
makarantar Hausa ta Farko a kasar malam
Abdoul Rasmane Nagarba, bayan
ragowar manyan baki sun yi na su jawabin sai ministan ya jagoranci
manyan baki da mahalarta taro zuwa bude dakin da aka
ajiye kayan tarihi da al'adun
Hausa na da da na yanzu daga nan kuma sai aka bude wasan kokowa don
nishadantarwa ga baki.
Washe gari ranar Asabar aka ci gaba da gabatar da takardun karawa juna sani
karkashin jagoranci Dakta Bukar Usman OON,tsohon sakatare a fadar
shugaban kasar Nijeriya, a
wannan rana wadanda suka samu
damar gabatar da takarda akwai:

Ado Ahmad Gidan Dabino MON
shugaban kamfanin Gidan Dabino International da ke Kano-Nijeriya.

Dr. Nasiru Aminu Kalgo
Jami'ar Usman Dan Fodiyo Sokoto.

Mai girma Ibrahim Muhammad Dan Madami
Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Zamfara a Nijeriya.

Malam Nasir AUK
Jami'ar Musulunci ta Alkalam da ke Katsina
su makamar ranar farko bayan kammala takardunsu an yi masu tambayoyi
sun kuma bayar da
amsa daga nan sai aka tafi duba
kayan gargajiya na mata da maza da nau'ikan abincin gargajiya wanda
ake bajakolinsu a harabar gidan Adana kayan tarihin kasar.

An dawo filin wasa da karfe bakwai na yamma nan kuma mawakan kasar ne
suka baje kolin fasaharsu don nishadantar da mahalarta taro wadanda
suka kasance yan cikin gida da baki yan kasashen waje.

Ranar Lahadi ita ce rana ta karshe daga ranakun taron kuma wannan rana
an gabatar da abubuwa
kamar haka:
taron karawa juna sani karkashin jagorancin Dakta
Bukar Usman OON. Wadanda suka gabatar da takarda a ranar sun
hada da
Abubakar Muhammad
Mukhtar AUK
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
Shugaban Tsangayar Adabin Hausa kuma Daraktan Makarantar Al-Huda Women
Educational Centre da ke Kano.
Bayan kammala tambayoyi sai aka tafi ziyarar wuraren tarihi na kasar
cikin wurin da aka ziyarta akwai gidan sarkin Musawa Mogho Naba wadda
aka fi sani da kabilar Mossi sarkin wanda ya kasance shi ne
babban basaraken kasar, an samu izza sosai kafin daga bisani a samu
ganawa da shi, bayan fitowar an gindayawa masu ziyarar sharadin kada
su dauki hoto a masarautar, sarkin ya yi maraba da bakin da suka
ziyarci fadarsa musamman 'yan kasashen waje, bayan kammala tattaunawa
da sarki sai aka wuce gidan sarkin Hausawan zango na birnin Wagadugu
mai suna sarki Dankambari Jibril da kuma ziyarar muhimman wurare daga
nan sai kowa ya koma masaukinsa, hutu da zimmar zuwa dare a ci gaba
da taro.
Karfe takwas daidai aka ci gaba da taro, bayan jawabin maraba da kuma
gabatar da manyan baki daga mai gabatarwa Rabiu Muhammad Abu Hidaya,
wanda ya yi da harshen Hausa sai kuma Asma'u Makeri da yi da harshen
Faranci bayan gabatar da manyan bakin da suka halarci taron, abu na
gaba shi ne rabawa dalibai mata na makarantar Hausa ta
Burkina Faso takardar shedar
kammala karatunsu na matakin farko a ilimin Hausa wanda
makarantar AL-HUDA WOMEN EDUCATIONAL CENTRE da ke Kano Nijeriya ta ba
su, tsohon gwamnan Kano kuma sanatan kano ta tsakiya Injiniya Dakta
Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne ya jagoranci ba su takardar shedar, daga
nan kuma
sai hukumar Adana kayan
tarihi da al'adun kasar Burkina Faso tare da hadin gwiwar Kungiyar
Makarantar Hausa ta Burkina suka karramawa wasu muhimman mutane da
suke bawa Hausa gudummuwa a duniya da kambun
karramawa, cikin wadanda aka
karrama a ranar akwai:
Dakta Bukar Usman OON
an karrama shi da kambu mai taken (Jakadan Adabin Hausa)

Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso
An ba shi kambun karramawa mai taken (Gwarzon Shekara2017 )

Farfesa Abdulkadir Dangambo
Ya samu karramawa mai taken (Garkuwan Adabin Hausa)

Farfesa Abdalla Uba Adamu(Gwarzon Shekara 2017 ) Da sauransu.
Gidauniyar Bukar Usman da Dakta
Bashir Aliyu Sallau babban
Darakta a hukumar tarihi da al'adu ta jihar Katsina sun bayar da
kyaututtukan littattafai ga
kungiyar makarantar Hausa don ci
gaba da gabatar da karatu.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata a halin yanzu Dakta
Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayar gudummuwar kudi ga kungiyar makarantar
Hausa kimanin dala dubu biyu, har ila yau tsohon
gwamnan kanon da yake jawabi
a madadin wadanda aka karrama ya ce "Sun ji dadi kwarai da wannan
karramawa da aka yi musu kuma za su ci gaba da bayar da hadin kai
wajen ci gaba da assasa irin wannan taro a ko'ina cikin duniya a
karshe ya yi kira ga
al'ummar Hausa a duk inda suke cewa su zama masu hadin kai da kaunar
juna kada su bari kawunansu su rarraba".
Shi ma Dakta Bukar Usman OON tsohon magatakarda a fadar shugaban kasar
Nijeriya ya matukar nuna jin dadinsa da wannan karramawa da hukumar
adana kayan tarihi da al'adun kasar Burkina faso suka yi
masa " Ya ce duk da cewa a rayuwarsa
ya samu kambun karramawa da yawa amma zai ci gaba da alfahari da
wannan karramawa kuma tamkar kara masa kwarin gwiwa
aka yi game da ayyukansa na
rubutu". Da yake fadar burinsa a yanzu ya ce "Bai
wuce ya hidimtawa harsunan
da suke bukatar taimako ba". A dai wannan rana aka yi wasan karshe na
kokowa inda aka fitar da zakaran gasar.

Manufar wannan taro dai ita ce fito da al'adun
kabilun kasar na Burkina Faso
wanda ake yi duk shekar karkashin jagorancin hukumar adana kayan
tarihi da al'adun kasar wadanda suke da kabila sitti da uku(63), kuma
kamar yadda bincike ya nuna tunda ake gabatar da wannan taro ba a taba
yin wanda ya hada kasashe da dama ba kamar
wannan na kabilar Hausa.
Ana sa ran shekara mai zuwa za a sake maimaita
irin wannan taro a kasar ta
Burkina Faso.

Duk da cewa wasu suna ganin Burkina Faso ba kasar Hausawa ba ce amma
dai a ganin sun jima a kasar wadda har ta kai yanzu suna rike da
mukaman gwamnati kuma kasar ta sanya su cikin harsunan kasar da
cikkakun yan kasa.
Manyan bakin da suka samu halartar taron daga
kasashe akwai:
Kasar TOGO

Alhaji Ousman Mahmoud Salifou Baba Keke || Sarkin Zangon Lome

Alhaji Issifou Garba Kalambe Sarkin Zango Aneho

Alhaji Aoudou Shikuru Ibrahim Sarkin Zango Kpogam

Alhaji Ali Ousman Sarkin Zangon Garin Kuka.

Malam Mamman Moutala

NIJERIYA (NIGERIA)
Dakta Bukar Usman OON
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso Dakta Nasir Aminu Kalgo
Dakta Bashir Aliyu Sallau(Sarkin Askar Yariman Safana)
Maigirma Ibrahim Muhammad (Dan madamin birnin Magaji).
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON

NIJAR (NIGER)

Alhaji Garba Sani
Madam Nana Hadiza Louali
Madam Malika Koda killy
Madam Binta Alterna
Abdul Nasir

SANIGAL (SENEGAL)
Malam Hassan Musa katsina, sauran kasashen sun hada da Kwadebuwa da kamaru.
An kammala taron lafiya.