0
TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) +2348065025820 gmail:abuhidya@gmail.com A bisa al'ada duk shekara mutanen garin Agadez da ke Jamh...

0
AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya) Bikin kaddamar da littafin Alhaji Alhassan Dantata ya samu tagomashin halartar manyan mutane d...

0
JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) Director Al-Huda Women Literacy Center Kano-Nigeria Abu ne sananne cewa kasar Hausa tana girma haka ma ha...

0
AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017) AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017)

Daga Rabiu Muhammad(Abu Hidaya) Babban birnin kasar Kamaru wato Yawunde ya yi cikar dango da dukkan hausawan kasar Kamaru da wasu hausaw...

0
TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya) Hajiya Hafsat M.A Abdulwahid fitaccen marubuciya ce wadda sunanta ya shahara a duniyar rubutu mus...

TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya)
+2348065025820
gmail:abuhidya@gmail.com

A bisa al'ada duk shekara mutanen garin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar
kan yi wani biki da ake kira bikin Bianou kuma su kan gayyaci mutane
daga sassa daban-daban
na duniya ciki kuwa har da 'yan
jaridun duniya tare da kungiyoyi gami da hukumomin da suke na al'adu.

MENE NE BIANOU?
Bianou salla ce ta abzinawa mutanen Agadez, suna
fara yin wannan bikin tsawon wasu kwanaki amma manyan ranakun bikin su
ne ranakun tasu'a
da ashura don ana fara bikin tun ranar 17 ga watan Zhul-hijja, an ce
bikin ya samo asali tun iyaye da kakanni.

MENE NE TARIHIN BIANOU?
A hakikanin zance babu wanda zai ce ga shekarar da aka soma bikin
Bianou a garin Agadez amma dai an
tabbatar da cewa tarihin bikin Bianou ya samo asali tun shekaru
masu yawa, kuma ana yin wannan biki ne saboda kwaikwaiyon
Ma'aiki(SAW)a lokacin da ya yi hijira daga
Makka zuwa Madina inda mutanen Madina suka fito
suka tare shi da murna, wasu kuma suka ce Bianou biki ne kawai na
al'ada da ake yi don samun nishadi kuma raya al'adar kasar don
bayyanawa duniya karfin da matasa suke da shi a garin Agadez, da wani
yake karin bayani game da wannan magana ya ce "ma'anar Bianou shi ne a
yi ta rawa sai gari ya waye".Wannan shi ne tarihin
Bianou a takaice.

MARAICEN ADO.
Ita wannan rana mai suna
maraicen ado mata ne ke yin kwalliya da yamma su fito gari, amma kafin
yammacin wannan rana ko wani gida ana yin abinci nau'ika kala-kala
amma da alkama kuma akwai wadanda suke ajiyar naman kai da kuma kashin
bayan ragon layyarsu a wannan rana suke
fitowa da shi su gyara a ci, zuwa yammacin sai kuma samari da
Tambari(Tambari shi ne shugaban da yake jagorantar masu yin bikin)
suma su fito a shiga kada tambura(Manyan ganguna) a yi ta rawa har
zuwa wani tudu da ake kira tudun Bianou wannan rana ita ce kamar ranar
bude Bianou ko kuma
jajiberin sallar Bianou kuma a
wannan yammaci maza ke tafiya kwanan daji.

KWANAN DAJI
kamar yadda na fada a baya ana fara bikin Bianou tun 17 ga watan
Zhul-hijja amma manyan ranakun
bikin guda uku ne, su ne kamar haka:
1Maraicen Ado
2 Ranar sallar Bianou
3 Ranar kare wasa ko
Tudun makera.
To kamar yadda bisa tsarin da
al'adar Bianou ta tsara da an gama maraicen ado sai mazaje masu
sha'awar kwanan daji su shirya su wuce daji domin kwana a can don yin
shirin washe gari wadda ake
yi wa lakabi da ranar sallar Bianou sunan dajin da ake zuwa dajin
Alansis yana nan kilo mita biyar da garin Agadez, dajin dauke yake da
bishiyun dabinai da kuma yan
bukkokin mutane mazauna dajin.

ABUBUWAN DA AKE YI A DAJIN.
Da yake masu kwanan dajin sun kasu kashi biyu, akwai mutanen Gabas da
kuma na yamma don haka ko a dajin ka shiga sai ka fara wuce mutanen
yamma sannan za
ka iske mutanen gabas.
Abubuwan da ake yi a wannan dare, yawanci abubuwan da ake yi a wannan
dare a kan dora
girki wanda kwamitin masu kula da shirya wannan biki suke daukar
nauyin yi, wasu kuma su kan taho da abincinsu tun daga gida a kunna
wuta a gefe a yi ta hira har gari
ya waye,to amma yanzu masu wasa kan je daga cikin gari a kunna wutar
lantarki a yi wasanni da wakoki har wani adadi na dare sannan a koma
makwanci.
Zuwa da safe kuma sai a ci abinci a yi shiri a nufo gari.
'yan yamma su ke fara yin gaba sannan yan gabas na biye da su.
Dalilin da yasa ake wannan kwanan daji shi ne don raya waccan sunnar
ta ma'aiki inda
wadanda suka yi wannan kwanan daji da safe za
su yi shiga ta al'ada su shigo gari suna kada Tambari da
Akanzam(Akanzam wani karamin Bandiri ne) suna waka da rawa, su kuma
mutanen gari su fito su tarbe su, kowannesu yana rike da ganyen dabino
suna jinjina musu tare da musu lale marhaban kamar dai yadda ya faru a
lokacin hijirar Ma'aiki(S.A.W) daga Makka zuwa Madina.

RANAR SALLAR BIANOU KO DAUKAR TAZIDAI.
Ita kuma wannan rana ita ce rana
ta biyu a manyan ranakun Bianou kuma ita ce babbar ranar da kowa
yake yin kwalliya da abinci don nuna murnarsa, a wannan rana kowa kan
fito rike da tazidai(ganyen dabino) don tarbar mazajen da suka yi
kwanan daji, a kuma ranar ne kusan gaba daya
ake zagaya gari. Amma kafin a shiga gari malamai kan tarbi mazajen
Bianou a wajen gari a yi addu'o'i sannan sai a shiga gari da gidajen
iko (mahukunta) ana kada musu Tambari da Akanzam tare da
rera wakoki yawanci gidajen da ake zuwa wasu kan bayar da abinci ko fura a sha.
Bayan an gama wannan zagaye sai kuma a wuce gidan sarkin Agadez
(Sultan) a gaishe shi, shi kuma sarki ya yi nasa jawabin sai kuma a
wuce
zuwa cikin gari a yi ta wasanni da rawa da juyi har zuwa yamma sai a
aje sai kuma gobe.

RANAR QARE WASA KO TAFIYA TUDUN MAKERA.
Ita wannan rana ta kare wasa ko tafiya tudun makera ita ce rana ta uku
daga cikin manyan
ranakun Bianou kuma ita ce rana ta karshe a wannan biki wasu ma kan
kira ta da ranar cikon
shekara. Ita wannan rana ba kowa ne ke fitowa ba, akasari
ma ranar matasa sun fi yawa a ciki kuma dalilin da yasa ake Bianou a
wannan rana shi ne domin a tafi
tudun makera saboda makera a garin Agades sun kokawa sarki cewa ba a
zuwa wurinsu ana musu wasan Bianou domin suna gabas da gari don haka
sarki ya sanya a dinga zuwa ana musu na su wasan don inganta da
armashin wannan biki, amma kafin akai ga tafiya tudun makera sai an
zagaya gari ana yin wasa kamar kowacce rana ta Bianou inda mata da
maza suke
fitowo suna kallo suna yabawa samarin da suka yi
kwalliyar birgewa kamar yadda ake hawan sallah a arewacin Nijeriya,
zuwa can yamma sai a wuce tudun makera a yi wasa daga nan kuma an gama
Bianou sai wata shekarar, don haka ne ma ake kiran wannan rana da
wannan rana da ranar kare wasa har ila yau a wannan rana ne
yan gabas da yamma suke Randayya(wato nuna bajinta ko gasar rawa, kida
da kuma
kwalliya).

Agadez dai ita ce jiha ko kuma yankin da ya fi kowanne yanki
girma a
Nijar, wanda girmansa ya
kai murabba'in kilo mita
634,209
watau kwatankwacin kashi 52 cikin dari
na girman Nijar baki daya.Yankin Agadez ya hada da hamadar Tenere da
Bilma da kuma yankin Ayir mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar
yankin Abzinawa ne; akwai
kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar yankin
ta asali ita ce cinikin
gishiri da dabino sai dai a shekarun 1990 harkar
bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin,
hakanan karfen Uranium da ake samu a
garin Arlit
na samawa Nijar kashi 20 cikin dari na kudin shigar
da take samu. A 'yan shekarun bayan sun sha fama da ta'adaccin tawaye
da fari(rashin albarkar kasa) da aka rika samu wadanda suka kai yankin
ga shiga wani hali na durkusar da tattalin arzikin yankin amma yanzu
komai yana dawowa daidai musamman ziyarar baki 'yan kasashen waje da
kuma bunkasar tattalin arzikin yankin mutanen Agadez mutane masu son
baki da kuma girmama su.
Su na da guraren tarihi masu yawa kamar babban masallacin Agadez da
Tafadak da Tchirro da Arlit da dutsen Bagazam wadanda suke ciki da
abubuwan al'ajabi.
(C)
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
2018

AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)



Bikin kaddamar da littafin Alhaji Alhassan Dantata ya samu tagomashin
halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar Nijeriya, taron
dai an fara shi da misalin karfe 10am na safiyar Asabar 16\12\2017 a
babban dakin taro na Meena Event dake kan titin Lugard Road. Domin
kaddamar da littafin da aka rubuta game da rayuwar marigayi Alhaji
Alhassan Dantata tare da gudummuwarsa wajen ci gaban tattalin arzikin
Afrika.
AlHassan Dantata mahaifine ga hamshakin dan kasuwar nan na Kano wato
Aminu Alhassan Dantata shugaban rukunin kamfanonin Dantata, kuma kaka
ne a wajen fitaccen dan kasuwar nan na Afrika wato Alhaji Aliko
Dangote GCON, kafin rasuwarsa ya kasance babban dan kasuwar da ya yi
harkar kasuwanci tun daga kasar Hausa har zuwa kasashen larabawa.
An haifi Alhaji AlHassan Dantata a shekarar 1877 ya kuma rasu a watan
Satumba shekarar 1955 ya rasu ya bar 'yaya da dama, daga cikin
zuri'arsa Alhaji Aminu Alhassan Dantata ne kawai ya rage.
Marubucin wannan littafin wato Hassan Sunusi 'yan biyu Dantata, wanda
ya kasance dan'uwa ne ga Hajiya Mariya Sunusi Dantata wadda ita kuma
ta kasance mahaifiya ga Alhaji Aliko Dangote. Ya yi matukar kokari
wajen rubuta wannan littafi musamman wajen shiga lungu da sako don
tattaunawa tare da tattaro muhimman bayanai game da tasirin
kasuwancinsa da gudunmuwarsa ga Kasuwanci da 'yan kasuwar Afrika.
Tagwayen littattafan sun kasance cikin harshen Hausa da turanci, na
farkon wanda shi ne na Turanci an sanya masa suna (The Life And Times
Of Alhaji AlHassan Dantata, A Merchant Par Excellence) sai kuma na
Hausa mai suna AlHassan Dantata Tarihin Rayuwarsa Da Gudummuwarsa Ga
Tattalin Arzikin Afrika.
Alhaji Aminu AlHassan shi ne ya fara jawabi a wurin taron, inda ya ce
"duk da cewa littafin kakansa yana cike da kurakurai wanda bai kamata
a ce an yi bikin kaddamar da shi a wannan lokaci ba, kamata yayi a
bari a kammala gyare-gyaren da suke cikinsa, amma dai duk da haka
littafin ya zo a lokacin da yakamata domin tun tsawon lokaci ake ta
kira ga wasu daga cikin yaya da jikokin marigayi Alhaji AlHassan
Dantata da su yi wannan gagarumin aiki amma ba su yi ba, sai wannan
lokaci da marubucin ya yi, don haka yana alfahari da wannan aiki kuma
yana fatan alhari ga dukkan jama'ar da suka samu halartar wannan taro
kuma In sha Allah littafin za a sake duba shi domin shigar da abin da
ba a shigar ba".

Sai kuma Dakta Bello Sunusi Dantata wanda ya yi jawabin maraba ga
mahalarta taro da kuma takaitaccen jawabi na tarihin zuriar Alhaji
Alhassan Dantata.
Sai jawabi daga Dattijo Adhama inda shi ma ya bayyana irin amana da
taimakon da marigayi Alhaji Hassan Dantata ya shahara a kai.

Mamuda AlMustapha Dantata shi ne ya wakilci Alhaji Aliko Dangote
Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR
(Gwamnan Jihar Kano)

Malam Hassan Lamin Haidar shi ne ya yi sharhin littafin da cewa
"Wannan littafi fito da abubuwa da yawa game da kasuwa tun daga zuwan
turawa da harkar bayi da kuma bunkasar kasuwanci a Afrika, duk wanda
ya karanta wannan littafi zai samu abin dogora wajen fahimtar yadda
kasuwanci yake wato kalubalensa da kuma nasarorinsa" A karshe ya ce an
yi wannan sharhi ne a matakin farko nan gaba za a sake yin wani
sharhin bayan an gyara yan kurakuran ciki.

Bayan nan mutane da dama sun su yi jawabi a wajen taron irin su:
Gwamnan Jihar Kano
Justice Mamman Nasir
Malam Ibrahim Shekarau
Sarkin Shanun Damagaram
Mininstan Nijar
bayan kammala wadaccan jawabai kai tsaye bikin Kaddamar da Littafin aka shiga.
wadanda suka jagoraci kaddamar da su ne:
Alhaji Aliko Dangote 10M
Gwamnatin Jihar Kano 10M
Hajiya Mariya Sanusi Dantata 2M
Alhaji Aminu Alhassan Dantata 10M
Alhaji Sani Dangote 2M
Alhaji Sayyu Dangote 2M
Alhaji Tajuddeen Dantata 2M
Alhaji Sadik Dantata 2M
Alhaji Hassan Dantata 2M
'Yaya mata na Alhaji Aminu Alhassan Dantata 2
Ilyalan Alhaji Aminu Alhassan Dantata 2
Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u 2.5M
Iyalan Mudi Dantata 1M
Iyalin Nasiru Dantata 1M
Janaral Abdussalam Abubakar 100k
Dan Bilki Kwamanda 100K
Alhaji Garba Sanusi Dantata100k
Alhaji Ahmad Sadauki 500k
Alhaji Mutari sanusi Dantata 100k
Iyalin amadu dantata 2M
Alhaji Alhassan Abdulkadir Dantata 1M
Durbin Kano 100k
Alhaji Nabahani 50k
Gambo Dan pass 100k
Hajiya Aishatu H Dantata 100k
Alhaji Sa'adi Hamidu Dantata 5M
Da wasu da dama wadanda suka saya.

Manyan baki da dama sun halarci taron, kadan daga cikinsu su ne:
Alhaji Aminu AlHassan Dantata
Alhaji Salisu Sambajo
Dakta Malam Ibrahim Shekarau(Sardaunan Kano)
Sheikh Ibrahim Khalil
Alhaji Dattijo Adhama
Hon. Ahmad S Aruwa
Alhaji Usman Alhaji
(Sakataren Gwamnatin Kano)
Sarakunan Zinder
Kanal Abubakar Mai Malari
(Shi ne ya wakilci tsohon shugaban kasa Janaral Abdussalam Abubakar)
Wakilin sarkin Nupe. Da sauransu.
An tashi taro da misalin karfe 1pm

JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) Director Al-Huda Women Literacy
Center Kano-Nigeria Abu ne sananne cewa kasar Hausa tana girma
haka ma harshen wanda yana
cikin manyan harsunan Afrika har wasu na kiran
kasar Hausa da Biladin Sudan
kuma bincike ya nuna Hausawa suna yin fatauci
daga wannan zango-zuwa wani zango don gabatar da harkar kasuwanci da sauran
al'amuran rayuwa wannan ne
dalilin ma da wasu suke ganin hausawa sun zama
mazauna wasu kasashen saboda
dadewa ta harkar kasuwanci, har ila yau wannan
rubutu nawa zai gasgata wannan nazari na masana in da Hausawa suke a
kasar Burkina Faso kuma zai
karawa masu bincike damar sanya kasar cikin
kasashen da ake amfani da
harshen Hausa. Kamar yadda tarihi ya tabbatar bahaushe ba rago
ba ne, mutum ne da yake da
hikima da kuma yin sana'o'in dogaro da kai, a
saboda da haka ne yake yin
fatauci daga wannan gari zuwa wani gari don yin
kasuwanci, har zuwa wasu kasashen kamar Sudan, Ghana, Kamaru Chadi da
sauransu, a irin wannan
tafiye-tafiyen kasuwanci wasu suke yin aure a
wasu kasashen, wasu kuma
kasuwancinsu ya kan yi karfi a wurin sai su zauna
sai lokaci zuwa lokaci za su dinga ziyartar gida, a haka har zamani ya tafi da
su, to kamar yadda
yake a sauran kasashe haka ma ya faru a kasar
Burkina Faso Bayan tsawon
lokaci da hausawa suke zuwa kasar domin
kasuwanci lokaci ya ba su dama har sun samar da wani zango wanda ya
game ayarinsu
da kabilarsu wuri guda inda
suke gabatar da sha'aninsu cikin farin ciki da
walwala kamar bikin suna
aure da kuma sauran shagulgula na ibada kamar
bikin karamar sallah da babba har izuwa Maulidi da sauransu kuma sun auri wasu
kabilu da suke kasar,har
ila yau suna da tsarin sarki da 'yan majalisarsa a
cikin zangon. Idan ka shiga wannan wurin na zango za ka ji
cewa kamar a kasar Hausa ka
ke, domin yawan da hausawa ke da shi a wannan
wuri, sun ci gaba da wanzuwa
a wannan wuri karni bayan karni inda da dama
wasu idan aka ce su koma garuruwan da suka zo ba za su iya gane asalin
gurbin da ahalinsu suke ba,
saboda nisan lokaci, domin tun kaka da kakanni
suke wannan wuri har izuwa
lokacin mulkin shugaban Kasa Bless komfore
wanda ya rusa musu tsarin iyali da jin dadi ta hanyar rushe musu wannan gari da
suke kira zango, a
yunkurinsa na samar da ci gaban zamani a birnin
wagadugu a shekarar 2003 Wannan aiki da shugaba komfore ya yi ba karamin
rusa kabilar hausawa ya yi
ba a Burkina faso duk da cewa ya ba su sabon
wurin da za su koma amma da
yawansu ba su koma ba saboda suna ganin wurin
ya yi musu nisa, sun ce wai da a ce wurin da aka ba su ya yi hanyar kasar
Hausa ne to da za su iya
komawa amma wannan sabon wuri da aka ba su
ya kara musu nisa da gida ba za
su iya komawa ba, a sabili da haka ne sai mafi yawa
daga cikinsu suka famtsama cikin kasa, wannan shi ne farkon
rikicewar sanin kansu, kamar
yadda na fada a baya wasu daga cikin hausawan
waccan lokaci sun auri wasu
kabilun kasar to sai hakan ya bayar da damar
gurbatar harshen na su ba kamar yadda suke a tsohon zangon ba, wasu ma
da suke wasu garuruwan da ba
su ci gaba da harshen ba sai ya bace musu gaba
daya sai 'yan kalilan ne
suke jin sa, wadannan garuruwa kuwa sun hada
da Koufela da Fadar Gurma da Kantchari da kuma Zangoten su dama ba su a cikin
tarayyar zangon da aka
zauna, don haka a kabila kawai suke hausawa
amma a rukunin harshen sun
baude daga harshen Hausa na asali sai dai kana iya
gane wasu daga sunayen zuriyarsu kamar Kano ko Makeri da kuma Katsina
har yanzu akwai wadanda suke
amfani da ire-iren wadannan sunaye a cikin
sunayensu. Amma duk da haka wadanda suka yi saura a cikin
birni sun ci gaba da gabatar
da zumunci kamar yadda su ke yi a tsohon zango,
misali idan aka yi wa mutum
haihuwa to a ranar suna duk inda bahaushe yake
zai zo a yi taron suna da shi haka ma bikin aure ko jana'iza da dai sauran
sabgogin lokaci zuwa
lokaci. Kamar yadda na ambata a baya wasu daga cikin
hausawan Kasar Burkina Faso
sun riga sun bace don haka ragowar da suka yi
saura suma sai guguwar da ta
tafi da yan'uwansu ta taso musu ta hanyar aurensu
da kabilar Musawa take yi wanda kuma harshen Musanci shi ne babban
harshen kasar, abin da ya faru shi
ne, cikin biyu idan har ka ji mutum ba ya faransanci
ka tabbatar musanci
yake yi domin su ne manyan harsunan da ake
amfani da su a kasar ta Burkina, amma dai ana samun wani sa'i a yi harshen Jula
(Babban harshen kasar Mali)to
wannan alakar aure da ta shiga tsakanin hausawa
da kabilar Musawa ta yi
tasiri kwarai da gaske domin za ka shiga gidan
hausawa zalla ka ji suna yin musanci, dalili kuwa shi ne, yarinyar gidan dan
kabilar Musawa take aure
don haka idan ta zo da yaranta gida dole ne ta yi
musu harshen mahaifinsu
saboda shi suke ji, su ma kuma kakanninsu
harshen dai za su yi musu kenan, wani karin cin karfi da harshen
Musanci ya yi wa
harshen Hausa a Burkina
Faso shi ne auren kabilar musawa ba shi da
wahala, kusan ana iya cewa duka
dauka ne, wato su da ka ga yarinyarsu kana so to
ba su damuwa da abin da ka ke da shi duk kankantar abin hannunka kawai za a
daura aure, wani sa'in ma
daga wajen tambayo auren ake daura auren,
wannan sauki ya sa da dama daga
cikin hausawa maza sun auri mata kabilar Musawa
to da yake hausawa ba su da yawa sosai a kasar kuma sun warwatsu cikin kasa
sai matayensu ba su jin
harshen Hausa don haka wajibi ne duk namijin da
ya auri Bamusa ya ci gaba
da yin harshen musanci da ita a gidansa haka ma
idan ta haifi yaro da wannan harshen zai tashi domin ita ke reno da
kuma hira da shi a ko da
yaushe, a bangaren matan hausawan ma haka
idan Bamushe ya aure ta to wajibi
ne Musanci za ta yi da shi haka 'ya'yansu, wannan
abu ba karamin ci wa dattawan hausawan Burkina faso tuwo yake a
kwarya ba, suna ji suna gani
harshensu zai mutu, wasu da suka ga haka sai
suka nufi garuruwansu da ke
kasar Hausa kamar Zamfara, Sokoto, Katsina Kebbi
da kuma Kano cikin ikon Allah wasu sun samu danginsu daga nan suka yi
zamansu a gida, dama hausawa
na cewa"komai dadin garin wasu naka ya fi shi".
Ganin haka sai wasu daga
cikin dattawan Hausawa wadanda ba su da inda ya
wuce kasar kuma harshen na su ya zama har kasa don yana cikin harsuna sittin
da uku da kasar ta fitar
a cikin jadawalin kabilun da ta yarda yan asalin
kasar ne, kuma a nan aka
haife su har su ma sun yi jikoki ga shi kuma
kasuwancinsu da aikinsu a nan yake sai suka kafa wata kungiya wadda suka
sanyawa suna So Dangi, inda suke
tattaunawa da sauran hausawa da suke wasu
garuruwan kasar, manyan abubuwan
da suke tattaunawa shi ne yadda yaransu za su
dinga magana da harshen uwa a tsakakinsu da kuma auren junansu babban abin
da suka cimma shi ne sanyawa
inda suka fi yawa sunan tsohon wurin da suka
baro wato Zango. To da yake kowa yana sha'anin gabansa kuma
suna mabambanta wurare sai
wannan yunkuri bai yi armashi ba kamar yadda
suka yi masa fata. Hasalima
sarakunan na su suna wuraren daban-daban
kamar sarkin Zango da kuma sarkin Hausawa, haka dai aka ci gaba da
tafiya har izuwa
shekarar 2016 in da
matasan kabilar hausawa suka gano cewa jirgin da
suke ciki fa baya bisa
hanyar da ayarinsu suke fata, wannan hange ya
samu ne daga wani matashi da ake kira Abdourahmane Nagarba wanda yake da
digiri biyu a fannin harshen
Ingilishi da kuma Faransanci daga nan sai ya yi kira
ga ragowar matasan
hausawan cewa ya kamata su kafa wata
makaranta da za su dinga koyar da harshen Hausa ta hanyar rubuta shi da kuma
karanta shi, saboda su koyar da
ragowar yan'uwansu da ba su jin harshen da kuma
iya rubuta shi, wannan
tunani na sa ya samu karbuwa a wajen iyaye mata
da matasa da kuma dattawan kabilar hausawan kasar, da wannan tunani aka
kafa makarantar Hausa ta farko
a kasar Burkina Faso cikin babban birnin kasar mai
suna Wagadugu, an kuma
sanyawa wannan makaranta suna kungiyar
Makaranta wadda a turance suke kira(Association Makaranta)aka kuma damka
ragamar makarantar a hannunsa
tunda shi ne ya samar da tunanin duk da cewa ba
hausar ya yi nazari ba a
jami'a amma haka ya dukufa wajen koyawa
daliban yadda za su yi rubutu da kuma furta wasu kalmomi, ya kan yi bincike a
kafafen Intanet don samun salo
da dabarun yadda ake koyarwa ya kan kuma
tuntubi masana wadanda ya ci karo
da su a yanar gizo game da abin da ya shige masa
duhu har ila yau ya samu mallakar wasu littattafai wadanda suke masa
jagora wajen koyar da Hausar,
babban aikin da ya yi shi ne, kokarin kulla alaka da
wasu hukumomi da
ma'aikatu na ilmi a cikin Burkina Faso da wasu
kasashen ketare kamar Nijar da Nijeriya, sannu a hankali sai wannan makaranta
ta samu karbuwa a ko'ina
cikin babban birnin Wagadugu mutane da dama
suka dinga aiko da 'ya'yansu,
lokutan da ake gabatar da karatun su ne: ranakun
Asabar da Lahadi saboda yawanci daliban makarantar suna karatu a jami'a
wasu kuma sakandire. Wannan makaranta ta ci gaba da bunkasa har cikin
garuruwan kasar inda
ragowar hausawa suke. Ga sunan wasu garuruwan inda Hausawa suke da
zama a Burkina Faso kafin
zuwan turawa. koufela: Kantchary(Kan Cari) Namounou(Asalin sunan garin
shi ne Namu ne
saboda suna jin garinsu ne na
Hausawa zalla) Kaya Dori Gorom-Gorom Ouahigouya Bobo-Dioulasso da kuma
Nouna. wadannan
garuruwa bayan sun samu labarin
wannan makaranta sai suka nuna sha'awarsu
akan su ma idan da hali a je a
kafa musu wannan makaranta ta koyar da Hausa
da al'adu don suna kishirwar abi NEMAN AGAJI DAGA BURKINA FASO ZUWA
NIJERIYA Bayan da wannan kira na wadannan garuruwa ya
isa ga makarantar Hausa ta
farko da ta ke Wagadugu sai hukumar makarantar
suka nemi agajin malamin da
zai koyar da kuma inganta masu Hausar da suke
nazari a wagadugu in ya so a bai wa daliban farko horon da su kuma za su
baiwa ragowar mutanen da suke
wadancan garuruwa ma'ana su zama malamai a
can, to kamar yadda na fada a
baya shi jagoran makarantar wato Abdourahmane
Nagarba ya yi kokari ya samu alaka da wasu kasashe da hukumomi tare da
kungiyoyi musamman masu nazarin
harshen Hausa cikin wadanda ya kulla a alaka da
su akwai Makarantar Al-Huda
Women Literacy Center da ke Nijeriya a Kano, inda
kuma ita ce makaranta ta farko da ya nemi agajinta don ta bayar da malamin
da zai ba da wannan horo,
bayan cimma yarjejeniya ni ne malamin da ya dauki
nauyin gabatar da wannan
tafiya domin bayar da wannan horo, daga nan
kuma sai kungiyar Arewa Community da ke Afrika ta yamma wadda ta ke da
babban ofis a kasar Guinee
Bissau ta bayar da tallafin guzuri ga malamin da zai
tafi. YADDA NA GA BIRNIN WAGADUGU Na isa kasar Burkina Faso cikin babban birnin
kasar wato Wagadudu ranar
alhamis 29-12-2016 babban abin da na ya burge
ni a kasar shi ne kiyaye doka
da 'yan kasar suke yi haka kuma tsaftar birnin ya
kayatar da ni kwarai kuma karamcin mutanen garin ya burgeni sosai, wani
abin mamaki da na gani shi ne
yadda mafi yawan masu hawa keke a kasar mata
ne, duk da cewa bani jin
harshen 'yan kasar amma na gabatar da komai na
wa cikin walwala, bayan na isa ba mu dau dogon lokaci ba a washe gari ranar
juma'a da misalin karfe 4
na yamma mu ka fara karatu, da yake daliban sun
iya rubutu da karatu karin
ilimi ne da horo kawai za a ba su, don haka
abubuwan da mu ka yi nazari su ne:- -Ka'idoji da dokokin rubutu da
Karatun Hausa. -Nahawu da sarfun Hausa. -Lissafi da Hausa(Tarawa/Kari,
Debewa, Ribawa da
Rabawa) -Al'adun Hausa(Bukukuwa,Wasanni,Abinci) -Koyarwar Manya. Mun
kammala wannan bita a ranar laraba
11/1/2017 wani abin burgewa a wannan makaranta shi ne
yadda daliban suke son karatun
sosai, sukan yi nishadi kwarai a lokacin da ake
gabatar musu da darasi
sannan gasu da yawan tambaya kan abin da ya
shige musu duhu, da kansu suka kafa dokar hana yin wani harshe a cikin
a ji idan ba
Hausa ba, kuma Ofishin
Jakadancin Nijeriya a kasar ya kan ziyarci dalibai
lokacin gabatar da
karatun na su, har ila yau a lokacin gabatar da
hutun rabin lokaci na karatu akan baiwa duka daliban abin ci da sha don
samun karsashinsu,
sa'annan dattawan hausawan su ma wani lokaci su
kan ziyarci wannan
makaranta a gabatar da darasin tare da su. Manufar dai kafa wannan
makaranta ita ce ceto
harshen Hausa da al'adunsa
wanda suke da barazanar bacewa daga cikin
harsunan kasar da kabilunta, da
fatan ragowar masu ruwa da tsaki game da abin da
ya shafi harshen da Hausawa a duk in da suke a duniya za su tallafawa
wannan yunkuri na
Hausawan Burkina Faso. AL'ADUN HAUSAWAN BURKINA FASO Kamar sauran
kabilu a kasar su ma hausawa suna
gabatar da al'adunsu
musamman lokacin aure da suna da kuma sauran
shagulgulan bikin karshen
shekara,sai dai yadda suke gabatar da wasu
al'adun na su ya sha bamban da yadda na ke gani a kasar Hausa, domin su idan za
su yi aure ango ne yake
yin kayan daki haka kuma a lokacin daurin aure
ango zai mike a yi masa
tambayoyi game da aure sai kuma waliyansa su
mike tare da waliyan amarya su ma kowa ya gansu sannan su gaisa kowa yana
kallo daga nan sai a dauko
abinci a raba jama'ar da suka zo daurin aure. A bangaren bikin suna ma
yana da na shi al'adar
kamar yadda na gani a ranar
suna maza kan taru a kofar gidan wanda aka yi
haihuwa a yi radin suna daga
nan sai mutane su yi ta zuwa suna taya mahaifin
jaririn murna har zuwa yamma, KARSHE Na dawo gida Nijeriya ranar
Asabar cikin farin ciki
da koshin lafiya. Ina godiya ga kungiyar Arewa Kwaminiti reshen
afrika ta yamma da kuma
Ofishin Jakadancin Nijeriya a Burkina da
takwaransa na kasar Nijar da kuma
daliban makarantar Association Makaranta, tare da
ma'aikatar Ilimin Manya ta jihar Kano a tarayyar Nijeriya da kuma hukumar
makarantar Al-Huda Women
literacy Center Kano.

AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017)

Daga Rabiu Muhammad(Abu Hidaya)

Babban birnin kasar Kamaru wato Yawunde ya yi cikar dango da dukkan
hausawan kasar Kamaru da wasu hausawan daga sassan duniya don halartar
taron bikin nuna al'adun Hausa da kuma bayyana matsayin bahaushe a
kasar Kamaru, taron dai wanda aka yi wa lakabi da "Festi Houssa"an
fara shi tun ranar 1 ga watan Disamba zuwa babban taron a ranar 2 ga
Disamba har zuwa 3 ga wata, kuma taron ya samu tagomashin sanya
albarka daga yan siyasar kasar da Sarakuna da 'yan Jarida da kuma masu
rike da mukaman gwamnati da manyan yan kasuwa irinsu Alhaji Aliko
Dangote da kuma al'ummar sauran jihohin kasar
a taron an gabatar da wasannin gargajiya na bahaushe da kuma jawabai
kan asalin bahaushe da kuma fitar da sarauniyar kyau da wasu
sha'anonin nishadi don nishadantar da mahalarta taro.
Taron dai an jima ana shirya shi tun a watan October 2017 kuma ya samu
karbuwa daga ko ina na kasar
kamar:
Garwa
Duwala
Yawunde
Gawondare da sauransu
kuma kasashe da dama sun samu halartar taron kamar:
Faransa
Nijeriya
Togo
Chadi
Burkina Faso
Senegal
Germany
Ghana, da sauransu, duk cewa taron ya gamu da kalubale da dama kafin a
yi shi, amma a jawabin wasu daga cikin mahalarta taron na ganin a
tarihin kasar Kamaru ba a taba samun al'ummar da ta shirya taron da
kabila daya suka hadu wuri guda ba har da na sauran kasashe kamar
wannan taro na al'adun hausawan duniya ba, taron ya samu hadin kai
daga dukkan sassan da ake ganin akwai hausawa a kasar, kuma gwamnatin
kasar ta yi namijin kokari wajen ganin an yi taron lafiya an gama
lafiya.
Kuma manyan kamfanonin sufuri da sauran ma'aikatu da masu kudi tare da
sarakuna su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin taro ya yi
armashi.
Babbar manufar taron dai ita ce sada zumunci da kuma jaddada halin
karamci da amana da jin tausayin juna tare da taimakon juna irin na
bahaushen da aka sani tun asali.
Taron dai shi ne na biyu da aka shirya game da Hausawan duniya, a
watan Afrilu 2017 ma an yi irin wannan taro a kasar Burkina Faso wanda
hukumar adana kayan tarihi da al'adu tare da hadin gwiwar kungiyar
Association Makaranta na Kasar suka shirya, ana kuma sa ran a shekarar
2018 za a yi irin wannan babban taro na al'adun hausawan duniya a
kasar Nijar jahar Damagaran.

TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID

Daga
Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)

Hajiya Hafsat M.A Abdulwahid fitaccen marubuciya ce wadda sunanta ya
shahara a duniyar rubutu musamman na Hausa, ba za ka shiga tarihin
marubuta ba, ba tare da ka yi gamo da ayyukanta ba, ta fara rubutu tun
kafin marubuta su yawaita, kusan ma ana iya cewa ita ce ta fara bude
hanyar rubutu ga marubuta mata.An haifi Hajiya Hafsat Abdulwahid a
jihar Kano a ranar 5th May, (1952)Ta yi karatun firamare ɗinta a
'Shahuci Primary
School' da ke a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren ƴan mata ta
Provincial Girls School wanda aka
sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary
School.
Ta yi aure a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida
(1966),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwahid,
tana zaune a jihar Zamfara. Ta na da ƴaƴa, daga cikin ƴaƴanta akwai Kadariya
Ahmad fitacciyar ƴar jarida.
Marubuciya ce da ke rubutunta cikin harshen
Hausa.
Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana
makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar
l ambobin yabo daga British Council. A shekarar (1970) Hajiya. Hafsat
ta shiga gasar Rubutu
da kamfanin maɗaba'ar wallafa littatafai ta Northern
Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar,
inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR
DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biyar na
firamare. Labarin SO ALJANNAR DUNIYA ya samu tagomashin zuwa mataki a
na biyu a gasar.

Hajiya Hafsat Abdulwahid ita ce mace ta farko da
ta fara rubutu a harshen Hausa cikin mata
marubuta da ake da su a yankin Arewa.

Ta rubuta littatafai da dama fiye da talatin , inda ta
samu damar fitar da guda biyar daga ciki. Kadan daga cikinsu sun haɗa
da So Aljannar
Duniya, Ƴardubu Mai Tambotsai, Nasiha Ga
Ma'aurata, Namijin Maza Tauraron Annabawa, sai
littafinta na waƙe a cikin harshen Turanci mai taken
Ancient Dance.

Hajiya Hafsat mace ce jaruma kuma ƴar gwagwarmaya mai rajin kare
hakkin mata (woman
right activist).
Tana daga cikin matan da su ka taɓa fitowa takara r
muƙamin gwamna a yankin arewacin Nijeriya.
Haƙiƙa tana cikin Matan Arewa da su ka kafa tarihi a
cikin mata. Tauraruwa ce, a bar koyi ga matan Arewa.
Babban littafinta na Hausa a yanzu shi ne SABA DAN SABABI wanda ake
ganin yana iya maye gurbin littafin magana jari ce na marigayi
Abubakar Imam.
Hajiya Hafsat Abdulwahid mace ce mai sha'awar tafiye-tafiye don nazari
da rubutu game da rayuwar al'umma, tana da saukin kai tare da son
jama'a.