0
RAYUWAR 'YAN MATANCI RAYUWAR 'YAN MATANCI

Sa'adatu Baba Ahmad Rayuwar 'yan matanci da mata ke yi abu ne da ya dace a lura da shi tamkar yadda a ke lura da sauran al'...

0
KASAR HAUSA DA TARIHINTA ! KASAR HAUSA DA TARIHINTA !

Ibrahim Hamisu Galibin kasar Hausa a shinfide ta ke,gata kuma da yawan sarari .Akwai kuma tsaunuka da tuddai jifa-jifa,kuma tanada man...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 9 DABARUN RUBUTUN WAKA - 9

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A darasinmu na baya mun duba ire-iren baiti ne guda hudu. To yau za mu dora: ...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 8 DABARUN RUBUTUN WAKA - 8

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya mun fara magana kan baiti, inda muka bayyana ma'anarsa. To y...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 7 DABARUN RUBUTUN WAKA - 7

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya muka karashe magana kan ma'auni ko karin waka. To yau kuma z...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 6 DABARUN RUBUTUN WAKA - 6

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya mun fara magana a kan ma'aunin waka, wato karin da akan gina...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 5 DABARUN RUBUTUN WAKA - 5

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA (5) Assalamu alaikum. Yau wata tambaya zan amsa: Ta Yaya Zan Zama Marubucin Waka? Wannan ita ce tambayar da m...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 4 DABARUN RUBUTUN WAKA - 4

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya mun duba yadda marubucin waka kan samu ne. Amma kamata ya yi kaf...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 3 DABARUN RUBUTUN WAKA - 3

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Nasir G Ahmad Assalamu alaikum. A makon jiya mun duba ma'anonin rubutacciyar waka ne, kamar yadda manya...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 1 DABARUN RUBUTUN WAKA - 1

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Nasir G Ahmad Assalamu alaikum. A makon jiya mun yi shimfida ne kan adabi da manyan rabe-rabensa don gano muha...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA DABARUN RUBUTUN WAKA

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Nasir G Ahmad Assalamu alaikum. Wannan shiri, "Rubutattun Wakokin Hausa" zai rika zuwar muku a duk r...

0
Rikice-rikice na kara yawan zawarawa Rikice-rikice na kara yawan zawarawa

Rikice-rikice na kara yawan zawarawa. Sa'adatu Baba Ahmad Yadda rikice-rikicen da ke faruwa a sassa daban-daban na kasar nan ke tas...

RAYUWAR 'YAN MATANCI


Rayuwar 'yan matanci da mata ke yi abu ne da ya dace a lura da shi tamkar yadda a ke lura da sauran al'amuran da su ka shafi rayuwa. Don a irin wad'annan lokutan
mata da yawa su ke lalacewa, wasu kuma su koyi munanan d'abi'u ko ta sanadin samarinsu ko ta sanadin kawayensu, abin da ke haifar da haka shi ne gurbacewar al'adunmu da kuma samun shigowar sababbin bak'in al'adu. Sannan sababbin nau'o'in na'urorin fasaha, wanda su ka hada da wayar selula da kuma intanet da 'Facebook' da 2go Sai ka ga yarinya mace wacce ba ta fice Shekaru goma sha uku ba ta mallaki wayar kanta, wani bi ma iyayenne su ke siya mata su bata don gata, ba tare da sun lura ko sun sa ido a kan su waye da waye za su bugo mata ba, 
ko kuma za ta bugawa ba. Ko da kuwa mace ta mallaki wasu shekaru ni ban ga 
ribar hirar waya ga wandanda ba ma'aurata ba ko muharramai ba, saboda hak'i
k'a irin wannan hirarrakin na samari da 'yan mata a yawancin lokuta ba sa haifar da alheri. Musamman in a ka yi la'akari da lokutan da a ke yin hirar 
lokacin kwanciyar bacci ne, su kan yi amfani da kalmomi ne ba ma na so ba, 
na sha'awa zalla don kwantarwa juna zuciya, da wuya ka ji su na tattaunawa 
kan batun aure da zamansa. Yarinya k'arama sai ka ga ta san komi, kuma in har zuciyarta ta yi zurfi a kan sha'awar abokin hirarta ko wani daban sai a 
ga ba wuya ta lalace, kafin iyaye su farga labarin ya munanta. Yadda mace ta ke da kunya sai ka ji ta saki baki, wai kawai don namiji ya turo mata kati.

Ni dai a nazarin da na yi na fahimci in har ba'a lura an yi gyara ga rayuwar 'yanmatanci ba to, wallahi kar mu taba saka ran al'umma za ta gyaru, ko kuma shugabanni za su gyaru su dinga gudanar da mulki a cikin adalci Sabo
da tarbiya ta na samuwa ne tunda daga gida. In muka waiwaya baya muka dubi 
rayuwar 'yan matan da sai muga tana da bambanci da ta yanzu, tun daga kan '
yan matan da iyayensu, dan galibin iyayen da suna kokari suna bayar da gudu
mmawa wajen kame kansu daga kwadayin irin mazajen da suke zuwa wurin 'ya'yansu, kuma su na tsawatarwa 'ya'yan tare da sa mu su idanu a kan al'amuransu
na yau da kullum. Kuma al'adun mutanen da su ka shude wajibi ne makwabci da 'yan uwa su taimaka wajen tarbiyar 'ya'ya, kuma ko wanne irin laifi ya ga
d'an makwabcinsa ya yi kai tsaye zai tsawatar masa ko ya tari uban ya sanar da shi don a gaggauta daukar mataki, amma yanzu iyaye ba sa son laifukan 
'ya'yansu, Sun fi so ai ta yabon 'ya'yan, ko da kuwa ba su yi abin yabon ba, ko a yi shiru a zuba musu ido su ci karensu ba babbaka, ba dama makwabci ya fad'i wani gyara ga d'an makwabcinsa sai abin ya zama jidali, in an yi sa'a uban ya yadda to uwa mace sai ta ce atabau ba ta yadda ba, an yiwa 'yarta sharri.

Wasu iyayen dai fatansu su ga saurayi dan mutunci na zuwa gurin 'ya'yansu. Yayin
da mafi yawancin iyayen yanzu idanunsu suka fi karkata kan mai dukiya, ko 'ya'yan manya ba 
wai dole mai kyakykyawan hali ba ko mai mutunci. Sannan al'adun ma na 'yanmatanci ya sauya, irin su kunya da kawaici yanzu galibin 'yan matan ba sa yi, su kan bude baki su fadi duk wata kalma da su ka san za ta ja hankalin namijin da ba mujinsu ba, don kawai cimma wasu bukatu na kyale-kyalen rayuwa. Wasu ma kan fita wuraren shakatawa tare, su hole son ransu iyaye na gida. Har kullum wajibine mace ta-gari ta san cewa babu Soyayyar da ta kai ta aure dadi da armashi. Masana da yawa sun bayar da bayanai kan dad'in Soyayya a gidan aure
saboda halaccin aure a tsarin ko wacce al'ada ya ba da damammaki na kusantar juna tare da debe kewa. Don haka in har namiji na son mace da gaske to ya aureta ya kaita gidansa ya gwada mata duk launin son da ya dace. Ba maganar doguwar Soyayya a waje, a yi Shekara da Shekaru ana abu daya, wani bi ma har sai an kai ga yin abin da ba'a so, Sannan kuma daga baya ai aure, to, wajibine mace ta sani tsawaita rayuwar 'yan matanci na kashe sha'awarta a gidan aure a na yinsa ne don kunya da mutunci, in su ka gushe kuma da wuya zaman aure ya yi dadi

Ai da ba'a faye yawan sake-saken aure ba kamar yanzu, saboda 'yan matan da
yawancinsu suna matukar kame kansu daga duk wani abu da zai zubar musu da mutunci, kuma da wuya ka samu soyayyar son zuciya, wato mace ta rinka 
nunawa namiji soyayya a fili bayan a zuciyarta ba ta son shi abin hannunsa 
ta ke so. Su sukan yi soyayyane dan suna son mutum har zuciya, dan Allah ba wai dan wani abin duniya ba, ko kwadayin wani mukami ko matsayi da ya ke da shi ba, Sannan ba su da wata cikakkakiyar sakewa da namiji in ba mujinsu ba ne, kuma ko wayewar tara samari barkatai ma ba su da ita, irin na 'yanmatan yanzu wanda sai ka samu mace da samari goma kuma duk iyayenta na sane, a cewarsu wai ba sa son su yi mata auren dole. Sabanin mutanen da, in dai mutum na farko ya turo ta ce bata son shi, to da wuya ta k'i na biyun, wanda da wuya a hada shekara a na zance ba ai auren ba. Haka ne yasa auren mutanen da ya ke karko saboda an gina shi da tubala ma su kwarin gaske.

Yakamata mu lura cewa mu al'umma a yau mun gaza a kan duk-kan al'amuran da 
mu ke gudanarwa, amma me ya sa ba mu gaza ba wajen ciyar da cikkunanmu abin
ci ba?, mu kan yi ko wanne irin aikin wuya don mu samu abincin da za mu ci,
to, in haka ne me ya sa zamu gaza wajen bin dokokin da addinanmu da al'adunmu su ka shimfida ma na? Kar mu zuba idanu a kan rayuwar 'ya'yanmu mu ce wai zamani ne ya zo da haka, ya zama tilas mu gyara tarbiyarsu dai-dai gwargwadon iyawarmu. Allah ya sa mu dace.

Sa'adatu Baba Ahmad
(mrs Shehu Bayero Sanusi)

KASAR HAUSA DA TARIHINTA !


Galibin kasar Hausa a shinfide ta ke,gata kuma da yawan sarari .Akwai kuma tsaunuka da tuddai jifa-jifa,kuma tanada manyan Koguna guda biyu da suka ratsa ta cikinta,da Kogin Rima da Kogin Hadeja,shi kuma kogin kwara kamar iyaka ne daga yammacin Kasar. Kogin Rima shi ne ya taso daga 'Kasar Zamfara,ya gangara yayi Arewa zuwa Nigar,sa'anan ya karkata kudu,ya bi ta yamma da Sakkwato,ya je ya fada cikin Kogin Kwara.
Shi kuwa kogin Hadeja, masominsa a 'Kasar Kano ne. Daga nan ne ya gangara gabas ya bi ta Gashuwa ta Gaidam,ya je ya fada tabkin Cadi.
Akwai wani masharin Katon Daji da ya ratsa Kasar Hausa,wanda kowane shiyya akwai sunan da ake kiransa,amma guda daya ne. A Sakkwato ana kiransa dajin Gwamna, a Katsina dajin Rubu, a Kano kuwa ana ce masa dajin Folgore, a Kasar Bauchi su ce dajin Yankari, haka ya nausa har zuwa cikin 'kasar Kamaru.

Mu hadu Mako mai InshaAllah.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 9

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A darasinmu na baya mun duba ire-iren baiti ne guda hudu. To yau za mu dora:

5. Tahmisi
Tahmisi, kalmar Larbci ce da ke nufin biyartawa.. Wato mayar da wani abu da adadinsa bai kai biyar ba zuwa biyar. A nan, wani mawaki ne kan shirya waka mai dango biyu-biyu. Daga baya sai wani mawakin daban ya kara wa kowane baiti na wakar dango uku-uku, su zama dango biyar-biyar ga kowane baiti. Wato daga mai kwar biyu ta koma mai kwar biyar.
Tahmisi tamkar sharhi ne ko karin bayani ga kunshiyar waka. Domin dangogin da mai tahmisi kan kara sukan saje da kunshiyar dangogi bi-biyu na ainihin wakar.
Misalin tahmisi shi ne "Wakar zuwa birnin Kano" ta Malam Yahawa Gusau, wadda Malam Bello Gidadawa ya yi wa tahmisi. Da wakar "Arew Mulukiya ko Jamhuriya" ta Malam Sa'adu Zungur, wadda Malam Yusufu Kantu Isa ya yi wa tahmisi. Ga misali:
Sa'adu Zungur,
In za ka fadi fadi gaskiya,
Komai taka ja maka ka biya.

Bello Gidadawa,
n zance za ka yi kai tsaya,
In nuna ma hanya daya,
In ka san ka isa Zabiya,
In za ka fadi fadi gaskiya,
Komai taka ja maka ka biya.

6. Tarbi'i
Tarbi'i na nufin huduntawa. Kamar dai tahmisi da muka yi bayani ne. Sai dai shi mawaki na biyu na kara dango biyu-biyu bisa biyun mawakin farko ne, baitocin wakar su zama masu dango hudu-hudu. Kamar wata wakar Isa da Shehu Mujaddadi da Malam Muhammad Auwal ya yi wa tarbi'i. Misali:
isa dan Shehu:
A mu gode badini zahiri,
Jama'ag ga Karimi Kadiri.

Muhammad Auwal,
Ya musulmi kui mana hanzari,
A mu zamka yabo gun Gafiri,
A mu gode badini zahiri,
Jama'ag ga Karimi Kadiri.

Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 8

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun fara magana kan baiti, inda muka bayyana ma'anarsa. To yau za mu dora:

NAU'O'IN BAITI
Ana so tsarin rubutacciyar waka ya zamo dayan wadannan nau'o'i:

1. Gwauruwa
Waka gwauruwa ita ce mai dango daya-daya a kowane baiti nata. Misali:
Alhamdu lillahi mun samo fita hadari,
Wancena jan zamani da ke sa maza wadari,
Jama'a musulmi ku ce amin mu zam shukuri.
(Sa'adu Zungur)

2. 'Yar Tagwai
Ana kuma ce mata 'Mai Kwar Biyu.' Wato wakar da kowanne daga baitocinta ke kunshe da dango biyu-biyu. Misali:
Ko akwai wani wanda ya tambaya,
Mene ne sargartacciya?

Diyar da ta taso ba kula,
Ba zuwa makaranta ko daya.

Babu tarbiyya a wajen uwa,
Da uba sai shashancin tsiya.

Sai tallace-tallace barkatai,
Wai su tara kudi su yi dukiya.
(Baba Maigyada Agege)

3. Mai Kwar Uku
Ita ce waka mai dango uku-uku a kowane baiti nata. Misali:

Rashin hada kai shi ka ba makiya,
Damar su bata zaman lafiya,
Su kawo akida marar ci gaba.
(Wakar Hada kai)

4. Mai Kwar Hudu:
Ita ce wakar da kowanne daga baitocinta ke da dango hudu-hudu a cikinsa. Misali:

Ga abin da hali ya kawo,
An yi dauri yau kuma ya dawo,
Na kudurta buri na sawo,
Rabbana nufe ni da dacewa.
(Wazirin Gwandu, Umaru Nasarawa)

5. Mai Kwar Biyar
Ita ce wakar da ke da dango biyar-biyar a cikin kowane baiti nata. Misali:

Mutum kadan ba shi sani,
Kira shi jaki da zani,
Da tambaya kan yi sani,
Abin da zan zo na sani,
Ba zan ki tambayar sa ba.
(Akilu Aliyu: Wakar Kokon Mabarata)

Mu kwana nan.
Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 7

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya muka karashe magana kan ma'auni ko karin waka. To yau kuma za mu duba:

2. DANGO
Dango na nufin sadara ko layi guda na rubutacciyar waka. Wato yankin zance wanda akan harhada ya tayar da waka. Sau da yawa dango kan ci gashin kansa, wato ya ba da cikakkiyar ma'ana, ba tare da jinginuwa da wanda ya gabace shi ko wanda ke biye da shi ba. Misali:

jama'a ku taho zan wallafa,
zan wakar sangartacciya.
(Baba Maigyada Agege)

3. BAITI
Dangogi su ne ke harduwa su ba da baitin rubutacciyar waka. Baiti kan zo a tsarin gunduwoyi (layuka), wadanda ake kira dangogi, kamar yadda bayani kan dango ya gabata.

Mu kwana nan.
Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 6

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun fara magana a kan ma'aunin waka, wato karin da akan gina waka kansa, inda muka duba tarihin samuwar ma'aunan rubutattun wakokin Hausa. To yau za mu karasa tare da misali.

Duk da kasancewar har zuwa yau akan samu rubutattun wakoki da akan shirya bisa ma'aunan Larabci, mafi yawan mawakan wannan zamani ba su ma san da zamansu ba, duk kuwa da kasancewar wasu wakokin nasu za su iya hawa ma'aunan Larabcin, wadanda galibi da su akan fara auna waka yayin nazarin ta.
Kada wannan dogon labarin ya dami mai sha'awar fara rubuta waka. Babban abin da ake bukata shi ne, duk karin da ka zabi ka rubuta waka da shi, ya zamo ka bi hawa da saukar muryarsa sau-da-kafa. Wato kalmomin da za ka zaba su zamo dai dai yawan gabobin wancan kari, ba tare da sun gaza ko sun zarta ba. Ga misalin wani baiti na wata wakar Abubakar Imam:

Maraba da kai muhammadu dan Amina,
Maraba da shugaban duka Annabawa.

Ga yadda za a bi sawun karin:

maraabadakai/Muhammadudan/amiinaa,
maraabadashuu/gabandukaan/nabaaawaa.

Sai mu ce:

idankaasoo/kazaabikarii/nawaakaa,
kaluuradashii/dakyausannan/kabiishii

Wato:
idan ka so ka zabi kari na waka,
Ka lura da shi da kyau sannan ka bi shi.
Mu lura da cewa, yayin auna waka ana nuna dogon wasali ta hanyar rubanya wasalin sau biyu.

Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 5

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA (5)

Assalamu alaikum.
Yau wata tambaya zan amsa:

Ta Yaya Zan Zama Marubucin Waka?
Wannan ita ce tambayar da mutane da dama da ke sha'awar rubuta waka za su iya yi. To ni a ganina amsa ita ce, ba za ka zamo marubucin waka ba, sai ka fara zama makarancin waka, mai sauraron ta, ko mai nazarin ta. Ba kuma za ka zama makarancin waka, mai sauraron ta ko mai nazarin ta ba, sai ka zamo kana sha'awar waka. Sha'awar nan ita ce za ta rika ingiza ka ga karanta wakokin mawallafa daban-daban, kan al'amuran rayuwa mabambanta. Ta haka ne za ka nakalci salale iri-iri, har watan wata rana ka yi kokarin rubuta taka wakar, bisa kwaikwayon karin wata waka da ta fi ba ka sha'awa, kake jin dadin karanta ta ko rera ta.
Ga jerin wasu littattafai da ya kamata mai sha'awar waka ya neme su ya rika karantwa:
*Zababbun Wakokin da da na Yanzu. Na Dandatti Abdulkadir
*Tsofaffin Wakoki da Sababbin Wakoki. Na Mudi Sipikin.
*Fasaha Akiliyya. Na Akilu Aliyu
*Wakokin Sa'adu Zungur
*Wakokin Mu'azu Hadeja
*Wakokin Hausa. Na Kamfanin NNPC
*Wakokin Aliyu Dansidi; Sarkin Zazzau
*Wakokin Imfiraji. Na Aliyu Namangi
*Wakokin Hikima. Na Kungiyar Hikima Kulob
*Wakokin Hikimomin Hausa. Na Ibrahim Yaro Muhammad
*Wakokin basirorin Hausa. Na Ibrahim Yaro Muhammad
*Wakar Furen Gero da Tsarabar Madina. Na Aliyu Namangi
*Alkalami a Hannun Mata. Na Hauwa Gwaram da Hajiya 'Yar Shehu Dambatta
*Cikin Carbi. Kundin Wakokin Malam Kabiru Inuwa Magoga
*Fasahar Garba Gashuwa. Na Mal. Garba Gashuwa.
Da makamantansu.

Allah ya ba mu dacewa.


Sigogin Rubutattun Wakoki
Abin nufi a nan shi ne, siffofin rubutacciyar waka ko tubalan gina ta, wadanda ta kebanta da su, da su ne kuma ake iya bambance rubutacciyar waka da ta baka.

1. Ma'auni/Kari
Ma'aunin waka shi ne karinta. Wato muryar da ake rera wakar da ita, wadda ga al'ada takan saba da magana ta yau da kullum.
Rubutattun wakokin Hausa na farko, har zuwa cikin karni na Ashirin, an gine su ne daga ma'aunan wakokin Larabci, inda aka tabbatar da cewa an yi amfani da karuruwa goma sha uku daga cikin sha shida da ake da su a Arulin (ilimin awon waka na) Larabci.

 
A cikin karni na Ashirin ne aka fara samun sauyi wajen ma'aunan rubutattun wakokin Hausa, inda wasu mawakan suka shiga aro karuruwan wakokin baka iri-iri, suna rubuta wakokinsu da su, ko ma su kirkiri nasu karin na kashin kansu. Misali, Malam Aliyu Namangi Zariya ya ari karin wakar baka ta Caji, ya rubuta wakarsa ta "Imfiraji." Malam Akilu Aliyu ma ya ari karin wasu wakokin shata da na sauran wakokin baka, ya rubuta wakoki da dama da su. Kamar wakarsa ta "Isra'i" da wakar da ya yi kan samun 'yancin kan Nijeriya, wadda ya gina bisa bisa karin wakar almajirai da sukan yi ranar Salla.

Mu kwana nan.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 4

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun duba yadda marubucin waka kan samu ne. Amma kamata ya yi kafin nan mu yi dan gajeren bayani kan tarihi samuwar rubutattun wakokin. Don haka yau za mu yi kara'i ne.

ASALIN RUBUTATTUN WAKOkIN HAUSA
Rubutattun wakokin Hausa sun samo asali ne daga rubutattun wakokin Larabci, wadanda malaman kasar Hausa na dauri suka nazarta don kara fahimtar luggar Larabci wadda za ta zame musu jagora wajen fahimtar Alkur'ani da sauran fannonin ilimin addinin musulunci, al'amarin da ya kai su ga kwaikwayon wakokin (na Larabci), suna rubuta nasu kan wa'azi da fadakarwa da ilmantarwa cikin harshen Larabci.
Da suka nuna a fagen rubuta wakokin Larabci da ilimin awon waka (Aruli), sai kuma suka shiga wallafa wakoki cikin harsunanmu na gida, kamar Fulatanci da Hausa, bisa zubi da tsari da sauran ka'idojin wakokin Larabci.
Tun cikin karni na goma sha bakwai ake hasasashen an fara rubuta wakar Hausa, inda aka binciko wata wakar Wali dan Masani, wanda ya yi zamaninsa a kasar Katsina, mai suna "Wakar Yakin Badar." Amma habaka da bunkasa da shaharar rubutattun wakokin Hausa sun samu ne cikin karni na goma sha Tara, lokacin wa'azi da jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo da sahabbansa, inda masu jihadin suka wallafa wakoki masu tarin yawa cikin harsunan Hausa da Fulatanci, don wa'azi da fadakarwa koyar da ibada, wadanda almajiransu kan juya su haddace, suna rerawa a wuraren wa 'azi. Jigogin rubutattun wakokin Hausa a wancan lokaci duk na addini ne. Sun kuma rubuta wakokin nasu ne cikin rubutun ajamin Hausa.
Bayan zuwan Turawa da samuwar rubutun boko a karni na ashirin ne, aka fara samun sabbin jigogi na rubutattun wakokin Hausa, kamar siyasa, tafiye-tafiye, soyayya, da makamantansu. A wannan karni na ashirin da daya da muke ciki kuma, aka kara samun sauye-sauye a rubutattun wakokin Hausa wajen zubi da tsarinsu, salon aiwatar da su, da hada su da kida.

Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 3

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun duba ma'anonin rubutacciyar waka ne, kamar yadda manyan masana suka bayyana. To yau kuma za mu duba:

Wane ne Marubucin Waka?
Marubucin waka, kamar yadda manyan manazarta suka bayyana, yana samuwa ne ta hanyar dayan wasu dalilai uku:

1. Baiwa
Akwai mutanen da shirya waka wata dabi'a ce da Allah ya halicce su da ita. Sukan ji wakar na zuwar musu a duk sa'ad da suka bukace ta, ko sa'ad da duk ta so zuwa musu don kanta. Duk da haka karatu, musamman na nazarin waka kan taimaka wajen kara inganta wannan baiwa tasu.

2. Koyo
Wasu mutanen kan zamo marubuta waka ne sakamakon zama da mawaka da yin hulda da su, musamman kan abin da ya shafi waka. Ta haka yau da gobe sukan lakanci dabarun rubuta wakar a aiwace, har ta kai wata rana su ma su fara rubuta nasu wakokin, ko su zamo manyar masu ba da shawara kan abin da ya shafi waka.

3. Larurar Rayuwa
Wasu mutanen kuma kan fara rubuta waka ne sakamakon wata larurar rayuwa da ta same su, mai dadi ko marar dadi, al'amarin da kan sa matsanancin halin farin ciki da murna, ko bakin ciki da damuwa da suka samu kansu a ciki, ya kai su ga rubuta waka kan wannan al'amari. Wasu daga nan sukan zarce da rubuta wakoki kan sauran al'amuran rayuwa, har su wayi gari cikin manyar mawaka.
Wallahu a'alamu.

Bis Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 1

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA
Nasir G Ahmad

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun yi shimfida ne kan adabi da manyan rabe-rabensa don gano muhallin rubutacciyar waka cikinsa. To yau za mu fara magana kan rubutacciyar waka.

Ma'anar Waka
Akwai ta'arifai (bayanin ma'ana) na rubutacciyar waka masu yawa, daga masana daban-daban, wadanda duka suka hadu kan cewa maganar hikima ce. Tsara ta ake yi. Ana zaben kalmomin da za a gina ta da su. Zance ne mai reruwa, wanda ya saba da magana ta yau da kullum. Ga wasu daga wadannan ta'arifai:

"Waka wani salo ne da ake gina shi kan tsararriyar ka'ida ta dango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (kafiya), da sauran ka'idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaben su da amfani da su, cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba." (Dangambo:2007)

"Waka ta bambanta da tadi na yau da kullum. Abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna kwarewar harshe. Harshen waka cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu ka'idojin nahawu." (Gusau:2001)

"Waka dai ita ce tsararriyar maganar hikima, da ta kunshi sako cikin zababbun kalmomi masu azanci da aka auna don maganar ta reru, ba wai a iya fadar ta ba kawai." (A.B. Yahaya: 2001)

"Rubutacciyar waka ita ce wadda aka tsara, aka rubuta ta a takarda don a karanta." (Bello Sa'id:1981)

"Rubutacciyar waka, wata hanya ce ta gabatar da wani sako cikin kayyadaddun kalmomi da aka zaba, wadanda ake rerawa a kan kari da kafiya a cikin baitoci." (Mukhtar:2006)

Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Nasir G Ahmad

Assalamu alaikum.
Wannan shiri, "Rubutattun Wakokin Hausa" zai rika zuwar muku a duk rana irin ta yau (Litinin), don tattauna dabarun rubuta wakar Hausa ga mai sha'awar farawa, da kuma inganta rubuta su ga wanda ke sha'awar kara kwarewa wajen rubuta su. 

A yau shimfida za mu yi, mako mai zuwa in Allah ya kai tai sai mu tsunduma cikin abin sosai.

RUBUTACCIYAR WAKA
Zai yi kyau mu dauko abin daga tushe, wato daga bayani kan adabin Hausa.
Adabi a dunkule, shi ne duk wani abu da ya shafi ayyukan fasahar al'umma ta hanyar sarrafa harshe don samar da abokin hira, da nishadantarwa da debe kewa.
Adabin Hausa ya kasu zuwa kashi biyu: adabin baka da rubutacce.
Adabin baka shi ne wanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni. Shi da ka ake shirya shi, a fade shi da baki, a kuma adana shi a ka. Ya kunshi labarun baka, kamar tatsuniya, da zantukan hikima da sarrafa harshe, kamar karin maganganu, da wakokin baka, da wasannin gargajiya.

Shi kuwa rubutaccen adabi, ya samu ne bayan da Hausawa suka fara hulda da wasu al'ummomin, musamman Larabawa da Turawa. A rubuce ake shirya shi, a bayar da shi a rubuce, a kuma adana shi a rubuce. Ya kunshi rubutun zube (na labarai), kamar Ruwan "Bagaja," da wasannin kwaikwayo, kamar "Uwar Gulma" da kuma rubutattun wakokin Hausa, wadanda wannan shiri zai rika magana kansu.

Rikice-rikice na kara yawan zawarawa

Rikice-rikice na kara yawan zawarawa.

Sa'adatu Baba Ahmad

Yadda rikice-rikicen da ke faruwa a sassa daban-daban na kasar nan ke tasiri wajen kara yawan zawarawa da marayu da gajiyayyu da nakasassu. A bara kawai karkashin wani bincike an yi kiyasin an bar zawarawa dubu uku da dari biyar tare da marayu a k'alla dubu shidda. Ban da nakasassu bila adadin tare da gajiyayyu wadanda su ka rasa ma su tallafa musu.

Irin wadannan rikice-rikicen sun had'a da na addini da na k'abilanci da na siyasa da sauransu, ko wacce tarzoma dai kan taso ne sakamakon rashin fahimta ko rashin adalci ko danniya da cin zali ko kuma dalilin son zuciya tare da gidadanci na zamantakewa.

Tun dai kafuwar wannan duniya da wacce ta gabaceta mutane ke ganin matakin zubda jini ne kadai hanyar kau da raini, da kuma cimma nasara. Tarihin musulunci ya nuna cewa an samar da duniyoyin da suka gabatane domin bautar Allah, amma sai halittun cikinta suka baude, yayin da su kai ta zubda jini a doron kasa wato su kai ta kisan juna wanda dalilin haka Allah ya
rushe su. Wannan da ma wasu dalilai na nuna cewa Allah na girmama halittarsa ba kamar mu 'yan adam da mu ke ganin kauda kara ba wuya ba ne.

In muka waiwayi sauran kasashen duniya sai mu ga cewa mu fa talauci da gidadanci ne kawai shimfidar kwananmu.
Ko nan jamhuriyar Nijar ma ai da wuya ka ji irin wadannan a na zubda jini haka duk da akwai kabilu daban-daban irin su zabarmawa da azbinawa da hausawa da Fulani da buzaye da sauransu. A duk wadannan kabilun da na lissafo ba wai rikice-rikicen ne da kashe-kashe ba a yi ba sai dai ba irin na Najeriya ba wanda ba doka ba ka'ida ba. Ba babba ba yaro.

Akasari dai rashin adalci da rashin hukunci yana jagorantar ma fi yawan munanan laifukan da mutane suke aikatawa, ba wai kawai wanda ya dauki bindiga ne ya ke barnar rayuka ba, har ma wanda ya dauki biro ya rubuta hukuncin rashin adalci da dokar tayar da zaune tsaye da kuma rahotannin k'arya wanda suke jefa zuciya a cikin tashin hankali tare da haddasa fitintinu.

Kamar yadda muka dubi al'amuran da ke kawo rikice-rikice wajibine mu dubi illar da su ke haifarwa a cikin al'umma, musamman ga rayuwar mata da yara, an kashe da yawan mazaje a sanadiyar rikice-rikicen nan, ko na baya-bayan nan irin rikicin zangon kataf, da shagamu da Kaduna da Kano da jos da Maiduguri da Damaturu da Gombe a kalla nazari ya nuna an kashe mazaje sama da dubu uku, wannan ba karamar asara ba ce a irin gudummowar da suke bawa al'umma, musamman ma iyalansu wanda suka dogara da su.

Na kan zauna kusan a lokuta da dama ina kukan tausayin marayu mata da maza
daga ko wanne jinsi ko yare ko kabila shin yaya su ke fafutukar rayuwarsu,
yadda al'ummar wannan zamani ta shagala da rashin temakawa mabukata ta yaya
matan da a ka bari da marayu su ke gwagwarmaya. Na taba jin labarin wata mata da 'ya'yanta marayu sun yi ciki gaba-daya da a ka sa ta a gaba sai tace tunda mujinta ya rasu ya barsu babu wani mutum da ya taba basu ko da kuwa tallafin hatsi ne wannan shi ya kaisu ga halakar da su ka samu kansu. Shin za mu iya tuna ko da maraya guda a unguwarmu ko a cikin danginmu da mu ke tallafawa da abin da mu ke da damar yi don ya samu ingantacciyar rayuwa?

Maraici wani abu ne mai ban tausayi, mai matukar tasirin raunana mutum ta hanyoyi da dama na rayuwa.

Rabe-raben kabilu ko yare ko addini a kullum mutane suke dubawa wajen cimma burin ransu na kashe-kashen juna amma ba sa tuntubar bangaren sakamakon abinda su ke yi, 'wai kaza da na yi mai ya ke haifarwa ga al'umma.

In har rayuwar wanda za ka kashe ba ta da amfani a gareka to, na tabbatar kashe shi ba zai amfaneka da komi ba sai dakon zunubansa wanda a kalla ya shafe Shekaru ya na yi, watakila ka bar shi ya amfanarwa iyalansa da 'yan uwansa zai fi maka daukar fansa ko huce fushin zuciya.

Kuma abin dubawa kashe wadansu mutanen a yayin da rikice-rikicen su ke tasowa su na tasirin dakushewar al'ummar ko addinin da a ke rigimar da su?, ko kuwa danniya da rashin adalci da zalunci da aikata munanan laifukan na raguwa?
Kashe-kashe ba sa maganin matsalolinmu kullum kara bude kofar matsaloli da rigingimu su ke yi. In kuma suna magani me su ka maganta mana?
In har wannan amsar a'a ce, to, gaskiya muna yaudarar kanmu wajen cutar da
juna ta hanyar kisa. Ya na da kyau mu bar kisan kai a kan wadanda Allah ya
umarta.

A zahiri irin kashe-kashen da a ke a kasar nan ya keta dokar mutuncin dan adam, ko a kwanakin baya na ga gawawwakin mace da yara da a ka kashe an kai wani asibiti, wannan ya fi komi ta'addanci da cin fuska a ganina,.

Mu sani gasar kashe-kashen rayuka da mu ke yi muna tozarta rayuwar matanmu
ne da 'ya'yanmu kuma ba zamu amfana da komai ba sai dakushewar al'ummarmu.
In muka dubi yawan yaran da a ka kashewa iyaye yadda su ke tasowa a cikin kunci da kadaici sai mu ga cewa lallai muna da hakki babba da watakila zai dinga bibiyarmu. Sannan a gefe guda muna kara haifar da yawan zawarawa duk da ko galibin mazajen ba aure su ke bisa tsari na taimakon al'umma ba, a ce yau namiji ya tausayawa macen da aka mutu a ka bari da marayu ya aureta ya rike 'ya'yan kamar nasa, ko ya dinga tallafa musu da abincin da za su ci don ya samu lada su kuma su ji dadin rayuwa, da wuya a samu haka. In kuwa a ka samu namiji zai auri matar mamaci ya rike mata 'ya'yanta galibi sai idan mamacin ya mutu ya bar dukiya mai tarin yawan gaske wacce zai zauna ya ci garabasa amma akasari in mace ta rasa mujinta in har ya barta da yara to, sai dai ta kaiwa iyayensa ko 'yan uwansa Sannan ta je ta yi aure, in kuwa ta
dage sai dai a aureta da 'ya'yanta don ta rike su ta basu kulawa da tarbiyyar da ta dace to, ba shakka zai wuya ba ta kare rayuwarta a gwauruwa ba.

Wahalar da muke gudu har yanzu ita ta ke bibiyarmu, yara da mata su na da rauni kuma su na bukatar tausayawa daga mazaje, lallai suna bukatar tallafi don mace komi girmanta yarinya ce a gun iyayenta da mujinta, ranar da ta rasa su kuwa tamkar mutum ne ba hannu ba kafa, shin ta yaya zai tallafawa kansa ba a tallafe shi ba.

A karshe ina kira ga:

Malamai,

Alkalai,

Sarakai,

Kungiyoyi.

A dubi Allah a tausayawa rayuwar mata da yara a kan duk wani hukunci da za'a zartar domin yana shafarmu ta fuskoki da dama, a kamanta adalci, sannan duk tsarin da ya kaucewa shari'a shi ke haifar da fushi tare da da-na-sani, a dinga aure don taimakawa addini da al'umma, kuma tallafawa marayu tallafawa baki dayan al'umma ne.

Sa'adatu Baba Ahmad

(Mrs Shehu Sanusi Bayero )