Daga
Rabiu Muhammad Abu Hidaya
Sunana Hajara daga kauyen Sambisa Allah ya hore mini kyau na
gani a fada, tun ina yarinya na taso cikin gata karkashin kulawar iyaye da
yan'uwana, duk abinda nace ina so, kafin wani dan lokaci an bani.
Mun shaku da mahaifina matukar shakuwa Allah ya yi ni da
jarabar tsokana, amma tsoran kada a taba ni mahaifina ya yi fada haka ake
kyaleni lokacin dana kammala makarantar Firamare sai aka kaini wata sakandiren
mata ta kwana da ke gabas da garinmu, babu abinda ya dameni a makarantar sai
dai kadaicin iyayena, har so nake a ce lokacin hutu ya yi don kawai na dawo
gida na ga mahaifina da yan'uwana Allah ya yi ni yarinya mai kokari wannan ce
tasa na zama fitacciya a makarantar, domin duk gasannin da ake sawa ni nake
cinyewa, haka ni ce na ke yin ta daya ajinmu.
A kwana a tashi yanzu saura shekara daya in kammala
makaranta, yanzu kuma kewar kawayena nake ba gida ba, domin mun saba sosai
musamman babbar kawata Mufeedah muna son juna ni da ita lokaci-lokaci takan
bani labarin birni da irin abubuwan birgewar da suke can don ita yar wata gari
ce a birnin Mambil mai suna santanbul, tun ina jin maganarta a matsayin labari
har na soma marmarin zuwa birni sakamakon yadda take gaya min garin.
Watarana muna hira da ita sai na ce mata Mufeedah ni fa duk
kin sa min sha'awar zuwa garin nan naku. Sai dai babanmu ba zai yadda ba.
Sai Mufeedah ta ce kinga kuwa da zai yadda sai ki cigaba da karatunki
a can birni tunda akwai makaranta a can kinga ni ma idan na gama wannan wata
za'a sama min in cigaba da yi a can garinmu,
tun ranar da muka yi wannan hirar da Mufeeda na kuduri
aniyar duk yadda za'a yi ni ma sai na cigaba da karatu.
Komai ya yi farko yana da karshe yau makarantarmu cike take
makil, da mutane ana ta dibar dalibai domin rana ce da muka kammala jarabawar
mu ta karshe cikin shesshekar kuka muka rabu da mafi yawa daga cikin kawaye na
saboda shakuwa, musamman Mufeeda duk da ta bani kwatancen gidansu amma da kyar
muka rabu cikin kuka.
Wata sabuwa wai in ji yan caca, bayan komawata gida sai wani
dan kanen babata ya fito wai yana so na ya kuwa ci sa'a kowa a gidan yana
sonsa, dan haka babana ya ce ya bashi ni, kawai sai a zo a yi biki, haba ni
kuwa sai na yi tsalle na dire na ce bana son shi, wannan abin ba karamin mamaki
ya ba mutanen gidanmu ba, domin basu taba tsammanin haka daga gareni ba.
Cikin tsanani yayyuna suka hayayyako min da zagi da masifa
wai lalle sai na aure shi, ni kuwa na tubure ganin haka sai Mahaifina shi da
Mahaifiyata suka kira ni, bayan na gama cin abinci sai na nufi turakarsa, na
same su zaune suna Hira Mahaifina ya ce Hajara me yasa baki son auren
dan'uwanki?
Kaina a kasa na ce, baba ba son sa ne bana yi ba, kawai ina so
na cigaba da karatu ne, saboda so nake na zama likita.
Zancen banza zancen wofi! Mahaifiyata ta fada yanzu ke akan
wannan banzan tunanin naki kike kin aure?
To wallahi tun wuri ki fita idona in rufe tun muna sheda
juna, ku ji mu da yarinyar zamani, an gaya miki karatun likita sauki ne dashi a
yadda kike din nan kafin ki kammala kin tsofe kuma ba me aurenki,
ke bari ta wannan ma a gidan ubanki za'a samo wannan kudin
karatun da kike magana?
Duk wannan maganar da Mahafiyata take Mahaifine bai ce
kanzil ba, sai bayan ta dan tsahirta sai ya dube ta, ya ce haba Hajjo! me yasa
kike haka ne? Ki bita a sannu mana, kin san yarinya ce karama, ke Hajara tashi
je ki, zan neme ki mahaifina ya bani umarni.
Ina jiyo lokacin da mahaifiya ta haushi da fada tana cewa
daman ai kai kake goyon bayanta shi yasa take abinda ta ga dama a gidan nan.
Bayan kamar mako guda da faruwar wannan abin cikin ikon
Allah sai jarabawarmu ta fito na kuwa yi sa'a ina ciki mutum uku da muka fi
kowa cin jarabawar, dan haka gwamnati ta dauki nauyin karatunmu mu uku wadanda
muka fi nuna kwazo a makaranta, ana dara ga dare ya yi, kowa a gidanmu sai da
ya nuna baya son wannan karatun nawa, mahaifiyata ma cewa idan na tafi birni
lalacewa zan yi.
Da kyar mahaifina ya shawo kanta ta hakura ta barni, ranar
da zan bar gida Mahafina ya kusan kwashe awa biyu yana mini Nasiha game da kula
da kaina da kuma yin karatu tukuru.
Hajara nasanki kina da kokari, to ki kara akan wanda na
sanki dashi, sannan ki sani zaman birni daban yake dana kauye ki kula sosai da
kanki kada ki zubar da mutuncinki, ki mai da hankali sosai akan karatunki,
Allah ya taimaka Allah ya bada sa'a, idanuna na zubar da kwallah na ce amin, a
haka muka rabu dashi.
BIRNIN MAMBIL JAMI'AR SANTABUL.
Kwanci tashi kwana nesa yau wata na biyu da sati daya a
makaranta babu abinda ke damuna sai zulumi gaskiya zaman kauye ya fi na birni
dadi, domin birni ta cika cunkoso sannan ga hayaniya kamar ana yaki, uwa uba
kuma zaman kadaichi ya dameni duk da tare muke da Mufeedah amma ina jin kewar
gida da yawa.
Duk karshen mako lokacin da ba karatu ran juma'a mukan ta fi
gidansu Mufeeda mu kwana, sai litinin da sassafe mu dawo, gaskiya gidansu
Mufeedah mutane ne domin sun rike ni tamkar yarsu, mun shaku da yan gidan
sosai, dan haka duk lokacin dana aka mana hutu na koma gida nakan bawa Mahafina
labarin gidansu Mufeedah da irin karamcin su gareni, shi kuma yakan ce dama
haka rayuwa take, Allah ke hada jinin mutane ke dai ki dinga kula sosai
musamman kan abinda kika je yi.
Lalle kwanaki suna gudu yau saura shekara biyu mu kammala
karatunmu
A cikin wannna hali ne soyayya mai karfi ta kullu tsakanina
da wani wan Mufeeda mai suna Yasir, duk da bana son yin soyayya a wannan hali
amma ba zan iya juyar da soyayyar da yasir ya min ta yi ba, musamman idan aka
yi la'akari da yadda gidansu suka nuna min kauna, a haka muka cigaba da gudanar
da soyayyarmu da shi yawanci idan muna makaranta har can yake binmu ya shiga
lacca in mun fito mu yi ta hira sai wajen yamma zai koma gida, washe gari kuma
ya dawo.
Gaskiya Yasir ya iya soyayya domin duk ya sanya min son sa
cikin jini na yanzu ta kai idan ban ganshi ba har wani dan zazzabi nake ji,
ranar da bamu da karatu Yasir yakan dauke mu a mota mu shiga kasuwa ya yi mana
siyayya.
Watarana mu biyu kawai mu ke fita kasuwa, wani sa'in Yasir
yakan tafi dani wajen shakatawa mu yi kalle-kalle, sannan mu dawo gida na lura
Mahaifiyarsa bata son haka dan haka na ce masa Yasir yakamata fa mu dena fita
mu biyun nan na lura mama bata son haka?
Daga wannan rana Yasir ya dena daukata mu fita idan ina
gidansu sai in ina makaranta, ita ma Mufeeda na lura bata son fitar da muke
kawai shiru ta yi.
Tashin Hankali ba'a sa masa rana a cikin wannan fita da muke
da Yasir ne ya yi amfani da son da nake masa yace na raka shi gidan wani
abokinsa da ya yi aure za mu gaisa da matarsa, ashe gidan ba kowa dakin wani
abokinsa ne, da daddare ya keta mutuncina ranar na ci kuka kamar raina zai
fita, amma da yake Yasir mai wayo ne sai ya shawo kaina, tun daga wannan rana
muka shiga yin abinda mu kaga dama dashi sai da ta kai Yasir ya mai da ni
tamkar matarsa.
Bana taba mantawa da wata ranar laraba da rana mun tashi
daga lacca, sai na ji yanayin garin ya canja mini a hankali kuma sai jiri ya
soma dibita cikin yan dakiku kadan sai idanuna suka rufe, ban tashi bude ido ba
sai ganina na yi a asibiti, da yake asibitin a shashen da muke karatu yake kowa
ya san ni kuma malamanmu ne likitocin, yanayin kallon da naga malamin yana min
shi ya tsorata ni, bayan kamar minti uku haka da bude ido na, sai ya ce dani
Hajara kina da aure ne?
Ras! gabana ya fadi bakina na karkarwa na bashi amsa a'a.
To ina kika samu ciki?
Cikin fargici na mike tare da dafe kirji na shiga uku! malam
ciki fa ka ce?
Eh ciki ne dake kin kuma san dokar wannan makaranta ba'a
yarda mace ta yi ciki ba dan haka hukumar makaranta ta kore ki, yana gama fadin
haka sai ya miko min takarda ya fita abinsa.
Tabbas ciki ne dani abinda sakamako ya nuna kenan, wayyo!
Allah na, yau ina zansa kaina? cikin karaji na fashe da kuka duk wannan abin da
ake Mufeedah na gefe ta zuba uban tagumi, sai da taga kukan nawa yaki karewa
sannan ta taso ta matso inda nake ki yi hakuri Hajara ki dauki kaddara, sai
hakuri daga nan ita ma ta fashe da kuka.
A ranar na hada kayana bamu zame ko ina ba sai gidansu su
Mufeeda Muka kwashe labari tsaf muka gayawa mahaifiyarta, mahaifiyar su
Mufeedah ta nuna tausayi sosai a fuskarta ta ce daman sai da zuciyata ta bani
wani abu game da fitar da kuke, bari Ya zo ya sameni ki yi hakuri kin ji Hajara
zan san yadda zan bullowa al'amarin, zuwa can dare sai ga Yasir ya shigo ina ji
Mahaifiyarsa ta kira shi suka shiga daki, zuwan can sai gata ta fito, ta zo
inda muke zaune ta tsaya, a yanayin dana ganta sai da gabana ya fadi, ke Hajara
yanzu da abinda zaki saka mana kenan?
Ki rasa wa zaki yi wa sharri sai dan cikina yanzu duk irin
gatan da muka nuna miki da wannan zaki mana sakayya? lalle kin cika yarinyar
kauye, to tun muna shaida juna ki kwashe komatsanki ki bar gidan nan.
Babu irin lallashin da Mufeeda bata yi wa Mahaifiyarsu ba
akan ta fahimtar da ita gaskiyar al'amari amma sam, ta rufe ta kore ni.
Ko sallama bata bari mun yi da Mufeeda ba, ta turo ni ni da
kaya na waje, wayyo Allah Duniya yanzu ina zansa kaina? Yanzu wace duniya zan
nufa?
A cikin wannan hali ne na dawo kauyenmu, tunda na bayyana
musu abinda ya faru kowa a gidanmu ya tsanane ni ba mai shiga harkata,
mahafiyata ta dena yi min magana gaba daya, tunda nake da mahaifina ban taba
ganin fushinsa ba, kamar na wannan rana ba.
Cikin zafin rai yake magana yana cewa:
"Hajara me ya dawo dake gida? Yanzu abinda zaki saka mini
dashi kenan, Hajara me na yi miki a rayuwa dana cancanci wannan tukwicin daga
gareki?
Yanzu ina kike so in sa kaina da wannan abin kunya da kika
debo kika kawo mana gida... Kuka ne, ya kwace masa, tuni zuciyata ta gama
karyewa.
Hakuri na dinga bashi, tsakanin Mahaifi da sai Allah bayan
dogon lallashin dana yi ta masa sai samu ya sauko, duk gidan ba wanda yake
shiga harkata sai kusan kullum ina dakinsa.
Kwanci tashi kwana nesa ranar wata juma'a da safe da safe na
tashi da nakuda ban dau wani dogon lokaci ba na haihu, na haifi santalelen
yaron sai dai wani ikon Allah yaron ba rai ya zo, amma duk da haka mutanen
gidanmu basu hakura ba, har yau ba wanda yake shiga harkata.
ganin abin yana neman ya wuce makadi da rawa sai mahafina ya
tara duk yan gidanmu ya yi musu nasiha akan yadda suka kyamace ni, bai da ce ba
Allah yana iya jarabtar kowa a cikinsu, dan haka daga ranar kada ya kara ganin
wani ya min kallon banza.
Daga wannan rana rayuwata ta dawo sabuwa a cikin gidanmu,
bayan kamar wata bakwai da faruwar wannan al'amari sai ga yan gidan su Mufeeda
sun zo gidanmu sun bada hakuri tare da neman aure na gashi Yasir din, mahaifina
bai yi musu ba ya ba su aure na cikin sati biyu aka yi biki.
Yaushe shakararmu goma kenan da aure yaranmu uku kuma muna
zaune lafiya da miji na.
Babu abinda ke damuna sai tunanin Mahaifina da ya rasu a yan
kwanakin nan.
KARSHE.