0
TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) +2348065025820 gmail:abuhidya@gmail.com A bisa al'ada duk shekara mutanen garin Agadez da ke Jamh...

0
AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya) Bikin kaddamar da littafin Alhaji Alhassan Dantata ya samu tagomashin halartar manyan mutane d...

0
JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) Director Al-Huda Women Literacy Center Kano-Nigeria Abu ne sananne cewa kasar Hausa tana girma haka ma ha...

0
AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017) AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017)

Daga Rabiu Muhammad(Abu Hidaya) Babban birnin kasar Kamaru wato Yawunde ya yi cikar dango da dukkan hausawan kasar Kamaru da wasu hausaw...

0
TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya) Hajiya Hafsat M.A Abdulwahid fitaccen marubuciya ce wadda sunanta ya shahara a duniyar rubutu mus...

0
ASALI DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA'IDOJINTA ASALI DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA'IDOJINTA

Daga Malumfashi Ibrahim Tarihin rubutu da karatu irin na boko a kasar Hausa da muka sani ya biyo matakai-matakai a tsawon tarihi, wanda d...

0
BULAGURON MARUBUCI BUKAR USMAN ZUWA BURKINA FASO BULAGURON MARUBUCI BUKAR USMAN ZUWA BURKINA FASO

A cikin Afirilun bana, Gidan Adana Kayan Tarihi na kasar Burkina Faso tare da hadin gwiwar Kungiyar Makaranta sun karrama marubuci Dokta ...

0
MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU

MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU Tare da Dokta Balbasatu Ibrahim (Mrs) Tun da Allah ya halicci duniya ya jarabi dan adam da abubuwa guda uku. W...

TARIHIN BIKIN AL'ADAR BIANOU A GARIN AGADEZ JAMHURIYYAR NIJAR

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya)
+2348065025820
gmail:abuhidya@gmail.com

A bisa al'ada duk shekara mutanen garin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar
kan yi wani biki da ake kira bikin Bianou kuma su kan gayyaci mutane
daga sassa daban-daban
na duniya ciki kuwa har da 'yan
jaridun duniya tare da kungiyoyi gami da hukumomin da suke na al'adu.

MENE NE BIANOU?
Bianou salla ce ta abzinawa mutanen Agadez, suna
fara yin wannan bikin tsawon wasu kwanaki amma manyan ranakun bikin su
ne ranakun tasu'a
da ashura don ana fara bikin tun ranar 17 ga watan Zhul-hijja, an ce
bikin ya samo asali tun iyaye da kakanni.

MENE NE TARIHIN BIANOU?
A hakikanin zance babu wanda zai ce ga shekarar da aka soma bikin
Bianou a garin Agadez amma dai an
tabbatar da cewa tarihin bikin Bianou ya samo asali tun shekaru
masu yawa, kuma ana yin wannan biki ne saboda kwaikwaiyon
Ma'aiki(SAW)a lokacin da ya yi hijira daga
Makka zuwa Madina inda mutanen Madina suka fito
suka tare shi da murna, wasu kuma suka ce Bianou biki ne kawai na
al'ada da ake yi don samun nishadi kuma raya al'adar kasar don
bayyanawa duniya karfin da matasa suke da shi a garin Agadez, da wani
yake karin bayani game da wannan magana ya ce "ma'anar Bianou shi ne a
yi ta rawa sai gari ya waye".Wannan shi ne tarihin
Bianou a takaice.

MARAICEN ADO.
Ita wannan rana mai suna
maraicen ado mata ne ke yin kwalliya da yamma su fito gari, amma kafin
yammacin wannan rana ko wani gida ana yin abinci nau'ika kala-kala
amma da alkama kuma akwai wadanda suke ajiyar naman kai da kuma kashin
bayan ragon layyarsu a wannan rana suke
fitowa da shi su gyara a ci, zuwa yammacin sai kuma samari da
Tambari(Tambari shi ne shugaban da yake jagorantar masu yin bikin)
suma su fito a shiga kada tambura(Manyan ganguna) a yi ta rawa har
zuwa wani tudu da ake kira tudun Bianou wannan rana ita ce kamar ranar
bude Bianou ko kuma
jajiberin sallar Bianou kuma a
wannan yammaci maza ke tafiya kwanan daji.

KWANAN DAJI
kamar yadda na fada a baya ana fara bikin Bianou tun 17 ga watan
Zhul-hijja amma manyan ranakun
bikin guda uku ne, su ne kamar haka:
1Maraicen Ado
2 Ranar sallar Bianou
3 Ranar kare wasa ko
Tudun makera.
To kamar yadda bisa tsarin da
al'adar Bianou ta tsara da an gama maraicen ado sai mazaje masu
sha'awar kwanan daji su shirya su wuce daji domin kwana a can don yin
shirin washe gari wadda ake
yi wa lakabi da ranar sallar Bianou sunan dajin da ake zuwa dajin
Alansis yana nan kilo mita biyar da garin Agadez, dajin dauke yake da
bishiyun dabinai da kuma yan
bukkokin mutane mazauna dajin.

ABUBUWAN DA AKE YI A DAJIN.
Da yake masu kwanan dajin sun kasu kashi biyu, akwai mutanen Gabas da
kuma na yamma don haka ko a dajin ka shiga sai ka fara wuce mutanen
yamma sannan za
ka iske mutanen gabas.
Abubuwan da ake yi a wannan dare, yawanci abubuwan da ake yi a wannan
dare a kan dora
girki wanda kwamitin masu kula da shirya wannan biki suke daukar
nauyin yi, wasu kuma su kan taho da abincinsu tun daga gida a kunna
wuta a gefe a yi ta hira har gari
ya waye,to amma yanzu masu wasa kan je daga cikin gari a kunna wutar
lantarki a yi wasanni da wakoki har wani adadi na dare sannan a koma
makwanci.
Zuwa da safe kuma sai a ci abinci a yi shiri a nufo gari.
'yan yamma su ke fara yin gaba sannan yan gabas na biye da su.
Dalilin da yasa ake wannan kwanan daji shi ne don raya waccan sunnar
ta ma'aiki inda
wadanda suka yi wannan kwanan daji da safe za
su yi shiga ta al'ada su shigo gari suna kada Tambari da
Akanzam(Akanzam wani karamin Bandiri ne) suna waka da rawa, su kuma
mutanen gari su fito su tarbe su, kowannesu yana rike da ganyen dabino
suna jinjina musu tare da musu lale marhaban kamar dai yadda ya faru a
lokacin hijirar Ma'aiki(S.A.W) daga Makka zuwa Madina.

RANAR SALLAR BIANOU KO DAUKAR TAZIDAI.
Ita kuma wannan rana ita ce rana
ta biyu a manyan ranakun Bianou kuma ita ce babbar ranar da kowa
yake yin kwalliya da abinci don nuna murnarsa, a wannan rana kowa kan
fito rike da tazidai(ganyen dabino) don tarbar mazajen da suka yi
kwanan daji, a kuma ranar ne kusan gaba daya
ake zagaya gari. Amma kafin a shiga gari malamai kan tarbi mazajen
Bianou a wajen gari a yi addu'o'i sannan sai a shiga gari da gidajen
iko (mahukunta) ana kada musu Tambari da Akanzam tare da
rera wakoki yawanci gidajen da ake zuwa wasu kan bayar da abinci ko fura a sha.
Bayan an gama wannan zagaye sai kuma a wuce gidan sarkin Agadez
(Sultan) a gaishe shi, shi kuma sarki ya yi nasa jawabin sai kuma a
wuce
zuwa cikin gari a yi ta wasanni da rawa da juyi har zuwa yamma sai a
aje sai kuma gobe.

RANAR QARE WASA KO TAFIYA TUDUN MAKERA.
Ita wannan rana ta kare wasa ko tafiya tudun makera ita ce rana ta uku
daga cikin manyan
ranakun Bianou kuma ita ce rana ta karshe a wannan biki wasu ma kan
kira ta da ranar cikon
shekara. Ita wannan rana ba kowa ne ke fitowa ba, akasari
ma ranar matasa sun fi yawa a ciki kuma dalilin da yasa ake Bianou a
wannan rana shi ne domin a tafi
tudun makera saboda makera a garin Agades sun kokawa sarki cewa ba a
zuwa wurinsu ana musu wasan Bianou domin suna gabas da gari don haka
sarki ya sanya a dinga zuwa ana musu na su wasan don inganta da
armashin wannan biki, amma kafin akai ga tafiya tudun makera sai an
zagaya gari ana yin wasa kamar kowacce rana ta Bianou inda mata da
maza suke
fitowo suna kallo suna yabawa samarin da suka yi
kwalliyar birgewa kamar yadda ake hawan sallah a arewacin Nijeriya,
zuwa can yamma sai a wuce tudun makera a yi wasa daga nan kuma an gama
Bianou sai wata shekarar, don haka ne ma ake kiran wannan rana da
wannan rana da ranar kare wasa har ila yau a wannan rana ne
yan gabas da yamma suke Randayya(wato nuna bajinta ko gasar rawa, kida
da kuma
kwalliya).

Agadez dai ita ce jiha ko kuma yankin da ya fi kowanne yanki
girma a
Nijar, wanda girmansa ya
kai murabba'in kilo mita
634,209
watau kwatankwacin kashi 52 cikin dari
na girman Nijar baki daya.Yankin Agadez ya hada da hamadar Tenere da
Bilma da kuma yankin Ayir mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar
yankin Abzinawa ne; akwai
kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar yankin
ta asali ita ce cinikin
gishiri da dabino sai dai a shekarun 1990 harkar
bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin,
hakanan karfen Uranium da ake samu a
garin Arlit
na samawa Nijar kashi 20 cikin dari na kudin shigar
da take samu. A 'yan shekarun bayan sun sha fama da ta'adaccin tawaye
da fari(rashin albarkar kasa) da aka rika samu wadanda suka kai yankin
ga shiga wani hali na durkusar da tattalin arzikin yankin amma yanzu
komai yana dawowa daidai musamman ziyarar baki 'yan kasashen waje da
kuma bunkasar tattalin arzikin yankin mutanen Agadez mutane masu son
baki da kuma girmama su.
Su na da guraren tarihi masu yawa kamar babban masallacin Agadez da
Tafadak da Tchirro da Arlit da dutsen Bagazam wadanda suke ciki da
abubuwan al'ajabi.
(C)
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
2018

AN YI BIKIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ALHASSAN DANTATA

Daga Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)



Bikin kaddamar da littafin Alhaji Alhassan Dantata ya samu tagomashin
halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar Nijeriya, taron
dai an fara shi da misalin karfe 10am na safiyar Asabar 16\12\2017 a
babban dakin taro na Meena Event dake kan titin Lugard Road. Domin
kaddamar da littafin da aka rubuta game da rayuwar marigayi Alhaji
Alhassan Dantata tare da gudummuwarsa wajen ci gaban tattalin arzikin
Afrika.
AlHassan Dantata mahaifine ga hamshakin dan kasuwar nan na Kano wato
Aminu Alhassan Dantata shugaban rukunin kamfanonin Dantata, kuma kaka
ne a wajen fitaccen dan kasuwar nan na Afrika wato Alhaji Aliko
Dangote GCON, kafin rasuwarsa ya kasance babban dan kasuwar da ya yi
harkar kasuwanci tun daga kasar Hausa har zuwa kasashen larabawa.
An haifi Alhaji AlHassan Dantata a shekarar 1877 ya kuma rasu a watan
Satumba shekarar 1955 ya rasu ya bar 'yaya da dama, daga cikin
zuri'arsa Alhaji Aminu Alhassan Dantata ne kawai ya rage.
Marubucin wannan littafin wato Hassan Sunusi 'yan biyu Dantata, wanda
ya kasance dan'uwa ne ga Hajiya Mariya Sunusi Dantata wadda ita kuma
ta kasance mahaifiya ga Alhaji Aliko Dangote. Ya yi matukar kokari
wajen rubuta wannan littafi musamman wajen shiga lungu da sako don
tattaunawa tare da tattaro muhimman bayanai game da tasirin
kasuwancinsa da gudunmuwarsa ga Kasuwanci da 'yan kasuwar Afrika.
Tagwayen littattafan sun kasance cikin harshen Hausa da turanci, na
farkon wanda shi ne na Turanci an sanya masa suna (The Life And Times
Of Alhaji AlHassan Dantata, A Merchant Par Excellence) sai kuma na
Hausa mai suna AlHassan Dantata Tarihin Rayuwarsa Da Gudummuwarsa Ga
Tattalin Arzikin Afrika.
Alhaji Aminu AlHassan shi ne ya fara jawabi a wurin taron, inda ya ce
"duk da cewa littafin kakansa yana cike da kurakurai wanda bai kamata
a ce an yi bikin kaddamar da shi a wannan lokaci ba, kamata yayi a
bari a kammala gyare-gyaren da suke cikinsa, amma dai duk da haka
littafin ya zo a lokacin da yakamata domin tun tsawon lokaci ake ta
kira ga wasu daga cikin yaya da jikokin marigayi Alhaji AlHassan
Dantata da su yi wannan gagarumin aiki amma ba su yi ba, sai wannan
lokaci da marubucin ya yi, don haka yana alfahari da wannan aiki kuma
yana fatan alhari ga dukkan jama'ar da suka samu halartar wannan taro
kuma In sha Allah littafin za a sake duba shi domin shigar da abin da
ba a shigar ba".

Sai kuma Dakta Bello Sunusi Dantata wanda ya yi jawabin maraba ga
mahalarta taro da kuma takaitaccen jawabi na tarihin zuriar Alhaji
Alhassan Dantata.
Sai jawabi daga Dattijo Adhama inda shi ma ya bayyana irin amana da
taimakon da marigayi Alhaji Hassan Dantata ya shahara a kai.

Mamuda AlMustapha Dantata shi ne ya wakilci Alhaji Aliko Dangote
Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR
(Gwamnan Jihar Kano)

Malam Hassan Lamin Haidar shi ne ya yi sharhin littafin da cewa
"Wannan littafi fito da abubuwa da yawa game da kasuwa tun daga zuwan
turawa da harkar bayi da kuma bunkasar kasuwanci a Afrika, duk wanda
ya karanta wannan littafi zai samu abin dogora wajen fahimtar yadda
kasuwanci yake wato kalubalensa da kuma nasarorinsa" A karshe ya ce an
yi wannan sharhi ne a matakin farko nan gaba za a sake yin wani
sharhin bayan an gyara yan kurakuran ciki.

Bayan nan mutane da dama sun su yi jawabi a wajen taron irin su:
Gwamnan Jihar Kano
Justice Mamman Nasir
Malam Ibrahim Shekarau
Sarkin Shanun Damagaram
Mininstan Nijar
bayan kammala wadaccan jawabai kai tsaye bikin Kaddamar da Littafin aka shiga.
wadanda suka jagoraci kaddamar da su ne:
Alhaji Aliko Dangote 10M
Gwamnatin Jihar Kano 10M
Hajiya Mariya Sanusi Dantata 2M
Alhaji Aminu Alhassan Dantata 10M
Alhaji Sani Dangote 2M
Alhaji Sayyu Dangote 2M
Alhaji Tajuddeen Dantata 2M
Alhaji Sadik Dantata 2M
Alhaji Hassan Dantata 2M
'Yaya mata na Alhaji Aminu Alhassan Dantata 2
Ilyalan Alhaji Aminu Alhassan Dantata 2
Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u 2.5M
Iyalan Mudi Dantata 1M
Iyalin Nasiru Dantata 1M
Janaral Abdussalam Abubakar 100k
Dan Bilki Kwamanda 100K
Alhaji Garba Sanusi Dantata100k
Alhaji Ahmad Sadauki 500k
Alhaji Mutari sanusi Dantata 100k
Iyalin amadu dantata 2M
Alhaji Alhassan Abdulkadir Dantata 1M
Durbin Kano 100k
Alhaji Nabahani 50k
Gambo Dan pass 100k
Hajiya Aishatu H Dantata 100k
Alhaji Sa'adi Hamidu Dantata 5M
Da wasu da dama wadanda suka saya.

Manyan baki da dama sun halarci taron, kadan daga cikinsu su ne:
Alhaji Aminu AlHassan Dantata
Alhaji Salisu Sambajo
Dakta Malam Ibrahim Shekarau(Sardaunan Kano)
Sheikh Ibrahim Khalil
Alhaji Dattijo Adhama
Hon. Ahmad S Aruwa
Alhaji Usman Alhaji
(Sakataren Gwamnatin Kano)
Sarakunan Zinder
Kanal Abubakar Mai Malari
(Shi ne ya wakilci tsohon shugaban kasa Janaral Abdussalam Abubakar)
Wakilin sarkin Nupe. Da sauransu.
An tashi taro da misalin karfe 1pm

JUYIN JUYA HALIN HAUSAWA A BURKINA FASO

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) Director Al-Huda Women Literacy
Center Kano-Nigeria Abu ne sananne cewa kasar Hausa tana girma
haka ma harshen wanda yana
cikin manyan harsunan Afrika har wasu na kiran
kasar Hausa da Biladin Sudan
kuma bincike ya nuna Hausawa suna yin fatauci
daga wannan zango-zuwa wani zango don gabatar da harkar kasuwanci da sauran
al'amuran rayuwa wannan ne
dalilin ma da wasu suke ganin hausawa sun zama
mazauna wasu kasashen saboda
dadewa ta harkar kasuwanci, har ila yau wannan
rubutu nawa zai gasgata wannan nazari na masana in da Hausawa suke a
kasar Burkina Faso kuma zai
karawa masu bincike damar sanya kasar cikin
kasashen da ake amfani da
harshen Hausa. Kamar yadda tarihi ya tabbatar bahaushe ba rago
ba ne, mutum ne da yake da
hikima da kuma yin sana'o'in dogaro da kai, a
saboda da haka ne yake yin
fatauci daga wannan gari zuwa wani gari don yin
kasuwanci, har zuwa wasu kasashen kamar Sudan, Ghana, Kamaru Chadi da
sauransu, a irin wannan
tafiye-tafiyen kasuwanci wasu suke yin aure a
wasu kasashen, wasu kuma
kasuwancinsu ya kan yi karfi a wurin sai su zauna
sai lokaci zuwa lokaci za su dinga ziyartar gida, a haka har zamani ya tafi da
su, to kamar yadda
yake a sauran kasashe haka ma ya faru a kasar
Burkina Faso Bayan tsawon
lokaci da hausawa suke zuwa kasar domin
kasuwanci lokaci ya ba su dama har sun samar da wani zango wanda ya
game ayarinsu
da kabilarsu wuri guda inda
suke gabatar da sha'aninsu cikin farin ciki da
walwala kamar bikin suna
aure da kuma sauran shagulgula na ibada kamar
bikin karamar sallah da babba har izuwa Maulidi da sauransu kuma sun auri wasu
kabilu da suke kasar,har
ila yau suna da tsarin sarki da 'yan majalisarsa a
cikin zangon. Idan ka shiga wannan wurin na zango za ka ji
cewa kamar a kasar Hausa ka
ke, domin yawan da hausawa ke da shi a wannan
wuri, sun ci gaba da wanzuwa
a wannan wuri karni bayan karni inda da dama
wasu idan aka ce su koma garuruwan da suka zo ba za su iya gane asalin
gurbin da ahalinsu suke ba,
saboda nisan lokaci, domin tun kaka da kakanni
suke wannan wuri har izuwa
lokacin mulkin shugaban Kasa Bless komfore
wanda ya rusa musu tsarin iyali da jin dadi ta hanyar rushe musu wannan gari da
suke kira zango, a
yunkurinsa na samar da ci gaban zamani a birnin
wagadugu a shekarar 2003 Wannan aiki da shugaba komfore ya yi ba karamin
rusa kabilar hausawa ya yi
ba a Burkina faso duk da cewa ya ba su sabon
wurin da za su koma amma da
yawansu ba su koma ba saboda suna ganin wurin
ya yi musu nisa, sun ce wai da a ce wurin da aka ba su ya yi hanyar kasar
Hausa ne to da za su iya
komawa amma wannan sabon wuri da aka ba su
ya kara musu nisa da gida ba za
su iya komawa ba, a sabili da haka ne sai mafi yawa
daga cikinsu suka famtsama cikin kasa, wannan shi ne farkon
rikicewar sanin kansu, kamar
yadda na fada a baya wasu daga cikin hausawan
waccan lokaci sun auri wasu
kabilun kasar to sai hakan ya bayar da damar
gurbatar harshen na su ba kamar yadda suke a tsohon zangon ba, wasu ma
da suke wasu garuruwan da ba
su ci gaba da harshen ba sai ya bace musu gaba
daya sai 'yan kalilan ne
suke jin sa, wadannan garuruwa kuwa sun hada
da Koufela da Fadar Gurma da Kantchari da kuma Zangoten su dama ba su a cikin
tarayyar zangon da aka
zauna, don haka a kabila kawai suke hausawa
amma a rukunin harshen sun
baude daga harshen Hausa na asali sai dai kana iya
gane wasu daga sunayen zuriyarsu kamar Kano ko Makeri da kuma Katsina
har yanzu akwai wadanda suke
amfani da ire-iren wadannan sunaye a cikin
sunayensu. Amma duk da haka wadanda suka yi saura a cikin
birni sun ci gaba da gabatar
da zumunci kamar yadda su ke yi a tsohon zango,
misali idan aka yi wa mutum
haihuwa to a ranar suna duk inda bahaushe yake
zai zo a yi taron suna da shi haka ma bikin aure ko jana'iza da dai sauran
sabgogin lokaci zuwa
lokaci. Kamar yadda na ambata a baya wasu daga cikin
hausawan Kasar Burkina Faso
sun riga sun bace don haka ragowar da suka yi
saura suma sai guguwar da ta
tafi da yan'uwansu ta taso musu ta hanyar aurensu
da kabilar Musawa take yi wanda kuma harshen Musanci shi ne babban
harshen kasar, abin da ya faru shi
ne, cikin biyu idan har ka ji mutum ba ya faransanci
ka tabbatar musanci
yake yi domin su ne manyan harsunan da ake
amfani da su a kasar ta Burkina, amma dai ana samun wani sa'i a yi harshen Jula
(Babban harshen kasar Mali)to
wannan alakar aure da ta shiga tsakanin hausawa
da kabilar Musawa ta yi
tasiri kwarai da gaske domin za ka shiga gidan
hausawa zalla ka ji suna yin musanci, dalili kuwa shi ne, yarinyar gidan dan
kabilar Musawa take aure
don haka idan ta zo da yaranta gida dole ne ta yi
musu harshen mahaifinsu
saboda shi suke ji, su ma kuma kakanninsu
harshen dai za su yi musu kenan, wani karin cin karfi da harshen
Musanci ya yi wa
harshen Hausa a Burkina
Faso shi ne auren kabilar musawa ba shi da
wahala, kusan ana iya cewa duka
dauka ne, wato su da ka ga yarinyarsu kana so to
ba su damuwa da abin da ka ke da shi duk kankantar abin hannunka kawai za a
daura aure, wani sa'in ma
daga wajen tambayo auren ake daura auren,
wannan sauki ya sa da dama daga
cikin hausawa maza sun auri mata kabilar Musawa
to da yake hausawa ba su da yawa sosai a kasar kuma sun warwatsu cikin kasa
sai matayensu ba su jin
harshen Hausa don haka wajibi ne duk namijin da
ya auri Bamusa ya ci gaba
da yin harshen musanci da ita a gidansa haka ma
idan ta haifi yaro da wannan harshen zai tashi domin ita ke reno da
kuma hira da shi a ko da
yaushe, a bangaren matan hausawan ma haka
idan Bamushe ya aure ta to wajibi
ne Musanci za ta yi da shi haka 'ya'yansu, wannan
abu ba karamin ci wa dattawan hausawan Burkina faso tuwo yake a
kwarya ba, suna ji suna gani
harshensu zai mutu, wasu da suka ga haka sai
suka nufi garuruwansu da ke
kasar Hausa kamar Zamfara, Sokoto, Katsina Kebbi
da kuma Kano cikin ikon Allah wasu sun samu danginsu daga nan suka yi
zamansu a gida, dama hausawa
na cewa"komai dadin garin wasu naka ya fi shi".
Ganin haka sai wasu daga
cikin dattawan Hausawa wadanda ba su da inda ya
wuce kasar kuma harshen na su ya zama har kasa don yana cikin harsuna sittin
da uku da kasar ta fitar
a cikin jadawalin kabilun da ta yarda yan asalin
kasar ne, kuma a nan aka
haife su har su ma sun yi jikoki ga shi kuma
kasuwancinsu da aikinsu a nan yake sai suka kafa wata kungiya wadda suka
sanyawa suna So Dangi, inda suke
tattaunawa da sauran hausawa da suke wasu
garuruwan kasar, manyan abubuwan
da suke tattaunawa shi ne yadda yaransu za su
dinga magana da harshen uwa a tsakakinsu da kuma auren junansu babban abin
da suka cimma shi ne sanyawa
inda suka fi yawa sunan tsohon wurin da suka
baro wato Zango. To da yake kowa yana sha'anin gabansa kuma
suna mabambanta wurare sai
wannan yunkuri bai yi armashi ba kamar yadda
suka yi masa fata. Hasalima
sarakunan na su suna wuraren daban-daban
kamar sarkin Zango da kuma sarkin Hausawa, haka dai aka ci gaba da
tafiya har izuwa
shekarar 2016 in da
matasan kabilar hausawa suka gano cewa jirgin da
suke ciki fa baya bisa
hanyar da ayarinsu suke fata, wannan hange ya
samu ne daga wani matashi da ake kira Abdourahmane Nagarba wanda yake da
digiri biyu a fannin harshen
Ingilishi da kuma Faransanci daga nan sai ya yi kira
ga ragowar matasan
hausawan cewa ya kamata su kafa wata
makaranta da za su dinga koyar da harshen Hausa ta hanyar rubuta shi da kuma
karanta shi, saboda su koyar da
ragowar yan'uwansu da ba su jin harshen da kuma
iya rubuta shi, wannan
tunani na sa ya samu karbuwa a wajen iyaye mata
da matasa da kuma dattawan kabilar hausawan kasar, da wannan tunani aka
kafa makarantar Hausa ta farko
a kasar Burkina Faso cikin babban birnin kasar mai
suna Wagadugu, an kuma
sanyawa wannan makaranta suna kungiyar
Makaranta wadda a turance suke kira(Association Makaranta)aka kuma damka
ragamar makarantar a hannunsa
tunda shi ne ya samar da tunanin duk da cewa ba
hausar ya yi nazari ba a
jami'a amma haka ya dukufa wajen koyawa
daliban yadda za su yi rubutu da kuma furta wasu kalmomi, ya kan yi bincike a
kafafen Intanet don samun salo
da dabarun yadda ake koyarwa ya kan kuma
tuntubi masana wadanda ya ci karo
da su a yanar gizo game da abin da ya shige masa
duhu har ila yau ya samu mallakar wasu littattafai wadanda suke masa
jagora wajen koyar da Hausar,
babban aikin da ya yi shi ne, kokarin kulla alaka da
wasu hukumomi da
ma'aikatu na ilmi a cikin Burkina Faso da wasu
kasashen ketare kamar Nijar da Nijeriya, sannu a hankali sai wannan makaranta
ta samu karbuwa a ko'ina
cikin babban birnin Wagadugu mutane da dama
suka dinga aiko da 'ya'yansu,
lokutan da ake gabatar da karatun su ne: ranakun
Asabar da Lahadi saboda yawanci daliban makarantar suna karatu a jami'a
wasu kuma sakandire. Wannan makaranta ta ci gaba da bunkasa har cikin
garuruwan kasar inda
ragowar hausawa suke. Ga sunan wasu garuruwan inda Hausawa suke da
zama a Burkina Faso kafin
zuwan turawa. koufela: Kantchary(Kan Cari) Namounou(Asalin sunan garin
shi ne Namu ne
saboda suna jin garinsu ne na
Hausawa zalla) Kaya Dori Gorom-Gorom Ouahigouya Bobo-Dioulasso da kuma
Nouna. wadannan
garuruwa bayan sun samu labarin
wannan makaranta sai suka nuna sha'awarsu
akan su ma idan da hali a je a
kafa musu wannan makaranta ta koyar da Hausa
da al'adu don suna kishirwar abi NEMAN AGAJI DAGA BURKINA FASO ZUWA
NIJERIYA Bayan da wannan kira na wadannan garuruwa ya
isa ga makarantar Hausa ta
farko da ta ke Wagadugu sai hukumar makarantar
suka nemi agajin malamin da
zai koyar da kuma inganta masu Hausar da suke
nazari a wagadugu in ya so a bai wa daliban farko horon da su kuma za su
baiwa ragowar mutanen da suke
wadancan garuruwa ma'ana su zama malamai a
can, to kamar yadda na fada a
baya shi jagoran makarantar wato Abdourahmane
Nagarba ya yi kokari ya samu alaka da wasu kasashe da hukumomi tare da
kungiyoyi musamman masu nazarin
harshen Hausa cikin wadanda ya kulla a alaka da
su akwai Makarantar Al-Huda
Women Literacy Center da ke Nijeriya a Kano, inda
kuma ita ce makaranta ta farko da ya nemi agajinta don ta bayar da malamin
da zai ba da wannan horo,
bayan cimma yarjejeniya ni ne malamin da ya dauki
nauyin gabatar da wannan
tafiya domin bayar da wannan horo, daga nan
kuma sai kungiyar Arewa Community da ke Afrika ta yamma wadda ta ke da
babban ofis a kasar Guinee
Bissau ta bayar da tallafin guzuri ga malamin da zai
tafi. YADDA NA GA BIRNIN WAGADUGU Na isa kasar Burkina Faso cikin babban birnin
kasar wato Wagadudu ranar
alhamis 29-12-2016 babban abin da na ya burge
ni a kasar shi ne kiyaye doka
da 'yan kasar suke yi haka kuma tsaftar birnin ya
kayatar da ni kwarai kuma karamcin mutanen garin ya burgeni sosai, wani
abin mamaki da na gani shi ne
yadda mafi yawan masu hawa keke a kasar mata
ne, duk da cewa bani jin
harshen 'yan kasar amma na gabatar da komai na
wa cikin walwala, bayan na isa ba mu dau dogon lokaci ba a washe gari ranar
juma'a da misalin karfe 4
na yamma mu ka fara karatu, da yake daliban sun
iya rubutu da karatu karin
ilimi ne da horo kawai za a ba su, don haka
abubuwan da mu ka yi nazari su ne:- -Ka'idoji da dokokin rubutu da
Karatun Hausa. -Nahawu da sarfun Hausa. -Lissafi da Hausa(Tarawa/Kari,
Debewa, Ribawa da
Rabawa) -Al'adun Hausa(Bukukuwa,Wasanni,Abinci) -Koyarwar Manya. Mun
kammala wannan bita a ranar laraba
11/1/2017 wani abin burgewa a wannan makaranta shi ne
yadda daliban suke son karatun
sosai, sukan yi nishadi kwarai a lokacin da ake
gabatar musu da darasi
sannan gasu da yawan tambaya kan abin da ya
shige musu duhu, da kansu suka kafa dokar hana yin wani harshe a cikin
a ji idan ba
Hausa ba, kuma Ofishin
Jakadancin Nijeriya a kasar ya kan ziyarci dalibai
lokacin gabatar da
karatun na su, har ila yau a lokacin gabatar da
hutun rabin lokaci na karatu akan baiwa duka daliban abin ci da sha don
samun karsashinsu,
sa'annan dattawan hausawan su ma wani lokaci su
kan ziyarci wannan
makaranta a gabatar da darasin tare da su. Manufar dai kafa wannan
makaranta ita ce ceto
harshen Hausa da al'adunsa
wanda suke da barazanar bacewa daga cikin
harsunan kasar da kabilunta, da
fatan ragowar masu ruwa da tsaki game da abin da
ya shafi harshen da Hausawa a duk in da suke a duniya za su tallafawa
wannan yunkuri na
Hausawan Burkina Faso. AL'ADUN HAUSAWAN BURKINA FASO Kamar sauran
kabilu a kasar su ma hausawa suna
gabatar da al'adunsu
musamman lokacin aure da suna da kuma sauran
shagulgulan bikin karshen
shekara,sai dai yadda suke gabatar da wasu
al'adun na su ya sha bamban da yadda na ke gani a kasar Hausa, domin su idan za
su yi aure ango ne yake
yin kayan daki haka kuma a lokacin daurin aure
ango zai mike a yi masa
tambayoyi game da aure sai kuma waliyansa su
mike tare da waliyan amarya su ma kowa ya gansu sannan su gaisa kowa yana
kallo daga nan sai a dauko
abinci a raba jama'ar da suka zo daurin aure. A bangaren bikin suna ma
yana da na shi al'adar
kamar yadda na gani a ranar
suna maza kan taru a kofar gidan wanda aka yi
haihuwa a yi radin suna daga
nan sai mutane su yi ta zuwa suna taya mahaifin
jaririn murna har zuwa yamma, KARSHE Na dawo gida Nijeriya ranar
Asabar cikin farin ciki
da koshin lafiya. Ina godiya ga kungiyar Arewa Kwaminiti reshen
afrika ta yamma da kuma
Ofishin Jakadancin Nijeriya a Burkina da
takwaransa na kasar Nijar da kuma
daliban makarantar Association Makaranta, tare da
ma'aikatar Ilimin Manya ta jihar Kano a tarayyar Nijeriya da kuma hukumar
makarantar Al-Huda Women
literacy Center Kano.

AN YI TARON AL'ADUN HAUSAWA NA DUNIYA A KASAR KAMARU(FESTI HOUSSA YOAUNDE 2017)

Daga Rabiu Muhammad(Abu Hidaya)

Babban birnin kasar Kamaru wato Yawunde ya yi cikar dango da dukkan
hausawan kasar Kamaru da wasu hausawan daga sassan duniya don halartar
taron bikin nuna al'adun Hausa da kuma bayyana matsayin bahaushe a
kasar Kamaru, taron dai wanda aka yi wa lakabi da "Festi Houssa"an
fara shi tun ranar 1 ga watan Disamba zuwa babban taron a ranar 2 ga
Disamba har zuwa 3 ga wata, kuma taron ya samu tagomashin sanya
albarka daga yan siyasar kasar da Sarakuna da 'yan Jarida da kuma masu
rike da mukaman gwamnati da manyan yan kasuwa irinsu Alhaji Aliko
Dangote da kuma al'ummar sauran jihohin kasar
a taron an gabatar da wasannin gargajiya na bahaushe da kuma jawabai
kan asalin bahaushe da kuma fitar da sarauniyar kyau da wasu
sha'anonin nishadi don nishadantar da mahalarta taro.
Taron dai an jima ana shirya shi tun a watan October 2017 kuma ya samu
karbuwa daga ko ina na kasar
kamar:
Garwa
Duwala
Yawunde
Gawondare da sauransu
kuma kasashe da dama sun samu halartar taron kamar:
Faransa
Nijeriya
Togo
Chadi
Burkina Faso
Senegal
Germany
Ghana, da sauransu, duk cewa taron ya gamu da kalubale da dama kafin a
yi shi, amma a jawabin wasu daga cikin mahalarta taron na ganin a
tarihin kasar Kamaru ba a taba samun al'ummar da ta shirya taron da
kabila daya suka hadu wuri guda ba har da na sauran kasashe kamar
wannan taro na al'adun hausawan duniya ba, taron ya samu hadin kai
daga dukkan sassan da ake ganin akwai hausawa a kasar, kuma gwamnatin
kasar ta yi namijin kokari wajen ganin an yi taron lafiya an gama
lafiya.
Kuma manyan kamfanonin sufuri da sauran ma'aikatu da masu kudi tare da
sarakuna su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin taro ya yi
armashi.
Babbar manufar taron dai ita ce sada zumunci da kuma jaddada halin
karamci da amana da jin tausayin juna tare da taimakon juna irin na
bahaushen da aka sani tun asali.
Taron dai shi ne na biyu da aka shirya game da Hausawan duniya, a
watan Afrilu 2017 ma an yi irin wannan taro a kasar Burkina Faso wanda
hukumar adana kayan tarihi da al'adu tare da hadin gwiwar kungiyar
Association Makaranta na Kasar suka shirya, ana kuma sa ran a shekarar
2018 za a yi irin wannan babban taro na al'adun hausawan duniya a
kasar Nijar jahar Damagaran.

TAKAITACCEN TARIHIN HAJIYA. HAFSAT M.A ABDULWAHID

Daga
Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)

Hajiya Hafsat M.A Abdulwahid fitaccen marubuciya ce wadda sunanta ya
shahara a duniyar rubutu musamman na Hausa, ba za ka shiga tarihin
marubuta ba, ba tare da ka yi gamo da ayyukanta ba, ta fara rubutu tun
kafin marubuta su yawaita, kusan ma ana iya cewa ita ce ta fara bude
hanyar rubutu ga marubuta mata.An haifi Hajiya Hafsat Abdulwahid a
jihar Kano a ranar 5th May, (1952)Ta yi karatun firamare É—inta a
'Shahuci Primary
School' da ke a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren Æ´an mata ta
Provincial Girls School wanda aka
sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary
School.
Ta yi aure a shekarar alif É—ari tara da sittin da shida
(1966),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwahid,
tana zaune a jihar Zamfara. Ta na da Æ´aÆ´a, daga cikin Æ´aÆ´anta akwai Kadariya
Ahmad fitacciyar Æ´ar jarida.
Marubuciya ce da ke rubutunta cikin harshen
Hausa.
Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana
makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar
l ambobin yabo daga British Council. A shekarar (1970) Hajiya. Hafsat
ta shiga gasar Rubutu
da kamfanin maÉ—aba'ar wallafa littatafai ta Northern
Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar,
inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR
DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biyar na
firamare. Labarin SO ALJANNAR DUNIYA ya samu tagomashin zuwa mataki a
na biyu a gasar.

Hajiya Hafsat Abdulwahid ita ce mace ta farko da
ta fara rubutu a harshen Hausa cikin mata
marubuta da ake da su a yankin Arewa.

Ta rubuta littatafai da dama fiye da talatin , inda ta
samu damar fitar da guda biyar daga ciki. Kadan daga cikinsu sun haÉ—a
da So Aljannar
Duniya, Ƴardubu Mai Tambotsai, Nasiha Ga
Ma'aurata, Namijin Maza Tauraron Annabawa, sai
littafinta na waƙe a cikin harshen Turanci mai taken
Ancient Dance.

Hajiya Hafsat mace ce jaruma kuma Æ´ar gwagwarmaya mai rajin kare
hakkin mata (woman
right activist).
Tana daga cikin matan da su ka taɓa fitowa takara r
muƙamin gwamna a yankin arewacin Nijeriya.
Haƙiƙa tana cikin Matan Arewa da su ka kafa tarihi a
cikin mata. Tauraruwa ce, a bar koyi ga matan Arewa.
Babban littafinta na Hausa a yanzu shi ne SABA DAN SABABI wanda ake
ganin yana iya maye gurbin littafin magana jari ce na marigayi
Abubakar Imam.
Hajiya Hafsat Abdulwahid mace ce mai sha'awar tafiye-tafiye don nazari
da rubutu game da rayuwar al'umma, tana da saukin kai tare da son
jama'a.

ASALI DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA'IDOJINTA

Daga Malumfashi Ibrahim
Tarihin rubutu da karatu irin na boko a kasar
Hausa da muka sani ya biyo matakai-matakai a
tsawon tarihi, wanda daga nan ne aka samar da
ka'idojin rubutun da kuma samar da Daidaitacciyar Hausa. Tun daga
farko dai abin da ya dace mu
fahimta shi ne tun kafin zuwan Turawa an rubuce
Hausa cikin wasu haruffan da ba na Turawa ba;
akwai dai masu hasashen an rubuce Hausa cikin
Girkanci, daga baya kuma aka sake rubuce ta cikin
Larabci da Ajami. Da yake ba wani rubutun Hausa da muka gani a kasa na
Girkanci har zuwa yau, za
mu iya cewa an fara daidaita rubutun Hauda ne da
Ajami, wato da haruffan Larabci. Wannan
dadaddiyar hanya ita ce Turawan Mishau suka iske,
suka gyara, suka bi domin kokarin daidaita
rubutun Hausa a cikin Romanci ko Latinanci a cikin littattafansu da suka samar.
Ke nan za mu iya cewa an soma yin rubutun Hausa
ne da kuma daidaita shi a cikin Ajami, zuwan Boko
ya kara masa muhibba da martaba a tsakanin
masana, saboda haka muna iya cewa daga abin da
Ajami ya tanadar ne aka samar da tsarin rubutun Bokon Hausa.
Ka'idojin farko na rubutun Boko da aka samu a
rubuce su ne wadanda R. H. Robinson ya gabatar a
1848 karkashin kungiyar CMS, inda bayan samar
da bakaken Hausa da wasullansu an fito da batun
haruffan nan da ke da lankwasa, wato d da k da b wadanda aka dinga yi
masu digo a karkashi domin
a bambanta da wadanda ba su da lankwasa.
Bayan Robinson sai kuma Raberan Schon wanda
ya rayu tsakanin 1803-1889, ya yi rubuce-rubuce
da dama da suka hada da:
Vocabulary of the Hausa Language (1843) Dictionary of the Hausa Language (1876)
Grammar of the Hausa Language (1862)
Magana Hausa (1885)
Duk da cewa Schon bai ziyarci kasar Hausa kai
tsaye ba, amma ta hulda da wadanda suka ziyarta
da kuma 'yan kasa da ya hadu da su a cikin rayuwarsa ya sa ya shiga
cikin aikin raya da rubuta
Hausa domin na baya. Shi ma ya tabbatar da kusan
dukkan bakake da wasullan Hausa da Robinson ya
samar, wadanda kuma har yau ana amfani da su,
sai dai babbar matsalar da ya fuskanta ita ce ta
haruffa masu lankwasa da ya bari kamar yadda Robinson ya samar da su,
don ya rasa yadda zai yi
da su. Haka kuma ya ci karo da matsalar hamza,
wato haruffa irin su:
/Tsami/, wanda ya rubuta kamar haka, /Sami/
/'Ya'ya/ da ya rubuta kamar haka /Yaya/
/Waje/ ya rubuta kamar haka, /Waze/ Wani da ya yi wa rubutun Hausa
bauta shi ma shi
ne Charles H. Robinson (1861-1925), shi ma
manazarcin harshe ne kuma dan Mishau, ya iya
Larabci sosai, ya kuma nakalci Ajami gwargwado.
Ya yi rubuce-rubuce da dama da suka hada da:
Specimen of Hausa Literature (1896) Hausa Grammar (1897)
Dictionary of the Hausa Language (1899)
Tun farkon nazarinsa ya san da haruffa masu
lankwasa, saboda haka ya bar su da digo a
karkashin haruffan d da b da k. Sai dai shi ma ya
samu matsala wajen raba da kuma hada kalmomi ta yadda da yawa suka ba
shi ruwa. Alal misali yana
rubuta wasu jimloli kamar haka:
/Akakama/ a maimakon /Aka kama/
/Anayaki/ a maimakon /Ana yaki/
Wani dan Mishau da ya taka rawar gani wajen
rubuta da daidaita Hausa shi ne Hans Vischer Dan Hausa (1876-1945). Da
farko aikin Mishau ya fara,
daga baya kuma ya shiga aikin mulkin mallaka,
inda ya zauna a kasar Hausa, ya nakalci Hausar da
al'adun Hausawa har aka dinga kiran sa Dan Hausa
saboda sajewar da ya yi. Shi ne ya samar da
makarantar Boko ta gwamnati ta farko a kasar Hausa, ya kuma kasance
jami'i mai kula da sha'anin
Ilimi a kasar Hausa. Shi ne ya fito da ka'idonjin
rubutun Hausa na farko a shekarar 1912, wato
Rules for Hausa Spelling, inda ya tabbatar da
bakake da wasullan Hausa da muke gain yanzu, ya
kuma nemi ya gyara matsalar haruffa masu lankwasa, inda a maimakon
yadda ake rubuta su a
da a karkashin haruffan d da b da k sai ya maido a
sama da alamar hamza, domin a gan su a fili a kuma
fade cikin sauri wajen karatu. Ga yadda ya tsara su
da sauran wasu daga cikin dokokin da ya samar.
/'b/ /'d/ /'k/ /Mache/ a maimakon /Mace/
/'Ya/ a madadin /Y/
/Rigas Sarki/ a maimakon /Rigas Sarki/
/Sayam Masa/ a madadin /Sayar Masa/
/Farri/ a matsayin /Fari/
/Fatta/ a madadin /Fata/ /Sayesaye/ a madadin /Saye-saye/
Wanda ya biyo layi shi ne Raberan G.P Bargery
(1876-1960), shi ma kamar sauran da ya biyo
bayansu ya bauta wa Mishau, a cikin haka ya
inganta rubutun Hausa da ka'idojinsa. Babbar
gudunmuwar da ya bayar ita ce ta samar da kamus na Hausa-English
Dictionary and English–Hausa
Vocabulary. A cikin wannan gagarumin aiki da ya
yi a shekarar 1934, ya ci gaba ne daga inda Hans
Vischer ya tsaya, ta amincewa da haruffa masu
lankwasa, sai dai shi ma ya rubuta su a saman
haruffa da hamza, kamar yadda Vischer ya yi. Sai dai ya sake canza
wasu haruffa masu aure ko
tagwaye, irin su /Ch/ ta koma /C/, wato ya rubuta /
Caca/ a maimakon /Chacha/, ya soke amfani da
nannagen haruffa a cikin kalmomi wato irin su /sh/
ko /ts/ a tsakanin kalma ya mayar da su zuwa /s/
ko /t/ alal misali, /shashshaka/ ake rubutawa a da, shi kuma ya rubuta
kamar haka, /shasshaka/ ko
kuma /tsatstsafa/ ya mayar da ita kamar haka, /
tsattsafa/. Haka kuma shi ne ya fara bayani a fili
bambanci tsakanin ka'idojin rubutun Hausa na
Karin Harshe da Daidaitacciyar Hausa, inda yake
bambanta su a cikin aikinsa, misali: /Sayar da shi/, a maimakon /Sayad
da shi/ wanda
Katsinanci ne.
/Rigar Sarki/, a maimakon /Rigas Sarki/ wanda
Katsinanci ne.
Bargery ne kuma ya fara tabbatar da samuwar
karin sauti a cikin rubutun Hausa, yana sanya alamar – a karkashin
kowane harafi mai dauke da
karin sauti na kasa, na sama saboda yawan fitar sa
a cikin harshen bai ba shi wata alama ba. Haka
yana nuna yadda ake rubuta dogo da gajeren
wasali.
Daga Bargery sai dalibinsa R. C. Abraham (1890-1963), ma'aikacin
gwamnatin mulkin
mallaka ne wanda ya taba zama ADO a Kano. Ya
bauta wa Hausa gwargwadon iyawarsa, inda ya
rubuta littattafai da suka hada da Principles of
Hausa a 1934 da A Modern Grammar of Spoken
Hausa a 1941 da Dictionary of the Hausa Language a 1949 da kuma The
Language of Hausa People a
1959. Kodayake aikin Abraham ya kasance na
zamani, duk da haka daga abin da Bargery da
Gwamnatin Arewa ta shirya ne ya gina nasa. Sai dai
ya kasance mai kawo nasa canjin shi ma domin shi
ne ya fara rubuta haruffan Hausa masu lankwasa kamar yadda suke a
halin yanzu, wato a shekarar
1938. Haka kuma ya bambanta tsakanin haruffan /
n/ biyu, wato ra-gare da ra-kade, misali a hanci da
tankade. Ya kuma nuna inda karin sauti ke fita da
tsawon wasali, inda yake sa wannan alamar – a
saman dogon wasali da kuma – a kasan harafi mai karin sauti na kasa,
kamar yadda Bargery ya yi.
Daga wannan lokaci ne aka tabbatar da samuwar
Daitattaciyar Hausa da ka'idojin rubutun Hausa.
Dukkan abubuwan da suka faru a baya za a ga
daidaikun mutane ne ke yi da kulawar hukuma, sai
dai hukuar ba ta sa baki ba sosai da sosai sai a shekarar 1955 da aka
kafa Hukumar Kula Da
Lamurran Hausa, wadda hukuma ce da ta yi
kokarin daidaita Hausa da samar da ka'idojin
rubuta Hausar. Ta yi abubuwa da dama, ita ce ta
gyara da tantance duk wadansu kalmomin aro da
na kimiyya da fasaha. Wannan hukuma ce kuma ta waiwayi aikin da Hans
Vischer ya yi a 1952 domin
daidaita tunani da zamani, ta samar da kundin da ta
kira Rules for Hausa Orthography a 1958. A daidai
wannan lokaci ne aka tsayar da karin Hausar Kano
a matsayin Daidaitacciyar Hausa, sai dai an shelanta
cewa duk inda aka sami kalmomi da a cikin garin Kano kadai ake furta
su, ana iya maye gurbinsu da
wadansu daga kare-karen Hausa can daban da
suka fi karbuwa.
Bayan da Turawan mulkin mallaka suka bar kasar
Hausa, an yi ta kokari daga 'yan gida a daidaita
rubutun Hausa. Taro na farko da aka yi shi ne a birnin Bamako na kasar
Mali a shekarar 1966,
karkashin jagorancin Hukumar UNESCO, inda aka
tattauna yadda za a daidaita rubutun Hausa a
Yammacin Afrirka. A wannan taron ne aka amince a
rubuta Hausa kamar haka.
Haruffa masu lankwasa /b/ da /k/ da /d/ kamar yadda suke yanzu.
Aka samar da tagwayen haruffa /sh/ da /ts/ da /
gy/ da /ky/ da /ky/ da /gw/ da /kw/
A kuma raba /su/da /na/ wato /su na/ ko /ka na/
ko /ki na/ da /ya na/ dss
A shekarar 1970 kuma an yi wani taron a jami'ar Ahmadu Bello, Zaria
inda aka sake kallon aikin da
Hukumar Kula Da Lamurran Hausa ta yi a 1958, aka
samar da sababbin bayanai kamar haka:
A dinga rubuta /ko'ina/ ba /ko ina/ ba
Haka a rubuta /yake/ ba /ya ke/ ba, ko /yakan/
ba /ya kan/ ba, /suna/ ba /su na/ ba. Da kuma /mutum/ ba /mutun/ ba
Da /malam/ ba /malan/ ba
/Ranar kasuwa/ ba /ranak kasuwa/ ba
A shekarar 1972 kuma an sake gudanar da wani
taro a a jami'ar Bayero Kano, wanda shi ma ya yi
kokarin daidaita ka'idojin rubutun Hausa, an amince da 'yan
gyare-gyare da dama, wadanda za
iya cewa su ne har yau ake amfani da su a duk
fadin duniyar Hausa.
Ga kadan daga abubuwan da aka amince da su a
wurin taron, kamar yadda M.K.M.Galadanci ya
kattaba. Universal nouns are written as one word
/komai/ ba /ko mai/ ba
/kowa/ ba /ko wa/ ba
/koyaushe/ ba /ko yaushe/ ba
Where the pre-verbal pronoun precedes the tense
marker it is written as one word. /yakan/ ba /ya kan/ ba
/yana/ ba /ya na/ ba
Where the tense marker precedes the pre-verbal
pronoun it is written separately.
/za mu/ ba /zamu/
/za su/ ba /zasu/ ba A short possessive is joined to the preceding
nominal
/dokina/ ba /doki na/ ba
/rigarsa/ ba /rigar sa/ ba
/zanenta/ ba /zanen ta/ ba
But the long possessive is written separately /wani doki nawa/ ba
/wani dokinawa/ ba
/wata riga tawa/ ba /wata rigatawa/ ba
/wani zane nata/ ba /wani zanenata/ ba
The pronoun object is written separately
/ya ba ni/ ba /ya bani/ ba
/mun sa shi/ ba /mun sashi/ ba /ana kiran ka/ ba /ana kiranka/ ba
Haka kuma an jaddada cewa /saboda/ da /
watakila/ kalmomi ne a cure wuri guda, ba a
rubuta su a ware ba, wato /sabo da/ ko /wata kila/
ba da sauran su.
Taron karshe da aka yi na daidaita rubutun Hausa shi ne wanda aka yi a
Niamey, a kasar Nijar a
shekarar 1980, karkashin jagorancin Kungiyar
Hada Kan Afirka, (OAU). An shirya wannan taro ne
don a mayar da hankali wajen daidaita rubutun
Hausa a Nijeriya da Nijar, shi ma wannan taro ya
amince da muhimman bayanai da suka hada da: An tabbatar da gajerun
wasullan Hausa: i,e,a,o,u
An tabbatar da dogayen wasullan Hausa:
ii,ee,aa,oo,uu
Da kuma bakaken Hausa kusa 33
Daga lokacin da aka kashe Hausa Language Board
(Hukumar Kula Da Lamurran Hausa) da aka kafa a 1958 sai aka mayar da
yawancin ayyukanta ga
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya da ke karkashin
Jami'ar Bayero, Kano, ita ce mai kula da ka'idoji da
daidaita rubutun Hausa, kuma tun daga 1982 ta yi
iyakacin kokarinta na yin wannan aiki tukuru. Ita
ce ke shirya tarurrukan inganta harsunan Nijeriya (musamman na Hausa
da Fulfulde da Kanuri), ta
kuma samar da aikin fassara kalmomin zamani
zuwa Hausa da kuma Kamusun Hausa da ta buga a
shekarar 2007, bayan sama da shekara 30 ana
bincike da nazari da bita.
Inda muke ke nan yanzu, ba wani taro kuma da aka kara yi har zuwa yau
da na sani domin daidaita
ko sake shata ka'idojin rubutun Hausa, wanda da
zarar an samu wannan dama duk wata matsala a
nan za a tattauna ta, a kuma samar da matsaya
domin amfanin sauran al'umma. Allah shi ne
masani!

BULAGURON MARUBUCI BUKAR USMAN ZUWA BURKINA FASO

A cikin Afirilun bana, Gidan Adana Kayan Tarihi
na kasar Burkina Faso tare da hadin gwiwar
Kungiyar Makaranta sun karrama marubuci
Dokta Bukar Usman da kambin girmamawa,
bisa la'akari da gudunmowarsa wajen bunkasa
Adabin Hausa da kuma jaddada zaman lafiya tsakanin al'ummar Hausa da
duniya baki daya.
Bayan ya dawo, ya rubuta wannan tsaraba ga
masu karatu, kamar haka: Ita dai Kungiyar Makaranta, kungiya ce mai zaman
kanta, wacce ba ta gwamnati ba kuma al'ummar
Hausawa mazauna kasar Burkina Faso ce ta kafa ta
a 2006, da nufin bunkasa al'adu, ilimi,
zamantakewa, tattalin arziki da kuma harshen
Hausa a kasar. Domin tabbatar da wannan kuduri nata, sai kungiyar ta
shirya gagarumin biki, wanda
ya hada da kalankuwa, baje kolin kayan gargajiya,
babban taron masana daga ko'ina a duniya da
kuma karrama wasu muhimman 'yan Afrika da
suka taimaka wajen bunkasa al'ummar Hausawa.
Ina daya daga cikin wadanda aka zaba, domin karramawa. Haka kuma, ba
yan ni kaina, an kuma
zabi Sanata (Injiniya) Rabi'u Musa Kwankwaso,
tsohon Gwamnan Jihar Kano. Sanata Kwankwaso da ni kaina, mun halarci
bikin a Babban Birnin Burkina Faso, Ouagadougou
(Wagadugu). Ma'anar sunan birnin nan shi ne
'Wurin da ake karrama da girmama mutane' - babu
shakka birnin ya ci sunansa, domin kuwa hakika
ana girmama baki da daraja su. An karrama ni da kambi tare da takardar
shaida mai taken 'Jakadan
Adabin Hausa.' Wannan taro na kasa-da-kasa, an yi masa lakabi
da "Gudunmowar Al'adun Hausa Wajen Wayar Da
Kan Al'ummar Afirka." Kasar Hausa ta yi fice wajen
saka da rini da kira da jimar fata da ginin tukwane
da sauran ayyukan fasaha da zayyana, wadanda
ake sayarwa har wajen kasar ta Hausa. Harshen Hausa na daya daga cikin
manyan harsunan
duniya. Adabin Hausa na ci gaba da bunkasa,
musamman ana samun rubuce-rubuce a fannoni
da dama na ci gaban al'umma, duk kuwa da cewa
akwai bukatar a rika amfani da na'urorin zamani
tare da tsarin dauri wajen taskance harshen da al'adunsa domin amfanin
gida da ma al'ummar
duniya baki daya. An nuna sha'awar sanin ainahin
sunayen da ake amfani da su a kasar Hausa, kafin
zuwan Musulunci, sannan kuma aka nuna takaici
da yadda yara kan gaza yin magana da harshen
iyayensu. A yayin bikin nunin kayan al'adun gargajiya na
Hausa, wanda Ministan Al'adu Da Shakatawa na
Burkina Faso, Mista Tahirou Barry ya bude, an baje
kolin kayayyaki daban-daban, har ma da abincin
gargajiya. Kayan sun hada da zayyane-zayyane da
aka yi na fata, duwatsu, tabarmi da mafutai, kayan aikin noma, kayan
girki da na cin abinci, korai,
sakakkun suturu da kuma tukwane iri daban-
daban da aka yi wa zayyana masu kyau. Haka
kuma akwai ingantattun magungunan gargajiya
da sake-saki, nama iri-iri da kayan sha na gargajiya
daban-daban. An sha kallo kuma an nishadantu da kade-kade
da wake-waken gargajiya na Hausa, ga wasanni,
musamman na kokowa da aka gudanar. Wasan
kokowa na daya daga cikin wasanni masu tashe a
kasar Burkina Faso. Tawagar karfafa kuma
gwanayen kokowa daga Jamhuriyyar Nijar ta halarci bikin. A yayin da
aka gudanar da tarukan
kara wa juna ilimi a ranakun 14-16 na watan Afrilu,
an ci gaba da baje kolin kayayyakin gargajiya,
wanda zai dore har zuwa tsakiyar Yunin bana. Zan iya tunawa, a
lokacin da nake makarantar
sakandare, a 1960, na samu labarin madaukakun
Daulolin Mossi Dagomba da ke yankin Tsakiyar
Afrika ta Yamma. A wannan zamani a yau, a
Burkina Faso, irin wadannan dauloli da suka
bunkasa, sun ci gaba da bunkasa har zuwa lokacin da Turawan mulkin
mallaka na Faransa suka
murkushe su a wajajen 1896. Wannan dalili ma na
daga cikin dalilan da suka sanya na yi kwadayin
ziyartar kasar, musamman domin in tantance
wadannan kayatattun labarun da suka shafi kasa
da al'ummomin Burkina Faso, kamar yadda aka gaya mana a can baya.
A sakamakon tsawon lokacin da na yi ina
nazarin tsarin al'umma, na fahimta da cewa duk mai
son ya fahimci tarihi da al'adun al'umma, zai iya
samun ilimi mai yawa daga almara da
tatsuniyoyinsu. Wannan ya sanya a lokacin da na
sauka a birnin Wagadugu, tun ma kafin in sauka a masaukina na otel,
sai na yi wa shagon sayar da
littattafai tsinke, domin in samu littafin da ya yi
bayani game da kasa da al'ummar Burkina Faso.
Tabbas kuwa na ga littattafai da yawa da za su yi
mani amfani, amma abin takaici, babu ko daya da
aka rubuta da Ingilishi. Na yi kokarin tambayar inda zan samu littattafan
da nake nema, amma ban dace ba. Don haka sai na
maida hankali ga intanet, inda na samu bayanai irin
na kunne-ya-girmi-kaka. Na fahimta da cewa a
kasar, manyan yarukan da ake amfani da su, su ne
Moore da Djula da kuma Faransanci. Burkina Faso na da kabilu 63,
cikinsu har da Fulani da Yarabawa
da Ibo, tare da shugabanninsu. Burkina Faso, wadda ke nufin 'kasar mutane
masu gaskiya' tana da tarihi mai tsawo. Tarihinta ya
faro ne tun 1896, lokacin da Faransa ta yi tunga a
yankin a matsayin mallakinta. A 1904, Faransa ta
mallaki kasar Upper Senegal da Yankin Nijar a
Afrika ta Yamma, inda birnin Bamako ya kasance hedikwata. Daga bisani
aka canja wa yankin suna
zuwa French Upper Volta mai hedikwata a
Wagadugu, a 1919. A shekarar 1932 aka rushe
wannan tsari, aka karkasa kasashen zuwa Ivory
Coast da Sudan da Nijar. An sake maida ta tsarin
baya a 1947, inda aka dawo da yankin Upper Volta, aka mayar mata da
iyakokinta. An ba ta
mulkin kanta a 1958, sannan aka ba ta 'yancin kai
da sunan Jamhuriyyar Upper Volta a 1960. Kamar dai yadda ta faru
a Najeriya, sojoji sun
tsoma hannunsu a mulkin Jamhuriyyar Upper Volta
a 1966, inda gwamnatin ta soja ta kare a 1976.
Sabuwar gwamnatin farar hula da ta gaji ta soja, an
tunkude ta ita ma a 1980, inda sojan suka ci gaba
da mulki zuwa 1983. Thomas Sankara da Blaise Campaore ne suka ci gaba
da mulki a kakin soja
kuma wannan gwamnatin ce ma ta canja wa kasar
suna zuwa Burkina Faso a 1984. Bayan an yi wa
Thomas Sankara kisan gilla a 1987, kasar ta samu
natsuwar mulki a karkashin Shugaban Kasa Blaise
Campaore na tsawon shekara 27. An matsa masa lamba, dole ya sauka daga
mulki a 2014. Tsohon sunan kasar na Upper Volta, an samo shi
ne daga Koramar Volta, wacce ta hade har zuwa
Kogin Atilantika, wanda ya ratsa har zuwa kasar
Ghana a yanzu. Wani Baturen Fotugal ne ya rada
mata sunan "Volta" domin ya yi la'akari da yadda ta
yi ta kwana-kwana. Koramar tana da manyan bakuna uku, Farar Volta, Jar
Volta da kuma Bakar
Volta, wanda haka ke nuna launin kasar wuraren.
Launin kasar Wagadugu ja ce kuma Jar Volta na
Arewa Maso Yammacin Wagadugu. Burkina Faso a yanzu haka tana da yawan
mutane miliyan 20, inda Wagadugu ne Fadar
Gwamnati, wanda ke kunshe da yawan mutane
kimanin miliyan 2. Birnin Kasuwancin kasar,
sunansa Bobo-Dioulasso, yawan al'ummarsa na
kasa da miliyan daya ne kuma an yi kidayar jama'a ta karshe a 1982.
Mossi ita ce kabila mai mafi yawan mutane a
kasar kuma suna da karin harshe kala biyu,
Kompela da Tenkodogo. Mutanensu sun yi suna
wajen hakuri da juriya, don haka Turawan Faransa
suka rika daukar mazansu aikin soja, kuma aka
rika ba su aikin gina hanyoyin jirgin kasa da na mota. Haka ma
matansu, ba su da son jiki, suna da
kokarin neman abinci. Ba su jin nauyi, domin za ka
gan su suna tuka babur da motocin haya a babban
birnin kasar. Suna yin noma, ban ruwa a fadamu,
aikin buga bulo ko yin aikin siminti. An taba
haramta auren mace fiye da daya a zamanin mulkin Sankara amma daga
baya gwamnatin da ta gaje shi
ta dawo da shi. Wannan ya sanya mutane da suke
daraja al'ada suka rika auren mata da yawa. Duk
macen da mijinta ya mutu, ba ta fita daga gidan
aurenta, sai dai kawai ta zabi namiji daya daga
dangin mijinta, ta sake aure. Noma, shi ne babbar sana'ar mutanen kasar.
Suna noma jar dawa da gyada, haka ma suna noma
acca. Kamar Masar da Sudan, su ma Burkina Faso
suna noma auduga mai yawa da suke sayarwa
kasashen waje. Suna da ma'aidinan zinari da azurfa
da sauransu, wadanda kasashen Australia da Afrika ta Kudu da Faransa
da Japan da Ghana da
sauransu ke amfana sosai ta hanyar hako su. Kasar
tana dogaro da agajin kasashen waje ta bangaren
tattalin arziki. Otel din Laico, wanda kuma ake kira
da Hotel Libya shi ne kusan otel mafi inganci a
Wagadugu. Marigayi Muamar Gaddafi ne ya gina shi kuma yana daya daga
cikin abin alherin da 'yan
kasar ke tuna marigayin shi da shi. Wasu daga ciki
wuraren bude ido a Wagadugu sun hada har da
'Zauren Shahidai' wanda yake kan hanyar Muamar
Gaddafi. An gina shi ne domin tunawa da mutanen
da aka rasa a hautsinin da ya faru a 2014. Masu masaukina a kasar
Burkina Faso, sun
kasance tsatson Hausawa. Kakanninsu sun yo hijira
ne daga Najeriya, musamman daga Kano,
Sakkwato, Katsina, Kebbi da sauran biranen Arewa.
Sun ce sun sauka a Upper Volta ne a matsayin 'yan
kasuwa, masaka, masunta, tun kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka na
Faransa. Sun ce su ne
ma tun farko suka fara kai sana'ar rini da sakar
tufafi a kasar. Har zuwa yau kuwa, irin suturunsu
ne ake alfahari da su a kasar. Akwai al'ummar Hausawa da dama a biranen
kasar Burkina Faso, suna zaune ne a
unguwanninsu da ake wa lakabi ba Zango, sunan
da aka samo a sanadiyyar kasuwancin da ya
gudana shekaru masu yawa da suka shude, inda
'yan kasuwa kan keta sahara daga wannan kasa zuwa waccan a kan rakuma.
Wuraren da suke yada
zango ne ake lakaba wa sunan unguwar ta
Hausawa. A birnin Wagadugu, an canza wa Zango
na ainahi matsuguni har sau biyu, domin kuwa
ayyukan raya birnin ya shafe shi. Zango na farko
yana kusa da tashar jirgin kasa, shi kuwa Zango na biyu, inda nan
Hausawan suka zauna tsawon
shekara 85, yana cikin kawyar birnin, nisan
kilomita biyu daga Fadar Masarautar Moogo Naaba,
Sarkin Gargajiyar Mossi; wanda suke da
kyakkyawar mu'amala da shi. A 2001, Gwamnatin
Blaise Campaore ce ta canza wa Zangon wuri zuwa inda yake yanzu, kusa
da Fadar Shugaban Kasa. Kalilan daga cikin Hausawa da suka yi
karatun
Boko, sun rike manyan mukamai a Ma'aikatun
Gwamnatin Burkina Faso da sauran wurare har ma
da wajen kasar. Daga bisani ne suka farga da
muhimmancin ilimin zamani, inda suka kafa
Kungiyar Makaranta, wacce ke taimakawa wajen fadakar da al'ummarsu,
muhimmancin da ke tattare
da ilimin na zamani. Akwai abubuwa da yawa da mutum zai nazarta
kuma ya karu a kasar Burkina Faso, duk kuwa da
cewa karamar kasa ce da ba ta da yawan
albarkatun kasa kamar wasu. Suna tafiyar da
al'amuransu a kan tsari, ga su da bin doka da oda. Moogo Naaba
(Sarkin Duniya), shi ne lakanin
Sarkin Gargajiya na Mossi da ke Wagadugu. Ana ba
shi girma da daraja sosai. Kasancewar fadarsa na a
babban birnin kasar, yana da martaba ta
musamman, duk kuwa da cewa shi ne na hudu a
tsarin martabar sarakuna a Daular Mossi ta Burkina Faso. Tarihi
ya nuna cewa Daular Mossi a Burkina Faso
ta samo asali ne tun a Karni na 7. Kamar yadda
tarihin ya tabbatar, Sarkin Gambaga na kabilar
Dagomba a Arewacin Ghana, diya mace kawai ya
haifa. Bayan ta yi aure, wata rana sai ta fita kilisa a
doki, ta shiga daji kuma ta yi makuwa. Wani maharbi dan kasar Mali ya
tsince ta kuma suka yi
aure, suka haifi da namiji. Kasancewar a kan doki
aka samu mahaifiyar jaririn, sai aka rada masa suna
Ouedraogo (sunan namijin doki ke nan a Daular
Mossi). Shi Ouedraogo ne ya zama Sarki na farko a
Daular Mossi kuma shi ne ya kafa Masarautar
Tenkodogo. Sarkin Mossi na yanzu a Wagadugu,
Naaba Booggo, shekararsa 34 ke nan a kan
karaga. Shi ne sarki na 147 a jerin sarakunan
daular. Masarautar tana daraja al'ada sosai, musamman akwai wata
al'ada da har yanzu take
wanzuwa. Kamar yadda sauran sarakunan kasar
suka rika yi, duk Jumu'a, Naaba Booggo kan shiga
sulke, ya hau doki da nufin tafiya yaki da wasu
al'umma da ke Mali. Haka za a yi ta lallashinsa, ana
ba shi hakuri, sannan ya sauko. Wannan shauki na yaki ya zama jiki a
masarautar, duk Jumu'a. Mai martaba Naaba Booggo ya amshi
bakuncin
mu mahalarta wannan muhimmin taro. Kafin mu
kai ga ganawa da shi, sai da aka yi ta kai-komo
wajen bin ka'idoji daban-daban amma duk da
haka kwalliya ta biya kudin sabulu. Mutanen
Burkina sun yi suna wajen hakuri, don haka sun dauka bakinsu ma haka
ne. Sarkin na zaune a bisa
karaga, tsakiyar butumbutumin zakoki biyu,
hakoransu a bude, gwanin ban tsoro. Da yarensu
ya yi mana jawabi, tafinta ya rika fassara mana. Ya
yi mana jawabi ne game da rainon yara, inda ya
nuna cewa zamani ya canja, don haka akwai bukatar dattawa su maida
hankali wajen kyautata
rainon yara, domin su tashi da da'a da biyayya, a
matsayin 'yan kasa nagari. Na fahimta da cewa, irin
wannan sakon ne yake isarwa ga dukkan tawagar
da ta ziyarci fadar tasa. Domin kare martabar al'adun Masarautar Mossi,
an haramta wa kowane mutum daukar hoton wani
abu a fadar masarautar ba tare da izini ba. Sarkin
dai ya karrama mu, inda ya amince muka dauki
hoto da shi a wajen fadar. Akwai wani azancin
magana da aka rubuta baro-baro a wata hasumiyar masarautar da harsuna
uku na Moore
da Djula da Fulatanci, kamar haka: "Duk inda ka ga
dattijo, da wuya a aikata ba daidai ba a wurin." Naaba Booggo,
dan kwallo ne. Babu mamaki,
watakila shi ya sanya ma aka gina babban filin
wasa na kasa kusa da fadar masarautarsa. Na samu
bayanin cewa, shahararren dan kwallon nan na
kasar Kamaru, Samuel Eto ne ya gina shingayen
karfe da suka kewaye kofar fadar sarkin saboda nuna gamsuwa da yadda
sarkin ke sha'awar
wasan kwallon kafa. Mun karu da wasu karin azancin magana a fadar
Sarkin Hausawa a Zango. Kakakin Fadar ya ambata
cewa: "Abu ne mai sauki ka ga makiyayi yana
sarrafa garken shanu da sanda guda, a yayin da
abu ne mai matukar wahala ka mulki jama'a kamar
haka." Wannan yana yi mana ishara da yadda mulki ke da wahala.
Taron kara wa juna sani da kuma bikin,
kasancewarsu na kasa-da-kasa, an gayyaci
mahalarta daga kasashen Benin, Kamaro, Afrika Ta
Tsakiya, Chadi, Ghana, Nijar, Najeriya, Togo da
kuma Sudan kuma dukkan wadannan kasashe,
akwai al'ummar Hausawa da yawa. Taron ya samu halartar baki sosai, sai
son barka, domin kuwa
sarakunan gargajiya har uku suka zo daga kasar
Togo kadai. Ba domin matsalolin sufuri da ke
addabar nahiyar Afrika ba, da an samu mahalarta
taron fiye da kima. Amma duk da haka, taron ya
samu yabo daga mahalarta, a yayin da kasashen Togo da Senegal suka
dauki alkawarin shirya irinsa
a nan gaba. Tafiya ta jirgin sama daga Abuja zuwa
Wagadugu akwai wahala. An ba ni shawarar in
shiga jirgi zuwa Kairo (Masar), ko kuma in bi ta
wasu kasashen ma da ba na Afrika ba domin zuwa
Wagadugu. Hanya mafi gajarta, ita ce ta Lome
(Togo) ko Abdijan (Kwaddabuwa) kuma sai mutum ya kwana biyu a hanya.
Matafiya daga
Najeriya da suka biyo ta hanyar mota, sai da suka yi
kwana uku, sun yada zango a Maradi da Yamai
(Jamhuriyyar Nijar), sannan suka isa Wagadugu a
rana ta ukun saboda jidalin bincike-binciken
jami'an tsaro a iyakokin kasashen. Kodayake duk da wannan
jidalin, tafiya ta mota
na tattare da nishadi, domin kuwa mutum zai karu
sosai da sababbin abubuwa a hanya, na mutane iri-
iri da kuma wurare. Ta fannin gane-gane a hanya
kuwa, masu tafiya ta jirgi ma sun karu, domin kuwa
mutum zai samu damar ganin falalen kasa, da itatuwa nan da can da
hanyoyin kasa marasa
kwalta da kuma gidaje warwatse, nan da can. Lallai
akwai yalwar kasa, wacce ya kamata a aikata ta,
domin ceto ta daga balbalcewa. Na yi hira da wasu abokan tafiyata, wadanda
suka bayyana abubuwan burgewa game da
Najeriya. A jirgin da na shiga zuwa Abdijan zuwa
Wagadugu, wani tsohon malamin Kwalejin Fourah
Bay, Saliyo ya bayyana takaicinsa game da Najeriya.
Ya bayyana yadda Allah Ya albarkaci Najeriya da albarkatun kasa amma
saboda halin ko-in-kula na
al'ummar kasar, an kasa amfana. Domin kawo
gyara, ya ce 'Najeriya na bukatar shugaba mai
nuna karfa-karfa, amma ba mai zuciyar kisa ba.' Haka kuma mun
tattauna kan al'amuran da suka
shafi 'yancin dan Adam, musamman sakamakon
yadda wasu mutum biyu suka rika cacar baki da
juna. Daya daga cikinsu ma Bature ne. Wani mutum
ne da ke zaune a bayan Baturen, yake ta magana a
waya da karfi, shi ne Baturen ya kasa daurewa, ya shiga damuwa sosai,
ya yi korafi. Shi kuma mai
waya sai ya harzuka, ya maida masa martani mai
kaushi, sai suka fara fada. Kafin ka ce kwabo, sai
fadan ya girma har da zage-zagen juna, kowa na
nuna cewa shi ke da gaskiya. Baturen ya roki
ma'aikacin jirgin da ya sanya baki amma hakan ba ta samu ba. Haka suka
ci gaba da cacar bakinsu,
har suna cewa za su dambace, da zarar sun sauka
daga jirgin. Duk dai a cikin jirgin nan, wasu fasinjoji biyu,
daya dattijo, daya kuma budurwa ce, su ma sun yi
nasu wasan kwaikwayon. Dattijon ne yake ta buga
kwamfutarsa (laptop) abinsa, sai ita kuma matar ta
yi korafin cewa gwiwar hannunsa na tunkurinta.
Shi kuma mutumin ya yi biris da ita. Haka abin ya ci gaba, ba a samu
maslaha ba sai da matar ta canja
wurin zama. Babu shakka akwai darussa daga abubuwan
nan da suka faru. Wani babban darasi daya a nan
shi ne, a lokacin da mutum ke neman kare
hakkinsa, yana da kyau ya yi la'akari da hakkin
sauran mutane. Idan na kalli wadannan al'amura
da suka faru a jirgi kuma na duba dalilin da ya sanya aka gayyace ni
zuwa Burkina Faso domin a
karrama ni, sai na fahimta da cewa a rayuwa muna
bukatar mu kasance masu fahimtar juna, mu daraja
ra'ayin juna a mu'amala, mu daraja al'adu da
ra'ayoyin juna kuma mu yi iyaka kokarinmu wajen
wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umma. Dokta Bukar Usman,
marubuci ne kuma
tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban

MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU

MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU Tare da Dokta
Balbasatu Ibrahim (Mrs)
Tun da Allah ya halicci duniya ya jarabi dan adam
da abubuwa guda uku. Wadannan abubuwa kuwa
su ne yare, dukiya, da jinsi. Har yau da muke raye wadannan abubuwa na
ci gaba da ci wa Dan adam
tuwo a kwarya. Dalili kuwa shi ne a duk sanda aka
ce wannan shi ne yaren mutum, to zai yi kokarin
ganin cewa martaba da kwarjinin wannan yaren
nasa sun fi na kowa. Alal misali ja-in-jar da aka yi ta
yi tsakanin Turawa da bakar fata a kasar Afrika ta Kudu a shekarun
baya da kuma kisan gillar da 'yan
kabilar Hutu suka yi wa 'yan kabilan Tutsi a kasar
Ruwanda a shekara 1989, haka kuma rikicin da
ake ciki yin a halin yanzu tsakanin Larabawa da
bakar fata a Darfur ta kasar Sudan sun kasance
misalai na irin yadda yare ke tayar da takaddama tsakanin mutane.
Ita ma dukiya ko mulki kan haifar da zalunci da
danniya tsakanin masu hannu da shuni da
talakawa a cikin al'umma. Idan muka dubi irin
tsare-tsaren siyasar da aka yi ta yi a kasashen Turai,
kamar tsarin jari-hujja da na gurguzu da kuma na dimukradiyya da ake
ikirari a yanzu, sai mu ga har
yanzu ba su hutar da talakan ba, sai kara tsotse shi
ake yi, ana kara wa masu karfi, karfi.
Matsala ta uku kuwa ita ce wariyar jinsi, wadda
Jennifer (1985) ta yi bayanni cewa "ta wanzu ne a
sanadiyar ra'ayi ko akidar nan ta cewa "akwai bambancin fifiko
tsakanin namiji da mace a cikin
al'umma". Wannan matsalar ita ce take tashe a halin
yanzu a ko'ina cikin duniya. Tashenta kuwa ya
hada da fagen siyasa da na tattalin arziki da na
yanayin zamantakewa da fasaha da ilmi da sauran
su. A takaice babu bangaren rayuwar da matsalar wariyar jinsi ba ta
kutsa kai ba.
Shigowar wannan matsala ta haifar da ka-ce-na-ce
tsakanin manazarta ciki kuwa har da na adabi.
Ganin cewa bincikena ya shafi harkar bambancin
da ake iya samu tsakanin mace da namiji ta
bangaren rubuce-rubuce ko kuma adabi, na ya dace na soma da fahimtar
yadda wannan
takaddama ta samo asali da yadda take taimakawa
wajen ginawa da raya harkar nazarin ayyukan
mata.
Daga 'yan karance-karancen da na yi, sai na fahimci
cewa duk da cewa ana ta hayagaga kan wannan fage na wariyar jinsin ba
a cika aza tunanin fagen
bisa tafarkin da ya dace ba. Wannan na daga cikin
abin ya shiga cikin zuciyata a lokacin da na soma
tunanin wannan bincike. Shi ya sa ma na na ce a
zuciyata wai me zai hana in dauki fanni daya daga
cikin abubuwan da suka shafi mata in gudanar da zuzzurfan bincike a
kan sa, ta yadda ni ma zan iya
bada gudunmuwa game da irin gudunmuwar da
matan Hausawa ke bayarwa ta fuskar adabi.
Sai dai kafin na shiga cikin gonar aikin nawa ya
kamata mu san cewa wannan hayaniya ta wariyar
jinsi ba sabuwar aba ba ce, ta dade da kutso kai a tsakanin al'umma.
Wasu masana na ganin ewa ta
taso ne tun a wajajen shekarar 1960 har zuwa
shekara 1975 lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta
bullo da shirinta mai take "Shekarar Mata" da na
"Shekarun Mata"a shekarar 1985 aka yi taron
Majalisar na Nairobi, sannan aka yi babban taro wanda yake shi ne na
hudu irinsa da aka taba yi a
kan mata duk duniya, a birnin Beijing na kasar Sin.
Wannan taro an yi masa lakabi da " Taron
Beinjing" (Beinjing Conference), wanda shi a
shekarar 1995 aka gudanar da shi. Wannan taro ya
tattara mahalarta daga ko'ina cikin duniya, ya kuma yanke shawara a
kan sha'anin daidaita jinsi
na in-ba-ka-yi ba-ni wuri. Wato tun daga wannan
taro ne maganar daidaita jinsi take a bakin
kowa;'yan jarida ne ko masana ko manazarta ko
marubuta.
Kafin in ci gaba, na ga ya dace a san menene jinsi da kuma asalin ita
kanta matsalar a da, da kuma
yanzu a cikin al'ummomi daban-daban.
Jinsi kamar yadda aka sani shi ne bambancin da ke
tsakanin namiji da mace a halicce. Wanda kuma ya
shafi tsarin rayuwarsu ta zahiri da badini. Haka
kuma wadannan bambance-bambancen na canzawa da canjin zamani da rayuwar yau da
kullum, Graddol (1993) daga Kassam (1996).
Kodayake wasu masana suna ganin ma'anar jinsi
ba ta tsaya nan ba kawai, alal misali a ganin De
Beauvair (1973:301) "jinsi abu ne wanda mutum
ke iya zabar wa kansa". Ita a ganinta irin rayuwar da mutum ya zabar
wa kansa ita ce take nuna
jinsinsa, ba wai yadda aka halicce shi ba. Namiji na
iya daukar rayuwa irin ta mata, haka kuma mace na
iya zabar rayuwa irin ta maza, ko da kuwa al'umma
ta kyamaci wannan abu.
Haka su kuma Butler (1986.36)da Zimmerman (1991: 13-15) cewa suka yi
al'adu da dabi'un
mutum ko na al'ummarsa, su ne ke da alhakin
bayyana jinsinsa da kuma matsayinsa. Ita kuwa
Riley (1997; 2-6) tana ganin ma'anar jinsi ta wuce
bambanci halitta kawai, ta hada da bambace-
bambancen da ake samu ta bangaren abubuwan da al'umma ke shatawa a
al'adance a kan yadda ya
kamata mata ko maza su kasance. Haka kuma
wadannan ka'idojin sun shafi kowane bangare na
rayuwa, kamar yanayin zamantakewa na yau da
kullun da tattalin arziki da siyasa da neman ilmi da
makamantan su. Har wa yau kuma wadannan tsare-tsare na al'ada su ne
suke haifar da matsalar
daukakar wani jinsi a kan wani ko danniyar da ake
yi wa jinsin mata a cikin wata al'umma. Haka kuma
ana bayyana jinsi a matsayin tsare-tsaren al`umma
a kan da`bi`u da ayyuka da matsayin da ake ganin
ya dace da maza da wadanda suka fi dacewa da mata.
A fahimtata ana iya gwama wadannan ra'ayoyin na
masana a kan ma'anar "jinsi" a tayar da ma'ana
daya kamar haka, mai nufin bambancin halitta
tsakanin mace da maniji da kuma dukkan
sakamakon da wannan zai haifar ta fuskar rayuwar wadannan halitta guda
biyu a doron kasa ta fuskar
wadansu al'adu da ake shatawa ko gindayawa
domin a cimma wadansu manufofi na siyasa ko
zamantakewa.Bisa irin wannan tunani ne za mu
fahimci cewa wariya ko bambancin jinsi y hada
bambancin halitta da kuma bambancin rawar da kowane bangare zai taka
ta fuskar tattalin arziki ko
al'ada ko siyasa da dai duk wata fuska ta rayuwa.
Sai dai wannan bayani bai kasance an yi shi haka
nan sakayau ba, ya samu tubalin gina shi tun da
dadewa, kama daga addini ko siasa ko canjin
rayuwa ta yau da kullum. Saboda haka ya dace mu koma cikin tarihi
domin fahimtar yadda wannan
tunani ya ginu da kuma yadda ake daukar ko
kuma irin matsayin da ake ba wa jinsin mata cikin
al'ummomin daban-daban ta fuskoki daban-daban
.
MATA A ZAMANIN JAHILIYYA Bari mu koma cikin tarihi, mu kuma soma da nan
kusa, musamman wanda ya shafi addinin matan da
za mu yi nazari, wato Musulunci. Za mu ga tun a
zamanin jahiliyyar Larabawa8 ba a dauki mace a
bakin komai ba. Ana ganin an hallice ta kawai
domin ta yi wa maza hidima. Haka kuma ana iya sarrafa ta yadda aka ga
dama. Alal misali, zamanin
jahiliyyar Larabawa sun kasa halitta ga baki daya
zuwa gida uku, kaso na daya su ne mutane, kashi
na biyu kuwa su ba su kai matsayin mutane ba,
amma sun dara dabba, na uku kuwa su ne
dabbobi. Halittar da aka dauka ba ta kai mutum ba, amma ta fi dabba
ita ce mace. Saboda su a wurinsu
mata ba su da kima, ba su da wani zabi a rayuwa
sai yadda aka yi da su. Ana aurar da su yadda aka
ga dama ko kuma a saka su yin karuwanci ko aikin
wahala ba tare da an biya su lada ba. Har ma don
wulakanci gadonsu ake yi kamar dukiya. Wato idan mijin mace ya mutu,
idan yana da wani da
wanda ba nata ba sai ya gaje ta. A nan yana da
damar ya ajiye ta a matsayin matarsa ko baiwa ko
kuma ya sayar da ita. Haka kuma namiji yana da
damar ajiye mace ko nawa yake bukata ba tare da
wata ka'ida ba, saboda irin wulakanci da kaskanci da suka lika wa
mata, har ya kai suna binne
'ya'yansu mata masu rai tun suna jarirai idan ba su
bukata.
A tsohuwar daular Indiya kuwa a al'adar Hindu, an
dauki cewa namiji shi ne ubangijin matarsa (abin
bautarta). Idan ya mutu a tare za a kone gawarsu, alhali tana da rai.
Haka kuma har yanzu mata
mabiya addinin Hindu suna shiga halin kaka- ni-
kayi, idan mazansu sun mutu, sun bar su, domin
ana yi musu kallon "gawa", wato sun mace a
duniya, ba su da sauran jin dadin duniya. Mata da
suka shiga cikin irin wannan yanayi ba su kwalliya, ba su ma ko cin
abinci, mai kyau, ko mai dadi, sai
wanda aka zabar musu. Ba a hulda da su balle a
aure su. Sai dai dangin mijin maza su dinga yi musu
fyade (shige), idan suka ki ba su hadin kai sai a
kore su daga gidan. A halin yanzu mafi yawansu
suna gudun hijira zuwa wuraren ibada irin nasu, inda a can kadai suke
samu dan sauki. Haka kuma
a wancan lokaci a kasar Hindu akan yi matar iyali
wato idan da namiji goma ko kusa da haka a gida,
sai su dauko mace daya a matsayin matarsu su
duka.
Irin wannan ko makamancin haka ya faru a kasar Girkawa, inda aka dauki
mace tamkar dabba. Ana
iya kama ta a yanka kamar yadda ake yanka dabba
duk lokacin aka ga dama a matsayin horo. Misali
idan mace ta kuskura ta haihu ba a lokacin da ya
kamata ta haihu ba, ko ta rinka haihuwar 'ya'ya
mata zalla, to za a yanka ta. Idan kuwa ta rinka haihuwar 'ya'ya maza
kawai, to sai a rinka daukar
ta ana kai wa baye ga shahararrun baraden kasar,
kamar yadda ake kai dabba, wai don ta haihu
'ya'ya su biyo baraden a sami zaruman da za su
rinka yi wa kasa yaki.
A kasar Sin kuwa mace ita ce kasa da kowa wajen daraja, ko wajen cin
abinci ba a ba mata, sai an
tabbatar maza sun koshi. Haka ma waje bada
magani, amma kuma matan ne aka fi tura wa wajen
neman abinci.
A nahiyar Afrika ma haka lamarin ya kasance,
domin a nan ma maza ke jan ragamar al'umma a cikin kowane irin lamari.
Mace kuwa ba ta ma san
kanta ba balle ta sami bakin fada a ji cikin al'umma.
An dauki mata tamkar shanu, sai dai a debe su
zuwa gona ko nemo itace. Saboda raunin da ake
gani ga mata a kasar shi ya sa tun kafin su karbi
kowane addini suna da al'adar aure, wanda suke yi domin mace ta sami
galihu irin na maza wanda ake
ganin idan ba shi, tana iya fadawa cikin garari. Sai
dai wannan galihun da namiji ke ba mace yana da
tsada. Domin kuwa duk ita take aikin wahala,
kamar zuwa gona, nemo itace, dafa abinci, kula da
yara da dabbobi da kuma ayyukan gayya. A kasar Hausa da alama ba ta
canza zane ba, haka
aka dauki mata, har wata karin magana Hausawa
ke yi wanda suke cewa wai "namiji dutse, mace
sakaina", wannan maganar ta kara tabbatar da
matsalar jinsi kamar yadda Babba (1986) ta
bayyana. Kuma wannan ne ya kara dakushe armashin da ake ganin matan
Hausawa na da shi,
domin su ma kan su sun dauka cewa ba su iya yin
komi sai yadda jinsin ya tanada. Irin wannan
tunanin shi ya ne ya jawo koma bayan mata a cikin
al'ummar Hausawa. Haka kuma wannan ne ya sa
Hausawa suka fi kwadayin haihuwa 'ya'ya maza bisa ga mata. Har ya kai
ma aure na iya mutuwa
idan mace ba ta haihuwar 'ya'ya maza, wai babu
magaji.
Ko a addinin da suka yi tashe a duniya an sama irn
wannan tunani. Addinin Kirista na daya daga cikin
su. Domin kuwa a bisa tsarin addinin da kuma littafin da suke bi, cewa
ya yi mace ita ce uwar
zunubi, wadda ta yi dalilin fitar Annabi Adam daga
aljanna. Haka kuwa wannan addinin (na Kirista) ya
hana wa mace 'yanci kai da zarar ta yi aure, ba a
kiranta da sunanta ballantana na mahaifinta sai dai
na miji. A wani taro na Kiristoci da aka taba yi a shekarar 1856 domin
a gano mace 'yar Adam ce
ko dabba, bayan an tattauna sosai an yarda cewa
mace 'yar Adam ce, amma wadda aka halitta domin
ta bauta wa namiji. Haka kuma an sake yin wani
taro a zamanin Daular Romawa domin a gane ko
mace na da ruhi kuma ana iya sanar da ita addini. Haka dai al'amarin
mata ya kasance a mafi yawan
al'ummomin duniya, kafin zuwan addinin
Musulunci. Kuma addinin Musulunci shi ne ya
kwato wa mace "yancinta kamar yadda za mu gani
nan gaba.
MATA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI Addinin musulunci ya 'yantar da mata daga
kukumin da dan Adam ya sa musu tun shekaru
aru-aru da suka gabata. Addinin ne ya ba mata
dama da matsayin daidai da na maza a cikin mafi
yawan al'amurra. Misali a cikin Alkur'ani mai tsarki,
Allah (S.W.T) yana cewa: "Mun halicci mutane daga namiji da mace".(Hujrat
:13)
A wata sura kuma ya ce:
"Wanda ya yi kyakkyawan aiki namji ko mace alhali
shi yana mumuni, to lalle za mu raya shi rayuwa mai
tsarki, kuma za mu saka musu ladarsu da mafi kyau abin da suka kasance
suna aikatawa" (Nahl : 97)
Da kuma inda ya ce:
"Domin Allah ya azabantar da munafukai maza, da
munafikai mata, da mushirikai maza da mushirikai
mata. Ya kuma karbi tubar muminai maza da
muminai mata. Allah kuwa ya kasance mai gafara ne, mai jin kai"(Al-ahzab:73).
Duk wadannan ayoyin suna nuna cewa ubangiji da
kansa bai bambanta mace da namiji ba, domin duk
inda ya ambaci maza sai ya ambaci mata. Haka
kuma a wajen sakayya yana saka wa kowa da abin
da ya aikata ba wani bambanci. Haka kuma Musulunci ya ba mace wasu hakkoki da
aka danne a sakamakon al'adu da kuma zalunci
irin wanda aka saba wa mata tun a zamanin
jahiliyya. Misali a can da mace ba ta da iko a kan
abin da ta mallaka sai dai mijinta. Haka kuma ba ta
gado sai dai a gaje ta, ita kashin kanta da abin da ta mallaka, amma
Allah (S.W.T) ya ce:
"Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfata
(abin da suka nema domin amfanin kan su). Mata
ma suna da rabo daga abin da suka tsirfata.":32).
Game da gado kuma ayar farko da Allah (S.W.T) ya
fara saukarwa cewa ya yi: "Maza suna da rabo daga abin da iyaye biyu da
makusanta dangi suka bari, kuma mata suna da
rabo daga abin da ya karanta daga gare shi ko
kuwa ya yi yawa, a rabo yankakke."(4: 7).
Wannan ayar ta nuna muna cewa mace tana da
hakki gadon iyayenta da mijinta da 'ya'yanta da kuma 'yan uwan
haihuwarta, idan ba su haihu ba.
Bayan wannan kuma Musulunci ya ceto rayuwar
mace, ya ba ta damar rayuwa cikin al'umma tamkar
namiji, domin ya hana a bizne ta da rai. Inda Allah
(S.W.T) ke cewa:
"Kuma idan aka yi wa dayansu albishir da ('ya) mace sai fuskarsa ta yi
murtuk yana cike da
tsananin bakin ciki. Ya buya daga (idon) mutane
saboda mummunan abin da aka yi masa albishir da
shi. Shin zai riki ne a wulakance ko kuma zai binne
shi ne a cikin kasa, Na'am abin da suka hukunta
kam ya munana."(Nahl 58:59). Bagu da kari kuma addinin Musulunci ya ba mace
damar neman ilmi kamar yadda ya ba namiji. Akwai
hadisin Manzo (S.A.W) da ke cewa:
"Neman ilmi wajibi ne a kan kowane musulmi da
musulma. (Bukhari).
Mace ita ce kashin bayan al'umma, idan ta gyaru to al'ummar ta gyaru,
idan kuma ta lalace to al'ummar
za ta lalace."(Hadisi Nisa'i).
Haka kuma, Annabi (S.A.W) ya ce,
"Idan ka ilmantar da mace daya tamkar ka ilmantar
da al'umma ne ga baki daya". (Bukhari)
A nan mun ga Musulunci ya karfafa ilmin mata fiye da na maza domin
ganin cewa mace ita ke kula da
tarbiyar yaro, idan ba ta samu ilmi ba, ba za ta iya
tarbiyartar da 'ya'yanta ba balle su girma su gina
al'umma ta gari.
MATA A WANNAN ZAMANI
Da yake mun ga yadda ake kallon mata a wasu nahiyoyi tun a zamanin
jahiliyya da sauran lokuttan
da suka shige da kuma ceton da Musulunci ya yi wa
mata. Sai kuma mu leka yadda ake kallon su cikin
wannan zamani, musamman daga karni na sha-
tara zuwa na ashirin da daya. Daga abin da wannan
binciken ya samo dangane da matsalolin mata da yadda ake kallon su, a
iya cewa har yau da sauran
rina a kaba. Har yanzu al'adar nan ta daukar mata a
matsayin 'yan baya ga dangi tana nan sake cikin
zukatan al`umma duk kuwa da juyin da Musulunci
ya kawo da kuma canjin zamani. Domin ko a
kasashen Turai masu ikirarin ci gaba da wayewar kai, inda kuma ake ta
hayaniya kan 'yancin mata
har yanzu matsayin mace na mai rauni akan
kowane sha'ani, yana nan. Mata suna fuskantar
matsaloli da dama ta bangaren ilmi da siyasa da
fasaha da aure da aikin gwamnati da sauran su, a
ko'ina cikin duniya. Alal misali idan muka dauki bangaren ilmi wanda
shi ne mabudin arziki na
duniya da lahira, ta hanyarsa ne mutum ke fita
duhun jahilci, ya san addini da sauran al'amurran
rayuwar duniya. Da ilmi ne mutum ke iya samun
babban matsayi a cikin aikin gwamnati. Haka kuma
da ilmi mace za ta san kanta, har ta sami damar bada gudummawa a cikin
al'umma. Amma a mafi
yawan kasashe, musamman masu tasowa, mata ne
a baya, wajen samun ilmi. Misali a wata kididdigar
yawan jama'a da aka gabatar, an gano cewa a
kasashe Sin da Bangaladash yawan mazan da ke
da ilmi ya ribanya na mata sau uku. A Afirka kuwa matan da ke da ilmi
kalilan ne, kuma mafi yawanci
ilmin nasu ba mai zurfi ne ba33, Umar (1990).
A wata kididdiga ta "UNESCO" a shekarar 2000
yawan matan da ke cikin jahilci sai kara hauhawa
yake yi. Mangwat da Abama (1999) sun nuna cewa
a shekarar 1958 yawan mata marasa ilmi ya kai kashi hamsin da takwas
bisa dari, sai kuma kara
hauhawa da ya yi ta yadda a shekarar 1985 inda
yawan mata marasa ilmi ya kai miliyan 133. Har wa
yau wata kididdiga ta "UNESCO" ta karshen karni na
ashirin ta nuna cewa daga cikin yaran da suka
shiga makaranta a Nijeriya, kashi talatin da uku ne mata, sauran duk
maza ne. Saboda matan ko da
sun shiga akan janye su daga baya, saboda wasu
dalilai da masana da manazarta suka sha
bayyanawa.
A Arewacin Nijeriya ma tun kafin da bayan zuwan
turawan mulkin mallaka an maida mata baya a fagen ilmi. Domin ko da
Turawa suka ci Sakkwato
da yaki suka kwace mulki da karfi sun sami mata
masu ilmi da yawa wadanda suka gaji su Nana
Asma'u da 'yanuwanta da kuma takwarorinta,
wadanda suka yi ilmin addinin musulunci, suka
kuma yi rubuce-rubuce cikin harsunan Larabci, Fulfulde da kuma Hausa
don fadakar da al'umma,
ciki har da rubutatatun wakoki. Amma sai Turawa
suka yi biris da sha'anin ilmin mata har sai bayan
lokaci mai tsawo, a farkon karni na 20 da suka
bude makarantar maza a Kano ba su bude ta mata
irinta ba sai a shekarar 1933. Haka kuma Mulkin mallaka ya raunanar da
makarantun allo da ya iske.
Wannan ba karamin ci baya ya janyo wa Arewa ba
domi mata su ne asasin gyaran al'umma da son ci
gaba da samun ilmin addini kamar yadda aka
dauko a karni na 19. Da an yi hakan da alam aka
ba su ilmin zamani a lokacin da ya dace su same shi da Arewa ba ta
tsinci kanta a sahun 'yan baya ga
dangi ba a fagen ilmi da ci gaban al'umma. Daga
baya da aka sami makarantu don mata kuwa sai
aka yi rashin sa'a da cewa mutane na dari-dari da
ilmin boko, saboda addini da akidun wadanda
suka kawo shi. Dangane da wanna ga abin da Babba (1986) ke cewa :
iyaye na hana yaransu
mata karatu, domin kada su rasa miji. Saboda
al'umma, musamman ta Hausawa sun dauki cewa
boko ke sa yarinya ta hinjire wa mijin, saboda za ta
dauki kanta tana da wani matsayi cikin al'umma
tun da tana da ilmi, alhali kuwa a zahiri ba haka abin yake ba. Domin
mata da suka yi ilmi, su ne za a
same su masu tsabta da sanin ya kamata. Ga sanin
addini da kuma iya biyayya ga miji, ta hanyar kula
da shi da 'ya'yansa da kuma kayansa.
Haka kuma Congleton (1988) a cikin wata hira da
aka yi da shi, ya yi bayanin cewa, mutanen Arewacin Nijeria sun fi ba
wa tarbiyar da yaro ke
samu a gida muhimmanci a kan wadda za a ba shi a
makaranta. Har suna ganin cewa ana gurbata wa
yaransu, musamman mata tarbiya idan suka bar su
suka yi zurfi a cikin makaranta. Wanda kuma a dalili
haka maza ba su cika son su auri mata masu ilmi sosai ba. Babban
dalili kuwa bai wuce na akidar
nan ta cewa mace ta bi miji sau da kafa, ko da kuwa
yin haka din zai jawo mata cikas a rayuwarta. Suna
ganin cewa mace mai ilmi ta san hakkinta a kan miji
da kuma san hakkin miji a kan ta, ba za ta yarda a
tauye ta ba a cikin gida kamar dabba, ba kulawa ba wani abin yi.
Azare (2000) cewa ya yi babban dalili da ke sa ana
hana ko janye mata daga makaranta, shi ne rashin
isasshen kudin da za a dauki dawainiyar karatun
duka 'yaya, maza da mata ga baki daya, kuma
gudun lalacewar tarbiyarsu, wadda al'adar al'ummarsu ta tanadar musu.
Amma kuma sai abin
ya zan "an ki cin biri, an ci dila", domin sai a hana su
makaranta amma a tura su wajen kwadago ko
tallace-tallace, inda suke shiga cikin hadurra kala-
kala, kamar yin cikin shege ko kamuwa da cutar
kanjamau . Idan muka dubi matsalar ta fuskar siyasa kuma za
mu ga cewa a wannan fagen maza ne suka yi
kaka-gida, domin a yawanci kasashen duniya ba a
ba mata damar da ta kamance su a sha'anin siyasa
ballantana a ce su kai ga taka rawar gani a cikin
sha'anin mulki, Ashford (1995:17) ta yi bayanin cewa ana dai babatun
dimokuradiyya ne a baki
kawai, amma ayyanawar ba haka take ba. Da kyar
ne mace take kai ga shiga takarar mukamin siyasa.
Idan kuma ta samu shiga din, za ta fuskanci
tarnakin al'ada, wanda ke iya hana al'umma ta zabe
ta. Saboda idan aka dubi siyasar duniya a yau, mata irin su Margaret
Thacher ta Ingila, da Indira Ghandi
ta Indiya, da Komaratonga ta Sirilanka, da Benezir
Bhuto a Pakistan da wasu kalilan kadai ne
wadanda suka taba samun nasarar zama
zababbun shugabanin kasashe, wanda yake idan
aka kwatanta su da maza da suka taba shugabanci ba su kai ko kashi
biyar bisa dari ba. Haka kuma a
mafi yawan kasashe masu tasowa, musamman irin
su Mexico da Brazil da yawancin na nahiyar Afrika,
kujerin da ake ba mata a majilisar dokokin kasa ba
su taka kara sun karya ba. Har ma a kasashen da
suka ci gaba idan aka kwatanta maza da ke rike da mukamin siyasa da na
mata, za a sami bambanci
mai yawan gaske. A Arewanci Najeriya abin ma ya
fi muni, domin al'umma sun dauki cewa mata
karuwai kawai ke yin siyasa.
A lokacin da muka dubi matsalar shugabanci sai a
ga cewa a cikin matan da suka yi ilmi, kalilan ne ke samun yin aikin
gwamnati. Wadanda kuma suka
sami aikin, sukan fuskanci matsaloli ta fuskoki da
yawa. A kasashen duniya da yawa, har da
wadanda suka ci gaba, a kan nuna wa mata
bambanci ta fuskar matsayi ko makami da awoyin
aiki. Haka kuma akan nuna musu bambanci wajen biyan ladar aiki. A
kasar Amurka ga misali, Riley
(1997) ta yi bayanin akan tauye 'yancin mata ta
fuskar mayar da su saniyar ware a fagen siyasa. Ta
kai ga har shata wani tsari aka yi wanda yake
tabbatar da cewa matan da suke aikin gwamnati
ko na manyan kamfuna ba su rika manyan mukamai ba, wanda ya sa
bambanci tsakanin mata
da maza ya dade kafin a kawar da shi a kasar. Ta
kara da cewa ta kai ma ga albashin namiji ya fi na
mace yawa ko da kuwa aikinsu iri daya ne.
Wannan bambancin kuma ya kasance har a
kasashen Ingila da Kanada da kuma Siriya. Wannan akidar ba a can kadai
ta tsaya ba, ko a nahiyar
Afrika da kasar Nijeriya, har ma Arewa, mata sun
kasance a matsayin saniyar ware a fagen siyasa,
domin matan Arewa ba su fara ko jefa kuri`a ba sai
1976, ballantana su shiga takara a zabe su,
Dityavyar(1998;145). Matan da ke aiki ma ana yi musu kallon wasu
tsiraru ne, wadanda suka fi
karfin mazajensu a cikin al'umma. A wajen aikin
kuwa akwai mukaman da ake ganin cewa mata ba
su isa su rika su ba sai dai maza.
A fagen tattalin arziki mata na bakin kokarinsu,
domin kamar yadda Osunde and Imorayi (1999) suka bayyana, mata na yin
ayyuka da dama
wadanda ke taimaka wa wajen habaka arzikin
al'umma. Inda suka bada misalin cewa, mata na
noma, kiwo da kuma sana'oin hannu irin su saka,
har ma da fatauci, suna kuma yin ayyukan gayya.
Ita ma Riley (1997) ta yi bayani cewa A kasar Sin 'ya'ya mata ne ake
turawa gona ko wajen ga aiki,
domin su nemo wa iyaye da sauran 'yan uwansa
da suka hada da maza abin masarufi. Haka kuma
sanannen abu ne cewa a kasar Indiya mace ke
neman kudin biyan sadakin aurenta. A nahiyar
Afrika, har a arewacin Nijeriya mata na kokarin neman na kai. Inda
suke yin duk abubuwan da
aka ambata a sama, har ma da kari, domin sukan yi
`yan sana`oin hannu, suna dora wa 'yayansu
tallace-tallace, su kuma suna can suna yin wasu
sana'a wadanda suka hada har da kitso, dinki, da
sayar da abinci a wurare daban-daban. Mack (1992) ta yi bayanin har da
cinikin bayi matan
kasar Hausa suna yi a zamani da ake yin sa. Amma
abin mamaki shi ne duk da wannan gagarumar
gudumawar da mata ke bayarwa ta fannin tattalin
arziki, al'umma na ci gaba da yi musu kallon cima-
kwance wadanda komi sai an nemo an ba su. A yanayin zamantakewa na yau
da kullum, mata su
ne kashin bayan zaman lafiya da mu'amala mai
kyau cikin al'umma. Domin su ne aka fi sani da
kokarin sada zumunta da hulda da makwabta da
tarbiyar yara da kuma yin 'yan sana'o'in hannu,
masu taimakawa wajen gudanar da rayuwa cikin sauki. Haka kuma tarihi
ya nuna mata suna da
tausayi da kokari wajen kula da marasa lafiya,
musamman a zamanin da ake yawan yake-yake.
Ko a nan kusa lokacin jihadin su Shehu Usman
Danfodiyo, Boyd (1989) ta yi bayani akan irin
gudumawar da su Nana Asma'u da sauran matan zamaninta suka bayar, ta
hanyar kula da wadanda
aka ji wa rauni da kuma bada abinci da daukar
kaya da kula da yara lokacin yaki. A wannan
zamani da ake ciki mata na gudanar da kusan duk
abin da maza ke yi a kowane bangare na rayuwa
idan dai an ba su dama. A harkar aure mata suna samun matsaloli a ko ina
ciki duniya. Sai dai bayanin da zan yi a nan shi ne a
kan matan arewacin Najeriya, inda har yanzu a kan
yi wa yarinya aure ba tare da an nemi yardar ta ba,
kuma a nemi ta zauna da mijin nan bisa ga ladabi
da biyayya ko da kuwa ba ta son sa. A wani bayani na Callway and
Greevey (1994:84) cewa suka yi:
"A kasar Hausa ana yi wa yarinya auren wuri, kuma
zaba mata mijin ake yi (ba tare da yardarta ba)
kuma dole ta zauna da shi, ta bi shi sau da kafa, ta
kuma zauna tare da kishiyoyi, ko tana so, ko ba ta
so". Wannan auren da ake yi musu, na wuri yakan jawo
musu matsaloli iri-iri, musamman idan suka yi
saurin daukar ciki idan an zo wurin haihuwa, mafi
yawa yaran da ba su yi kwarin haihuwa ba, sukan
sami matsalar yoyon fitsari. Inda kuma daga
karshen mazan ke juya musu baya, sai dai iyayensu su yi ta wahala da
su. Wannan kuma ba a kasar
Hausa kawai yake faruwa ba, yana faruwa a
yawanci kasashe masu tasowa. Misali a kasar
Somaliya, musamman sai da wata baturiya ta kafa
asibitin taimakon irin wadannan mata da ke samun
matsalar yankan gishiri, kuma al'umma ta juya musu baya48.
MATA DA ADABIN BAKA
Shahararrun masana da yawa wadanda suka yi
rubuce-rubuce a tarihi da al'adun kasar Hausa,
kamar Clapperton da Lander (1829), da Jeroma
(1970,1972,1973), da Joseph (1973), da Palmer (1978) da Mark (1985) da
Boyd (1989) da Hill
(1972), da sauransu, duk sun yi bayanin cewa
kafin zuwan baki a kasar Hausa, matan Hausawa
sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen
ciyar da kasar da al'ummarsu gaba. Irin wannan
rawa tasu ta shafi bangaren tattalin arziki da siyasa, tarbiya da
fasaha da kuma ciyar da harshen Hausa
gaba, ta hanyar tatsuniyoyi da labarai da kacici-
kacici da karin magana da salon magana da badda-
bami da sauran su. Wadannan suna cikin
abubuwan da Fafunwa (1982) ya kira makarantun
farko na 'yan Afirika kafin su sami ilmin karatu da rubutu. Amma kuma
idan aka tashi bayani game da
irin wannan ci gaba sai ya zan gudummuwar maza
kadai ke fice.
Haka dai al'amarin mata ya kasance rayuwarsu na
cikin tawaya da rashin walwala wanda ba kome ya
hassada masu shi ba sai al'adu, wadanda ke ci da yawun addinai da
siyasa domin biyan bukatun
wani jinsin da ba mace ba. Wadanna al'adun sun yi
tasiri sosai cikin al'ummomi musamman a nahiyar
Afirika yadda har su ma matan an dasa wannan
akida ta namiji dutse, mace sakaina, har ya zan ba
su iya kalubalantar matsalolin da ke tattare da su, Remi(2003). Sai a
'yan shekarun baya –bayan nan
da aka sami mata kalilian masu matsawa, suka
tunkari wannan matsalar ta danniyar jinsin mata, ta
hanyoyi daban –daban.
MATA DA RUBUTACCEN ADABIN HAUSA
Daga abin da muka ga a sama mun fahimci abubuwa da dama. Da farko dai
matsalar nazari da
sharhi game da mata ba ta wuce irin mizanin da aka
dora batun ba, ko a adinance ko siyasance ko
kuma tafuskar ilmi da zamantakewa. Na biyu kuwa
shi ne duk da cewa an yarda mata na taka rawa a
gnuwar rayuwa ta kowace irin fuska, da alama akwai wadansu katangai da
ake jefawa a gabansu
domin kada su kai ga gaci.Na uku ga alama, yadda
ake kallon mata a kowane fage da irin rawar da
suke takawa da matsalolin da suke fuskanta su ne
suka yi katutu ko da a fagen nazarin ayyukan
adabin Hausawa. An fadi haka ne ganin cewa mata kamar
takwarorinsu maza su ma sun samu ilmin karatu da
rubutu bayan zuwan addinin Musulunci. Amma
duk da cewa Musulunci ya wajabta neman ilmi,
musamman na addini a kan kowane musulmi,
namiji ko mace, tarihi ya nuna cewa a kasar Hausa al'umma ta yi watsi
da sha'anin ilmin mata, wanda
shi ne ya haifar da barin mata cikin jahilci. Wannan
ya sa mata suka kasance tamkar dabbobi cikin
duhun jahilci. Abin da al'umma ta tanadar musu shi
ne aikin zaman gida. Da yake kuma rubutaccen
adabi ba ya samuwa sai da karatu da rubutu, dole rawar mata a wannan
fage ta takaita.
Rawa ba ta canza ba sosai, sai lokacin jihadin su
Shehu Danfodiyo da magoya bayansa, a karni na
19, Inda Shehu ya lura da wannan matsalar ya
kuma tashi tsaye domin kawar da ita. Ga abin da
Shehu ke cewa game da matan kasar Hausa a wancan lokaci:
Maza sun dauki matansu tamkar wasu rubabbun
kayan gida, wadanda aka gama amfani da su, sai
yar a shara. Kash wannan hali ya saba wa ka'ida.
Yaya za su bar su cikin duhun kai, bayan ga shi
kuwa suna ba dalibansu sani a waje." Shehu ya ci gaba da cewa fadar
nan ta Hausawa
mai cewa "aljannar mace tana karkashin kafafun
mijinta", ba ta da wani tasiri sai idan mace ta bauta
wa Allah yadda ya kamata. Bauta wa Allah ba ta
inganta sai da ilmin addinin Musulunci.
Wannan ne ya malamai da magidanta da 'yan uwan Shehu da kuma `ya`yansu
duk sun karbi kiran da
ya yi. Nan da nan sai makarantu suka budu a
gidajen mutanen da sassa a can cikin gidaje wurin
mata. Mafi yawan matan malamai suka zama
malamai su kansu. Alal misali matan Shehu da
'yanyansa da sarakunansa, kamar su Hadiza, Asma'u, 'yayan Shehu da
A'ishatu matar Aliyu Jedo,
da Maryam da Fatima, matan Sarkin Musulmi Bello
da Maryam 'Yar Shehu duk sun bude azuzuwan
karatun allo a cikin gidajen mazansu. Idan an
manta da rawar da wadannan suka taka to da kyar
ne za mu manta da rawar da Nana Asma'u ta taka. Dubi Boyd (1989),
wadda ta kawo bayanin `yan
taru, wadanda suka samo asali daga shirin ba mata
ilmi na Nana Asma'u. Haka kuma duk wadannan
mata sun yi rubuce-rubuce da suka hada har da
wakoki. A kan abubuwan da suka shafi rayuwar
al'umma dangane da addinin musulunci, Boyd (1989) ta yi bayanin cewa
Nana Asma'u kadai ta
rubuta wakoki da dama, amma kuma duk
wadannan ayyukan da mata suka yi, saboda su
mata ne, sai wannan ya kasance musu tarnaki
wajen yin fice da kuma samun shiga cikin
mashahuran marubuta. Ko Nana Asma'u idan ba domin bincike-binciken
Boyd da wasu ba da har
yanzu mutane da dama ba san irin gudumawar da
ta bayar ba. Domin ita Boyd ce ta yi kokarin binciko
wadannan ayyukan ta kuma buga cikin littattafai
da mujallu daban-daban. Amma kuma har yanzu
mutane kalilan ne a cikin wannan al`umma suka san ayyukanta. Wannan
dabi'ar ta rashin ba aiki
mata muhimmaci ba wai a ciki al'ummar Hausawa
kadai take ba, har ma da sauran al'ummomin
duniya. Misali kasar Ingila, tun a shekarar 1866
wata marubuciya mai suna Anne Evans ta yi rubutu
a kan matsalar mata, ta ce 'mace ba ta da zabi… sai dai ta dogara ga
duk abin da ta samu ko ya same
ta. Ta kuma tsaya iya dan matsayinta". Babban abin
takaici a nan shi ne ita wannan mata sai da ta lika
wa kanta sunan namiji wato "George Elliant' kafin
rubutunta ya sami karbuwa ga al'umma. Haka
kuma idan muka koma ga tarihi, za mu ga cewa daga cikin shahararrun
marubuta da suka yi suna a
duniya, wadanda aka yi ta nazarce-nazarce a kan
ayyukansu, da kyar ne idan za a sami mace. Misali
mun ga an yayata su Plato da Aristottle da
Shakesphere da Milton da Chaucer da Samuel
Johnson da T.S. Elliot da sauran su. Amma ba a damu da shahararrun
marubuta mata ba irin su
Austen da Broute, Woolf da Hurston da sauran su a
duniyar Turai da Amurka, ba domin komi ba sai
don suna mata.
Idan har hakan ya kasance dangane da su Nana
Asma'u da dangoginta a zamanin masu jihadi, ba abin mamaki ba ne idan
ba a ba mabiyansu wani
muhimmanci ba, duk kuwa da cewa an samar da
mata mashahurai da suka tashe a wannan fage.
Faga cikin irin wadannann an ci gaba da samun
mata da suka ci gaba da yin rubuce-rubuce cikin
Hausa da sauran harsunan Arewacin Nijeriya,musamman a fannin rubutattun wakoki
domin su ne suka fi saukin hardacewa ga matan da
ke daukar karatu da kuma dadin saurare ga
sauran jama'a. Amma saboda matsalar wariyar jinsi
da tarnakin al'adu wanda ya tauye mata ga samun
shawarwari daga kwararru game da rubuce- rubucen da kuma gudun
korafe-korafe a cikin
al'umma, sai aka kara samun dakushe aikace-
aikacen mata na rubutaccen adabin Hausa. Idan
kuma aka dubi bangaren maza ba haka abin yake
ba.
A halin yanzu ambaton Akilu Aliyu da Aliyu Namangi ko Abubakar Imam ko
Yusufu Kantu ko
Alkali Haliru Wurno ko Bello Kagara da dimbin
mazan da suka yi rubuce-rubucen cikin adabin
Hausa a shekarun baya, sai ka taras an san su. To
amma matan fa? Kodayake akwai su ba a ba su
damar fitowa su yayata kansu ba, ba a kuma taimaka aka yayata su ba.
Ko 'yan wadanda suka yi
fice, ba da yawun bakin maza suka yi shi ba. Domin
mata ne 'yan uwansu, suka yi kokarin da suka fito
da su. Wato mata irin su Baturiya Beverly Mark da ta
yi kokarin buga littafin "Alkalami a Hannun
Mata" (1983),wanda yake dauke da rubutattun wakoki na wasu mata a
Kano, wato Hajiya Hauwa
Gwaram da Hajiya 'Yar Shehu. Sai kuma Gambo U.
Babba, wadda ta rubuta kundin digirin farko a
Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, a kan wata malama
marubuciya a1986, wato Hajiya Hasana Sufi, sauran
matan da aka ji sunansu kuwa, su ne suka yi kokarin rubuta labaransu,
suka kuma buga abin su
da kan su. Wato irin Hafsat Abdulwaheed (1980)
da Yaya Hasana Umar (1980) da kuma marubutan
zamani, wato irin su Bilkisu Funtuwa da Balaraba
Ramat da Zuwaira Isah da sauran su. Inda kila za a
ga wannan aiki ya kankama shi ne littafin Ibrahim Yaro Yahaya
(1988),wato Hausa a Rubuce, shi ma
rubuce-rubucen maza ya fi yawa, kila saboda
rubuce-rubucen mazan ne ya fi yawa, ga abin da
yake cewa game da wannan batu:
Mata su ma ba a bar su a baya ba wajen ciyar da ilmi
gaba ta yin rubuce-rubuce da ajami ko boko, a buga a littattafai.
Harsashin da nana Asma'u 'yar
Shehu da Maryama 'yar Shehu suka aza a kan ilmin
mata ya samu kafuwa sosai, har ma ana ta dora gini
a kansa tun daga wancan karni har zuwa wannan
zamani namu, domin ana samun mata a ko'ina a
kasar Hausa suna neman ilmi a makarantun allo da na Islamiyya da ilmin
zamani ma. Wasu daga
cikinsu in an yi musu aure, suna gudanar da
azuzuwan koyarwa a gidajen mazajensu.
Akwai mata da dama irin wadanda Yahaya (1988)
ya ambata, wadanda suka nemi ilmi har suka zama
malamai, kuma marubuta cikin ajami da boko. Haka kuma rubuce-rubucen
nasu sun tabo fannoni da
dama, sai dai saboda kasancewar mafi yawansa
matan aure ne ko kuma 'yan matan da ke
karkashin kulawar iyayensu ba su da damar zuwa
wasu wurare don nuna fasaharsu, kamar yadda
maza ke samun yi, ya sa ba a san da zaman mafi yawansu ba, wannan
matsalar ta fi shafuwar
marubuta wakoki, kila shi ya sa mazan suka fi
tashe fiye da matan. Lallai akwai marubuta mata
kamar yadda aka sha fada, amma ga nawa tunanin
ba wai fadar cewa akwai matan ne kawai da ke
rubuce-rubucen ajami ke da muhimmanci ba, a'a, a ga ayyukan nasu a
zahiri. Wannan shi ne kashin
bayan wannan tunani, a nemo matan marubuta
wakoki da kagaggun labarai da kuma wasan
kwaikwayo, domin kafa hujja ta fasalce-fasalcen
ayyukan adabi na mata a kasar Hausa. Ta haka ne
za a ga irin rawar da suka ko suke ko za su bayarwa a raya kasa da al'umma.