0
TSANGAYAR ADABIN HAUSA TA GABATAR DA TARON KARAWA JUNA SANI TSANGAYAR ADABIN HAUSA TA GABATAR DA TARON KARAWA JUNA SANI

Daga Danladi Haruna A ranar Asabar 20 ga Disamba, 2014 , kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa ma...

0
TARON TSANGAYAR ADABIN HAUSA TARON TSANGAYAR ADABIN HAUSA

A ranar Asabar 20 ga Disamba, 2014 , kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa maza da mata su ...

0
TATTAUNAWA DA MAWAKIN ZAMANI AMINU ALAN WAKA TATTAUNAWA DA MAWAKIN ZAMANI AMINU ALAN WAKA

Daga  Rabiu Muhammad Abu Hidaya Mahangar Arewa: da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihinka. Aminu Ala: To da farko sunana Aminudden Ladan...

1
MATSALAR BARA A KASAR HAUSA MATSALAR BARA A KASAR HAUSA

Daga  Rabiu Muhammad Abu Hidaya MA'ANAR KALMAR BARA. Idan aka ce bara a kalmar hausa. To ana nufin wani mutum wanda bashi da karfi, wand...

0
KURMAN SO KURMAN SO

Daga  Rabiu Muhammad Abu Hidaya Yanayi mai dadi, a lokacin yammaci, an yi ruwa an dauke kalar sararin samaniya ya yi fari kal gwanin ban sha...

0
NADAMA NADAMA

Na kasance yar gidan masu akwai domin mahaifina mutumne mai tarin dukiya na yi aure cikin jin dadi da walwala duk da cewa bani kadai ba ce a...

0
ZIYARARMU GARIN TANHIYA JAMHURIYAR NIJAR ZIYARARMU GARIN TANHIYA JAMHURIYAR NIJAR

Ranar Alhamis 13 ga watan maris 2014 ina zauna a gida ina dan Nazari sai na ji wayata ta soma ruri alamun a kawo mata agaji cikin hanzari na...

0
TAFIYA TA MASALLACIN IDI TAFIYA TA MASALLACIN IDI

KARFANCI RANAR SALLAH Firgigit na farka sakamakon jin karar hayaniyar yara a tsakar gida kallona na farko kan agogo na kai shi karfe Takwas ...

0
BIKIN RANAR MAWAKAN HAUSA TA BANA YA SAMU TAGOMASHI. BIKIN RANAR MAWAKAN HAUSA TA BANA YA SAMU TAGOMASHI.

Daga  Rabiu Muhammad Abu Hidaya A ranar larabar karshen shekarar 2014 ne mawakan hausa suka fara bikin ranar mawakan hausa na Afr...

TSANGAYAR ADABIN HAUSA TA GABATAR DA TARON KARAWA JUNA SANI

Daga
A ranar Asabar 20 ga Disamba, 2014 , kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa maza da mata su talatin da biyar, inda aka nuna musu hanyoyin dabarun kasuwancin zamani da ilmin na'ura mai kwakwalwa da kuma kalubalen da ke cikin gyaran wayar salula.

Sannan a karshen taron kungiyar ta karrama wasu fitattun mutane da ke bayar da gudunmawa a fannonin rayuwa dabam - dabam. Wadanda suka hada da:

- Dr. Abdulkadir Koguna, Sardaunan Agadez

- Ado Ahmad Gidan Dabino MON

- Aminu Alan Waka

-Alhaji Aliyu Dangida

-Hakimin Tarauni Alhaji Ado Kurawa

-Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Injiniya Mukhtar Umar Yarima

-Metron Salamatu Mu'azu

- Hajiya Bilkisu Yusuf Ali

- Hajiya Lami Sumayya Murtala

An gabatar da takardu ga mahalarta taron. Inda Malam Nasiru Wada Khalil, a takardarsa mai taken 'Matakan kafa kasuwanci da samun nasara' ya zayyano hanyoyin da ake bi a samu nasara a kasuwancin zamani. Ya nuna muhimmancin bincike da jajircewa da tunanin kawo wani abu sabo a matsayin hanyoyin kaiwa ga nasara.

Injiniya Yunusa Sha'aibu, a tasa takardar mai taken Kalubalen da ke cikin sana'ar gyaran waya' ya lissafo irin kalubalen da ke cikin sana'ar gyaran waya da irin fadi tashin da masu sana'ar ke shiga a yau da gobe. Sannan ya bukaci gwamnati ta samar da wani tallafi na musamman ga matasa domin samun ingantaccen ilmin gyaran wayar ta salula.

Takardar da Danladi Haruna ya gabatar mai taken, 'Ilimin kwamfuta a takaice', ya bayyana yadda na'urar kwamfuta ke aiki da abubuwan da ta kunsa da kuma takaitaccen bayani akan fasahar intanet. A karshe ya fadi cewa, ilmin kwamfuta ya zama wajibi ga kowa da kowa a wannan zamani.

Taron wanda aka gudanar a birnin Kano inda mahalarta suka nuna jin dadinsu game da ayyukan wannan kungiya. Da dama daga cikinsu, sun bukaci a sake samun wata rana domin a maimaita musu irin wannnan taron.

Shugaban kungiyar, Rabiu Muhammad Abu Hidaya, ya godewa Allah da ya ba su ikon gudanar da irin wannan taron a karo na uku. Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar za ta sake lalubo wani bangare daga al'ummar hausawa domin ta basu horo na musamman bisa al'amuran ci gaban rayuwa.

Malam Farouk Lawan Da'u wanda shine gabatarwa kuma sakataren tsare-tsare na kungiya shima ya nuna jin dadinsa da godiya ga Allah da ya basu damar yin wannan taro na lafiya ya kuma bukaci gwamnati da ta dinga shiga sha'anin kungiyoyi irin wadannan domin tallafa musu duba da cewa suna aiki tukuru wajen wayarwa da al'umma kai game da abinda ya shige musu duhu.

A jawabinsa na godiya kuwa a madadin wadanda aka karrama, Sardaunan Agadaz Dk Abdulkadir Koguna, ya yabawa wannan kungiya da ke hobbasa wajen bullo da abubuwan ci gaba a koda yaushe, sannan ya yi alkawarin ba da hadin kansa a dukkan abin da kungiyar ta sa a gaba.

An kammala taro da misalin karfe biyar na yamma.

TARON TSANGAYAR ADABIN HAUSA



A ranar Asabar 20 ga Disamba, 2014 , kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa maza da mata su talatin da biyar, inda aka nuna musu hanyoyin dabarun kasuwancin zamani da ilmin na'ura mai kwakwalwa da kuma kalubalen da ke cikin gyaran wayar salula.

Sannan a karshen taron kungiyar ta karrama wasu fitattun mutane da ke bayar da gudunmawa a fannonin rayuwa dabam - dabam. Wadanda suka hada da:

- Dr. Abdulkadir Koguna, Sardaunan Agadez

- Ado Ahmad Gidan Dabino MON

- Aminu Alan Waka

-Alhaji Aliyu Dangida

-Hakimin Tarauni Alhaji Ado Kurawa

-Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Injiniya Mukhtar Umar Yarima

-Metron Salamatu Mu'azu

- Hajiya Bilkisu Yusuf Ali

- Hajiya Lami Sumayya Murtala

An gabatar da takardu ga mahalarta taron. Inda Malam Nasiru Wada Khalil, a takardarsa mai taken 'Matakan kafa kasuwanci da samun nasara' ya zayyano hanyoyin da ake bi a samu nasara a kasuwancin zamani. Ya nuna muhimmancin bincike da jajircewa da tunanin kawo wani abu sabo a matsayin hanyoyin kaiwa ga nasara.

Injiniya Yunusa Sha'aibu, a tasa takardar mai taken Kalubalen da ke cikin sana'ar gyaran waya' ya lissafo irin kalubalen da ke cikin sana'ar gyaran waya da irin fadi tashin da masu sana'ar ke shiga a yau da gobe. Sannan ya bukaci gwamnati ta samar da wani tallafi na musamman ga matasa domin samun ingantaccen ilmin gyaran wayar ta salula.

Takardar da Danladi Haruna ya gabatar mai taken, 'Ilimin kwamfuta a takaice', ya bayyana yadda na'urar kwamfuta ke aiki da abubuwan da ta kunsa da kuma takaitaccen bayani akan fasahar intanet. A karshe ya fadi cewa, ilmin kwamfuta ya zama wajibi ga kowa da kowa a wannan zamani.

Taron wanda aka gudanar a birnin Kano inda mahalarta suka nuna jin dadinsu game da ayyukan wannan kungiya. Da dama daga cikinsu, sun bukaci a sake samun wata rana domin a maimaita musu irin wannnan taron.

Shugaban kungiyar, Rabiu Muhammad Abu Hidaya, ya godewa Allah da ya ba su ikon gudanar da irin wannan taron a karo na uku. Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar za ta sake lalubo wani bangare daga al'ummar hausawa domin ta basu horo na musamman bisa al'amuran ci gaban rayuwa.

Malam Farouk Lawan Da'u wanda shine gabatarwa kuma sakataren tsare-tsare na kungiya shima ya nuna jin dadinsa da godiya ga Allah da ya basu damar yin wannan taro na lafiya ya kuma bukaci gwamnati da ta dinga shiga sha'anin kungiyoyi irin wadannan domin tallafa musu duba da cewa suna aiki tukuru wajen wayarwa da al'umma kai game da abinda ya shige musu duhu.

A jawabinsa na godiya kuwa a madadin wadanda aka karrama, Sardaunan Agadaz Dk Abdulkadir Koguna, ya yabawa wannan kungiya da ke hobbasa wajen bullo da abubuwan ci gaba a koda yaushe, sannan ya yi alkawarin ba da hadin kansa a dukkan abin da kungiyar ta sa a gaba.

An kammala taro da misalin karfe biyar na yamma.

TATTAUNAWA DA MAWAKIN ZAMANI AMINU ALAN WAKA

Daga 

Mahangar Arewa: da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihinka.

Aminu Ala: To da farko sunana Aminudden Ladan Abubukar wanda aka fi sani da Alan waka,

an haife ni a shekarar 1974 a unguwar Yakasai cikin birnin kano.

Na yi karatun zamani dana Addini dai-dai gwargwado.

Na yi karatun firamare a tudun Murtala primary school daga 1980 zuwa 1986 daga nan na wuce makarantar sakandire ta Dakata kawaji daga 1986-1992 daga nan kuma sai na samu tsaiko ban cigaba da karatuna ba sai na shiga harkar rubutun kirkira wanda daga baya kuma na shiga harkar waka ka'in da na'in inda har takai ina da kamfanin Waka mai suna Taskar Ala global.

Mahangar Arewa: A da mutane a fagen rubutu suka sanka ya aka yi ka koma harkar waka?

Aminu Ala: To gaskiyar magana waka dai ita na soma domin tun dan ina Islamiyya nake waka a wurin Maulidi amma wakar bata shiga cikin al'umma ba sai a shekarar 2003 ta kafar sadarwar gidan rediyon kano,

amma shi rubutu na fara shine a shekarar 1992 kuma bai fara fita ba sai 1999 wannan duk lamari ne na ubangiji ina waka ina rubutun littafi duk harka ce ta kirkira.

Mahangar Arewa: Matsayinka na cikakken mawaki a yau, me ya ja hankalinka ka shiga harkar ka'in da na'in?

Aminu Ala: to kamar yadda na fada maka waka na fara yin ta tun ina islamiyya inda ake koya mana karatu da wake da kuma wakokin yabon manzon Allah (S.A.W) don nuni da daraja da martabarsa, to daga haka muka fara rubuta waka har ma na rubuta wata waka mai suna raina fansa ne ga Annabi Babba dan Babba da kuma wata wakar mai suna Mai duka sa in je madina wadannan duk mu yi su ne a lokacin mauludi akan manbari kuma ni mai yawan sauraren wakoki ne tun da, ka ji dalilin da yasa na tsinci kaina a harkar waka.

Mahangar Arewa: In dai ana magana akan fitattun mawakan Hausa wadanda suka shahara dole sai an lissafa da kai, shin me kake ganin ya jawo maka wannan daukaka?

ALA: To wannan daga Allah ne, haka Allah yake ikonsa kuma babu mai hana shi idan yaso abu haka jama'a za su karbe shi, sannan kuma ina yin wakokin da suka shafi al'umma da fadakarwa akan siyasa da zamatakewa wanda in ka dauke masu wakokin madahu mafi yawa daga cikin mawakan yanzu sun fi yin wakokin soyayya da kuma na fina-finai, wannan shi yasa mutane suka fi karkata bangarenmu.

Mahangar Arewa: Yawanci wakokinka sun fi karkata ga sarakuna da wakokin fadakarwa, me yasa baka fiya wakokin siyasa ba?

ALA: To na lura wakokin siyasa suna jogarantarmu ga zubar da mutunci, baka samun komai a ciki sai ka taba mutuncin wani ko wani yasa kaci mutuncin wani ka kaskantar dashi sannan a baka wani abu wanda kuma gobe kana iya ganinsu tare, kuma ita waka ta riga ta shiga cikin kundin tarihi ka riga ka yi ta, waka tana da hadarin gaske shi yasa ko lokacin dana yi wakokin siyasa bana yin zagi na kan yi kokari na nuna mulki na Allah ne, shi yake ba wanda yaso sannan in fadi nagartar dan takara. Wannan shine dalilin daya sa na fi karkata ga sarakunan gargajiya da wakokin fadakarwa don sake fadada tarihi da Adabi.

Mahangar Arewa: Kana da Uban gida a harkar waka?

ALA:Kwarai kuwa ina da iyayen gida a harkar wakar da nake yi, wasun su mawaka ne wasun su ba mawaka bane daya daga cikin mawaka uban gidana shine Abdullahi sani Makarantar lungu malamine cikakke masanin fannoni amma kuma yana isar da sakonninsa ta hanyar wasan kwaikwaiyo a rediyo ko kuma wakoki na ilimantarwa to shine ubangidana a harkar waka sannan kuma a masana akwai farfesa Sa'idu Muhammad Gusau sai malamai na kwaleji irinsu malam Dalha da malam Aminu cigari, Malam Hassan da makamantansu wadanda idan sun ga na yi wani abu ba daidai ba sukan kira ni su min gyara, haka ma a bangaren Shari'a akwai alkali masanin shari'a Mahmud wanda zai zauna na yi masa tambayoyi akan duk abinda ya shafi shari'a.

Haka ma a rubutu akwai irin su Ado Ahmad Gidan Dabino da Farouk Lawan Da'u wanda yake abokinmu ne, amma mutumne mai ilimi da saukin kai gashi baya rowar abinda ya sani, duk suma in muka yi kuskure sukan taimaka mana wajen gyara, wannan a takaice kenan.

Mahangar Arewa: Tsawon lokacin da ka diba kana waka zaka iya gaya mana adadin wakokin da ka yi?

ALA: To wannan tambayar ana yawan yi min ita amma dai amsar wannan tambayar sai manazarta domin sune suke bin diddigin abinda mawaki ya yi don taskancewa, ni kuma waka faruwa take kuma kullum yi nake ina yin wakokin talla ina yin na sa kai, sannan ina yin wakoki na sarauta wanda samun wani abin alfahari ga sarki sai ya a yi masa waka inda zai baka jawabinsa, saboda haka ka ga wasu wakokin al'umma ne suke samar dasu dangane da faruwar wani al'amari, wasu kuma fadowa suke kana tafe, wannan shi yasa ban san adadin wakokina ba, ba kuma dan basu da adadi ba, amma dai nasan ina da kaset din hadakar wakokina wanda sun kai a kalla ashirin da biyu a kasuwa.

Mahangar Arewa: Daga cikin wakokin daka rubuta wacce ce tafi baka wahala kuma ba zaka manta da ita ba?

ALA:To wakar data fi bani wahala kwanan nan ne ma na yi ta Mai suan Budaddayir wasika ga shugaban kasa, saboda na rubutata a cikin lokaci kankani sai kuma na kasa karasawa sai washe gari kuma na kasa karantata an yi kida an gama har na fara na yi rabi sai kuma na kasa karasa ta haka nasa aka goge kidan na sake na yi na gama na ji kuma bata yi min ba, sai bayan na dena jinta cikin yan kwanakin nan ina tafiya a mota ina jinta sai kuma na ji ta yi min.

Mahangar Arewa: Daga cikin wakokinka wacce ce bakandamiyarka?

ALA: Bakandamiyata a baya ita ce lu'ulu'u a cikin juji saboda in aka ce bakandamiya ana nufin wakar data shafi abubuwa da yawa kuma ta shafi mawaki, amma yanzu ina cewa Alfiyya wadda ake kira Shahara sanadin sanina ita ce bakandamiyata.

Mahangar Arewa: A cikin ko wani abu akwai kalubale shin wani kalubale ka taba fuskanta a wannan sana'a ta waka?

ALA: Gaskiya mun fuskanci kalubale wanda a cikin kalubalen nema har kurkuku mun je, daga cikin kalubalen dana fuskanta nema na yi wakar shahara wanda mutane suke son su shahara abinda basa lura shine idan ka daukaka baka da ikon yin abinda wasu mutane zasu yi baka da ikon zama akan hanya ko cin abinci lalle ita daukaka kamar wata kurkuku ce, zaka yi alheri so dubu a ki kalla amma sharrinka daya sai ya zama abin magana saboda haka kullum muna cikin kalubale na rayuwa, sai dai kawai godiyar Allah.

Mahangar Arewa: A cikin wannan sana'ar taka wani alheri ka taba samu gagarumi da kake jin ba zaka manta dashi ba?

ALA: Wannan ita ce karramawar da sarkin kano Dakta. Ado Bayero ya yi min a shekarar daya cika shekara arba'in da biyar akan mulki sai kuma karramawar dana samu a jami'o'i irinsu B.U.K da kuma Danfodiyo inda suka bani jakadan Hausa da Jami'ar A.B.U da kwalejoji to wadannan sune kyaututtukan da bazan taba mancewa dasu ba.

Mahangar Arewa:A cikin mawaka su waye gwanayenka?

ALA: Ni ma'abocin jin wakokine iri-iri amma ina son wakokin su Narambada, Mai daji sabon Birin Dan Anace da Mamman shata gami da Dan kwairo.

A fagen larabci kuwa ina son wakokin Nancy da kuma Aisha Fallatiya irinsu Muhammad Wardi da Sahwa kai har da su Itofiya,

a mawakan yabon manzon Allah(S.A.W) kuma ina son wakokin Rabiu Usman Baba, Bashir Dandago, amma fitaccen gwanina a mawaka shine Marigayi Sa'adu Zungur saboda kaifin basirarsa da iliminsa.

Mahangar Arewa: Mafi yawa daga cikin wakokinka kana sanya azanci gami da bakin kalmomin hausa a ciki me yasa kake haka?

ALA: Wannan ai abubuwa ne na ilimi kamar yadda na gaya maka cewa daga cikin wadanda suke bani shawara akwai malaman addini dana zamani da lauyoyi, saboda haka iya wannan ya isa idan ka dauka kayi waka ya gajiyar da tunanin mai saurare, kuma ni bana raina baiwa ko ta waye wannan shine sirrin?

Mahangar Arewa: Tsawon lokacin da ka yi a masana'antar waka ka taba renon wasu mawaka wanda za'a kalla a ce kai ka kyankyashe su?

ALA:To renon mawaka muna yi kama daga bada shawarwari har zuwa samar da su irin su:

-Nasiru garkuwar Ala

-Sanin Baba tudun murtala

-Sa'id Nagudu da Abubukar mai bibiyu na kaduna wadannan duka ni nayi musu kaset na wakokinsu. Kuma wadannan mawaka ko gobe bana nan sune nake saran za su gajeni wato su dora daga irin wakokina na fadakarwa.

Mahangar Arewa:A karshe wani Fata kake dashi a wannan harka?

ALA: Muna fata gwamnati da malaman addini da kuma jama'a su marawa wannan aiki namu baya domin isar da kyakkyawan sako, idan suka abotake mu zamu dinga yin abubuwa dai-dai zamu wakilci harshen hausa da hausawa cikin nutsuwa sabanin yadda zamu dinga aro wasu abubuwan muna yafawa a ciki, saboda nisa da suka yi damu shi yasa aka bar abin kara zube wanda bashi da albarka sai daidaiku, wannan shine kirana da fatana a wannan harka Allah ya albarkaci wannan sana'a ya bunkasata fiye da tunaninmu.

Mahangar Arewa: Mun gode.

ALA: Ni ma na gode.

MATSALAR BARA A KASAR HAUSA

Daga 

MA'ANAR KALMAR BARA.

Idan aka ce bara a kalmar hausa.

To ana nufin wani mutum wanda bashi da karfi, wanda yake neman taimako a gurin mutanen da suka fi shi karfi.

Bara dai ta kasu kashi-kashi.

Misali.

Akwai bara ta yara kanana wadanda ake kawo su daga jihohi gurin malamai domin neman ilimi.

Akwai kuma bara wadda Makafi da Kutare gami da wasu mutane wadanda suka nakasa suke yi.

In ka dauke barar da yara wadanda ake kira Almajirai ke yi.

A yanzu muna iya kiran bara ta zama sana'a a kasar hausa.

Idan muka yi duba da yadda Kutare da Makafi kai har ma da wadanda suka samu wata yar nakasa suka mai da abin sana'a.

Domin za ka ga wani daga cikin Mabaratan a dalilin wannan barar da yake ya gina gida ya sayi motar da ake masa haya da ita, kamar yadda masu sana'a suke yi.

Amma duk da haka bai dena barar ba saboda ya riga ya maida ita sana'a.

BARA A MIZANIN JIYA.

A lokutan baya bara bata zama abar kyama ba, musamman a yankin Kasar Hausa.

Domin a lokacin da kafin zuwan turawa wajejen karni na sha biyu.

Muna iya kallon bara a wani janibi na dabam misali.

Lokacin muna da sarakuna masu mulki na hakika da malamai wadanda suke karantarwa yadda yakamata gami da kula da yara cikin mutunci da kamala.

Sannan waccan lokacin ba'a samu yawaitar jama'a kamar na yau ba.

Kuma mutanen waccan lokacin suna da karamci da tausayin wanda bai da shi,

kuma za kaga mabaratan na waccan lokacin ba da son ransu suke yin barar ba. Kuma da sun samu abinda suke bukata su kan koma muhallinsu.

Wannan yasa wasu mutanen idan suka yi noma a karshen shekara sukan ware wani kaso su kai wa wadanda suke ganin ba su da karfin da za su iya nomawa kamar kutare, guragu da makafi.

Wannan tasa wasu daga cikin Nakasassun dena fitowa waje bara domin sun samu abinda zai wadatar da su.

BARA A YAU

Bara a yau ana iya kiranta wata gagarumar matsala wadda ta dade tana kawo cikas ga rayuwar ya'yan hausawa.

Misali.

Bari mu fara da yara kasancewar sun fi yawa a cikin bara.

Iyaye kan dauki dansu su kai shi gurin wani mutum wanda yake bada karatu a matsayin Almajiri (mai neman ilimi) wanda daga nan kuma iyayen sai su manta da rayuwar yaron basu san cin saba basu san shan sa ba, domin suma talakawane abinda za su ci wuya yake musu, wasu ma da gangan suke kai yaran Almajiranci domin gidajen da suke kwana ya yi musu kadan kuma ga abincin da yake kawowa baya isar su ga yara an hayayyafa da yawa to daga nan sai kaga uba ya dauki dansa ya kai shi can wani gari mai nisa wai da nufin karatu ya kai shi.

Wasu iyayen su kan ce kada a bar yaro ya taho ganin gida har sai ya sauke su kuma daga nan sai sun kai wajen shekara guda da rabi ba su sake waiwayar sa ba, daga nan sai su kulle dan abinda bai kai ya kawo ba su kai wa malamin da yaron nasu a madadin ladan kula da yaron su da yake yi.

Wanda shi kuma malamin shi ma talauci yana damunsa gashi kuma babu wata kwakkwarar sana'a da ya dogara da ita, kuma gashi an tara masa yara gurinsa kuma iyayensu sun yi nisa da su.

Sai kaga bai da lokacin tarbiyar ko wani yaro kuma bai damu da halin da yara za su shiga ba,

Idan damina ta fadi wasu malaman kan dauki wadannan Almajiran nasu su ta fi dasu wani gari domin su yi wa Mutane Noma a biya su.

Yawanci wannan kudi da ake samu malaman ne kan sanya su a cikin aljihunsu, kuma ba su fiya damuwa da irin rayuwa da yaran kan kasance a ciki ba.

A halin da ake ciki a yau irin wadannan yara da ke kawowa Almajirci za ka dinga ganinsu wajen yan tuwo-tuwo da gurin Yan daudu gami da yin sana'ar Bola-bola(Gwangwan) daga nan sai kaga sun shiga shaye-shayen kananan kayen maye, irinsu Sholiso Madarar Suku dayin.

Domin guraren da suke ziyarta gurarene na matattarar masu irin wadannan dabi'u.

Yawanci malaman basa farga sai abin ya yi nisa domin yawan Almajiran da ke garesu gashi kuma iyayensu sun yi nisa da su balle har su san yanayin rayuwar ya'yansu shima kuma Malamin ga nashi Ya'yan ka ga da wan ne zai ji kenan?, dan haka da an tashi daga karatu bai damu da gurin da kowa zai je ba.

Wasu yaran daga nan sai su balle daga makarantar su dena zuwa su koma can tasha da Matattarar yan Bola-bola su cigaba da zama.

Lokaci-lokaci su kan bullo makarantar su baiwa malaman nasu dan ihsani(wasu yan kudade ko kaya) gami da sanar da ai suna nan aiki suka samu.

Su kuma malaman kan karba gami da yi musu wasu yan nasihohi.

Idan muka kalli samuwar wannan matsala za mu ga bara ce ta haifar da ita domin da yaron bai je ba da ba zai samu damar fita bara ba balle har yasan irin wadannan gurare.

Kuma yawanci irin illar da wadannan yara ke haifarwa tana da yawa ga kasa, domin basu samu cikakken ilimin da ake so su samu ba.

Gashi kuma ba su samu kyakkyawar tarbiya ba, hakanan sun yi biyu babu domin babu cikakken ilimin Addinin babu na zamanin sai kaga yaro ya tashi cikin rashin tausayi haka kuma yawanci irin wadannan yara basu fiye komawa garuruwansu ba.

Kaga an bata goma biyar bata gyaru ba.

Idan muka dawo bangaren manya kuma za mu ga yadda a yau suka mai da bara sana'a kai har ta kai ma da wanda ya nakasa da wanda bai nakasa ba duk bara suke.

Matsalar da wannan barar take hai far yana da yawa na farko.

a.Mutuwar Zuciya.

b.Hassada da gaba.

c.Rashin Wadatar Zuci.

Bari mu fara dana farko wato mutuwar zuciya.

Idan ya zama yau a baka gobe a baka to zuciyar takan mutu wajen yin tunanin hanyar da zaka yi wata sana'a dan dogaro da kanka.

Hassada da gaba.

Hassada da gaba takan shiga tsakanin mabaraci da masu bayarwa, domin duk lokacin da ya zo ya yi bara baka bashi ba haushinka ya ke ji tare da bakin ciki dangane abinda kake da shi.

Rashin wadatar zuci.

Irin wadannan mabarata kan tara dukiya ta hanyar bara, amma kullum zaka gansu jiya i yau. Babu wanka balle kyakkyawar sutura.

KURMAN SO


Daga 

Yanayi mai dadi, a lokacin yammaci, an yi ruwa an dauke kalar sararin samaniya ya yi fari kal gwanin ban sha'awa.

Tafe nake ina tunani kala-kala kan abubuwan da suka faru dani a rayuwa.

Allah sarki Manila ina jin har in koma ga mahaliccina ba zan taba mantawa dake a rayuwata ba,

ina sonki so na hakika,

Insha Allahu ke yar Aljanna ce,

na rasa dalili kusan kullum rana ta Allah sai na tunata a raina sau shurin masaki yanzu haka tafe nake zuwa kushewarta dan yi mata addu'a.

Manila dai wata kyakyawar yarinya ce da aka yi a garinmu, kuma Allah ya yi mata farin jinin mutane sosai domin kusan ko wani saurayi a garinmu burinsa shine a ce yau Manila shi take so.

Duk wannan tarin samarin na Manila bai hanani zuwa wajenta ba domin jarraba sa'ata, ranar dana gayawa abokaina cewa zan je wurin Manila zance dariya suka yi ta yi min wai ba zata soni ba.

Duk da cewa jikina ya yi sanyi da maganganunsu amma haka na jure na je a ranar dana fara zuwa wurin Manila ranar na samu karbuwa.

Tun daga wannan rana na zama abin birgewa a wurin abokaina kuma abin tsana a wajen wadanda na kore a gunta.

Soyayya mai tsabta ta kullu tsakaninmu da manila, ni kaina har mamaki nake wai me yasa Manila take sona?

Watarana na taba yi mata wannan tambayar sai tace hakanan take sona ita kanta bata san me yasa take sona ba.

Wannan shi ake kira kurman SO.

A cikin wannan hali na so da kaunar juna ne, ni da Manila muka yi aure.

Mutane da yawa sun yi mamakin wannan aure ganin cewa Manila tana da samari masu rufin asiri amma ta je ta auri mutumin da ko jarin kirki bai dashi.

Tunda muka yi aure da Manila komai nawa ya ja baya dama sana'ar sayar da burodi nake sai jarin nawa ya karye, na shiga yan dabaru.

A cikin wannan halin Manila ta samu juna biyu mai wahalarwa, domin haka muka yi ta dawainiyar zuwa asibiti.

Ita Manilan ita ke dan taimaka min da wasu abubuwan mu samu mu ci abinci ashe kayan dakinta take sayarwa ban sani ba

sai daga karshe na gane.

Tsanani ya kai tsanani a zamantakewarmu ga kuma tarin bashi da ya yi min yawa.

Kowa ya ganni ya san ina cikin damuwa.

Babu abinda ya fi damuna fiye da yadda mutane suka canja basa son taimako duk inda nasan zan je na samu kudi na je ba labari.

Sannan ga aikin duk ba labari.

Amma kusan kullum Manila cikin bani hakuri take tare da nuna min komai ya yi farko yana da karshe.

Ta kan ce dani Ado wallahi Allah bai manta damu ba yana sane damu kuma ka sani cewa ko wani mutum da irin jarabawar da ake masa ka yi addu'a Allah yasa mu ci jarabawar da ake mana.

Wani abin burgewa da Manila shine tsakar dare zan farka sai na ganta tana ta Nafilfili, idan na kalli Manila sai in ji tausayinta ya kamani wallahi duk wanda ya santa a da idan ya ganta yanzu sai ya yi mamaki domin duk kamanninta sun canja ta rame.

Duk randa ta je asibiti sai an rubuto mata abubuwan da zata dinga ci domin inganta lafiyarta kasancewar an ce jini ya mata karanci a jiki.

Ganin komai nawa ya tsaya ga mutanen da suke bina bashi suna min barazanar dauri,

Sai na yanke shawarar mayar da Manila gida ni kuma na tafi birni neman kudi,

Ado ka ji tsoron Allah a duk inda ka tsinci kanka karka yarda ka ci abinda ba hakkinka ba.

Zan cigaba da yi maka addu'a a koda yaushe.

Ina maka fatan Alkhairi Allah ya zamo gatanka a duk inda kake Allah ya bada sa'a kan abinda aka je nema.

Wadannan sune maganganun da Manila ta gaya min a lokacin da zamu rabu da ita.

Ban san kuka nake ba sai dai na ji dandanon gishiri a bakina sannan na lura ashe hawaye ne ke zuba daga fuskata.

Cikin sa'a na shiga birni domin ina shiga kwanaki kadan na samu aikin kamfani a wani kamfanin sarrafa fata kuma Alhamdulillahi tsawon wata uku da na yi a kamfanin na samu alkahiri.

Dan haka na yanke shawarar komawa kauye domin kula da Manila duba da cewa watan Haihuwarta ya kama.

Wannan shine abinda bazan taba mantawa dashi ba a tarihin rayuwata ba.

Anya akwai wanda ya kaini dandanar bakin ciki a rayuwa kuwa.

Rayuwa me yasa zaki mani haka?

Wayyo Allah rayuwata shike nan na shiga uku.

Shikenan na yi bankwana da farin cikina?

Haba Manila me yasa zaki mani haka, kin san bamu yi haka dake ba, me yasa zaki tafi ki barni.

Wannan shine sumbatun dana rika yi lokacin dana samu labarin rasuwar Manila...

NADAMA


Na kasance yar gidan masu akwai domin mahaifina mutumne mai tarin dukiya na yi aure cikin jin dadi da walwala duk da cewa bani kadai ba ce a gidan mijina akwai kishiyata amma kuma na fita fada a gunsa domin sai abinda na ce ganin bana rabo da yan silalla a tare dani kuma ana yawan aiko min da kayan alatu daga gidanmu.

Duk da cewa bani bace uwargida amma sai mijina ya mai dani uwargidan sai abinda na ce.

Duk duniya ba abinda na tsana irin kishiya na tsani koda jin labarinta sai gashi wai ni ce a gidan kishiya in banda kaddara.

Wannan damar dana samu a gurin mijina sai na yi amfani da ita wajen musguna mata ita da yaranta.

Ya'yan kishiyata uku biyu mata daya Namiji.

Ni kuwa ina da yara biyu duk maza

wannan ne dalilin da me gidana ya kara sona ganin daga zuwa na haifa masa yara biyu duk maza.

Na lura wannan al'amari ba karamin batawa kishiyata rai yake ba kawai sharewa take ni kuwa dana ga haka sai na shiga sabon salon kara kunsa mata bakin ciki domin kusan kullum sai na canja sabbin kaya kuma yawanci shi nake baiwa dinki ya kai min haka nan duk ranar da aka ce girki na ne sai in sa ya yo min cafane mai kyan gaske mu ci ni da yayana.

Haka kawai sai in kirkiri sharri in yi mata a gun mijinmu shi kuma ya yi ta mata masifu kala-kala har da barazanar saki, kullum ta Allah kafin in gaisheta ta gaishe ni.

Duk wani hakki da aka ce nawa ne kishiyata ta biya min kai hatta duk haihuwar dana yi kusan ita ke dawainiya da ni amma wannan bai sa na ji ina tausayinta ba kullum dada gallaza musu nake ita da ya'yanta.

Ana tsaka da wannan al'amari sai ciwo ya kamata wai ciwon zuciya da hawan jini an je asibiti sai aka ga ashe har zuciyarta ta kumbura kafin wani kwakkwaran mataki tace ga garinku nan.

Bayan rasuwarta da kamar wata biyu sai rikon yaranta ya dawo hannuna.

Ganin wannan damar ta dawo hannuna sai tsanar uwar yaran ta dawo kansu.

Na shiga gallaza musu ba dare ba rana kusan kullum sai na zane su haka kuma idan na ba 'ya'yana abinci da yawa su sai in basu kadan

kasancewar yaran suna zuwa makaranta sai Allah ya basu Nasibin haddace duk abinda aka koya musu kullum naga yaran nan sai in ji tsanar su ta kara kamani kai da abin ya ishe ni rana daya na fito na gayawa mijina cewa ni gaskiya ba zan iya zama da su ba dan haka yasan yadda zai yi dasu kasancewar babu yadda ya iya dani haka ya kwashi yaran ya mai da su can kauyensu wajen danginsa.

Wata rana na kwanta sai na yi mafarki wai gani na mutu an sanya ni a wuta ana ta yi min azaba kala-kala sakamakon tozarta kishiyata dana yi da kuma rukon sakainar kashin dana yiwa marayu.

Wannan mafarki ba karamin tsorata ni ya yi ba.

Kusan kullum cikin tunani nake wallahi abin ya tsaya min a rai.

Dan haka na rubuto muku wannan labarin nawa Aunty Lami ku bani shawara dan Allah ya zan yi?

ZIYARARMU GARIN TANHIYA JAMHURIYAR NIJAR


Ranar Alhamis 13 ga watan maris 2014 ina zauna a gida ina dan Nazari sai na ji wayata ta soma ruri alamun a kawo mata agaji cikin hanzari na dauki wayar na duba lambar sardaunan Agadez ce Dr. Abdulkadir koguna, cikin sauri na kara a kunne na tare da yin sallama.

Bayan ya amsa min sai yake gaya min wai takardar gayyata ce ta sallar Buzaye tare da wankan Sarauta aka aiko masa daga Tanhiya ta Nijar, kuma ba zai samu damar halarta ba dan haka yana so na wakilce shi.

Na amsa masa da insha Allah zan je a nan ne ma yake gaya min akwai abokin tafiya wato Abubukar Abdurrahman Dodo na Jaridar Aminiya shima zai je daukar rahoto,

muka aje magana akan da safe zan fito sai mu hadu a gidan Sardaunan mu tafi, haka kuwa aka yi tunda misalin karfe bakwai na safiyar ranar na gama shirin tafiya daga nan kai tsaye Gidan Sardauna na nufa ban dade da zuwa ba sai ga Abokin tafiyata Mal. Abubakar Dodo ya shima ya iso dauke da kayansa.

Mun bar garin garin Kano da misalin 11 zuwa garin Daura.

Da yake ranar ta juma'ace a Fago muka yi sallar juma'a.

Karfe biyu daidai muka shiga garin Daura wata sa'a da muka samu shine muna zuwa muka samu motar Damagaram sa'a kan sa'a mun soma tafiya sai direban motar yake tambayar mu daga Damagaram ina zamu?

Muka ce masa Tanout muka nufa ashe shima can za shi dan haka muka hada masa kudin motar zuwa Tanout.

Tafiya ta soma tafiya cikin yan sa'o'i kadan muka yada zango a Damagaram muka aje fasinjijo muka yi sallah muka ci abinci bayan mun dan huta kadan, sai yan kamasho suka karawa motarmu fasinja muka nausa hari sai Tanout.

Daga Damagaram zuwa Tanout tafiyar Sa'a uku ce amma da yake hanya ba kyau sai da muka shafe awa hudu a gajiye likis muka isa garin ba mu zame ko ina ba sai gidan Gwamnan Tanout, sojoji ne suka mana iso zuwa cikin Gidan, bayan mun gabatar da kanmu a wurin Gwamna sai yake gaya mana ai tuni sako ya zo masa akan zuwanmu, gaskiya mun samu kyakkyawar tarba a wurin Gwamna bayan gajeriyar hira kai tsaye masauki aka kaimu.

Da safe bayan mun kintsa mun yi karin kumallo sai mota ta zo ta dauke mu zuwa ofishin Gwamna inda a nan za'a taru zuwa Tanhiya a nan naga Manyan mutane Mahukunta daga sassa daban-daban na kasar nijar,

bayan mun gaisa da Gwamnan Tanout sai ya shiga gabatar damu a wurin manyan baki.

Cikin fara'a da barkwanci muka gaisa da kowa har suna tsokanarmu da cewa mun zo kenan basu barinmu mu koma Nijeriya,

Daga nan Gwamnan Tanout ya jagorinci walimar da aka shiryawa manyan baki nan muka sake cika cikinmu, bayan an gama walima sai aka shirya sansanin tafiya mu dama tuni Gwamna ya hada mu da abokanan aiki na Gidan Radiyo da Talabijin din kasar shiyyar Damagaram Mai suna ORTN.

To da yake ni ina tare da kyamarar daukar hoton bidiyo sai naki shiga motar da gwamna ya sani na shiga landirobar sojoji da nufin idan an soma tafiya na dinga daukar masu tafiya.

Sojojin motar suka nuna rashin yardar su akan zamana a motar amma ni sam naki nace a nan zan zauna ban san lokacin da direban motar ya je ya gayawa gwamna ba sai kawai ganin gwamna na yi ya zo ya ce na koma motarmu haka nan na sauko na koma motarmu ina yan kunkuni.

Cikin yan mintina mu ka soma tafiya na dauka tafiyar irin ta Kano zuwa Damagaram ce ashe ba ita bace,

daji muka nausa tafiya muke muna dada shiga cikin Sahara kamar ba zamu dena ba ga hanyar ba kwalta shahara ce kawai ga gwajab-gwajab ashe ba karamin sa'a ba na samu dana dawo motarmu dan har wuntsilawa muke idan muka shiga wani kwarin, duk karsashina ya ragu tun ina cewa an kusa ana da saura har na gaji na dena tambaya.

Ina ji ma'aikatan gidan talabijin suna magana da zabarmanci suna dariya da alamu dani suke, sun ga na gaji.

Ban san lokacin dana yi bacci ba sai kawai ji na yi ana cewa malam tashi an zo,

dandazon rakuma na hango can nesa damu bayan mun karasa gurin taron baka jin komai sai ihun buzaye.

Mun je har an soma gabatar da taron amma muna zuwa sai aka dakatar da taron aka dauke mu tare da manyan baki zuwa masaukai.

Kafin nan dama kowa an tanadar masa masaukinsa domin ko wani daki da sunan mutanen da za'a sa wadanda aka gayyata.

ALLAH DAYA GARI BAMBAM.

Ban taba tsammanin zan ga dan adam a wannan gurin ba bayan doguwar tafiya da muka sha a baya daji ne iya ganinka kuma sahara ce zalla.

Sai gashi mun cimma gari ciki har da mutane

wani abin mamaki shine yanayin dakunan mutanen garin ba irin na arewancin Nijar bane dakunan irin na bukkokin nan ne wanda kofofin kanana ne sosai sai ka sunkuya da kyau sannan zaka shiga daki wannan su ake kira dakunan bugaje.

Bayan mun huta mun ci abinci mun yi sallar azahar da la'asar sai kuma muka dunguma zuwa wajen bikin, a ranar na ga asalin buzaye irin wadanda ake kira buzaye duk su ne a wajen suna ta wasannin al'ada kala-kala bayan an gama wasanni sai kuma aka shiga gabatar da manyan baki tare da makasudin taron.

Da yake sallar manoma suke kiranta sai shugaban harkar noma ya mike ya gabatar da sabbin kayan noma da gwamnatin kasar ta samar da kuma magungunan dabbobi wanda za'a dinga basu kyauta don inganta kiwonsu.

Daga nan kuma sai gwamnan Damagaram ya mike ya yi jawabi kan zaman lafiya a kasar nijar.

Sannan aka shiga wakoki daga bakin mawaka wadanda aka gayyata irinsu duda mai waka da Aliyu sai kuma mawakan garin Tanhiya suma sun nishadantar da mahalarta a wajen taron.

Daga nan kuma kai tsaye sai aka fara kiran buzaye mahaya rakuma na gari -gari domin su gaida manyan baki.

Garuruwan da suka samu halartar taron akwai.

Agadez.

Taskir.

Goure.

Tanhiya.

Daga nan sai aka shiga babban al'amari wato yi wa sabon sarkin Tanhiya nadi a matsayin sarki mai gafaka ana gama nadawa sarki rawani sai na ji buzayen nan sun gauraye wajen da ihu alamun mubaya'a ga sabon sarkin nasu Ahmad Aghali Ibbah.

Daga nan sai magajin gari ya yi kira ga sabon sarkin akan ya rike yan kasar sa da amana kamar yadda suka san shi dama mai amana ne.

An kira gwamnan Tanout ya yi jawabi da godiya ga mutanen garin Tanhiya dangane da yadda suke zaune lafiya da junansu duk da cewa suna da bambancin jinsi.

Daga nan sai sarki Ahmad Aghali Ibbah ya amshi abin magana ya yi jawabin godiya ga mahalarta taro sannan ya yi kira ga gwamnatin kasar nijar akan ta kawo mu Sabis na wayar salula saboda su dinga gaisawa da dangin su na nesa kasancewar nan inda suke daji ne da kuma tsaro a yankin nasu dan maganin barayi masu satar musu bisashe(Rakuma) haka nan ya yi korafi game da rashin asibiti a yankin nasu, inda yace Tanhiya babban gari ne, kuma akwai mata da yawa suna haihuwa amma ba asibiti dan haka yana kira ga gwamnatin kasar Nijar ta gina musu asibiti a wannan yanki nasu.

Daga karshe ya yi kyautar rakuma ga gwamnan Tanout dana damagaram bisa jajircewarsu wajen ganin taron ya yi yadda ake so.

Daga nan aka buga tambari tare da jawabin godiya da nufin gobe a karasa abinda ya rage.

To ganin an yi duk abin za'a yi a wannan rana sai mafi yawa daga cikin manyan bakin da suka zo kowa ya kama hanyar komawa gida ciki har da gwamnan Damagaram.

Washe gari Lahadi aka cigaba da sha'anin bukuwan sallah dana sarauta da yake buzayen jinsi-jinsi ne sai ya zamana shigarsu ma daban-daban ce.

Buzayen sun kasu kashi uku.

Akwai makerin buzu akwai Jan buzu da kuma buzaye Abzinawa wani abin al'ajabi basa auratayya a tsakaninsu, kowa sai dai ya auri jinsin sa.

Sannan wani karin abin mamaki a garin shine ba'a sallar juma'a, dalili kuwa shine basu da masallacin juma'a, sai dai duk ranar juma'a mutanen garin su taru a fadar sarki a yi sallar azahar sannan a yi jawabai daga nan kowa ya koma gida.

A wannan rana aka kira mahaya rakuma da suka zo daga gari-gari aka musu kyauta.

Sannan aka shiga wake-wake a wannan ranar kuma mawakan da suka nishadantar sun hada da Mawaki Abdallah daga jahar Aghadez da kuma wata tsohuwar mawakiyar garin mai kidan goge.

NA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA.

Dana ga ana ta shagali a wurin taro sai na zame na shiga gari neman ruwa da yake ruwan roba muka ta fi dashi kuma duk ya kare gashi kuma ana ta kwallah rana, duk inda na je da kyar ake ban ruwa amma sai inga ruwan bai yi min ba, na tambaya ina suke samun ruwan suka nuna min wata hanya wai idan na bi ta zan samu ruwa to da yake ina tare da kyamarata sai na ji dadin hakan domin ina son in dauko inda suke samun ruwa musamman yadda na lura ana wahalar ruwa a yankin.

Na jima ina tafiya sai na fara hangen wani tarin abu nesa dani, ina matsawa kusa sai na lura ashe tarin rakuma ne da dabbobin buzayen suka kewaye wani abu, da kyar na isa wajen duk na galabaita kishirwa ta kama ni da yawa da isata na tarar da buzaye ne rakwacam su da matansu da tarin dabbobi ko wani buzu fuska rufe kuma rataye da takobi.

Aradu sai da na gwammace ban je gurin ba, domin wata rijiya na gani ban taba ganin irin ta ba, sai ko a tarihi, katti hudu ne a bakin rijiyar suke dauko gugan, kuma shanu ake daurawa wata doguwar igiya a yi ta duka sai sun yi tafiya mai nisa sannan gugan zai zo gaba su kuma buzayen sai su kama da kyar su fito da shi su zuba a wani katon duro da suka tanada.

Yanayin kallon da naga suna min sai nasha jinin jikina na ce musu ni bakon sarki ne daga Nijeriya ruwa na zo sha, suka nuna min wajen da zan sha ruwan ina zuwa na tarar da mutane da jakuna da rakuma, har da tinkiyoyi gami shanu duk suna shan ruwa a wata kwatanniya mamaki ya kamani na ce a raina yanzu mutanen basa tsoron cuta suke shan ruwa tare da dabbobi?

Ina tsaye sai na ji wata mata ta min magana cikin gurbatacciyar hausa "ke namiji jo ki sha ruwan" gaba na ya fadi yanzu wannan ruwan zan sha? Dana je wajen naga yadda ruwan yake sai da hantar cikina ta kada, ruwan ya zama kamar ruwan kwatami ga ledoji nan da yayi birjik a ciki,

duk da kishirwar da nake ji sai bazan iya shan ruwan nan ba, na ce mata na gode, na juyo zan dawo gida haba ai na ji kamar bazan iya taku goma ba zan fadi domin nasha rana ga kuma kishirwa, dole na juyo wajen matar nan na ce ta ban ruwan na sha, haka na rufe idununa ina addu'a, na sha ruwan nan sosai domin kishirwa ta ci karfina, bayan na gama sha sai dauko kudi na ba matar nan haba wa ashe ba'a matansu kudi sai na ji wani buzu ya kurma ihu ayyyiii "ya ce karya kake namiji ke bashi kudinshi yadda naga buzayen sun nufo ni sai na fara salati tsammani na tawa ta kare, suna zuwa sai suka amshi kudin dana bata suka dawo min dashi wani babba daga cikinsu "yace ka ce kai bakon sarki ne"?, na ce eh,

sai ya ce to ko bisashe(Rakuma) nawa ka kawo nan suka sha ruwa bakka biyan ko sisi je ka abinka, ni dai cikin tsoro na baro su.

Wata sabuwa in ji yan caca ina dawowa gari sai tarar da abokin tafiyata wato Abubakar dodo ya bi gwamnan Tanout sun tafi na kuma

dama tawagarmu ce kawai ta rage bata tafi ba, nan fa idona ya raina fata yanzu ya zan yi? Gashi kuma na ji sun ce ko a rakumi kafin mutum ya cimma babban gari sai ya kwana hudu a hanya.

Ina cikin zulumi sai na hangi mataimakin gwamnan Tanout can tare da sarki haba ai tuni raina ya yi fari, na je na tarbe shi muka gaisa ya yi mamaki da ya ganni ya ce, me kake a nan ba ta fi ba?

Na ce masa tafiya aka yi aka barni, sai ya ce to na yi hakuri na dan jira shi ya gama ganawa da sarki shi yanzu zai tafi, na masa to na koma gefe na zauna muka shiga hira ni da wani abokina buzu, yana ta bani labari garinsu da al'adunsu a nan na gane ashe idan suka ce fulani (Dosawa)Bararoji suke nufi, na ce masa wai zaman me suke a wannan daji ga gari can sun zo nan sun zauna?

Sai yace dani ai su nan zaman rakumansu suke, yanzu da zasu tatsi nono a jikin rakumi suka ba kamar yadda suka saba da tatsaba ko kuma suka ga rakumansu suna ramewa to a ranar zasu bar dajin su yi gaba, ya ce min a nan dana ke ganinsu akwai mai rakumi dari uku akwai mai dari biyu,

dana masa maganar abinci sai ya ce min indai da hatsi da kuma nonon rakuma su ai lafiya lau ne.

Muna tsaka da hira sai ga Mataimakin gwamnan Tanout ya fito muka yi sallama da sarki da abokina na shiga mota hari sai Tanout.

Ina zuwa Tanout na hadu da abokin tafiyata muka gaisa ya ce ai sun neme basu ganni ba, shine Gwamna ya ce su tafi za'a taho dani.

Daga nan muka yi sallama da Gwamnan Tanout tare da godiya muka shirya kayanmu hari sai gida Nijeriya.

Taron dai ya samu halartar mutane da dama daga kasashen ketare musamman yan yawon bude ido kuma an yi lafiya an gama lafiya.

Mun dawo gida iso gida Nijeriya lafiya, ranar litinin da misalin karfe daya na rana.

TAFIYA TA MASALLACIN IDI


KARFANCI RANAR SALLAH

Firgigit na farka sakamakon jin karar hayaniyar yara a tsakar gida kallona na farko kan agogo na kai shi karfe Takwas daidai agogon dakin ya nuna, cikin hanzari na mike na shiga bandaki domin wankan idi, ban fi minti biyar ba na fito har na gama wankan ni kaina nasan wankan Gwari na yi, (Kwaskwarima).

Turus na yi akan kayan sallar da zan sa gami fadin Allah ya tsinewa gugar dare, ashe jiya lokacin da nake goge kayan da zan sa yau duk na bata su da bakin gawayi kasancewar da Dutsin Chakwal na yi gugar.

Wasu tsofin kayana na sa ina wasu yan kunkuni.

Bakin titi na je na tsaya ina jiran mota zuwa masallacin idi, duk motar da ta zo a cike take zuwa ganin haka sai na yanke shawarar kawai in tafi a kafa.

Da gama wannan shawarar sai kawai na yanki hanya na somar tikar tafiya.

Kimanin minti talatin na kwashe a hanya sannan na isa masallaci, ina zuwa ana tayar da sallah.

Ana idar da sallar idi kawai sai na tuna ashe ban yi alwala ba na yi sallar, wani mugun abu ya zo ya tsaya min a wuya.

Can sai na ji wasu Mutane a bayana suna cewa ai kuwa masallacin hayin gangare basu tayar ba tunda nan sun idar ku zo mu je can.

Wani mai fiyawota na kira na sai na naira biyar na yi alwala.

Mun sha yar tafiya kafin zuwa masallacin duk na gaji tun kafin mu karasa masallacin na hangi mutane suna dawowa alamun an idar da sallah.

Tsaki na yi sannan na juyo na tsallako titi na hayo mota domin zuwa gida mun taba yar tafiya kenan sai kwandastan motar ya nemi da in bashi kudin mota Ras! Gabana ya fadi lokacin dana sanya hannuna a aljihu domin dauko kudin motar da zan ba yaron motar cikin hanzari na fara laluben sauren aljihunan kayana.

Babu inda ban duba ba amma babu kudin babu alamar su.

Wayet kwandastan ya fada, kiiii direban motar ya ja burki kana kwandastan yace dallah malam sauko irin wadannan mutanen barayine, ban iya ce masa komai ba na sauko, suka ja motar su suka yi gaba ni kuma na tsaya duk abin duniya ya dameni,

amma Allah ya tsine uwar barawon da ya sace min kudina domin duk kudin dana ke dasu ya kwashe.

Ganin tsayuwar bata da wani amfani sai na cigaba da tafiya a kafa zuwa gida, kasancewar jiya an kwana ana ruwa duk garin ya cabe babu dadin tafiya, fas ruwan kwatami ya wanke min jiki sakamakon wata katuwar mota da ta keta wani taron ruwa daya kwanta akan titi,

tsaye na yi ina kallon jikina duk ya 6aci ya yin da lokaci guda kuma na hangi motar can kan titi alamun direban motar bai san ya yi wannan abin ba, Allah ya isa na fada kana na ci gaba da tafiyata.

A gajiye likis na dawo gida duk raina a bace, wani karamin dana ya rugo a guje yana fadin baffa akuyar gidan su Talatu da barar da miyar mama.

Ina shiga gidan na tarar da katuwar tukunyar miyar a gefe ya yin da na hangi ruwan miyar a kasa.

Ka ga abinda shegiyar akuyar nan ta yi mana ko? wlh ina daki sai jin karar barewar miyar kawai na ji.

Duk wannan surutun da mai dakina take ni ban iya ce mata komai ba in banda kallonta kawai.

To yanzu sai ka kawo kudi a yi sauri a siyo wani kayan miyar kasan an jima su Amina(Kanwata) za su zo daukarwa Umma abincinta.(Mahaifiyata)

Wani mugun haushi ya kara turnike zuciyata yayinda na tuno bani da ko sisi a aljihuna...

BIKIN RANAR MAWAKAN HAUSA TA BANA YA SAMU TAGOMASHI.


Daga 

A ranar larabar karshen shekarar 2014 ne mawakan hausa suka fara bikin ranar mawakan hausa na Afrika wanda suka saba yi duk daya ga watan janairun sabuwar shekara a dakin taro na tunawa da Sardaunan Sakkwato sa Ahmadu Bello kan titin Alkali Road jihar Kaduna, sai dai wannan karon bikin ya sha bamban da na shekarun da suka gabata, shi dai wannan biki an fara yin sa ne tun a shekarar 2013 wanda mawaki Aminudden ladan Abubakar (ALA) ya assasa bisa sahalewar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero da Hakimin cikin Birnin kano babban dan majalisar Sarki, Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare wasu mawaka Inda aka yi taron farko a Taskar Ala Global da ke kan titin Manona cikin karamar hukumar Tarauni a jahar Kano.

Taro na biyu shi ma an gudanar da shi ne a jahar kano a Darul-Tauheed kusa da kantin sayar da kaya na Jifatu da ke kan titin zariya road.

Sai dai su kansu mawakan da suka saba halartar wannan biki na shekara-shekara sun ce bikin wannan shekara ya fi na dukkan sauran shekarun baya haduwa.

A zantawarmu da Mawaki Aminu Ala ya sake yin karin bayani game da yadda suka tsara taron na bana inda ya ce babu shakka sun fuskanci kalubale dab da taron saboda wanda ya yi musu alkawarin daukar nau'in taron na bana har ana saura mako guda taron basu samu damar ganawa dashi ba, amma cikin ikon Allah gashi a yau suna yin taron yadda basu yi tsammani ba.

Bikin wanda aka soma tun talatin da daya ga tsohuwar shekarar 2014 a daren ranar Gwamnan Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya halarci wajen taron inda yaba musu da bisa yadda suka hade kansu suka samar da wata rana ta musamman daga cikin ranakun shekara suke ganawa a junansu, kuma nuna damuwar bisa gayyatarsa da suka yi a kurarren lokaci, a karshen jawabinsa ya yi kira da mawakan hausa cewa su dinga yin wakokin fadakar da al'umma domin samun zaman lafiya a kasa ya kuma nuna jin dadinsa da kyauta ta musamman da wakar Tsumagiya wadda Adam Zango ya rera a wajen taron ya kuma bayar da gudummuwar naira miliyan biyu akan mujallar mawaka da aka sayar a wajen taron a karshen jawabin ya nemi ganawar sirri da duk mawakin da ya san ya yi masa waka ya kuma yi wa kungiyar mawakan Hausa alkawarin gwamnati zata kula da lamarinsu.

A washe garin ranar alhamis daya ga watan sabuwar shekarar 2015 ita ce ranar da mawakan hausa suke kira sallar mawaka ko ranar mawaka inda mawaka da yawa suka fito suka yi baje kolin fasaharsu, sannan a wannan rana an karrama wasu mawaka wadanda suke bada gudummuwa wajen ciyar da al'umma gaba a cikin wakokinsu daga cikin mawaka aka karrama akwai:

Fati Nijar.

Zayyanu Akilu Aliyu.

Abubakar Mai Bibiyu.

Maryam Sangadali.

Adamu Hassan Nagudu.

Adam A Zango da sauransu

hakanan an gabatar da takadu guda biyu domin karawa juna sani

inda Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero Kano ya gabatar da takardar farko Mai taken Mawaka a mahangar al'umma sai kuma Takarda ta biyu wadda Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na jami'ar Usman Danfodiya Sakkwato, ya gabatar

har tauraruwar Dallatun Zazzau Uwar gidan Gwamnan Kaduna Hajiya Fatima Ramalan Yero ta halarci taron inda itama ta yi kira ga mawakan cewa su mai da hankali wajen yin wakokin ciyar da al'umma gaba.

An kammala taron a ranar alhamis da misalin karfe shida na yammaci:

daga cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai:

-Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

-Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON

-Wakilin Sarkin Zazzau

- Alhaji Isa Bello Ja

-Hajiya Bilkisu Yusif Ali

taron dai ya samu sambarka daga bakin dukkan mahalarta taro an kuma zabi jihar Bauchi a matsayin da za'a yi taron shekara mai zuwa.