0
NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA(2) DAGA DAKTA ALIYU IBRAHIM KANKARA NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA(2) DAGA DAKTA ALIYU IBRAHIM KANKARA

(Ci gaba daga inda aka tsaya)  Bayan Yarjejeniyar Rubuta Littafin Shata Sai Me,  Wacce Rawa Aliyu Qanqara Ya Taka a Littafin ? A nan take mu...

0
KARAIRAYI 16 A MARTANIN ALIYU IBRAHIM KANKARA Daga IBRAHIM SHEME KARAIRAYI 16 A MARTANIN ALIYU IBRAHIM KANKARA Daga IBRAHIM SHEME

A ranar Juma'a da ta gabata, jaridar Aminiya ta soma buga hirar da wakilin ta, Bashir Yahuza Malumfashi, ya yi da ni a kan sabon bugun l...

0
NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA Dr. Aliyu Ibrahim Qanqara NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA Dr. Aliyu Ibrahim Qanqara

Na fara son Alhaji Shata da waqoqinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin...

2
KABILANCI NE BABBAR MATSALAR NIJERYA-Van der wel KABILANCI NE BABBAR MATSALAR NIJERYA-Van der wel

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya) A wani binciken sirri da wata baturiya yar kasar Kanada (CANADA) mai suna Marianne Van der wel ta yi wanda ...

0
A KASUWA NAKE DA NA SAMU MIJI ZAN YI AURE-Bintu A KASUWA NAKE DA NA SAMU MIJI ZAN YI AURE-Bintu

 Jaridar Sarauniya ta samu zantawa da daya daga cikin jaruman shirin wasan gidan talabijin mai nisan Zango (Series) "DADIN KOWA" ...

NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA(2) DAGA DAKTA ALIYU IBRAHIM KANKARA

(Ci gaba daga inda aka tsaya) 

Bayan Yarjejeniyar Rubuta Littafin Shata Sai Me, 
Wacce Rawa Aliyu Qanqara Ya Taka a Littafin ?

A nan take mu ka sasanta kawunanmu mu ka kuma sanya Sheme ya jagoranci wannan tafiya. Amma ko a sannan xin yawan littattafan da na wallafa na Hausa sun fi na Sheme yawa; ba wai akan littafin Shata na fara rubutu ba. Mun aminta ya zama jagoran mu saboda shi ke da Komfuta don haka a kyauta ya ce za ya sanya a buga littafin kafin a kai shi maxaba'a, kuma sannan ya gwanance wajen rubutu tare da basirar rubuta littafi. Mu ka xauki hotunan tarihi tare da Makaxa Shata har kala 12. 
Sauran hirarrakin da abokan mu su ka yi da wasu jama'a a cikin kasasuwan rikoda da ba su kai ga rubuta ko fassara su ba, su ka tattara su ka bamu. Shi kuma Sheme ya bani su, tare da bani umurnin in zauna in rubuta su in bashi. Na himmatu na yi aikin na kai masa. Daga cikin hirarrakin akwai ta Sidi mijin Hotiho da Hauwa mai tuwo.  Shima Sheme, hirarrakin da ya yi a kaset-kaset ya bani in dai rubuta, a ciki akwai ta Laila Dogonyaro, Musa Musawa da Bawa Dungun Mu'azu. Tun daga ran da mu ka bar gidan Shata su biyu su ka sakam mana aikin, su ka zare jikin su. 
A Kaduna, Sheme ya ke faxa mani cewa 'Aliyu ka ga mutanen nan sun bar mana aikin nan, sun daina yin intabiyu da mutanen Shata'. Idan mu ka yi masu qorafin haka sai su ce 'kun kira mu kun ce ga aiki kun ga mun qi amsa'? Sai ni da shi mu ka duqufa don nemo sauran hirarraki daga mutane, amma ni nawu aikin ya fi nashi faxaxa da nauyi, shi ma ya san haka. Don shima kan sa ba ya da lokaci, kullum aikin Edita na New Nigerian N ewspapers ya sha masa kai. Kuma galiban duk ni na ke bashi bayanan wasu da Shatan ya yi ma waqa da kuma waqoqin su, don bai sansu ba. Watau al'amarin sa na Shata bai yi nauyi kamar nawu ba. 

Kwaram tun ma ba a je ko'ina ba bayan watanni 9 sai Allah Ya yi ma Shata rasuwa ran Juma'a 18/6/1999. Hakazalika Sheme ya qirqiri wallafa mujallar FIM a cikin Mayun 1999. Ga kuma aikin wallafa tarihin Shehu Musa 'Ya'aduwa da sabuwar gwamnatin Obasanjo ta bashi. Duk abubuwa su ka rincave masa. A lokacin an sallame ni daga Kwalejin Kimiyya ta Kaduna ta hanyar rage ma'aikata, saboda haka ina zaune a Kaduna ba ni aikin komi (na zama abin tausayi) saidai rubuce-rubucen da ba za a rasa ba. Ganin haka, sai na duqufa, kuma muka shirya ni da Sheme, ina ta nemo labaru daga jama'a. Kuma ya kan tura ni ya bani kuxin mota da na abinci zuwa Musawa. Dama tun cikin Maris 1998 ya tura ni Gombe da Bauchi don ganawa da mutanen Shatan na can wajen. A taqaice ba a gama aikin littafin nan ba sai ina da kashi 65 na aikin littafin. Sheme ya bada gudunmuwar kashi 25, sauran abokan mu daga Kano sun bada gudunmuwar kashi 10. Allah Shi ne shaida ta, idan na yi masu qarya zan haxu da Allah. Ni fa xalibin kimiyya ne ina da ilimin qididdiga ko statistics. Tuni na yi wannan lissafin na fitar da sakamakon. 
Game da waqoqin Shata da na bada shawarar a tattara su a vangare xaya na qarshen littafin, shi da kan sa Sheme ya bani aikin nemo su. Gaba xayan waqoqi 638 da aka sanya duk ni na bada su. Yanda aka yi na tattara su shi ne: da na ji wata waqa ta Shata sai in rubuta ta a takarda in ofishin sa in bashi, koda ban tarar da shi ba sai in tura takardar a 'yar kafa ta qarqashin qofa. Shi kuma da ya zo ya buxe qofa sai ya gani. Sai ya xauka ya rubuta a kundin littafin. 
 
A littafin mu mai xauke da shafuka 604 ga dai gudunmuwar da na bada, watau wasu daga cikin waxanda na gana da su a lokuta daban-daban (kafin, da kuma bayan mun haxe da sauran abokan aikin littafin): 
Hakimin Musawa, Inde Magajin Musawa, Sa'in Katsina Amadu Na-Funtuwa (oga kwata-kwata a zancen Shata), Wasu dattawan Musawa, Hauwa matar Sarkin Bori Sule, Babba Qofar Gabas, Maigarin Sayaya Yahaya Salmanu, Tijjani Hashim Kano, Walin Kano Mahe, Ada tela Daura, Ali Scorpion, Walin Kano Mahe, Dagacin Falgore, Shu'aibu Bada-Bada, Alaramma Sulen Shata, Ali Xanqane Musawa da Mamman Tsalahu Musawa (da matan su), Hajiya Safiya Qumbula qanwar Shata, Xanbaba makaxi Musawa (makaxin sa na farko), Balan Guzun qanen Shata, Bilkin Sambo, Sani Bakatoshi, Inuwa Xalibi, Uwawu Kano, Mairo Munari, Indo Musawa, Indon Xanbaqi, Garba Xan Ammani, Musa Xan Amare Musawa, Ayuba mai nama Musawa, Bala Abdullahi Funtuwa, Halle Jani, Garba Ja, Abba Na Titi, Sabo Dogarai Kano, Ahmed Kari Garkuwan Bauchi, Bappa Ahmed Gombe, Musa Usman tsohon gwamnan NW,  Hajiya Indo 'Yar Mamman Gombe, Magaji Mai Ido Xaya, Amadu Doka mai kukuma, Alhaji Mayau Kaduna, 'Yayan Qungiyar makaxa da mawaqa ta Qasa, Ali Xan Saraki 'Yankara, Musa Xanbade, Sarkin Damben Haxejiya, Sanqira Isiyaku Usman Galo, Abashe Yaro maihoto, Dauda Mani da Garba (Yaro) Na-Gwandu mai nama, Ado Kankiya, Garba Kwagira, Salisu Bangul Xandaudu, Yahaya Xandaudu, Shehu Tsatso,  Abubakar Kashe-kura na qofar Qaura. 
Waxanda kuma su ka rasu,  na tattauna da iyalan su, kamar su: Sarkin Katsina Nagogo, Haruna Qasim, Maude Tabako, Ali Bagobiri, Mati 'Yammama, Xan Lagai-Lagai, Sani Audi, Sule Xan Wazifa, Sani Stores, Mamman Xa, Garba 'Yammama, Alhaji Abdulwahabu Malumfashi, Sani Xanqwara Malmfashi, Ahmadun Gaya, Ciroman Gombe Umaru, Adamun Pankshin (Ladi), Garba Sarkin malamai. 
Na kuma ziyarci RTK sau da yawa na yi hira da ma'aikatan su kamar su: Ofishin kasuwancin su, Xakin ajiye faya-fayi, Lawal Yusuf Saulawa, Nasiru Maiwada Malumfashi, Ahmed Aja, Rashida Bello, Shafi'u Zangon Aya, Yakubu Gombe, Ladan Kontagora, Ibrahim Baqo, Ahmed Girei (Xan uwan Xahiru Modibbo) Nine kuma na yi hira da wasu 'ya'ya da matan Shata kamar su: Binta Mami, Magaji, Salisu, Sanusi, Amina, Mamuda, Binta Iya, Asabe (Zuwaira), Hurera Yamai, Hadiza Falgore, Amina Dikke, Nasara Musawa, Yalwa, Binta Qanqara, Hajiya Kulu Kaduna, Halima, Jamila. 
Wasu ma mutanen da na gana da su na manta da su.  Amma duk aikin nan da aka yi, na rantse da Allah ko kwabo ban samu ba, na tashi a tutar asara. An qaddamar da littafi, amma bisa ga amana, ya dace mu zauna mu 4 mu kasafta xan abin da aka samu, kowa a bashi ko da a hannu ne. Sai ba a yi haka ba. Shi dai Sheme shi ne shugaba na, su kuma su biyu daga Kano sai Tijjani ya ke wakiltar su.  Kuxin da ba a amso ba daga mahalarta taro da su ka yi alqawari sai Sheme ya ce ya ranci gudunuwar Sarkin Zazzau ta N200, 000 ya gyara mota. Ganin haka, sai Shima Albasu, da ya amso kuxin Badaru Vavura (gwamnan Jigawa na yanzu, N100, 000) ya ranta shima ya gyara mota. Amma da Albasu ya faxa mani sai ya ce Sheme ya kwave shi ya ce kada ya faxa mana, mu sauran biyun. Zancen kenan har yau ba a qara tada shi ba. Ni kuma na sa masu hajar mujiya. Gudunmuwar Alhaji Xahiru Mangal ta N250, 000 na ke tababa ko sun amsa koko ba su amsa ba? Tunda na ji shiru itama ba a rasa amsar ta. 
A lokacin wannan hidima ta tarawa da kuma kasafta kuxin ina can Daudawa, wani lungu cikin daji ina koyarwa a Makarantar 'Yammata, su kuma abokaina su na Kano da Abuja a inda waxanda za a amshi kuxn daga wurin su su ke. Haka su ka yi qumuiniyar su ta kuxin ni ban sani ba. Sai daga baya xaya daga cikinsu ke faa mani. Har inda yau ta ke ban yi masu magana ba saboda kawaici da haquri. 
Sannan mu duka 4 mun yi alqawari wanda duk aka ba kofin littattafai ya kai wasu garuruwa, idan an sayar an bashi kuxin to ya turo a asusun da aka buxe ma littafin, kuma Sheme da Albasu kaxai ke da sa hannun ko ikon fitar da kuxi daga banki. 
Ni, na tafi Sokoto na kai littattafai, amma don tsoron kada a ce na sava alqawari, waxanda na sayas sai na tafi banki na aiko da kuxin. Waxanda na kai Funtuwa kuma, da ba a samu kasuwa ba sai Sheme ya umurce ni da in kai su Kano in ba Ali Malami don ya kai BUK, haka kuma na yi. To tsakanin kuxin qaddamarwa da na ciniki wallahi summa tallahi ban samu ko kwabo ba. Sai daga baya na fahimci kuxaxen an yi wani waje da su, bayan an sayar da littattafan. Yanzu an shirya mani gaskiya kenan? Kada fa ka manta kashi 65 na aikin littafin duk qoqari na ne. 
Don saboda wahalar da na sha a littafin lokacin shirya shi, ranar da zamu tafi Arewa House bukin qaddamarwa, na kwana gidan marigayi Adamu Yusuf BBC, amma da mu ka zo za mu shiga motar sa, sai ya kada baki ya ce: 'za mu tafi qaddamar da littafin da Aliyu Qanqara ya rubuta, ba su Ibrahim Sheme ba, domin su Sheme ba wata wahalar da su ka yi'. 
Na rantse da girman Allah abinda ya faxi kenan. Ya na lafira, na san zan bishi watarana. In na yi masa qarya na san zamu haxu a gaban Allah. 

Dalilan Da Su Ka Sanya NaWare Na Sake Rubuta Littafin Shata Ni kaxai Guda 8:

Duk da asarar da na yi na 'yan uwana sun rabe kuxin littafi sun manta da ni, ban damu ba, don babana ya bani haquri ya ce 'ba rabo na ba ne, rabon na nan tafe a gaba'. Na ce su zo a sake buga wani, sai su ka ce su sun gaji, idan ni ina da sarari in tafi in ci gaba. Kafin wannan lokacin, mun haxu a magana xaya cewa kowannen mu na iya xaukar littafin ko wani sashen sa ya rubuta wani abu game da Shata a gaba. Na rantse da Alkur'ani abinda Sheme ya bamu umurni kenan, kuma kowa ya yarda. Daga baya sai su ka yi mani gardamar maganar don sun ga ba rubutawa mu ka yi ba, ga kuma wani littafi ina ta qoqarin fitarwa. Don sun ga littafin ne ya sa su ka canza magana. Ka ga hassada ta shigo ciki kenan. 
Amma dalilan da su ka sanya na ware na haxa runduna ta ni kaxai su ne:

Na sha wahalar Sheme a littafin farko. Bai cika xaukar shawara ba, abin da kuma ya ga dama shi ya ke sanyawa ko ya ke cirewa ko da kuwa mu ba mu so hakan ba, alhali an ce tafiya ce ta mutum 4. Ai don ana so a samu idea ta kowa shi ya sanya aka game. To minene amfanin haxewar? A ce cikin mutum 4, mutum xaya shi kaxai za a xauki ra'ayinsa dole ? Ka ga ko tafiya ta tafi watarana sai an samu savani. Duk labarin da na kawo masa sai ya tace ya zubar da fiye da rabi, sannan ya sanya sauran. Vangaren tarihin Shata da ya fi garxi da gishiri da nuna, sai na ga Sheme ba ya son nan wajen. Alhali abubuwan da ya zubda suma masu amfani ne. Mahaifin Shata mahalbi ne kuma gagararre, duk hatsabibancin sa Shata ya gaje su. Don haka komin iya yin mutum ba ya raba Shata da wannan hatsabibanci don gadon sa ne, saidai in ba ya son gaskiya, kamar kwatsam a ga ya vace ko a ganshi cikin fili ba tare da an ga isowar sa wurin ba. 
(Idan ana taron aikin gayya ko na mahalba, ba a ganin lokacin da mahaifin Shata za ya iso wurin, saidai a ganshi a tsakiyar fili, to shima Shata ya sha saidai a ganshi a fili ba a ga ta inda ya zo ba. Da mutum ya cire wannan a tarihin Shata to ya vata shi, kuma zancensa ya tashi daga tarihin makaxin ya koma wani abu daban. Ka na iya raba mutum da abin da ya gada? An tabbatar Ibrahim Yaro ya na vacewa (ba mamaki ba ne saboda mahalbi ne) kuma ya na iya shiga cikin kukar gidan su ya kwana 2 bai fito ba. Ko kuma in ya shige ta sai a ga ya vulla a cikin tafkin Musawa. Daga gida kuma ya na kiran namun daji su zo wajen sa. Tsohuwar matar Shata da su ka zauna da shi a Musawa ta shaida mani haka, ta ce an yi abin a gabanta ba sau xaya ba, ba sau biyu ba.Ya na kuma ba mahalba asirin kama dabba. Don na faxi tarihin mutum ai ba aibata shi na yi ba. To don dai labarin daga gare ni ya fito saboda hassada da kushe sai a qaryata ni? Saboda ba'a qaunata ? Af, ba hatsabibancin su ka sanya shi ya yi kiwon kadoji har daga baya Shatan ya gaje su daga hannun sa ba? Tsofaffin da su ka bani labarin wasun su na nan da rai. Vangaren hatsabibancin Shata, Sheme babu ruwan sa da wannan, ni kuma vangaren da na fi so kenan. Ya ce wai babu scientific proof.  To Sheme ya je Musawa ya nemo tarihin Babu ya sha mamaki. In kuma an yi musun hakan, to a ce kiwon kadojin ma bai yi ba mana)  
Tun farko, yakamata a ce ra'ayin mu da aqidar mu da tunanin mu, mu marubutan sun zo iri xaya, sai aka samu akasin haka.  
A vangaren abubuwan da Sheme ke rubutawa akan Shata, akwai tawaya, saboda na rantse da Allah bai san Shata ba, ba ya kuma son ya san ko wanene shi. Tun a littafin farko, na jawo hankalin sa a kan matattun waqoqi da basu samu gatancin da aka naxe su a faya-fayin garmaho da Telbijin ba, cewa sun fi rayayyun waqoqin sa (waxanda aka xauka a Rediyo da Telbijin) garxi da azanci da hikima tunda su ya riga yi, har ya zuwa tsakiyar shekarun 1960. To duk waqoqin Shaa dodon hoto ne, ma'ana: su na da qanne ko yayye. Wadda duk ya yi, to watarana sai ya wanke ta ya yi samfurin wata irin ta. Amma Sheme bai yarda da wannan ba. Misali, Bakandamiya kala 130 ce, a cikin littafi na. Shi a wurin sa Bakandamiya ba ta fi kala 10 ba. A nan ma mun sha bambam. Da za a yi wa tarihin Sheme na Shata gwagwa za a gane cewa zunzurutun tarihin Shatan da ya sani ba wani abin a zo a gani ba ne. 

Irin fasalin intabiyu da Sheme ke yi ma mutanen Shata ya taqaita su kurum ga waxanda ya yi wa waqa. Shi ko wanda Shata ya yi wa waqa bai san Shata ba kamar maroq ko makaxin Shata, don shi da shi ake yawo. Shi wanda aka yi ma waqa ai zaune ya ke wuri xaya sai randa aka iske shi. Ni kuma a intabiyu, na fi son in karkata ga maroqa da Adamusawa ('ya amshin Shata) don su ke da tarihi. Su, sun yi ma Sheme nisa saboda a karkaru su ke zaune, su ko waxanda ya yi ma waqa ga su nan ko'ina birjik har cikin Abuja. Don haka Sheme ya huta ba sai ya wahala ya tafi karkaru ba. Shi ya fi jin daxin ganawa da su akan Adamusawa. 
Dama ni na yi wahala na shiga lunguna-lunguna da qauyuka na nemi zancen Shata daga hannn Adamusawa da waxanda ya yi zama da su. Na yi imanin cewa Sheme ba za ya iya yin wannan wahalar ba. 
Sannan intabiyun Sheme ba mai nauyi ba ce, kuma ba ta ba da wani abin kirki da ake son a samu, duk da ya ke shi Xan Jarida ne. Misli, mun je Zariya tare da shi wurin A'isha Yalwar Yakubi Shandam, amma saboda nawar sa da rashin yi mata allurar zaqulo labarin dangantakar ta da Shata sai ma ta ce mana aiki ta ke yi kuma ta na da baqi. Qarshe mu ka tashi aka yi asarar hira da ita. Sheme ya cika nuna lallashin mutum in ya je intabiyu, ni kuwa da zafi zan afka ma mutum, wannan zafin shi za ya sanya mutum ya zabura ya ga lallai da gaske na ke. Shi Shatan, ba da zafi-zafi ya kai ga shaharar ba? Da ya nuna son jiki ko nawa ko lallashi da ya samu xaukaka da shaharar da ya samu? Shi ya sanya ni ke da ideas masu yawa; idan na fara bayani mutane ba su so in daina, kuma sun a da tabbacin abin da duk aka tambayeni san bada gamsassar amsa, don na samo ta. Ina kua allurar yi a duk wanda na je wurin sa hira, ko bai so yin hirar ba dole ya tsaya ya saurare ni. Misali, Alasan Abdallah Dunu, da na same shi a Kano, da farko sai ya ce mani ba ya da lokaci. Amma ina ce masa 'ranka ya daxe da Kwastan qwara ne ya zo da kan sa da ka ce ba ka da lokaci ?'Sai ya yi znnbur ya tashi zaune ya ce 'yaro ina ka samo labarin Kwastan ? Ai kawai sai ya ce mani zauna, na zauna, sannan mu ka dosa hira, ya shiga bani labari tun lokacin da ya yi tuqi a gidan Kwastan xin a Malumfashi, shi da su Bawa Janke. Wasu mutanen da barkwanci-barkwanci, allura-allura ake kamo su da zaren labari, amma shi Sheme ba ya da wannan salon. Shi ya sanya hira ta ta fi ta kowa yawa. Bugu da qari, wanda duk zan je wurinsa, dama na haddace waqar sa a bisa kai, da na je saidai in yi ta rero masa baituttukan ina yi masa tambayoyi a kansu. Jin ina yin waqarsa  za ta say a qara bada azama. 

Gaba xayan aikin, Sheme na da jan qafa, ba ya da sauri. Ga shi ayyuka sun yi masa yawa. Ba ya da lokacin aikin littafin Shata. Ya na wallafa mujallar FIM, don haka ya na da ofis a Kano da Kaduna, daga baya ya buxe wani a Abuja. Ga aikin littafin Shehu 'Yar'aduwa. Kuma kullum ya na hanya, ba ya Kano ba ya Kaduna, ba ya Abuja. Gashi duk watan Duniya sai mujallarsa ta fito, kuma shi ke shirya ta yanda ya ke so, iyakaci ma'aikatan sa s nemo masa labaru. Amma saboda qwararren mai aikin jarida ne, kuma a Ingila ya yi kwas akan maxaba'ar littafi, shi ke tsara yanda mujallar za ta kasance don ta fito da kyau da inganci, kuma haka ta ke xin. Don haka, ya kasa zama ya tattara hankalinsa wuri xaya ya gama mana aikin mu. Shi kuma ya qi yarda ya bamu aikin mu tama shi, ya tattara ya riqe. Har ta kai an kai matsayin da ba mu ma san halin da ake ciki ba. Wannan ya sanya mu duka ukun mu ka ma vata da shi. Mun daxe ba mu magana ma. Sauran biyun su ka riqa lallashi na su na cewa 'mu rabi da shi, watarana in Allah Ya so ai dole ya gama aikin ya fiddo shi a buga'. A haka mu ka yi ta lallava shi har 2006 da aka buga littafin. 



Wasu Abubuwan Takaici ma su ne: 

A. wasu hirarrakin da na fassara a takardu na bashi na Hajiya Yalwa (matar) Shata da ta Musa Musawa da Laila Dogonyaro da Sidi Mijin Hotiho su ka vace ko salwanta a tsakanin kayansa saboda takardun sa sun yi yawa, kuma bai maida hankali ga aikin ba; ga na FIM ga na Tarihin 'Yar'aduwa. Saidai ni na dawo na sake rubuta wasu na bashi tunda su na cikin kai na na haddace su. 
B. Hotunan da mu ka xauka da Shata lokacin wannan ziyara ta tarihi kala 12, da kyamarar Sheme mu ka xauke su, wadda ya sawo a Ingila. Amma an kai wata 3 ina fama da shi ya kai ta a zare dodon hoton a wanke mana hotunan nan, kada mu yi wasa da su don a tarihi ne. Har na ke kwatanta masa cewa kyamara sumatsi ke gare ta. Qarshe ya qi, har abinda ba a so ya faru ya faru. Rannan ya shigo Kaduna daga Zariya, a daidai NDA wani mutum ya tsayar da shi, ya xauko shi, jikkar da kyamarar ke ciki ta na a bayan mota (tunda da ita ya ke yawo) Wannan tsinannen mutumen ya zage jikkar ya xauke kyamarar, duk da fim xin da ke ciki na hotunan mu da Dodon waqa. Su na kai wa junction  na Unguwar Sarki mutumin ya sauka. Sheme na qara gusawa gaba sai ya tuna, ya tsaya ya duba jikka ya ga mutumin nan ya sace wannan kyamara. To ka ga duk sakaci da nawar Sheme ta jawo mana haka. Yakamata Sheme ya bamu haquri akan wannan abin da ya yi mana. Nan dai wauta ce da sakaci. 
To tunda an rabu da qyar kai ka yi karambanin koma ma mutum a yi wani littafin tare ? Idan ka koma ka sake haxewa da mutum, duk abinda ya biyo baya kai ka ja ma kan ka kada ka yi kuka da wani. 
C. Lokacin da na tafi Katsina, bayan rasuwar Shata da wata 5, watau cikin Nuwamba 1999 sai na zarce Daura don in gana da Sarkin Daura, kan zancen yiwuwar xaukar xawainiyar bugawa. Tunda a lokacin babbar matsalar mu ita ce kuxin buga littafin. A fadar Sarki, aka ce mani ya na ciki ba za ya fito ba. Na gabatar da abin da ya kawo ni ga fadawa. Amma wani dogari ya ce mani idan na san wani mutum babba a Daura in je in samo takarda daga gare shi in kawo za su kai ma sa. Ana cikin maida magana sai su ka ji na ambaci Qanqara (gari na). Sai wani daga cikin su ya ce 'ai kuwa xazu da safe Ibrahim Tukur Qanqara manajan (tsohon almajrin mahaifi na ne a Qaramar Firamare ta Qanqara) Bankin Union na Daura ya zo su ka gaisa da Sarki, don mutumin sa ne. Sai su ka bani shawarar in tafi in same shi ofis. Na ruga na same shi, mu ka gaisa. Da na faxa masa abinda ke tafe da ni, wallahi summa tallahi,na rantse da Alkur'ani mai tsarki nan take ba vata lokaci ya xauko wayar teburi ya buga ma Sarkin Daura Bashar. Su ka yi magana, ya gabatar da ni ya kuma ce ina son inga Sarki akan littafin,  Sarki ya ce ya faxa mani in zo ranar talata mai zuwa da qarfe 12 na rana in kuma zo da littafin, don Litinin ya na da taro a Kano. Ibrahim Tukur kuma ya tabbatar mani cewa shi za ya sanya Sarki ya biya kuxin buga littafin. Tunda na bar Daura (ran Alhamis ne) na tafi Kaduna, ba zullumin da na ke shi ne yanda zan raba Sheme da littafin nan, don na san da qyar za ya yarda ya bani littafin. Kuma haka ta faru, don da na je na bshi labarin yanda mu ka yi da Sarkin Daura, amma wallahi summa tallahi ya hana ni littafin. Na ce masa ran Lahadi na ke son in koma Katsina, in kwana ran Litinin in tafi Daura, wanshekare in tafi in ga Sarki. Da ya xauki zancen har zucci da ya bani shi tun Lahadin. Amma har Litini bai ba ni ba, ina ta da lallashin sa. 
Ran Talata da safe na yi sammako na tafi gidan sa, na daxe a falo bai tashi barci ba. Matarsa ta shaida masa na zo. Sai da na daxe sannan ya fito ya bani littafin; don ya san bata yiwuwa. A lokacin qarfe 9 na sfe ta yi kuma ina a Kaduna, yaushe na gane Daura a cikin awa 3 ?
Abinda Sheme ke nufi shi ne; duk wani yunquri daga xayan mu a wurin sa aikin banza ne, ba mu isa ba, don ya raina mu. Ya na gani taimakon da za ya taso daga vangaren sa shi ne taimako, ba namu ba. Wai shugaban mu kenan a tafiyar Shata. Wallahi tallahi nan zance ya tsaya don ban ma tafi ba. Watarana nag a Ibrahim Tukur a Qanqara, ya tambaye ni mi yasa ban koma ba? Na faxa masa dalili. Ya ce 'Allah Shi kyauta'. 
D. Cikn Maris 2000, sannan dangantaka ni da Sheme ta yi yami, sai na same shi a gidan Shehu Musa 'Yar'aduwa da ke kusa da gidan gwamnati na Katsina, na same shi da dare. Ni na je ne don idan akwai rashin jituwa mu gyara varakar, mu ba juna haquri, sannan a ga minene kuma za a dosa a gaba don a ci nasarar fitar wannan littafi. Amma sai Sheme ya same ni ya yi mani kaca-kaca, ya wulaqanta ni ya ce 'littafi ba a baka, ka tafi duk inda za ka kai ni qara ka kai ni, kuma ni da kai har abada, kada ka qara zuwa inda na ke, ko ka ganni a wuri kada ka nuna ka sanni. Har ya na buga mani misali, ya ce a rayuwarsa mutum biyu ya tava yi ma haka saboda sun harzuqa shi. Daga wani abokin sa (ya faxa mani sunan sa, na manta) sai ni. Ya kuma ce:' littafi, idan Alla Ya hukunta za a wallafa shi, to sai a wallafa, idan kuma Bai nufa ba to. Ina fita kuma sai ya zo ya wuce ni a mota ya tafi cikin gari, ni ina ta tafiya qasa. Yanzu saboda Allah, mai karatu ka na ganin Sheme ya yi adalci a nan ?. Wai shugaba kenan. Shi shugaba, na yi tsammanin ya kamata a ce ya na da haquri akan wanda yak e yi ma shugabanci, kuma idan an smu masala, ya kamata shi za a fara gayyatar mutane don a gyara, to ban da Sheme. Da haka ya yi mana shugabancin tafiyar Shata. Idan na yi masa qarya kada Allah Ya bani abinda na ke nema Duniya da lafira.  

Ko an samu kuskure ko gyara, misali: a kan shekaru na faruwar wani abu, Sheme ba za ya gyara ba, ko da mun lurar da shi akan hakan. Ga hujja amma sai a yi ta gardama da shi. Da na fahmci haka, ko da na ga kuskure sai in yi shiru in qyale shi. Misali, a bukin 'Yan Sarki na su Ado Bayero, na ce Disamba 1952 ((tunda Galadiman Kano da Walin Kano da Sabo Dogarai da Inuwa Xalibi duk sun tabbatar mani haka) ne aka yi, shi kuma Sheme sai ya tsaya akan dole 1954 ne wai don ya ji Shatan na cewa '… a zamanin Sanusi Mamman' Na ce masa ai sannan Sanusi bai kai ga zama Sarki ba, ya na Ciroman Kano, amma shi ya yi hidimar bukin, shi ko Shata babu ruwansa, wanda ya ga ya na karakaina a buki shi a wurinsa shi ke da zamani. Misali na biyu shi ne ba Garba Goga ya fara kai Shata Funtuwa ba, don ya faxi haka a waqa ba dole ba ne a ce daidai ne, shi ya san abinda ya ke nufi da Kalmar. Bature makaxi Bakori shi ya fara kai Shata Funtuwa cikin Yuli 1943, sannan bai kai ga sanin Goga ba ma. Ba yanda ban yi ba da Sheme ya canza wannan zancen amma ya qi.  

Tarihin da Sheme ya fi so na Shata shi ne gama-gari wanda kowa ya sani. Ni kuma tarihin Shata da na fi so ya fito a littafin mu shine voyayye, wanda ya yi nisa, wanda Duniya ba ta san da shi ba. Ka ga nan dole mu raba gari. Don abinda mutanen Duniya ba su sani ba game da Shata shi su ka fi son su ji. Shi ya sanya ake matuqar son hirarraki na na Rediyo da Telbijin fiye da kowanne mai bada tarihin Shata. Wannan ya sanya Idan Sheme bai san mutum ba ko bai tava jin labarin sa ba, ko na yi masa intabiyu na kawo masa ba ya sanyawa sai ya zubas. Kada Sheme ya manta, tarihin Shata ya fi karkata ga waxannan qasqantattun mutane maroqa da makaxa (tunda karkara ya tashi) da ya ke ganin shi ya raina. 

Ina son idan za a yi hira da mutum, to a yi hira mai zafi, doguwa. Saboda ni mutum ne mai zafin hannu, mai azama, kamar dai yanda Shatan ya ke, watau tsaitsaye askin doki. To duk hirarrakin da abokaina su ka yi ba su gamsar da ni ba, don ba masu nauyi ba ne. Sabili da haka, galiban duk sai da na koma daga baya na sake hira da mutane, ba ma dai a nan qwaryar Kano. A baya kafin mu haxe, abokanmu sun yi hira da su Umaru da Uwawu da Hassan sarkin Dogarai, da Liman 'Yalleman, da sauran su, amma da ban gamsu ba sai da na bi su na sake ganawa da su, saboda ni abin na cikin jini na. Dama a rayuwata na fi son zama cikin dattawan mutane ba yara ba, shi ya sanya in na yi magana a rediyo sai a yi ta mamaki, ana cewa 'mun xauka tsarar Shata ne ma ashe ma yaro ne'. To zama da tsofaffi ya kawo haka. Kuma hira xaya tilo da wanda Shata ya yi ma waqa wallahi ba ta isa, sai an yi da yawa don a samu abinda ake so. Ta yiwu shi wanda ka je  wurinsa tsoho ne, ya manta wasu abubuwa da yawa, to in ka koma sai ka qara samun abin da ya tuna kuma. Su abokaina da sun yi hira sau xaya shikenan, ni kuma naci ke gare ni, yawan zuwa na wurin mutum ke sanyawa mu ma zama kamar 'yan uwa ma. 
Saboda wannan takardar yarjejeniya da mu ka rubuta shi ya sanya Sheme za ya yi ta yi mani cin kashi, kuma in yi ta haquri ba zan valle in samu 'yanci na ba? Ba zan yarda takarda ta tauye ni in rasa 'yanci na ba. 
Za mu xora a gaba insha Allahu.

KARAIRAYI 16 A MARTANIN ALIYU IBRAHIM KANKARA Daga IBRAHIM SHEME

A ranar Juma'a da ta gabata, jaridar Aminiya ta soma buga hirar da wakilin ta, Bashir Yahuza Malumfashi, ya yi da ni a kan sabon bugun littafin tarihin Alh. (Dr.) Mamman Shata Katsina mai taken "Shata Ikon Allah!" wanda ya fito kwanan nan. Za ta ci gaba da buga hirar a gobe Juma'a, in-sha Allah.

Jiya, sai ga martani ya fito daga Dr Aliyu Ibrahim Kankara, daya daga cikin mu hudu da mu ka yi binciken farko don a rubuta littafin. Ban so in yi cacar baki da Kankara kan wani abu da ya shafi littafin ba, shi ya sa ma na yi hirar da Aminiya gaba-gadi a bisa tunanin ko mutum ba ya kaunar Allah idan ya karanta zai yarda da cewar lallai hakikanin abin da ya faru kenan. Haka kuma akwai wadanda su ka ce mani, "Kada ka kula shi, domin ba matsayin ku daya a idon al'umma ba." 

To, ba maganar matsayi ba ce, magana ce ta menene mu ka bar wa tarihi; idan na yi shiru kan karan-tsayen da Kankara ya yi wa gaskiyar abin da ya faru, to ban yi wa tarihi adalci ba. Haka kuma ni ba irin mutanen nan ba ne da za su ga karya muraran su kyale saboda wani. Shi ya sa na ga dacewar in nuna wa jama'a cewa akwai karairayi jingim a rubutun na Kankara, wadanda na ke so a fahimta. Daga nan, idan mutum ya karanta, sai ya zabi na zabe!

Kafin in jero karairayin, ina so in yi shimfida da cewar ba wannan ba ne karo na farko da Aliyu ya fara shara karya game da tarihin Shata ko dangantakar da ya ce wai ya na da ita da mawakin. Tun a farkon haduwar mu, lokacin da ya kawo mani takardun da ya rubuta kan Shata don in gani, na ga dimbin abubuwan shaci-fadi da ya rubuta wadanda hankali ba zai iya dauka ba, wadanda ko d'an karamin bincike ma zai nuna wa mutum cewar karya ne. Irin wadannan abubuwan, na yi watsi da su a lokacin da na ke rubuta littafin "Shata Ikon Allah!" da aka kaddamar a cikin shekarar 2006. Na san Kankara bai ji dadin watsi da na yi da su ba, kuma hakan na daga cikin dalilan shi na warewa daga gare mu, mu "marubutan littafin Shata", ya tafi ya dauki littafin mu ya baddala shi ya fito da wani a matsayin nasa (zan yi magana kan wannan a nan gaba, ba a yau ba).

Na biyu, a zantuttukan sa a soshiyal midiya da hirarrakin sa a rediyo na sha jin irin yadda Kankara ya ke zubo karairayi game da Shata ko tarayyar da ya ke ikirarin ya na da ita da Shatan, ba tare da kawo hujjar da za ta tabbatar da hakan ba. Hasali ma dai, Kankara ya saba da sheka k'arya game da Shata ta yadda har akwai alamun ya yi amanna da cewa karairayin sa gaskiya ne. Shi ya sa a duk inda ya zauna, sai ya dinga zuba ratatata kan tarihin Shata da ba gaskiya ba ne, ya debo dahir ya gwamutsa da kirkira, ya fitar da wata magana wadda yawancin masu saurare ba za su kama ba. Har ta kai mutane da dama na mamakin yadda za a ce wai mutum mai PhD ne ke magana haka babu kangado, sai ka ce ko sakandare bai gama ba!

Irin wannan kame-kamen ne na gani a rubutun shi na jiya mai take irin na taken hira ta da Aminiya, wato "Ni Na Fara Rubuta Littafin Tarihin Shata", taken da shi kan sa ba daidai ba ne (kamar yadda na fada wa Bashir Yahuza bayan na karanta hirar da ya yi da ni).

Bari mu koma kan karairayin Kankara. Da farko, ban damu da yaushe ne Kankara ya soma kaunar Shata ba; ko tun ya na cikin ciki ya fara son sa, ba damuwa ta ba ce. Amma wace irin soyayyar ya ke yi masa har ta kasance iyalin marigayin ba su yarda da abubuwan da ya ke yad'awa game da mahaifin su ba? Sannan wace irin soyayya ce ya ke yad'awa a hirarrakin sa ta yadda duk manazarcin da ya bincika zai tarar da cewa zuk'i-ta-malle ce wadda ba ta iya tsayawa da kafafun ta? Misali, "sai da aljannu su ka yi wa wata 'yar bori bushara da haihuwar Shata!" "A ranar da aka haifi Shata, an ji kalangai su na tashi a sararin samaniyar garin Musawa!" "Kafin ranar sunan Shata, Shatan ya bace daga zanin goyon sa, ba a sake ganin sa ba sai bayan kwana uku!" "Kai, Shata ba mutum ba ne, aljani ne!" Da dai sauran su.

Bari mu duba martanin Kankara daki-daki.

1.
Cewar Kankara: "Cikin 1990 na ya kai wa Shata littafin da na rubuta": 

Wannan maganar, da makamantan ta da ya yi a baya, ba gaskiya ba ce. Ba zan ce Kankara ba ya son Shata kafin haduwa ta da shi ba, amma wallahi shi da Shata ba su san juna ba sai da na kai shi wajen Shatan a Funtuwa bayan hadewar mu. Zurfin hulda ta da Kankara, tare da zurfin sanayya ta da Alhaji Shata da yaran shi, ta isa ta sa in san idan Kankara da mawakin sun san juna kafin haduwa ta da Kankara. Babu wani lokaci da wani daga cikin su ya fada mani ya san dayan. In da Kankara ya san Shata kafin in kai shi wurin sa, to da ya fada mani. Haka kuma in da Kankara ya yi wani littafi kan Shata har ya kai masa, to da ya fada mani lokacin da na ce mu je in gabatar da shi ga Shata a cikin 1997. Kuma in da Kankara ya yi littafi kan Shata, to da ya ba ni shi lokacin da mu ka hade, mu ka shiga fafutikar tattara tarihin Shata domin yin littafi.

2. 
"Wai a 1994 Kankara zai tafi NYSC, ya kai wa Shata littafi". 

Wannan ma karya ce ya shirya. Ban san wani labarin Kankara ya nemo izinin Shata don ya rubuta wa wata kungiya a Kano tarihin Shata ba, wanda har ya rubuta ya kai masa da zai tafi bautar kasa. A rubutun shi, Kankara ya ce har ya kammala littafin a 1994, to ya aka yi a 1997 da ya ba ni warkokin da ya rubuta na ga ba su fi shafi 15 na rubutun hannu ba? Shi ne littafin? Ya aka yi bayan haduwar mu, mu ka dinga fadi-tashin bincike don fito da littafin, abin da ya dauke mu shekaru? Sannan idan har a 1994 ya rubuta littafin, to daga 1991 da na fara binciken tarihin har zuwa lokacin babu shakka da na samu labarin sa a wajen Shata ko Ya'u Wazirin Shata ko wani yaron Shata. A gaskiya, Kankara bai rubuta littafi ba a lokacin.

3. 
"Wai Shata ya umarci Kankara da ya yi hira da wasu mutanen Legas da ya wak'e". 

Wannan magana ba gaskiya ba ce, domin in da an yi hakan to babu shakka da Kankara ya je ya yi wadannan hirarrakin. Tun da mu ka fara bincike kan tarihin Shata har mu ka gama a 2006, Kankara bai kawo mana hira ko da kwaya daya da ya yi da daya daga cikin mazauna Legas da Shata ya yi wa waka ba.

4. 
"Wai a 1995 Ya'u Wazirin Shata ya yi wa Kankara maganar Ibrahim Sheme". 

A cikin 1995 ba mu hadu da Kankara ba, ban san shi ba. Hasali ma dai, sai bayan haduwar mu da na dauki Kankara na kai shi wajen Shata sannan ne ya san Ya'u Wazirin Shata. Ni ne na dauki Kankara a mota ta, bayan mun bar gidan Shata, na kai shi gidan Alh. Ya'u na gabatar da shi ga Ya'un. Ko kadan Ya'u Waziri da Kankara ba su nuna wa juna sanayya ba lokacin da na sada su. In da a ce an san Kankara a fadar Shata, to da shi mawakin da shugaban 'yan amshin nasa sun nuna haka lokacin da na kai Kankara wajen su.

5. 
"Wai Ibrahim Sheme ya zauna gida daya da wani Kabiru Dan'azumi Kankara a unguwar Badikko, Kaduna". 

A Badikko, na kama hayar gida sukutum ne (2-bedroom flat da garejin mota da filin tsakar gida). Ban zauna da kowa a gidan ba sai mata ta. Wannan magana shirme ce.

6. 
"Wai ba Ibrahim Malumfashi ya hada Kankara da Ibrahim Sheme ba". 

Babu shakka, ban taba jin ko sunan Kankara ba sai a bakin Malumfashi lokacin da ya bukace ni da in hadu da shi in ga abin da ya rubuta kan Shata. Farfesa Malumfashi na da rai, zai iya tabbatar da wannan magana ko akasin haka.

7. 
"Wai a 1995 Sheme da Kankara su ka hadu har Sheme ya nuna masa aikin littafin da ya yi. Daga nan ba su sake haduwa ba sai a 1997." 

Wannan ma wata karyar ce. A 1995, ban taba jin sunan Kankara ba, sai a 1997 lokacin da Ibrahim Malumfashi ya hada mu. Kuma tun da mu ka hadu ba mu taba rabuwa ba har lokacin da aka kaddamar da "Shata Ikon Allah!" a cikin 2006.

8. 
"Wai Sheme ya ziyarci Kankara a ofis din sa a Kaduna Polytechnic a 1997 inda ya nemi su hade su yi littafi daya".

Wannan ma karya ce. Tun lokacin da Malumfashi ya sada ni da Kankara, ba a yi ko mako daya ba na amince mu ka hade. Sannan ban taba zuwa ofishin Kankara a Kaduna Polytechnic ba; wani zuwa da na yi sau daya rak, na je ne domin in taimaka masa kan wata wuta da ya kunno wa kan sa. Matsalar ita ce wata yarinya daliba ta kai Aliyu Kankara ga hukumomin makarantar, har an kafa kwamitin musamnan ana bincike. Na je ne bisa bukatar Kankara in ga ko zan iya sasanta lamarin, a matsayin sa na abokin aiki na kan littafi. A karshe, ba mu samu nasara ba, domin kwamiti ya bada shawarar a kori Kankara daga aiki. Haka kuwa aka yi, aka kore shi daga aikin koyarwa bisa koken da dalibar sa ta yi. Wannan ne ya sa ya koma aiki a wani kamfanin wasu 'yan kasar Chaina masu hakar ma'adinai a yankin Sakkwato (aikin da Saleh Abu Katsina ya sama masa). Daga can ya kukuta aka dauke shi aiki a matsayin malamin makarantar sakandare (GDSS) ta garin Daudawa da ke Faskari LGA a Jihar Katsina. Malamin Polytechnic ya koma malamin sakandare kenan! Daga nan ne, bayan shekaru, aka dauke shi aiki a Jami'ar Umaru Musa Yar'Adua a Katsina. Nan gaba zan dawo kan ainihin kes din nan da ya sa aka kore shi daga Kadpoly da matsalar da ya samu da Chanis din nan da yadda aka yi ya koma Jami'ar Tarayya da ke  Dutsin-ma, musamman ma yadda wadannan matsalolin su ka kawo mana cikas wajen kammala littafin "Shata Ikon Allah!"

9. 
"Wai matar Kankara na shaidar...!" 

To, ni ban sani ba idan maganar Kassu Zurmi gaskiya ce ba da ya ce "mutum ba ya shaidar dan'uwan shi ko hwada" da kuma fadar Shata a wakar Dambu Dan Mamman cewa "wace shaidar d'an ka za yai ma, in ka hada duka duk dai Dambu ne?"

Wallahi, ban taba zawarcin Kankara don mu hade mu yi littafi ba. Kamar yadda na fada, mun hade da Kankara tun a satin farko na haduwar mu a cikin 1997. Idan na taba zuwa gidan shi, hakan bay a rasa nasaba da aikin da mu ka tsunduma yi ne, ba domin mu hade ba tunda mun riga mun hade. Amma shi ya kan zo gida nay a fi sau shurin masaki, idan za mu yi tafiya ko idan zai karbi kudi a waje na. Saboda haka maganar wai ina zawarcin sa domin mu hade ba gaskiya ba ce.

10. 
"Wai Sheme ya fito 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatu na biyu".

A 1997 lokacin da na fara ganin Kankara har mu ka hade mu yi littafi, ni ba sabon yanka rake ba ne wajen kammala karatun digiri na biyu. Na samu M.A. Journalism Studies daga Cardiff University, a U.K., tun cikin 1994 (shekaru 3 kafin in fara ganin Kankara a rayuwa ta). A 1997 ina daga cikin manyan editoci a kamfanin jaridar New Nigerian.

11. 
"Wai Sheme na tura Kankara ya yi masa hira da jama'ar Shata saboda shi ba ya da lokaci".

Kamar yadda na fada, na fara hira da Shata a 1991 domin rubuta tarihin shi. Shekaru 6 kenan kafin in fara ganin Kankara. A tsawon wannan lokacin, na yi hira da mutane masu yawan gaske. Misali: Garban Bichi, Indon Musawa, Sa'in Katsina Amadu Nafuntuwa, Amadu Doka, Tukur Othman, Turi Muhammadu, Musa Musawa, Munari Jikar Mairo, Nagwandu Mainama, Laila Dogonyaro, Amadu Doka, Danmaraya Jos, Hakimin Bakori Alhaji Tukur Idris Nadabo, Shehu Maigidaje, Halilu Ahmed Getso, Bala Maikaka, da sauran su da dama. Kuma na yi hirarraki da yaran Shata da su ka hada da shugaban 'yan amshi Alhaji Ya'u Wazirin Shata da shugaban makadan kalangun Shata, wato Bawa Dungun Mu'azu. Sannan na je Musawa na yi hira da 'yan'uwan Shata da abokin sa irin su Mal. Ali  Dankane. Duk wannan ya faru ne KAFIN in ma san wani wai shi Aliyu Kankara. Sannan bayan haduwar mu da shi, na ci gaba da yin wasu hirarrakin. Saboda haka maganar ba ni da lokaci ma karya ce.

Tura Kankara da na yi zuwa wasu garuruwan, kamar Bauchi da Gombe, da kuma Musawa saboda ya yi mana hira da Magajin Gari Malam Abdullahi Inde da wasu mutanen, duk cikin raba aiki da mu ka yi bayan mun hade mun zama mu 4 a aikin. Ko ya manta cewar mun raba aiki ta yadda su Yusuf Albasu da Ali Malami su ma za su samo mana wasu hirarrakin, musamman a Kano? Wannan shi ne dadin hadewar ai, wato wannan ya kama nan, wancan ya kama can. Hakan ne ya sa ni ne na yi hira da mutane irin su Dauda Mani da Sarki Jinjiri da Goshin Dangude ba tare da Kankara ya sani ba sai daga baya na fada masa. Abin lura shi ne duk da yake ina yin hirarrakin nan kamar yadda na lissafa a sama, ai kuma ni ne mai rubuta littafin; ni ne wanda ke karance duk abin das u Kankara su ka yayumo, ya fitar da ma'ana daga ciki, ya jera bayanan a cikin littafi inda ya dace; shin ko wannan bai isa aiki ba?

12. 
"Wai Kankara ya hada Sheme da wasu mutanen Shata a Kaduna tunda shi bai san su ba".

Hankali zai iya daukar wannan maganar kuwa? Mutum ne ya same ka ka na bincike domin rubuta littafi, har ka shafe shekara shida ka na yi. Kuma a Kaduna ka ke zaune. Ka yi tafiye-tafiye a wasu garuruwa. To ya za a ce ba ka ma san mutanen da su ne ka ke samo bayani a wajen su ba? 

Kankara ya ambaci Alh. Nagwandu Mainama, wai shi ya hada ni da shi. Wannan ba gaskiya ba ce. Na yi hira da Nagwandu a mayankar da ke Tudun Wada, Kaduna, ba tare da Kankara ba.

Kuma ya ambaci Alh. Amadu Doka mai kukuma, wai shi ya hada mu. Ka ji tantagaryar k'arya! Kankara ya manta cewa Amadu Doka amini na ne na tsawon shekaru tun kafin mu hade, sannan ni din nan ni ne na fara kai shi wajen Amadu Dokan har gida, na gabatar da shi? A nan ma dai, karya ce ya yi wa kwalliya domin ya sayar da ita ga wanda bai ankara ba!

Na yi hira da Amadu Doka domin sakawa a littafin Shata tun a cikin 1993 (shekaru 4 kafin in fara haduwa da Kankara). An buga hirar a mujallar Rana ta ranar 19 ga Oktoba, 1992. A lokacin, ni ne Editan mujallar, kuma ban san wani  Aliyu Kankara a duniya ba.

13. 
"Wai cikin 1998 Sheme ya tafi Funtuwa ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano".

Ban samu Shata domin ya kwanta a asibiti ba. Kamar yadda na sha fadi, a matsayi na na jagoran rubuta tarihin Shata, na sha zuwa in same shi kan wani abu da ya danganci aikin. Kuma ba lallai ba ne sai na je tare da Ali Kankara. Lokacin wannan ziyarar da Kankara ke magana, na je ne domin in yi wata sabuwar hira da Shata kan wasu abubuwa da na lissafa wadanda jama'a ke magana a kan su, misali batun cewar wai Sule Jikan Korau ya taba marin Shata, da batun wai Shata ne ya yi wa Ali Dansaraki makaru ya kasa waka, da batun Garba Goga ne ya fara kai Shata garin Funtuwa kamar yadda mawakin ya ke ambata a Bakandamiya. Kaset din hirar, na ba Kankara ya rubuta shi a takarda, kuma har yau din nan ya ki dawo mani da kaset din. To, a wannan zuwan ne Shata da kan shi ya ba ni labarin su Yusuf Tijjani Albasu da Ali Malami. A lokacin, ni dai ban taba jin wai an kwantar da Shata a asibiti ba.

14. 
"Wai Sheme ya dauki Kankara tare da wani abokin Shemen mai suna Aimana Datti Usman, su ka tafi Funtuwa".

Ban taba yin aboki mai wannan sunan ba. Ina jin dai Aimana abokin Yusuf Albasu ne da su ka je Funtuwa taro lokacin da na gayyato su daga Kano. Ni Yahaya Umar na dauka a Zariya.

15. 
"Wai Shata ne ya ce a hade a yi littafi daya".

Wannan ba gaskiya ba ne. Makasudin kiran su Albasu da Malami shi ne a kwace littafin su, a kore su, bisa hujjar cewa ba a ba su izinin rubuta littafin ba. Da ni aka yi wannan shiri, ba a gaban Kankara ba. Ni ne na bada shawarar a yi littafi daya, bayan mun fita waje na duba aikin da su ka yi, na ga ya burge ni matuka domin sun yi hirarraki da wasu mutane da mu ke so mu yi hira da su, irin su Abubakar Uwawu, Hassan Hadi, Delun Kunya, Hauwa Maituwo, da sauran su. Shawarar  da na bayar cewa a hade, ta ba kowa mamaki, har shi kan sa Shatan, domin ba ta cikin shirin da aka yi a makon da ya gabata. Sannan ko kadan Kankara ba ya goyon bayan hadewar, kawai dai don babu yadda zai yi ni ne a matsayi na na shugaban shi.

16. 
"Wai Shata ya manta da littafin da Kankara ya rubuta wa kungiya, shi kuma kawaici ya hana shi magana".

Wannan ma wani soki-burutsu ne. Lokacin da mu ka je taron da mu ka hade da su Ali Malami da Yusuf Albasu a Funtuwa, an fi shekara daya da hadewa ta da Kankara. Wato kenan Shata ya san ni da Kankara, saboda haka ya yi maganar wani littafin kungiya ai bai taso ba. Me ya sa ma a lokacin da na fara kai Kankara wajen Shata, na ce masa ga wani wanda za mu yi aikin rubuta littafin da shi, ba su nuna sun san juna ba? Dalili shi ne babu wata sanayya tsakanin Shata da Kankara, sannan Kankara bai taba kai wa Shata littafin da ya ke ikirarin ya rubuta ba. In da akwai littafin, kuma in da sun san juna, to da tun tuni na sani. Wannan maganar, kawai kirkira ce aljannun da ke damun kwakwalwar Aliyu Ibrahim Kankara su ka ba shi, shi kuma ya hau kai ya na kokarin yaudarar mutane da ita.

Ina kira ga Aliyu Kankara da ya nuna guntun rikodin ko kwaya daya da ya taba yi da Shata, wato wata hira da su ka yi, ko wani hoto da su ka taba dauka tare, a matsayin nuna sanayyar da ya ke karyar sun yi wa juna shi da mawakin. Na san babu. Dalili shi ne, Kankara da Shata ba su san juna ba kafin in kai Kankara wajen sa, kuma ko da na kai shi din, babu wata sanayya da Shata ya yi masa, domin bai taba zuwa wajen Shata ba tare da ni ba, sai idan na kai shi. Hasali ma dai, Kankara bai taba hyin hira da Shata domin yin littafi ba. Duk abin day a ke fada a bayan rasuwar Shata, kirkira ce irin ta marubucin da kwakwalwar sa ta motsu, ya na ganin dodon wani abu da ya ke ganin kamar ya taba faruwa a rayuwar sa bayan kuwa bai taba faruwa din ba.

Zan yi zango a nan. Zan kawo ci-gaban wannan raddi nan gaba kadan, domin wannan magana yanzu na fara ta.

Bissalam.

NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN TARIHIN SHATA A DUNIYA Dr. Aliyu Ibrahim Qanqara

Na fara son Alhaji Shata da waqoqinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Sa'ilin ban wuce shekaru 6 da haihuwa ba. Tun lokacin son da na ke ma Mamman Shata na musamman ne. Tun iyaye na ba su fahimta har su ka gane. Ko a Telebijin aka nuno shi ya na waqa na kama murna kenan, da zaran kuma an xauke wuta kafin ya ida waqar, to har kuka na ke yi kuma na dinga fushi kenan har safe. 
Ni babana ba ya da wata alaqa da Shata, amma ganin ina son sa ya kan zaunar da ni ya bani labarin sa, na zuwan da ya ke yi a RTK Kaduna (watau BCNN da kuma daga bisani NBC) a tsakanin 1969 da 1972 lokacin mahaifin nawu na aiki a can, da kuma ziyarar da ya kan kai ma amininsa Alhaji Hamza Qanqara har Musawa lokacin ya na aiki a gonar mahaifin Shata Malam Ibrahim Yaro. 
Sai cikin 1975, watarana da babana za ya tafi Katsina, ya ce in shirya in bishi tunda a sannan ban shiga firamare ba, a sa'annan ya na da wata mota Morris Marina. Ba zan manta ba mun shiga Funtuwa a tsakanin mangariba da isha'I, har mu ka bi santar gidan Shata. A daidai qofar gidan Shatan mun zo wucewa sai babana ya ce da ni: 'Ali Gadanga, ga gidan Shata, ga shi can ma zaune qofar gida'. Ya faxi mani hakane saboda sanin da ya yi ina matuqar son makaxin. Sai na ce masa 'mu tsaya in gan shi' Sai ya  ce : 'a'a, saboda mu na sauri'. Amma gab da za mu wuce Allah Ya jiye mani muryar Shatan, na ji ya na cewa 'a zo a kwashe kwanonin abincin nan'. Wannan kenan. 
A tsakanin 1976 da 1978 an kai ni riqo Daura wajen wana Ahmed Ibrahim Qanqara, lokacin ya na aiki a can. To a can mu kan ga wasan Shata a qofar fada in ya ziyarci Sarki, da kuma Neja Club da ke kan hanyar Zangon Daura. Har ma nine Shatan Islamiyya Firamare inda na yi karatu. Idan an gama shara da marece, sai a zo bakin ofishin Hedimasta a yi wasan kwaikwayo, to nan ni kan xan yi waqoqin Shata 'yan ajinmu na yi mani amshi. Sunan Hedimasta xin mu Hamisu Famili, wanda daga baya ya zama Matawallen Daura. 
Cikin 1979 ina aji 5 na Firamare a Qanqara (bayan babana ya bar Kaduna, mai riqo na kuma na bar Daura) sai Shata ya zo kamfe na GNPP a cikin tawagar 'yan siyasa a Qanqara, nan mu ka yi ta bin motar sa da gudu aka zagaya gari da mu, shi kuma ya na waqa. Wannan ta sa wanshekare ni da abokina Garba (Abubakar) Suleiman Qanqara (yanzu yana aiki a Xakin Awon Jini na Asibitin Tarayya ta Katsina) mu ka sawo littafi mai warqa 40 mu ka fara rubuta tarihinsa, har ma mu ka samu shuwagabannin GNPP na yankin Qanqara su ka bamu abinda su ka sani gameda makaxin. Amma a lokacin ana ta yarinta, ba mu xauki abin da gaske ba, sai dai mi? abin da yaro ya ke so kuma ya girma da abin nan a zuciyar sa watarana sai ya tabbata, to ashe Allah Za Ya tabbatar da abin a gaba.
A tsakanin 1986 da 1994 ina karakaina, in kai gwauro in kai mari a tsakanin Daura, Malumfashi, Dutsinma, Qanqara, Funtuwa da Katsina, duk samari masoya Shata sun sanni kuma inda duk na je ana maraba da ni ana kuma son in zauna in bada labari sabo na Shata da na kalato. Sai da ta kai ma a Malumfashi da Daura mun kafa Qungiya ta masoya Duna na Bilkin Sambo.  Cikin 1987 na fara zuwa gidan Shata kuma mu na haxuwa da shi a Zariya (a Magume gidan Sani Gadagau, Bakatoshi) da Kano da Funtuwa da Katsina (Nasara Guest Inn, gidan Sa'in Katsina). Ba wanda ya fara kai ni ya gabatar da ni wurin sa, ni na kai kaina, musamman saboda dalilan can na sama. Cikin 1990, ina tammanin ma ran Lahadi 3/9/1990 ne lokacin na kammala karatu a Kwalejin Ilimi mai zurfi (CAS) Zariya na tafi Funtuwa na samu Shata na kai masa wani littafi da na rubuta mai suna Karon Battar Qarfe (na yaqi ko hikaya ne), na kwana har da safe ni da shi da Mati Bomber mu ka tafi ofishinsa na kan hanyar Zariya, lokacin ya na shugaban Jam'iyyar SDP, nan mu ka wuni. Na gabatar masa da littafi, na kuma buqaci ina so ya biya kuxi a wallafa littafin. Amma ban samu nasara ba, don bai ce ya amince ba, bai kuma ce ba ya yi ba. Na yi waqoqin Shata a CAS Zariya a qungiyar mu ta Hausa, a matsayi na na Shatan CAS, sannan da ina Jami'ar Ahmadu Bello na zama Shatan ABU na qungiyar Hausa, duk don dalilin soyayya ta da Shata, mai benen-bene na Izzatu Musawa. Ka ga kenan wanda duk za ya bada labarin ko nuna son Shata baya na ya ke. Wanda duk ya sha wuta baran tsire ne, kuma labarin dare a tambayi kura. 

Mafarin Tunanin Wallafa Littafin Tarihin Shata, 1992
A cikin 1992, lokacin ina karatun Digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello, aji biyu (300 Level) Allah Ya haxa ni da wani yaro a Jami'ar mai qwazo mai ilimi ana ce masa Kabiru Husaini Gwangwazo, kuma lokacin ya na karanta Digiri akan harshen Turanci. Mun fara haxuwa da shi a taron OUA na wasan kwaikwayo na xaliban Turanci, inda ya fito a matsayin Shugaban Zaire watau Mobutu Sese Sekou. Sha'awar da ya bani ta sa na nemi mu yi abotaka, ya amince. Muna nan, mu na nan, ya zo wuri na, nima in je wurin sa. Sai rannan na xauki littafi na na Hausa da na rubuta mai suna Saqo Daga Birni Al-Shabdad (na hikaya ne) na ba Gwangwazo domin ya duba mani. Bayan kwanaki, sai wani xan rikici ya sanya aka rufe Jammi'ar. Ina gida Qanqara, sai na yi amfani da wannan damar na tafi Kano wajen sa domin in amso littafin. Sai na tarar an tsare shi a Ofishin 'Yan sanda na Bompai saboda littafin Xanmasanin Kano da ya rubuta, aka qaddamar, amma a baya ya ranci kuxaxen mutane saboda hidimar bai biya su ba, sun sa an kama shi. 
To, a unguwar Takuntawa inda ya ke da zama sai aka kai ni wajen abokan hulxar sa, to su su ka kai ni wajen sa a Bompai. Sai na tarar suna da wata qungiya mai suna Young Writers Club (YWC) Kano, wadda Kabirun ma mamba ne. To nan su ka riqe ni na yi kwanaki a wajen su, su ka yi mani abin arziki, nan kuma na riqa kwana wajen su. Kuma su ka bani fam na cika na zama xan qungiya. Ina tuna cikin su akwai Suleiman Gezawa, Rabi'u Kura, Rabi'u Mohammed, Mohammed Garzali, da sauransu. A cikin shirye-shiryen qungiyar ana rubuta tarihin mutanen da su ka shahara ko na garuruwa. To sai su ka bani shawara mi za ya hana in tafi Funtuwa in nemo izinin rubuta tarihin Shata daga wajen sa ? Tunda dama sun yi tunanin hakan tun kafin in baqunce su. Sai na amince. Na tafi Funtuwa, na yi sa'a na samu Shata a gida, na bashi labarin abinda ake ciki da qudurin wannan qungiya, da abin da ta sanya ni in yi mata. Ya yi murna. Har na ce masa : 'sun ce ka faxi mani ranar da ka ke a gari, don mu zo tare da su'. Ba zan manta ba har ya kama faxa ya na ce mani 'ai yanzu na girma, na daina yawon zage, bare a ce a za a zo ba a same ni ba, saidai fa ko in kun ji ana wani buki a Rediyo, watakila zan je, to sai ku dakata sai randa ku ka ji ba a yin wata sabga ko naxin sarauta'. Mu ka rabu a haka. Na koma Kano na shaida masu. Su ka bani dama da in rubuta littafin. Na fara rubutu, wanda ya kai ni har cikin 1994 (bayan shekara 2 kenan) Na kammala. Sai mu ka kai littafin ga Ahmed Mohammed wani mai kafanin buga littattafai a Gidan Goldie kusa da Singer, Kano. Ana ta cuku-cukun ya za a yi a samu kuxi a buga shi, sai na tafi bautar qasa a Legas. Ran da ma zani tafi, na biya ta Funtuwa na yi bankwana da Shata (ran Lahadi 13/11/1994) har ma na bashi kofin littafin, ya amsa ya riqa ya duba. Har ya na cewa 'yanzu nan wannan duk aikin tarihi na ne? Na ce masa 'e'. Ya yi fatar Allah sa albarka. Sannan ya ce idan na dawo daga Ikko za mu zauna. Ya kuma lissafa mani wasu a Legas da in na je in yi ma intabiyu, mutanen sa kamar su Alhaji Na'Allah Xan Ibrahim da Alhaji Salmanu Agege, shugaban 'Yan Daudu na Afirka, da sauran su. Kuma na yi hakan.
 
Shirya Littafin Shata Ikon Allah

Na dawo daga bautar qasa cikin 1995. Sai kuma abokan aiki na na Kano su ka nuna gazawa ga buga littafi na jan qafa. Waje xaya kuma na samu labarin Ibrahim Sheme daga Ya'u Wazirin Shata da wani abokina Kabir Xan'azumi Qanqara wanda mazaunin Kaduna ne, bil hasali ma gida xaya su ke zaune da Sheme xin a unguwar Badikko. Kafin Ya'u waziri ya qara tunkara ta da maganar Sheme, sai kwaram rannan Shata ya yi ma ni bayanin sa. Ya ce mani na san shi? Na ce masa 'ban san shi ba, ba mu tava haxuwa ba'. Shata ya ce mani ya kamata mu haxu, abinda ba ni da shi ya taimaka mani da shi, shi ma abinda ba ya da shi, da ni ni ke da shi sai in bashi'.  Amma bai nuna ya na so mu haxe ba, amma ni a fahimta ta haka Shata ke nufi.  A waje xaya Ibrahim Malumfashi (wanda ya zama Farfesan Hausa daga bisani) ma ya tava yi mani maganar sa, amma ba shi ya kai ni wurin sa ba.  Ni na kai kai na wurin Sheme a gidan san a Badikko xin nan da dare, ina kuma zaton cikin 1995 xin ne, don lokacin ban ma gama bautar qasa ba.  Sheme ya yi murna da gani na, cewa ya daxe ya na jin labari na amma sai rannan mu ka haxu. Ya zaunar da ni, ya xauko mani aikin san a littafin Shata na gani, na kuma yaba.  Tun daga rannan bamu qara haxuwa ba sai cikin 1997 da na koma Kwalejin Ilimin Kimiyya ta Kaduna da aiki. Ya tava samu na a ofis, ya nunaya kamata idan zamu haxe ayyukan mu wuri xaya mu yi haka, idan kuma ba mu yi to kowa ya kama gabansa. Matata Habiba ('yar mutanen Mangu)ta na sheda cewa Sheme, ban da ofis (tunda wannan ba ta gani ba) ya tava zuwa gida na a nan Kwanar PRP kusa da Angwan Sanusi duk akan zancen yiwuwar haxewar mu. Da, da farko Sheme na zawarci na amma na so in noqe saboda halin rayuwa a gaba, amma sai matata ta nuna tunda ya nuna yana so mu haxe in xauki aiki na in bashi, ta ce ta tabbata a gaba abin alheri za ya zama. Ta kuma tabbatar mani da cewa duk da ya ke ba ta tava ma ganin sa ba, ta san ba za ya cuce ni ba. Na rantse da girman Allah abin da ya faru kenan. Sai na aminta. Ran wata Asabar da safe Ibrahim Sheme ya zo waje na ya ce in xauko masa littafi na ya gani. Ba musu na shiga na xauko littafi gaba xaya na bashi, don ni ba na iya tsallake maganar matata. Na yarda da ita. Mu na nan mu na nan, sai ya tura ni in yi intabiyu da wasu mutanen Shata, don shi ayyukan ofis sun sha masa kai. Kuma ina ta yi masa biyayya saboda ko ba komi akwai tazarar shekaru kimanin 2 ko 3 ma kuma ya na gabana a makaranta. Gashi a lokacin ya na 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatun Digiri na Biyu daga Ingila, ya na ta bani sha'awa. Inda duk ya tura ni ba gardama sai in tafi, watau a nan Kaduna. Sannan kuma na kan xauke shi in kaishi ga wasu da Shatan ya yi ma waqa da shi bai ma san su ba, misali: Malam Na Gwandu mai nama, wanda ta hanyar Ahmadu Doka na san a Kaduna ya ke da zama. Sannan na xauke shi na kaishi ga Hauwa 'yar Bori matar marigayi Sarkin Bori Sule a Titin Vashama Tudun Wada Kaduna. Dole ne in fi Ibrahim Sheme sanin mutanen da Shata ya waqe sabili da a kullum ina tare da Ahmadu Doka (unguwa xaya mu ke zaune) da sauran makaxa da mawaqa da su ka sha yin kwaramniya da Shatan, su ke bayyana mani mutanen Shatan. Ni da Doka, kuluyaumin ba mu da wani labari sai na Shatan.
Cikin 1998 sai Sheme ya tafi Funtuwa, ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano. A nan ya samu labarin wasu 'yan Kano su 2 su na rubuta tarihin sa daga bakin Shatan, don sun ma same shi aasibiti sun nuna masa aikin da su ka yi. Saidai su Sarkin Daura ya sanya su. Saboda haka Shata ya ce ma Sheme ya tafi Kano ya nemo su ya ce su zo Funtuwa ya na kiran su, don ya sanya su haxe da mu. Amma Shata ya yi ma Sheme kashedin kada ya bayyana masu cewa buqatar sa a haxe. Sheme ya dawo Kaduna ya same ni gidan marigayi Adamu Yusuf BBC ya bayyana mani abinda ke faruwa. Har na vata rai sai ya bani haquri y ace haka Allah Ya so kuma mu yi fatan Allah sa abin ya zama alheri. Mu ka sa ranar tafiya Funtuwa, watau Asabar mai zuwa ta ran 19/9/1998. Tun ran Juma'a Sheme ya xauke ni, tare da wani abokinsa Aimana Datti Usman mu ka tafi mu ka kwana Funtuwa. Wanshekare da safe mu ka haxu da baqi daga Kano a gaban Shata. Nan da nan Shata ya nuna da za a haxe da ya fi, amma mu je mu yi shawara. Mu ka fito garejin motar sa mu ka yanke cewa mu 4 mu zama xaya ga wannan tafiya. Mu ka koma mu ka shaida masa.
Amma cikin ikon Allah sai Allah Ya mantar da Shata ya tuna ma Sheme da sauran baqin nan wancan zancen littafin sa da na ke yi da qungiyar YWC ta Kano su ka sanya ni. Ni kuma, saboda kawaici sai Allah Ya rufe mani baki, saboda ma ina ganin ga wani sabon shafi an buxe, to mi za ya sanya in kawo zancen abin da ma ya wuce? 
Mu kwana nan, za mu xora a gaba insha Allahu.

KABILANCI NE BABBAR MATSALAR NIJERYA-Van der wel

Daga Rabiu Muhammad (Abu Hidaya)

A wani binciken sirri da wata baturiya yar kasar Kanada (CANADA) mai suna Marianne Van der wel ta yi wanda ta wallafa a shafinta na sada zumunta(Facebook) ta bayyanawa duniya cewa matsalar Nijeriya ba ta addinin musulunci ko kiristanci ba ne ko kuma akidar falsafa.
Ta bayyana matsalar Nijeriya da cewa kabilanci shi ne babbar matsalar da ta hana kasar ci gaba.

Bayan fitar waccan bincike na baturiyar na yi kokarin ganawa da ita game da cewa shin taba taba zuwa Nijeriya?
Ga mamakina sai ta sanar da ni cewa ba ta taba zuwa Nijeriya ba kawai dai tana yawan bibiyar al'amuran yau da kullum ne na kasashen afrika musamman Nijeriya kasancewarta babbar cibiya a nahiyar afrika.

Shin ko gaskiya ne wannan baturiya ta yi bincike a kan daidai?

A KASUWA NAKE DA NA SAMU MIJI ZAN YI AURE-Bintu



Jaridar Sarauniya ta samu zantawa da daya daga cikin jaruman shirin wasan gidan talabijin mai nisan Zango (Series) "DADIN KOWA" mallakin tashar Arewa 24 akan tauraron dan Adam.

FATIMA SA'ID ABDULLAHI wada aka fi sani da Bintu a cikin shirin DADIN KOWA a tattaunawarta da editan labaran Sarauniya RABIU MUHAMMAD (Abu Hidaya) ta bayyana abubuwa da yawa da suka shafeta da kuma masana'antar shirya finafinan Hausa (Kannywood)

DA WA MUKE TARE?

Suna na Fatima Sa'id Abdullahi wadda aka fi sani da Bintu a cikin shirin DADIN KOWA.

WACE RAWA KIKE TAKAWA A CIKIN SHIRIN DADIN KOWA?

Na kan fito a 'yar masu kudi wadda ta kasance 'yar gata a wurin iyayenta, domin ni kadaice a wurin mahaifina da mamana, sannan mahaifiyata ta shagwa6ani abin da nake so shi ake min.


YAYA A KA YI KIKA TSINCI KANKI A SHIRIN DADIN KOWA?

(Dariya) to ka san da yake komai hanya ce, zan iya cewa hanya aka yi min, na yi dace kuma aka dauke ni.


DAMA KINA CIKIN MASANA'ANTAR SHIRYA FINAFINAI TA KANNYWOOD?

E ina ciki, amma ba wani dadewa na yi ba domin ba zan wuce shekara uku ba.


TSAWON SHEKARA UKU DA KIKA YI A MASANA'ANTAR ME ZA KI CE A KANTA?

To ni dai gaskiya ban mata kallon komai ba, kawai ni dai na zo na yi fim kuma sana'a na dauki abin, kuma kasan idan za ka zauna da mutane yau da gobe sai hakuri, za ka 6atawa wani, wani kuma ya 6ata maka haka dama zaman duniya yake komai sai an yi hakuri.


MUTANEN DA SUKE WAJEN KANNYWOOD SUNA MUKU KALLON LALATATTU ME ZA KI CE GAME DA HAKA?

To wannan gaskiya ne akwai mutane da yawa wadanda ba 'yan fim ba, idan mutum zai yi aure ko zai auri yar fim sai su ce su ba za su yarda na su ya auri 'yar fim ko dan fim ba.
Ban ce babu lalatattu a cikinmu ba, amma ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai masu mutunci da yawa a cikinmu.
Fim din nan sana'a ce, yadda kowa yake tafiya ya je wurin aikinsa haka muma muke tafiya wurin namu aikin, sana'a muka dauketa kuma iyayenmu suna mana addu'a game da haka.


SU WAYE SUKA FI YAWA A KANNYWOOD NAGARI KO NA BANZA?

(Dariya sosai) gaskiya ba zan iya bayar da amsar nan ba, amma dai ni nagari na hadu da su.


TSAWON SHEKARA UKU DA KIKA YI A KANNYWOOD FIM NAWA KIKA YI?

To a gaskiya na yi finafinai masu yawa amma fitattu a ciki su ne:-
Bilhakki
Sanadin Rayuwa
Wuta a masaka
Aikin Gida da sauransu.


WADANNAN FINAFINAI DA KIKA AMBATA A WANI MATSAYI KIKA FITO?

Gaskiya kowanne na taka rawa daidai gwargwado ga wadanda suka kalli fim din za su gani.


MATSAYIN KARATU FA?

To maganar karatu kam iya sakanadire na tsaya ban ci gaba ba, amma In sha Allahu ina sa ran ci gaba.

YA LABARIN AURE FA?

(Dariya sosai) to yanzu kam babu aure amma muna nan muna jira duk lokacin da Allah Ya kawo muna so, mu ai bama gudunsa.


AMMA KIN SAYAR KO ANA KASUWA?

(Dariya sosai tare da sunkuyar da kai)To zan iya cewa na siyar zan kuma iya cewa ban sayar ba. Amma maganar gaskiya a kasuwa nake ban sayar ba. Kasan halin naku na maza sai a hankali.


WANE KALUBALE KIKA FUSKANTA A KANNYWOOD?

To wallahi ni dai sai na ce na godewa Allah don babu wani kalubale da zance na taba fuskanta a wannan masana'anta ta wasan Hausa da har zan rike shi a zuciyata ko cikin rayuwata.


KIN TABA SAMUN WATA KYAUTA A SANADIN WANNAN SANA'A DA ZA KI YI ALFAHARI DA ITA?

Maganar gaskiya na samu alherai da yawa a wannan sana'a wadanda ba zan iya misalta su ba.


MENE NE BURINKI A WANNAN SANA'A?

To alhamdulillahi ni dai a wannan sana'a idan suna ne Allah Ya ba ni domin yanzu duk inda zan wuce za ka ga jama'a na cewa ga Bintu da dai maganganu masu yawa, ko iya nan, ni alhamdulillahi na godewa Allah, amma kasan hausawa na cewa "Kogi bai ki dadi ba" ko haka ubangiji ya bar ni burina ya cika.


WANE NE JARUMINKI A KANNYWOOD?
Ni duk wani jarumi mai taka rawa a masana'antar shirya fim jarumina ne.


WANE ABINCI KIKA FI?
Ni dai a rayuwata na fi son taliya.


YANAYI FA?
Na fi son yanayi na sanyi a rayuwata.

MUN GODE

Ni ma na gode.