33
YADDA HARSHEN HAUSA YAKE BUNKASA A DUNIYA YADDA HARSHEN HAUSA YAKE BUNKASA A DUNIYA

Daga  Rabiu Muhammad(ABU HIDAYA) Dakta Izabela Will, wadda aka fi sani da Asabe, Baturiyace kuma malama a sashin nazarin harshen Ha...

0
Bambancin Sakkwatanci da Katsinanci Bambancin Sakkwatanci da Katsinanci

Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken  Dangantaka da Bambance - Bambancen furuci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci da Katsinance...

0
Gwarzayen Makadan Hausa Gwarzayen Makadan Hausa

Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken Gwarzaye a Wakokin Makadan Baka  wadda  Sa'idu Muhammad Gusau  daga  Jami'ar Bay...

0
Mukalar Adabi Mukalar Adabi

Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken Dan wanzan: Tauraron Wasan Kwaikwayon Hausa Mafi Shahara a Lokacinsa wadda Aisha Yahaya Tambuwa...

0
Paper Presentation Paper Presentation

Download the paper titled Caliph Muhammadu Attahiru Ahmadu As A Hero of the Sokoto Caliphate by Dr. Umar Muhammad Jabbi of Hist...

YADDA HARSHEN HAUSA YAKE BUNKASA A DUNIYA

Daga 
Rabiu Muhammad(ABU HIDAYA)

Dakta Izabela Will, wadda aka fi sani da Asabe, Baturiyace kuma malama a sashin nazarin harshen Harsuna da al'adun Afrika a jami'ar Warsaw a kasar Poland.

Ta zo Nijeriya don yin bincike game da yadda gabobin dan adam ke aika sako ba tare da yin furuci ba.

Na hadu da ita a masaukinta da ke tsohuwar jami'ar Bayero da ke Kano. Mun tattauna game da yadda Hausa take a can kasar da kuma kallon da take yi wa harshen a duniya baki daya.

Kasancewarki Baturiya Mene ne Ya Ja Ra'ayinki Har Kika Ji Kina Sha'awar Karanta Harshen Hausa?

To wajen shekaru ashirin da suka wuce na fara karatuna a sashen al'adu da harsunan afrika a can jami'ar Warsaw Poland, to a lokacin sai aka ce dole za mu yi nazarin harsuna guda biyu wato harshen Hausa da harshen Swahili, amma bayan mun gama shekarar farko a karatunmu sai aka ce to yanzu za mu iya zabar harshen da muke son mu zama kwararru akansa, to daga nan sai na zabi nazarin kimiyyar harshen Hausa saboda ina matukar son harshen bisa yadda ake koyar da mu shi a baya, musamman ma yadda na lura a bangaren harshen Hausa akwai malamai da yawa, amma sashen Swahili ba su da yawa, to ganin haka sai na zabi na yi nazarin kimiyyar harshen Hausa ko don samun kayan karatu cikin sauki tunda akwai malama a sashin da yawa.

Malaman da suke koyar da ku turawa ne ko hausawa ne daga Nijeriya?

Duka malamanmu turawa ne kamar ni, babu bahaushe ko daya sune suke koyar da mu. Saboda akwai bangarori da yawa na harsuna kamar Larabci, Hebrew wato harshen Yahudawa daga baya kuma aka fara Hamharik yaren mutanen Habasha(Ethopia) to da yake harshen Hausa yana da yawa da kuma yado sai aka samu wata malama baturiya daga kasar Rasha ta zo ta fara koyar da harshen Hausa to wannan ne farkon da aka fara nazarin harshen Hausa a jami'ar Warsaw.

KE NAN KUNA IYA NAZARIN HARSHEN HAUSA A CAN JAMI'AR WARSAW BA TARE DA KUN ZO AFRIKA BA?

Kwarai kuwa muna yin nazarin harshen Hausa ba tare da mun taba zuwa yankin afrika ba, yanzu haka akwai dalibai da yawa da suke son zuwa afrika musamman Nijeriya don karin iliminsu, kuma idan kana Hausa da su za ka ji su, sun iya Hausa sosai. Saboda suna karanta jaridun Hausa da littattafan Hausa a can, matsalar kasar Hausa tana da nisa sosai daga yankin turai, kuma kasan dalibai ba su da kudi, saboda haka suna son zuwa amma basu da kudin jirgin da za su biya su zo wannan dalili ne yake hana mafi yawansu zuwa.

WASU IRIN LITTATTAFAN HAUSA KU KE NAZARI A CAN JAMI'AR WARSAW?

E muna nazarin littattafan Hausa da dama amma wadanda muka fi yin nazari su ne littattafan adabi irin na da kamar:

Magana jari ce.

Ruwan Bagaja.

Iliya Dan Makarfi.

shehu Umar.

Kulba Na Barna da sauransu, amma duk da haka muna karanta littattafai irin na zamani kamar na soyayya wanda muke rabawa dalibai kyauta su karanta.

WANE IRIN BINCIKE KIKA ZO YI A NIJERIYA?

To da yake ba ni kadai ce na zo ba, mu biyu ne mun zo ni da wata ce, wadda ita, ta yi bincike ne akan Darikun addinin musulunci, irin su Kadiriya da Tijjaniya da kuma malamai sufaye,ita kuma sunanta Gimbiya, ni kuma na yi nawa binciken a kan yadda ake magana ba tare da an yi furuci ba, wato Isharori, na ziyarci wurare da yawa na tara bayanai da yawa na yi bidiyo da yawa wanda idan na koma Poland zan samu lokaci na duba don nuna abin kallo game da yadda mutane suke isar da sako ta hanyar isharori a lokacin da suke magana.

A INA KIKA SAMU SUNAN ASABE?

(Dariya)kamar yadda ka sani ni dai suna na na gaskiya Izabela amma a lokacin da Jami'ar Bayero ta gayyace ni a shekarar 2007 na zo na koyar da harshen Hausa a sashen koyar da harsunan Nijeriya daga can Warsaw Poland to lokacin da na zo sai mutanen sashin nazarin harshen, suka tambaye ni ko ina da wani lakabi na Hausa? Na ce bani da shi, sai suka ce to dole ne mu baki lakabi, sai na yi dariya na ce to bismillah, sai suka tambaye ni yaushe aka haifa ni? Sai na gaya musu shekarar haihuwata amma na ce ban san ranar ba, sai suka tambaye ni to yaushe na zo Nijeriya? Na ce musu ranar Asabar sai suka to shi kenan yanzu sunanki Asabe, kina son sunan? Na ce musu E, ina so, shi kenan daga ranar na zama Asabe.

Kuma a saboda haka, mu ma can jami'ar Warsaw Poland mun radawa wasu dalibai da dama lakabi da sunan Hausawa kamar:

Amarya

Kande

Indo

Gimbiya

Halima sunayen suna da yawa wallahi, kuma muna ba su wadannan sunayen ne saboda su yi nazarin harshen da al'adu sosai.

A BINCIKEN DA KIKA GABATAR A KAN HARSHEN HAUSA WANI IRIN KALLO KI KE MASA A CIKIN SAURAN HARSUNA?

To kasan da yake a can baya turawa ne suka yi wa harshen Hausa gata wadanda suka yi bincike a kansa, amma yanzu mafi yawa masu bincike ko nazarin harshen Hausa, Hausawa ne, kamar yanzu a turai babu turawa masu bincike a kan harshen kamar da, saboda haka ina ganin matukar Hausawan suka dage da nazarin harshen na su da bincike harshen zai iya zama gagara gasa a duniya baki daya, musamman yadda na zo Kano na ga masu nazarin harshen da yawa ina fata Kano ta zama cibiyar nazarin harshen Hausa a Nijeriya dama duka duniya.

A NIJERIYA YA KIKE KALLON HARSHEN HAUSA DA SAURAN HARSUNA?

To a Nijeriya ina kallon harshen Hausa a babban matsayi kuma harshe mai ci gaba, saboda akwai harsuna da yawa a Nijeriya ta arewa amma wasu da yawa suna mutuwa saboda harshen Hausa yana cinye su, kuma yawan mutanen da suke magana da harshen Hausa kullum karuwa yake, kuma ko a kudu akwai wadanda suna yin magana da Hausa, ni dai zan iya cewa Harshen Hausa ya zama "ruwan dare game duniya"

SHIN KINA GANIN HARSHEN HAUSA ZAI IYA ZAMA HARSHE NA DAYA A AFRIKA?

To kamar yadda na ke gani a Afrika ta yamma harshen zai iya zama na farko wanda yafi ko wani harshe, amma a Afrika ta gabas Swahili ne ya fi zama babba, amma a kaf Afrika banda wadannan harsuna larabci da Swahili, bana jin akwai wani harshe da yafi na Hausa Muhimmaci, kuma ina ganin nan gaba kadan harshen Hausa zai zama babban harshe a Afrika saboda a nan Nijeriya dana zo na ga mutane da yawa wadanda ba su son harshen Turanci sai Hausa kawai,wani abin mamakin shi ne, suna iya karanta Turancin amma ba sa iya magana da shi, saboda haka ya zama dole wadanda za su zo Nijeriya su koyi harshen Hausa wannan ma yana karawa harshe ci gaba sosai.

SHEKARA TARA RABONKI DA NIJERIYA YA KIKA GA CI GABAN WACCAN LOKACIN DA WANNAN?

Gaskiya an samu ci gaba sosai musamman jihar Kano kasancewar ban taba zuwa Nijeriya ta kudu ba, daga cikin ci gaban da na gani tun a masaukina ne a waccan lokaci ba haka masaukin yake ba, bai yi kyau kamar yanzu ba, babu kayayyakin more rayuwa kamar yadda kake gani yanzu, sannan babu wutar lantarki a lokacin don bata fin sa'a uku a kowacce rana, haka kuma babu ruwan fanfo sai dai a ajiye min a randa, idan ya kare dole sai na kira yaro ya je ya debo min a can rijiya kusa da masallaci, kuma a waccan lokaci hanyoyin Kano ba su da kyau sosai, amma yanzu na ga an yi hanyoyi da gadoji da fitilu masu launi a kan hanya da yawa, abin ya burge ni matuka, sannan mako daya da ya wuce na ziyarci wurin sayar da kayayyaki na Ado Bayero Mall gaskiya wurin ya burgeni saboda muna da irin wadannan shaguna a can Turai, saboda haka da na tuna da Kano a waccan lokacin abin ya burgeni gaskiya an samu canje-canje da ci gaba sosai.

A KAN WANI FANNI KIKA KWARE ILIMI?

Abin da goge a kansa a bangaren ilimi shi ne Kimiyyar harshe da kuma hanyoyin isar da sako ba da harshe ba. (Non-Verbal Communications).

WANI ABU NE YA BAKI MAMAKI A NIJERIYA?

To ni dai yadda na ga randa da ake zuba ruwa abin ya bani mamaki saboda yadda ruwan yake yin sanyi a ciki, sai kuma zuwa na garin Daura na je rijiyar Kusugu na ga kofar da Bayajidda ya shiga garin Daura, na shiga fadar sarkin Daura cibiyar Hausawa na ga gine-gine masu tarihi na Hausa wadannan abubuwa dana gani sun bani mamaki sosai, kasancewar labarinsu kawai nake ji sai ga shi yanzu na zo na gansu.

DAGA CIKIN AL'ADUNKU NA MUTANEN KASAR POLAND WADANNE NE SUKE KAMA DA NA HAUSAWA?

Tabbas akwai, misali yadda ake karbar bako a kasar Hausa da girmamawa a bashi kulawa sosai kamar wani sarki, to mu ma a can Poland haka ne,har muna da wata karin magana a harshen mutanen Poland cewa bako a gida kamar Allah a gida. Wato dole a karbi bako da hannu bibiyu dole a nuna masa girmamawa a yi masa murmushi da kauna sosai, kamar yadda Hausawa suke cewa bakonka annabinka. To wannan ya yi kama da al'adunmu sosai.

Sai dai kuma wani abin mamaki da na gani a nan shi ne mutum zai mikawa mutum hannu don su gaisa, sai ya noke, ya yi alamar risinawa kuma wai girmamawa ce amma mu a can hakan wulakanci ne mutum ya baka hannu ku gaisa ka ki ka yi masa haka.

MENE NE YA FI BURGEKI GAME DA DABI'UN MUTANEN NIJERIYA?

Abin da ya fi burgeni game da dabi'un mutanen Nijeriya shi ne yadda suke da son mutane, dalilin da yasa na ce haka kuwa shi ne, ranar lahadi na shiga sabon gari zan je coci, sai na tarar akwai layi don haka sai na dawo baya na tsaya, to a gefen da nake akwai wani mai shayi sai na ce ya bani shayi da madara na sha, bayan ya bani na sha, sai na dauko kudi zan biya sai yace ai an biya min, sai na yi mamaki, na ce wane ne haka? Na duba sai na ga wasu mutane a gefe suna yi min barka(dago min hannu) sai wani yace a bani biredi, sai na ce bana cin biredi na gode, sai ya dauko kudi ya bani sai na yi dariya nace ina da kudi na gode. To gaskiya irin wannan mutumci da aka yi min na ji dadi sosai kasancewata bakuwa a wurin, kuma na lura da hakan tabbatacciyar dabi'ar Hausawa ce son mutane don haka ya faru da ni a gurare da yawa mutane sun taimake ni.

A CIKIN ABINCIN GARGAJIYA NA HAUSAWA WANI ABINCI KIKA FI SO?

(Dariya)gaskiya ina son abincin Hausawa da yawa don nasan Dan wake, Dambu,Alala amma duk a ciki na fi son waina(Masa)irin ta shinkafa ina samu wannan ina ci sosai.

DAGA YADDA KIKE JIN LABARIN NIJERIYA YA KIKA GANTA BAYAN KIN ZO?

To mu a can muna gani a kafafen yada labarai ana gaya mana Nijeriya akwai boko haram ana fada babu zaman lafiya amma yanzu mun gani babu boko haram akwai zaman lafiya a Nijeriya sosai,

kuma wasu abubuwa da yawa da muke bincike a kansu sai da muka zo sannan muka gansu kuma mun samu banbamci da yawa da yadda muke jin labarinsu.

YANZU IDAN KIKA KOMA KASAR POLAND SAI KUMA YAUSHE?

To sai abin da hali ya yi, amma watakila ina iya dawowa shekaru kadan.

Na gode.

Ni ma na gode.

Bambancin Sakkwatanci da Katsinanci



Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken Dangantaka da Bambance - Bambancen furuci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci da Katsinance wadda Aliyu Muhammad Nata'ala daga Kwalejin Ilmi ta Tarayya, Katsina ya rubuta

Latsa nan

Gwarzayen Makadan Hausa



Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken Gwarzaye a Wakokin Makadan Baka wadda Sa'idu Muhammad Gusau daga Jami'ar Bayero, Kano ya rubuta.



Mukalar Adabi

Kuna iya saukar da wannan mukalar mai taken Dan wanzan: Tauraron Wasan Kwaikwayon Hausa Mafi Shahara a Lokacinsa wadda Aisha Yahaya Tambuwal daga Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari Sakkwato ta rubuta.

Latsa nan


Paper Presentation





Download the paper titled Caliph Muhammadu Attahiru Ahmadu As A Hero of the Sokoto Caliphate by Dr. Umar Muhammad Jabbi of History Department, Usman Danfodio University, Sokoto