Daga
Rabi'u Muhammad (Abu Hidaya)
Gmail:abuhidya3@gmail.com
+2348065025820
A ranar Juma'a 14 ga watan Afrilu 2017 hukumar adana kayan tarihi da
al'adu tare da hadin gwiwar kungiyar Makarantar Hausa ta kasar Burkina
Faso suka gudanar da taron ranar bajakolin al'adun Hausawa na duniya
tare da gabatar
da taron karawa juna sani a babban birnin kasar Wagadugu(Ouagadougou),
taron dai wanda ya samu halartar kasashe da dama kamar:
Nijeriya (Nigeria)
Nijer (Niger)
Togo (Togo)
Sanigal (Senegal)
Kodebuwa (Ivory'Cost)
Chadi (Chad)
Mali da sauransu. An fara gabatar da shi da misalin karfe goma na
safiyar ranar juma'a, an soma da gabatar da takardu cikin harshen
Turanci da Faranci karkashin
jagorancin uban kungiyar makarantar Hausa, Alhaji Sani Dan
Tule. wadanda suka gabatar da
takarda a ranar akwai:
Sarkin Askar Yariman Safana
Dakta Bashir Aliyu Sallau da kuma Yusif Nuhu Inuwa.
Bayan sun kammala sai aka yi musu tambayoyi suka bayar da
amsoshidaga nan aka tafi
masallacin juma'a.
Da misalin karfe hudu na yammacin ranar dai aka ci
gaba da gabatar da taron,
ministan al'adun kasar ne ya bude taron a madadin shugaban kasar
Burkina Faso Roch Mark Cristian Kabore ya yi jawabi a
matsayinsa na babban bako inda
ya nuna cewa Hausa tana da girman da yanzu ba iya Afrika kawai take
ba, za a kira ta ne da harshen duniya ya kuma jinjinawa
wadanda suka shirya taron
musamman shugaban kungiyar
makarantar Hausa ta Farko a kasar malam
Abdoul Rasmane Nagarba, bayan
ragowar manyan baki sun yi na su jawabin sai ministan ya jagoranci
manyan baki da mahalarta taro zuwa bude dakin da aka
ajiye kayan tarihi da al'adun
Hausa na da da na yanzu daga nan kuma sai aka bude wasan kokowa don
nishadantarwa ga baki.
Washe gari ranar Asabar aka ci gaba da gabatar da takardun karawa juna sani
karkashin jagoranci Dakta Bukar Usman OON,tsohon sakatare a fadar
shugaban kasar Nijeriya, a
wannan rana wadanda suka samu
damar gabatar da takarda akwai:
Ado Ahmad Gidan Dabino MON
shugaban kamfanin Gidan Dabino International da ke Kano-Nijeriya.
Dr. Nasiru Aminu Kalgo
Jami'ar Usman Dan Fodiyo Sokoto.
Mai girma Ibrahim Muhammad Dan Madami
Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Zamfara a Nijeriya.
Malam Nasir AUK
Jami'ar Musulunci ta Alkalam da ke Katsina
su makamar ranar farko bayan kammala takardunsu an yi masu tambayoyi
sun kuma bayar da
amsa daga nan sai aka tafi duba
kayan gargajiya na mata da maza da nau'ikan abincin gargajiya wanda
ake bajakolinsu a harabar gidan Adana kayan tarihin kasar.
An dawo filin wasa da karfe bakwai na yamma nan kuma mawakan kasar ne
suka baje kolin fasaharsu don nishadantar da mahalarta taro wadanda
suka kasance yan cikin gida da baki yan kasashen waje.
Ranar Lahadi ita ce rana ta karshe daga ranakun taron kuma wannan rana
an gabatar da abubuwa
kamar haka:
taron karawa juna sani karkashin jagorancin Dakta
Bukar Usman OON. Wadanda suka gabatar da takarda a ranar sun
hada da
Abubakar Muhammad
Mukhtar AUK
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
Shugaban Tsangayar Adabin Hausa kuma Daraktan Makarantar Al-Huda Women
Educational Centre da ke Kano.
Bayan kammala tambayoyi sai aka tafi ziyarar wuraren tarihi na kasar
cikin wurin da aka ziyarta akwai gidan sarkin Musawa Mogho Naba wadda
aka fi sani da kabilar Mossi sarkin wanda ya kasance shi ne
babban basaraken kasar, an samu izza sosai kafin daga bisani a samu
ganawa da shi, bayan fitowar an gindayawa masu ziyarar sharadin kada
su dauki hoto a masarautar, sarkin ya yi maraba da bakin da suka
ziyarci fadarsa musamman 'yan kasashen waje, bayan kammala tattaunawa
da sarki sai aka wuce gidan sarkin Hausawan zango na birnin Wagadugu
mai suna sarki Dankambari Jibril da kuma ziyarar muhimman wurare daga
nan sai kowa ya koma masaukinsa, hutu da zimmar zuwa dare a ci gaba
da taro.
Karfe takwas daidai aka ci gaba da taro, bayan jawabin maraba da kuma
gabatar da manyan baki daga mai gabatarwa Rabiu Muhammad Abu Hidaya,
wanda ya yi da harshen Hausa sai kuma Asma'u Makeri da yi da harshen
Faranci bayan gabatar da manyan bakin da suka halarci taron, abu na
gaba shi ne rabawa dalibai mata na makarantar Hausa ta
Burkina Faso takardar shedar
kammala karatunsu na matakin farko a ilimin Hausa wanda
makarantar AL-HUDA WOMEN EDUCATIONAL CENTRE da ke Kano Nijeriya ta ba
su, tsohon gwamnan Kano kuma sanatan kano ta tsakiya Injiniya Dakta
Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne ya jagoranci ba su takardar shedar, daga
nan kuma
sai hukumar Adana kayan
tarihi da al'adun kasar Burkina Faso tare da hadin gwiwar Kungiyar
Makarantar Hausa ta Burkina suka karramawa wasu muhimman mutane da
suke bawa Hausa gudummuwa a duniya da kambun
karramawa, cikin wadanda aka
karrama a ranar akwai:
Dakta Bukar Usman OON
an karrama shi da kambu mai taken (Jakadan Adabin Hausa)
Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso
An ba shi kambun karramawa mai taken (Gwarzon Shekara2017 )
Farfesa Abdulkadir Dangambo
Ya samu karramawa mai taken (Garkuwan Adabin Hausa)
Farfesa Abdalla Uba Adamu(Gwarzon Shekara 2017 ) Da sauransu.
Gidauniyar Bukar Usman da Dakta
Bashir Aliyu Sallau babban
Darakta a hukumar tarihi da al'adu ta jihar Katsina sun bayar da
kyaututtukan littattafai ga
kungiyar makarantar Hausa don ci
gaba da gabatar da karatu.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata a halin yanzu Dakta
Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayar gudummuwar kudi ga kungiyar makarantar
Hausa kimanin dala dubu biyu, har ila yau tsohon
gwamnan kanon da yake jawabi
a madadin wadanda aka karrama ya ce "Sun ji dadi kwarai da wannan
karramawa da aka yi musu kuma za su ci gaba da bayar da hadin kai
wajen ci gaba da assasa irin wannan taro a ko'ina cikin duniya a
karshe ya yi kira ga
al'ummar Hausa a duk inda suke cewa su zama masu hadin kai da kaunar
juna kada su bari kawunansu su rarraba".
Shi ma Dakta Bukar Usman OON tsohon magatakarda a fadar shugaban kasar
Nijeriya ya matukar nuna jin dadinsa da wannan karramawa da hukumar
adana kayan tarihi da al'adun kasar Burkina faso suka yi
masa " Ya ce duk da cewa a rayuwarsa
ya samu kambun karramawa da yawa amma zai ci gaba da alfahari da
wannan karramawa kuma tamkar kara masa kwarin gwiwa
aka yi game da ayyukansa na
rubutu". Da yake fadar burinsa a yanzu ya ce "Bai
wuce ya hidimtawa harsunan
da suke bukatar taimako ba". A dai wannan rana aka yi wasan karshe na
kokowa inda aka fitar da zakaran gasar.
Manufar wannan taro dai ita ce fito da al'adun
kabilun kasar na Burkina Faso
wanda ake yi duk shekar karkashin jagorancin hukumar adana kayan
tarihi da al'adun kasar wadanda suke da kabila sitti da uku(63), kuma
kamar yadda bincike ya nuna tunda ake gabatar da wannan taro ba a taba
yin wanda ya hada kasashe da dama ba kamar
wannan na kabilar Hausa.
Ana sa ran shekara mai zuwa za a sake maimaita
irin wannan taro a kasar ta
Burkina Faso.
Duk da cewa wasu suna ganin Burkina Faso ba kasar Hausawa ba ce amma
dai a ganin sun jima a kasar wadda har ta kai yanzu suna rike da
mukaman gwamnati kuma kasar ta sanya su cikin harsunan kasar da
cikkakun yan kasa.
Manyan bakin da suka samu halartar taron daga
kasashe akwai:
Kasar TOGO
Alhaji Ousman Mahmoud Salifou Baba Keke || Sarkin Zangon Lome
Alhaji Issifou Garba Kalambe Sarkin Zango Aneho
Alhaji Aoudou Shikuru Ibrahim Sarkin Zango Kpogam
Alhaji Ali Ousman Sarkin Zangon Garin Kuka.
Malam Mamman Moutala
NIJERIYA (NIGERIA)
Dakta Bukar Usman OON
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso Dakta Nasir Aminu Kalgo
Dakta Bashir Aliyu Sallau(Sarkin Askar Yariman Safana)
Maigirma Ibrahim Muhammad (Dan madamin birnin Magaji).
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON
NIJAR (NIGER)
Alhaji Garba Sani
Madam Nana Hadiza Louali
Madam Malika Koda killy
Madam Binta Alterna
Abdul Nasir
SANIGAL (SENEGAL)
Malam Hassan Musa katsina, sauran kasashen sun hada da Kwadebuwa da kamaru.
An kammala taron lafiya.