A jiya laraba 10\10\2018 kungiyar Sardaunan Kano Vanguard suka gana da Dakta Malam Ibrahim Shekarau sardaunan Kano kuma wazirin raya kasar Nufe.
Taron wanda aka fara tunda misalin karfe goma na safiya a dakin taro na Marskhala Hotel da ke unguwar Kurmin Mashi a jihar Kaduna.
Bayan gabatar da jawabin maraba da mukaddashin shugaban kungiyar na kasa ya yi sai kuma uban taro wanda shi ne jagoran shirya taron wato Alhaji Nura Abdullahi Jos ya karbi abin magana ya sake yi wa mahalarta taro barka da zuwa da kuma babban bako mai jawabi Sardaunan Kano malam Ibrahim Shekarau.
Ya bayyana manufar taron da cewa don a taya mai girma sardaunan Kano murnar komawa jam'iyyar APC ne da kuma taya shi murna samun tikitin takarar dan majalisar Dattijai mai wakiltar kano ta tsakiya da jawabai masu yawa.
A jawabin nasa Sardaunan Kano ya bayyana babban jin dadinsa ga wanda ya shirya taron da kuma irin fuskokin da ya gani a taron ya kuma ce zai ci gaba da alfahari da mutanensa a ko'ina suke a Nijeriya da duniya baki daya.
Bayan kammala jawabinsa mahalarta taron sun yi masa tambayoyi masu yawa game da abin da ya shafi Nijeriya da ci gabanta a harkar siyasa, inda shi kuma ya bayar da amsa daya bayan daya.
Taron dai ya samu halartar duka shugabannin kungiyar Sardaunan Kano Vanguard na jihohi talatin da shida(36 States) da suke Nijeriya.
An tashi taro da misalin uku na yamma inda aka dauki hoton gamayya na mahalarta taron.