0

A jiya juma'a 26\10\2018 aka yi bikin bayar da kyautar zakarun gasar hikayata ta bbc Hausa.
Bikin wanda ya gudana a dakin taro na Ladi Kwali a birnin tarayya Abuja wanda ya samu halartar manya baki daga sassan jihohin tarayyar Nijeriya.
A wajen bikin bayar da kyaututtukan gasar wanda sashen Hausa na bbc yake shiryawa duk shekara, fitacciyar marubuciyar Hausa kuma mace ta farko da ta fara rubuta littafin kagaggen labari na Hausa hajiya Hafsat M. A Abdulwahid ta kalubalenci sashen Hausa na bbc cewa bai kamata a ce an samu namiji a cikin alkalan da suke tace labaran ba, inda ta ce "an ce abu na mata ne zalla a dauki kane na Malumfashi an dora an ce shi ne shugaban tace labaran, mu gaskiya wannan bai yi mana ba. Tunda harka ce ta mata a nemi mace ta yi shugabanci, ba mu hana a sa shi a ciki ba, amma harka ta mata a sa mata, muna da mata fitattu da suka yi Hausa da sauransu" Sannan ta yi kira ga sashen cewa a daina gwamutsa Turanci da Hausa a lokacin bikin bayar da kyaututtukan.
Wannan dai shi ne karo na uku da sashen Hausa na bbc ya samu kalubale a tsawon shekara uku da yake shirya wannan gasa, shekarar farko kasar Nijar ta yi korafi da cewa gasar ta 'yan Nijeriya ce kawai, kuma alamu sun nuna hakan.
Shekara ta biyu wani manazarci daga jihar Katsina ya kalubalenci alkalan gasar gaba dayansu cewa labarin da ya zo na daya bai cancanci haka ba.
Sai ga shi a bana ma an samu irin wannan korafi ga sashen Hausa din da fatan masu ruwa da tsaki za su duba lamarin.

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

WATA MARUBUCIYA TA KALUBALENCI SASHEN HAUSA NA BBC MASU SHIRYA GASAR RUBUTUN MATA TA HIKAYATA. Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya

No comments:

Post a Comment