0
IN BISHIYA TA GIGA..... IN BISHIYA TA GIGA.....

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya Kyakkyawace ajin farko,kallo daya zaka mata ka gane cewa bata son raini, tafiyarta kawai abin kallo ce domi...

0
RAYUWAR 'YAN MATANCI RAYUWAR 'YAN MATANCI

Sa'adatu Baba Ahmad Rayuwar 'yan matanci da mata ke yi abu ne da ya dace a lura da shi tamkar yadda a ke lura da sauran al...

0
KASAR HAUSA DA TARIHINTA ! KASAR HAUSA DA TARIHINTA !

Ibrahim Hamisu Galibin kasar Hausa a shinfide ta ke,gata kuma da yawan sarari .Akwai kuma tsaunuka da tuddai jifa-jifa,kuma tanada man...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 9 DABARUN RUBUTUN WAKA - 9

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A darasinmu na baya mun duba ire-iren baiti ne guda hudu. To yau za mu dora: ...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 8 DABARUN RUBUTUN WAKA - 8

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya mun fara magana kan baiti, inda muka bayyana ma'anarsa. To y...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 7 DABARUN RUBUTUN WAKA - 7

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya muka karashe magana kan ma'auni ko karin waka. To yau kuma z...

0
DABARUN RUBUTUN WAKA - 6 DABARUN RUBUTUN WAKA - 6

Nasir G Ahmad RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA Assalamu alaikum. A makon jiya mun fara magana a kan ma'aunin waka, wato karin da akan gina...

IN BISHIYA TA GIGA.....


Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya

Kyakkyawace ajin farko,kallo daya zaka mata ka gane cewa bata son raini, tafiyarta kawai abin kallo ce domin tamkar dawisu haka take tafiya.
Amina kenan budurwar da kowa ke shakkar kulawa. Bayan Amina da ake kiranta tana da sunaye kala-kala da ake kiranta da dasu tsabar jin kan da take dashi.
Wasu na kiranta Shu'uma, wasu ko Hatsabibiya, kai wasu ma Miskila ke kiranta tsabar nuna isarta.
Cikin nutsuwa ta kwankwasa kofar ofishin mutumin da ta zo nema tana tsaye tana cin cingam a bakinta ji kake kas-kas! karar sautin cin cingam din yana fitowa daga bakinta, kamar dakika biyu da buga kofar sai aka bude wani dan kakkauran mutumne baki ya bude kofar yana ganinta sai kawai ya wangame bakinsa yana fadin ashe yau muna da manyan baki a ofis  din namu? Bismillah shigo ciki mana, guri ta samu ta zauna, shi kuwa Mutumin ya rasa inda ma zai zauna tsabar zumudi, me za'a kawo miki ruwa ko lemu? Wani irin murmushi Amina ta sakar masa gami da lumshe idanu tace nafi son ruwan, cikin hanzari ya bude firji ya dauko mata ruwan roba ya aje a gabanta.
Bayan Amina ta gama shan ruwan sai ta juyo da kallonta gareshi Alhaji Mati kenan kuna sha'aninku tana magana tana cizon lebe da alamu akwai abinda Amina ta kullo a ranta.
Wata mika Alhaji Mati ya yi yana wangale baki kamar mai yin ihu ga duk alamu nufinsa dariya yake, duniya kenan Amina wai ina kika shige shekaru da yawa haka?
Kisan yau rabona da inganki wajen shekaru biyu kenan?
Amma ko a ina kike lalle kina jin dadi kinga yadda fatar nan taki take ta sheki kamar wata sabuwar Amarya?
Hala ta samu ne dan nasan ke ungulu ce bakya jewar banza.
Wani irin kallo Amina take yi wa Alhaji Mati a lokacin da yake maganarsa.
Hmm! Alh.Mati kenan kai dai baka rabo da tsokana, ba wata samuwa kawai na zo mu gaisa ne ganin mun dade bamu hadu ba.
Kin kuwa kyauta Yan mata, kinga kuwa yanzu zan tashi daga ofis a wani otal kika sauka ne?
Amina tace Banma kama otal ba saukata kenan.
Ok to bari yanzu sai muje awarwasa otal sai in kama miki daki, Kinga sai mu yi hirar yaushe gamo ko?
Murmushi Amina ta yi sannan tace kai dai baka da dama to godiya nake.
Sannu a hankali motar kirar Honda Sienna ta samu guri a harabar otal din wurin da aka tanada dan ajiye motoci ta yi fakin. Amina da Alh. Mati suka fito daga mator suna tafe suna dariya da alamu sun tuna da tsohuwar soyayyarsu ne .
Bayan karbar tikitin dakin da zasu zauna kai tsaye dakin suka nufa.
A ranar kusan kwana suka yi suna aikata barna dama kuma al'adarsu ce haka duk lokacin da suka hadu kamar tumaki haka suke kasancewa tsabar saukin juna.
Hasken rana ya keto ta tagar dakin da Alhaji Mati ke kwance wanda yake nuna alamun gari ya waye, cikin mikar gajiya ya mika hannu dan kamo Amina Ga mamakinsa sai ya ji wayam! ya kama iska, cikin hanzari ya karasa bude idanunsa domin ganin ko ta sauya bigiren kwanciya babu ita babu alamunta sai wata doguwar takarda a wurin da take kwance...

RAYUWAR 'YAN MATANCI


Rayuwar 'yan matanci da mata ke yi abu ne da ya dace a lura da shi tamkar yadda a ke lura da sauran al'amuran da su ka shafi rayuwa. Don a irin wad'annan lokutan
mata da yawa su ke lalacewa, wasu kuma su koyi munanan d'abi'u ko ta sanadin samarinsu ko ta sanadin kawayensu, abin da ke haifar da haka shi ne gurbacewar al'adunmu da kuma samun shigowar sababbin bak'in al'adu. Sannan sababbin nau'o'in na'urorin fasaha, wanda su ka hada da wayar selula da kuma intanet da 'Facebook' da 2go Sai ka ga yarinya mace wacce ba ta fice Shekaru goma sha uku ba ta mallaki wayar kanta, wani bi ma iyayenne su ke siya mata su bata don gata, ba tare da sun lura ko sun sa ido a kan su waye da waye za su bugo mata ba, 
ko kuma za ta bugawa ba. Ko da kuwa mace ta mallaki wasu shekaru ni ban ga 
ribar hirar waya ga wandanda ba ma'aurata ba ko muharramai ba, saboda hak'i
k'a irin wannan hirarrakin na samari da 'yan mata a yawancin lokuta ba sa haifar da alheri. Musamman in a ka yi la'akari da lokutan da a ke yin hirar 
lokacin kwanciyar bacci ne, su kan yi amfani da kalmomi ne ba ma na so ba, 
na sha'awa zalla don kwantarwa juna zuciya, da wuya ka ji su na tattaunawa 
kan batun aure da zamansa. Yarinya k'arama sai ka ga ta san komi, kuma in har zuciyarta ta yi zurfi a kan sha'awar abokin hirarta ko wani daban sai a 
ga ba wuya ta lalace, kafin iyaye su farga labarin ya munanta. Yadda mace ta ke da kunya sai ka ji ta saki baki, wai kawai don namiji ya turo mata kati.

Ni dai a nazarin da na yi na fahimci in har ba'a lura an yi gyara ga rayuwar 'yanmatanci ba to, wallahi kar mu taba saka ran al'umma za ta gyaru, ko kuma shugabanni za su gyaru su dinga gudanar da mulki a cikin adalci Sabo
da tarbiya ta na samuwa ne tunda daga gida. In muka waiwaya baya muka dubi 
rayuwar 'yan matan da sai muga tana da bambanci da ta yanzu, tun daga kan '
yan matan da iyayensu, dan galibin iyayen da suna kokari suna bayar da gudu
mmawa wajen kame kansu daga kwadayin irin mazajen da suke zuwa wurin 'ya'yansu, kuma su na tsawatarwa 'ya'yan tare da sa mu su idanu a kan al'amuransu
na yau da kullum. Kuma al'adun mutanen da su ka shude wajibi ne makwabci da 'yan uwa su taimaka wajen tarbiyar 'ya'ya, kuma ko wanne irin laifi ya ga
d'an makwabcinsa ya yi kai tsaye zai tsawatar masa ko ya tari uban ya sanar da shi don a gaggauta daukar mataki, amma yanzu iyaye ba sa son laifukan 
'ya'yansu, Sun fi so ai ta yabon 'ya'yan, ko da kuwa ba su yi abin yabon ba, ko a yi shiru a zuba musu ido su ci karensu ba babbaka, ba dama makwabci ya fad'i wani gyara ga d'an makwabcinsa sai abin ya zama jidali, in an yi sa'a uban ya yadda to uwa mace sai ta ce atabau ba ta yadda ba, an yiwa 'yarta sharri.

Wasu iyayen dai fatansu su ga saurayi dan mutunci na zuwa gurin 'ya'yansu. Yayin
da mafi yawancin iyayen yanzu idanunsu suka fi karkata kan mai dukiya, ko 'ya'yan manya ba 
wai dole mai kyakykyawan hali ba ko mai mutunci. Sannan al'adun ma na 'yanmatanci ya sauya, irin su kunya da kawaici yanzu galibin 'yan matan ba sa yi, su kan bude baki su fadi duk wata kalma da su ka san za ta ja hankalin namijin da ba mujinsu ba, don kawai cimma wasu bukatu na kyale-kyalen rayuwa. Wasu ma kan fita wuraren shakatawa tare, su hole son ransu iyaye na gida. Har kullum wajibine mace ta-gari ta san cewa babu Soyayyar da ta kai ta aure dadi da armashi. Masana da yawa sun bayar da bayanai kan dad'in Soyayya a gidan aure
saboda halaccin aure a tsarin ko wacce al'ada ya ba da damammaki na kusantar juna tare da debe kewa. Don haka in har namiji na son mace da gaske to ya aureta ya kaita gidansa ya gwada mata duk launin son da ya dace. Ba maganar doguwar Soyayya a waje, a yi Shekara da Shekaru ana abu daya, wani bi ma har sai an kai ga yin abin da ba'a so, Sannan kuma daga baya ai aure, to, wajibine mace ta sani tsawaita rayuwar 'yan matanci na kashe sha'awarta a gidan aure a na yinsa ne don kunya da mutunci, in su ka gushe kuma da wuya zaman aure ya yi dadi

Ai da ba'a faye yawan sake-saken aure ba kamar yanzu, saboda 'yan matan da
yawancinsu suna matukar kame kansu daga duk wani abu da zai zubar musu da mutunci, kuma da wuya ka samu soyayyar son zuciya, wato mace ta rinka 
nunawa namiji soyayya a fili bayan a zuciyarta ba ta son shi abin hannunsa 
ta ke so. Su sukan yi soyayyane dan suna son mutum har zuciya, dan Allah ba wai dan wani abin duniya ba, ko kwadayin wani mukami ko matsayi da ya ke da shi ba, Sannan ba su da wata cikakkakiyar sakewa da namiji in ba mujinsu ba ne, kuma ko wayewar tara samari barkatai ma ba su da ita, irin na 'yanmatan yanzu wanda sai ka samu mace da samari goma kuma duk iyayenta na sane, a cewarsu wai ba sa son su yi mata auren dole. Sabanin mutanen da, in dai mutum na farko ya turo ta ce bata son shi, to da wuya ta k'i na biyun, wanda da wuya a hada shekara a na zance ba ai auren ba. Haka ne yasa auren mutanen da ya ke karko saboda an gina shi da tubala ma su kwarin gaske.

Yakamata mu lura cewa mu al'umma a yau mun gaza a kan duk-kan al'amuran da 
mu ke gudanarwa, amma me ya sa ba mu gaza ba wajen ciyar da cikkunanmu abin
ci ba?, mu kan yi ko wanne irin aikin wuya don mu samu abincin da za mu ci,
to, in haka ne me ya sa zamu gaza wajen bin dokokin da addinanmu da al'adunmu su ka shimfida ma na? Kar mu zuba idanu a kan rayuwar 'ya'yanmu mu ce wai zamani ne ya zo da haka, ya zama tilas mu gyara tarbiyarsu dai-dai gwargwadon iyawarmu. Allah ya sa mu dace.

Sa'adatu Baba Ahmad
(mrs Shehu Bayero Sanusi)

KASAR HAUSA DA TARIHINTA !


Galibin kasar Hausa a shinfide ta ke,gata kuma da yawan sarari .Akwai kuma tsaunuka da tuddai jifa-jifa,kuma tanada manyan Koguna guda biyu da suka ratsa ta cikinta,da Kogin Rima da Kogin Hadeja,shi kuma kogin kwara kamar iyaka ne daga yammacin Kasar. Kogin Rima shi ne ya taso daga 'Kasar Zamfara,ya gangara yayi Arewa zuwa Nigar,sa'anan ya karkata kudu,ya bi ta yamma da Sakkwato,ya je ya fada cikin Kogin Kwara.
Shi kuwa kogin Hadeja, masominsa a 'Kasar Kano ne. Daga nan ne ya gangara gabas ya bi ta Gashuwa ta Gaidam,ya je ya fada tabkin Cadi.
Akwai wani masharin Katon Daji da ya ratsa Kasar Hausa,wanda kowane shiyya akwai sunan da ake kiransa,amma guda daya ne. A Sakkwato ana kiransa dajin Gwamna, a Katsina dajin Rubu, a Kano kuwa ana ce masa dajin Folgore, a Kasar Bauchi su ce dajin Yankari, haka ya nausa har zuwa cikin 'kasar Kamaru.

Mu hadu Mako mai InshaAllah.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 9

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A darasinmu na baya mun duba ire-iren baiti ne guda hudu. To yau za mu dora:

5. Tahmisi
Tahmisi, kalmar Larbci ce da ke nufin biyartawa.. Wato mayar da wani abu da adadinsa bai kai biyar ba zuwa biyar. A nan, wani mawaki ne kan shirya waka mai dango biyu-biyu. Daga baya sai wani mawakin daban ya kara wa kowane baiti na wakar dango uku-uku, su zama dango biyar-biyar ga kowane baiti. Wato daga mai kwar biyu ta koma mai kwar biyar.
Tahmisi tamkar sharhi ne ko karin bayani ga kunshiyar waka. Domin dangogin da mai tahmisi kan kara sukan saje da kunshiyar dangogi bi-biyu na ainihin wakar.
Misalin tahmisi shi ne "Wakar zuwa birnin Kano" ta Malam Yahawa Gusau, wadda Malam Bello Gidadawa ya yi wa tahmisi. Da wakar "Arew Mulukiya ko Jamhuriya" ta Malam Sa'adu Zungur, wadda Malam Yusufu Kantu Isa ya yi wa tahmisi. Ga misali:
Sa'adu Zungur,
In za ka fadi fadi gaskiya,
Komai taka ja maka ka biya.

Bello Gidadawa,
n zance za ka yi kai tsaya,
In nuna ma hanya daya,
In ka san ka isa Zabiya,
In za ka fadi fadi gaskiya,
Komai taka ja maka ka biya.

6. Tarbi'i
Tarbi'i na nufin huduntawa. Kamar dai tahmisi da muka yi bayani ne. Sai dai shi mawaki na biyu na kara dango biyu-biyu bisa biyun mawakin farko ne, baitocin wakar su zama masu dango hudu-hudu. Kamar wata wakar Isa da Shehu Mujaddadi da Malam Muhammad Auwal ya yi wa tarbi'i. Misali:
isa dan Shehu:
A mu gode badini zahiri,
Jama'ag ga Karimi Kadiri.

Muhammad Auwal,
Ya musulmi kui mana hanzari,
A mu zamka yabo gun Gafiri,
A mu gode badini zahiri,
Jama'ag ga Karimi Kadiri.

Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 8

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun fara magana kan baiti, inda muka bayyana ma'anarsa. To yau za mu dora:

NAU'O'IN BAITI
Ana so tsarin rubutacciyar waka ya zamo dayan wadannan nau'o'i:

1. Gwauruwa
Waka gwauruwa ita ce mai dango daya-daya a kowane baiti nata. Misali:
Alhamdu lillahi mun samo fita hadari,
Wancena jan zamani da ke sa maza wadari,
Jama'a musulmi ku ce amin mu zam shukuri.
(Sa'adu Zungur)

2. 'Yar Tagwai
Ana kuma ce mata 'Mai Kwar Biyu.' Wato wakar da kowanne daga baitocinta ke kunshe da dango biyu-biyu. Misali:
Ko akwai wani wanda ya tambaya,
Mene ne sargartacciya?

Diyar da ta taso ba kula,
Ba zuwa makaranta ko daya.

Babu tarbiyya a wajen uwa,
Da uba sai shashancin tsiya.

Sai tallace-tallace barkatai,
Wai su tara kudi su yi dukiya.
(Baba Maigyada Agege)

3. Mai Kwar Uku
Ita ce waka mai dango uku-uku a kowane baiti nata. Misali:

Rashin hada kai shi ka ba makiya,
Damar su bata zaman lafiya,
Su kawo akida marar ci gaba.
(Wakar Hada kai)

4. Mai Kwar Hudu:
Ita ce wakar da kowanne daga baitocinta ke da dango hudu-hudu a cikinsa. Misali:

Ga abin da hali ya kawo,
An yi dauri yau kuma ya dawo,
Na kudurta buri na sawo,
Rabbana nufe ni da dacewa.
(Wazirin Gwandu, Umaru Nasarawa)

5. Mai Kwar Biyar
Ita ce wakar da ke da dango biyar-biyar a cikin kowane baiti nata. Misali:

Mutum kadan ba shi sani,
Kira shi jaki da zani,
Da tambaya kan yi sani,
Abin da zan zo na sani,
Ba zan ki tambayar sa ba.
(Akilu Aliyu: Wakar Kokon Mabarata)

Mu kwana nan.
Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 7

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya muka karashe magana kan ma'auni ko karin waka. To yau kuma za mu duba:

2. DANGO
Dango na nufin sadara ko layi guda na rubutacciyar waka. Wato yankin zance wanda akan harhada ya tayar da waka. Sau da yawa dango kan ci gashin kansa, wato ya ba da cikakkiyar ma'ana, ba tare da jinginuwa da wanda ya gabace shi ko wanda ke biye da shi ba. Misali:

jama'a ku taho zan wallafa,
zan wakar sangartacciya.
(Baba Maigyada Agege)

3. BAITI
Dangogi su ne ke harduwa su ba da baitin rubutacciyar waka. Baiti kan zo a tsarin gunduwoyi (layuka), wadanda ake kira dangogi, kamar yadda bayani kan dango ya gabata.

Mu kwana nan.
Ma'as Salam.

DABARUN RUBUTUN WAKA - 6

RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

Assalamu alaikum.
A makon jiya mun fara magana a kan ma'aunin waka, wato karin da akan gina waka kansa, inda muka duba tarihin samuwar ma'aunan rubutattun wakokin Hausa. To yau za mu karasa tare da misali.

Duk da kasancewar har zuwa yau akan samu rubutattun wakoki da akan shirya bisa ma'aunan Larabci, mafi yawan mawakan wannan zamani ba su ma san da zamansu ba, duk kuwa da kasancewar wasu wakokin nasu za su iya hawa ma'aunan Larabcin, wadanda galibi da su akan fara auna waka yayin nazarin ta.
Kada wannan dogon labarin ya dami mai sha'awar fara rubuta waka. Babban abin da ake bukata shi ne, duk karin da ka zabi ka rubuta waka da shi, ya zamo ka bi hawa da saukar muryarsa sau-da-kafa. Wato kalmomin da za ka zaba su zamo dai dai yawan gabobin wancan kari, ba tare da sun gaza ko sun zarta ba. Ga misalin wani baiti na wata wakar Abubakar Imam:

Maraba da kai muhammadu dan Amina,
Maraba da shugaban duka Annabawa.

Ga yadda za a bi sawun karin:

maraabadakai/Muhammadudan/amiinaa,
maraabadashuu/gabandukaan/nabaaawaa.

Sai mu ce:

idankaasoo/kazaabikarii/nawaakaa,
kaluuradashii/dakyausannan/kabiishii

Wato:
idan ka so ka zabi kari na waka,
Ka lura da shi da kyau sannan ka bi shi.
Mu lura da cewa, yayin auna waka ana nuna dogon wasali ta hanyar rubanya wasalin sau biyu.

Ma'as Salam.