0

KWANKWASO DA GANDUJE A SIYASAR KANO.

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya

Yanzu dai ta tabbata Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne zababben gwamnan jihar kano bayan kammala zaben bana na shekarar 2015 kafin wannan zabe mutane da yawa suna ganin anya Gwamna Injiniya Rabiu Musa kwankwaso zai yarda maitamakinsa ya gaje shi a kujerar da zai bari ta gwamnan jihar kano?

Duba da irin kalaman da ya rika yi a wajen tarurruka in da yake cewa da Ganduje suka zo da shi za su koma, wadannan kalamai nasa sun sake bai wa zawaran kujerar irinsu Honarabil Abdurrahman Kawu Sumaila da Janar mai ritaya Lawal Jafar Isa damar fitowa bilhakki su nemi kujerar wala Allah ko za su samu damar samun tikitin zama halattatun 'yan takarar da jam'iyya za ta sanya a gaba don haye buzun gwamna mai bari gado.

Sai dai kuma daga baya gwamnan ya yi a mai ya lashe ya yin da rana tsaka ya bayyana yardarsa a kan mataimakin nasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbinsa a gidan gwamnatin jihar kano.

Wasu masana siyasa na ganin gwamnan ya yi hakan ne ba da son ransa ba, sai don kawai tsira da mutunci bisa la'akari da yanayin siyasar Kano cewa siyasar zabi sonka ake.
Wani nazarin kuma na ganin kila gwamnan ya dauki darasi ne daga mulkin gwamnatin daya gada a  hannun malam Ibrahim Shekarau wanda ya bai wa dukkan kwamishinoninsa dama suka ci suka tada kai har ta kai suna jin suma karansu ya kai tsaikon da za su fito su mulki jihar kano a ya yin karewar wa'adin mulkin Malam Ibrahim Shekarau, hakan kuwa a ka yi mutane irinsu Sani Lawan Kofar Mata da Malam Ibrahim Kankarofi da Malam Ibrahim Khalil da kuma Mataimakin gwamna shekarau din wato Dakta Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo suka fito cikin shiri da neman jam'iyya ta tsayar da su takarar neman kujerar gwamna a 2011 a ya yin da kowannensu yake ganin idan ba shi jam'iyya ta tsayar ba to ba wanda ya dace da gurin, ana tsaka da wannan dambarwa sai malam Ibrahim shekarau ya dauko kwamishinsa na kananan hukumomi wato Malam Salihu Sagir Takai ya nuna a matsayin magajin da zai gaje shi a mulkin jihar Kano. Wannan al'amari ba karamin batawa wadancan yan takara rai ya yi ba, in da hakan tasa har wasu suka kasa jurewa suka yi canjin sheka daga Jam'iyyar ANPP zuwa wasu jam'iyyun cikin, wadanda suka sauya jam'iyya akwai matakin gwamnan Dakta Abdullahi T Gwarzo wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ACN kuma ka bashi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar, sai kuma Sani Lawan Kofar Mata shi ma daya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP ya marawa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso baya ya yin da wasu kuma suka tsaya a jam'iyyar ta su ta ANPP amma suka yi mata zagon kasa a zaben na 2011 da a ka yi suka kayar da ita.

Masana siyasa na ganin wadannan dalilai da ma wasun su suka sanya kwankwaso ya sahalewa mataimakinsa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zama magajinsa a gidan gwamnatin jihar kano.

Har ila yau tarihin siyasar kano ya nuna ba a yi wa kanawa karfa-karfa kusan idan muka koma tarihi za mu gane haka tun zamanin su Malam Aminu Kano da jam'iyyun siyasa irin su PRP da NPP da kuma NPN in da aka yi siyasar 1979 tsakanin Marigayi Muhammad Abubakar Rimi da Aminu Wali a lokacin Aminu Wali a jirgi yake kamfen amma talakawa suka nuna Rimi suke so kuma shi suka zaba, a 1983 sai kuma mutanen kano suka juyawa Rimin baya  duk da cewa shi ke da mulki a hannunsa kuma Jam'iyyarsa ta NPN ita ake ya yi suka zabi Sabo Bakin Zuwo a matsayin gwamnan kano a jam'iyyar PRP.
Haka in zamu iya tunawa a shekarar 1999 kwankwaso ya zama dan takarar gwamna a ya yin da suka yi takarar fidda gwani shi da Dakta Abdullahi Umar ganduje ba don ya fi ganduje komi ba.

Hakan ya ci gaba da faruwa a 2003 in da Shekarau ya fito neman kujerar gwamnan kanon a jam'iyyar ANPP wanda Buhari yake jagoranta ba tare da kudi ko shahara a siyasa ba, amma kanawa suka yarje masa ya zama gwamnan kano, sannan a 2007 ma sun sake ba shi irin waccan damar ya yin da aka yi ta camfin wai ba a mulkin kano sai biyu. Watakila wannan damar da Shekarau ya samu ce ta sa shi rafkanuwa a siyasarsa in da yake ganin kamar duk abin da ya ce da kanawa su yi za su yi masa ya sa ya tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a 2011 ba don suna so ba, in da su kuma suka nuna masa cewa kada fa ya manta kano siyasar yanci ake ba mamure ba. Suka bijirewa zabinsa suka zabi Kwankwaso da Ganduje a karo na biyu don sake mulkar jihar.

Ba nan gizo ke sakar ba har ila yau wasu na kallon cewa firgicin siyasa ne ya sanya Kwankwason ya bai wa matamakinsa takarar gwamna a jihar. Babu shakka alamu sun nuna cewa Ganduje ya gina siyasarsa a kano tun sassafe a lokacin da hankalin Kwankwason ya ta fi izuwa takarar shugabacin kasa. Sai shi kuma ya siye duka kananan hukumomin jihar, dama kuma mafiya yawa daga cikin su yaransa ne, sannan kuma kaso mai yawa daga cikin ma'aikatan jihar kanon Gandujen suke so a matsayin wanda zai gaji Kwankwason ya yin barin gadon mulkin kano. Kalaman siyasa sun ci gaba da zagayawa a bakin mutane in da kalmar nan ta daga LIMAN sai NA'IBI ta karade ko ina a jahar kano, ya yin da masana siyasa suke kallon matukar Kwankwason ya nuna wani ba Ganduje ba to hakan na iya sawa mataimakin nasa ya bar jam'iyyar abin da kuma zai haifar da irin wautar da ta faru da gwamnatin baya faruwar hakan kuma watakila ya ba jam'iyyar adawa dama su samu mulki cikin sauki don haka hanya daya ce mafita ita ce Kwankwanso ya marawa Ganduje baya domin ya gaji buzunsa, haka kuma kalaman wasu daga cikin zawaran kujerar gwamnan sun nuna in dai Kwankwaso ya nuna Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi to za su hakura su bi shi, idan kuma har ya nuna wani ba shi ba to lalle sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi. A irin wannan turnukun siyasar ne wasu 'yan mu gani mu fada suke cewa kwankwason bisa tilas ya tsayar da Ganduje a kujerar gwamnan jihar don gudun ta bare, domin ba ya son Gandujen ya zama gwamna a Kano tunda a shekarar 2007 da aka haramta masa tsayawa takara me yasa bai dauko Gandujen ya tsaya takara ba?

Duk da haka kwankwaso ya nuna dalilin da ya sanya ya nuna goyon bayansa kan takarar mataimakinsa  Dakta Abdullahi Umar Ganduje, in da yake cewa Gandujen ne ya dace da kujerar gwamnan jihar a 2015 domin da shi a ka yi wa jihar ayyakun da mutanen kano suke gani a yau, kuma ya ce tun da har mataimakin nasa ya nuna yana son gadar buzun da zai bari to wajibinsa ne ya goya masa baya domin shi ne lamba 2 a jihar kuma ya tabbata zai karasawa jihar ayyukan alherin da suka dauko da ma wasu karin ayyukan.

To komai da mene ne Kwankwaso ya kafa tarihi a siyasar Nijeriya don shi ne gwamna na biyu da ya amincewa mataimakinsa ya gaje shi idan ya bar mulki a ya yin da tsohon gwamnan Zamfara kuma sanata a yanzu Ahmad Sani Yariman Bakura ya zama gwamna na farko da ya bai wa mataimakinsa dama ya gaje shi wato Mamuda Ali Shinkafi shi kuma ya tafi sanata amma kuma a karshe ya butulce masa.
To ko ya zata kasance a jihar kano?
Yanzu dai Ganduje ya zama Gwamna Kwankwaso kuma ya zama Sanata Allah yasa kada tarihi ya maimata kansa.

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

GANI GA WANE...

No comments:

Post a Comment