0
A ranar Juma'a ne 6\3\2015 Masarautar kano karkashin Mulkin Sarki Muhammadu Sanusi II ta yi nadin sarautar Iyan Kano wadda aka nada Hajiya Umma Aminu Sanusi a wannan matsayi, Ni Rabiu Muhammad Abu Hidaya na samu tattauna da ita a gidan Sarki na Gandun Albasa game da takaitaccen tarihinta da kuma asalin wannan sarauta ta Iya da aka yi mata kuma ta gaya mi ni har da ayyukan da wannan sarauta za ta yi a masarautar kano, a sha karatu.

RANKI YA DADE DA FARKO ZA MU SO MU JI TAKAITACCEN TARIHINKI?
IYAN KANO: Assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, kamar yadda aka sani sunana Umma Aminu Sunusi ni ce 'Yar fari ga marigayi Ciroman Kano Ambasada Aminu Sanusi, da kuma Mahaifiyata Hajiya Saudatu Hussaini Yakasai, an haifeni a shekarar 1957 bayan an yaye ni a gidan Sarki lokacin Sarkin Kano Marigayi Muhammadu Sanusi I a soronsa na tashi a hannun Kwarkwararsa ita ma ta rasu Allah ya jikanta, muna ce mata yaya Yalwa, saboda a waccan lokacin akwai kara kakata tana nan a raye mahaifiyar Ubana ita ce Uwar soro amma sai a dauki yaro a ba wani ya yaye shi.
Na shiga Makarantar Firamare ta Kofar Kudu ina yar karama sosai, to daga nan sai sarki ya koma Azare muka koma wajen Mahaifiyarsa, bayan nan sai na tafi makarantar shekara bayan na gama sai na shiga makarantar mata ta Dala da na kammala sai na shiga makarantar share fagen shiga jami'a wato kas Zariya bayan na kammala sai na shiga Jami'ar Bayero lokacin tana karkashin Ahmadu Bello, na karanta ilimin Hulda da Jama'a (Social Science) bayan na kammala sai na  ta fi na yi bautar kasa a ma'aikatar walwalar jama'a ta Kano(Social Walfare) daga nan sai a ka yi wa maigidana Kwamishina a Neja  dama kuma shi mutumin Neja ne Farfesa Musa Abdullahi tsohon mataikin shugaban Jami'ar Bayero(Vice Chancerlor) daga nan sai muka koma can gaba daya.
To kusan a nan Neja na fara harkokin mulki daga mataki-mataki kama daga mataimakin sakatare na daya har zuwa matakin sama, muna tsaka da aiki sai aka yi juyin mulki lokacin Shehu Shagari sojoji suka karbi mulki, sai me gidana ya dawo koyarwarsa  a jami'ar Bayero ni ma sai na nemi canjin wurin aiki na dawo Kano ma'aikatar Kananan hukumomi ta jahar kano na dan fuskanci kalubale kadan domin a lokacin ba'a baiwa mata gurbin aiki a bangaren Mulki (Administration) haka dai aka yi ta turzawa ana so na koma koyarwa ni kuma na turje har ana cewa za'a bani Shugabar Makaranta(Principal) magana dai har ta kai gaban Gwamna lokacin Major Hamza Abdullahi ne Gwamna a Kano daga nan sai Gwamna ya ce a barni na yi aiki a gurin, to wannan ne ya bani dama na zama mace ta farko bahaushiya kuma yar arewa wadda na fara aiki a bangaren mulki (Administration) amma dai wasu sun ce kafin ni akwai wata baturiya da ta yi amma ni banganta ba.
Muna nan ana tafiya harkar aiki tana ci gaba har aka kawo maganar Direkta a matsayin aiki a lokacin mulkin Babangida, saboda haka nan ma na zama ni ce Direkta ta farko mace a jihar kano saboda ina tafiya ina sake cigaba saboda haka duk wata mace da aka dauka a bayana take kuma kafin ta zo ni na riga na kai matsayin babbar mataimakiyar Sakatare, to ka ga akwai tazara tsakanina da kowacce mace.
Daga matsayin Direkta, sai Tabbatacciyar Sakatariya (Permanent Sectery) a hukumar Mata(Women Affairs) wanda na yi aiki da matar tsohon Shugaban Kasa Janar Babangida Hajiya Maryam Babangida, daga nan kuma sai nemi taransifa na koma aiki a Gwamnatin Tarayya a matsayin mataimakiyar Direkta, bayan wani dan lokaci sai muka yi jarrabawa na zama Direkta, to a wannan matsayi ne na yi ritaya na bar aiki Gwamnati a watan Disambar shekarar da ta gabata 2014.
A takaice dai na yi aiki a gurare da dama musamman bangarorin da suka shafi mata, dan haka na fi karfafa ayyukana kan abubuwan akan mata.
GAME DA ASALIN SARAUTAR IYA A KANO KO ZAMU IYA SANIN TARIHIN WANNAN SARAUTA?
IYAN KANO: (Dariya) wato asalin sarautar iya na samo ta ne daga  Neja kauyen da mai gidana ya fito ana ce masa Kotonkoro idan ka wuce kwantagora ne, to suna da sarautar Iya wadda ake baiwa jinin sarauta mace, matsayin Iya a wannan masarauta shi ne kamar kula da harkokin mata yawanci a kauyen idan aka yi radin suna a kan dauki cinyar ragon da aka yanka a ce wannan ta Iya ce Iya za'a kaiwa, to saboda haka da aka yi wa mai martaba Muhammadu Sanusi II sarkin kano,muna hira  tare da wasa da 'yan'uwa ana ta hirar sarautu sai na kawo wannan maganar ta sarautar Iya a masarautar Kotonkoro sai aka yi ta dariya shi kenan kamar wasa sai ake kirana Iya, ni kuma na kan ce musu to sai ku kawo cinya, to cikin ikon Allah sai na duba na ga sullubuwa basa yi wa mata sarauta, sai lokacin Mai martaba Sarki Sanusi II lokacin yana Dan Majen kano ya yi wa matarsa sarautar Giwar Dan Maje, sai kuma Marigayi Sarki Ado Bayero ya yi wa Yarsa sarautar Magajiya, daga nan sai ni kuma na duba abubuwan da sarki yake son yi na cigaban al'umma domin shi mutum ne mai son cigaban ilimin jama'a da ciyar da al'umma gaba musamman kan sha'anin mata da kananan yara, to sai naga me zai hana a yi sarautar Iya a nan, sai a bada ofis a kalla dai za mu bada gudummuwarmu kan harkar abinda ya shafi harkokin mata da kananan yara da masu karamin karfi tunda ni ina da kwarewa kan abinda ya shafi wannan bangare, kuma alhamdulillahi na fito daga gidan sarautar nan, to sai na ga ai wannan wata dama ce da za a taimakawa mai martaba sarki kan haka kamar sha'anin cikin gida wanda ya shafi mata ko bada shawara ce in dai za'a dauka zaka iya bayarwa, kuma za ka ga sau da yawa sarki ya je da kansa gidan marayu da gajiyayyu ya raba kyaututtuka kuma yana karfafawa mutane gwiwa su rika yin haka, sannan na lura da cewa wani lokacin zai so ya fita irin wannan aiki amma wani aiki zai iya gindayo masa, dan haka idan na shigo sai na wakilce shi kan irin wadannan ayyuka da sunansa, tunda dama abu ne mun riga mun saba da irinsa, mu kan koyawa mata sana'o'i. Sannan zaka ga wasu suna son su taimakawa al'umma amma ba su san inda za su kai ba, saboda suna tsoron su bada dukiyarsu ta bi ta wata hanya daban, to mu kuma sai muka dauki alkawari idan sarki ya yi wannan sarauta za mu kula da wadannan fannoni ta hanyar kula da koyar da sana'o'i ga mata da matasa sannan za mu dinga bi muna ganin yadda wadannan ayyuka da muke koyarwa ba su ta fi a banza ba.
Sannan zamu kula da karatun yara saboda idan ka kalli yaranmu, yara ne masu kwakwalwa idan ka koya musu abu yanzu nan zaka ga sun koya dan haka za mu lura da wannan sosai.
MENENE BURIN IYA A HARKAR FADA?
Burina a harkar fada ina so mu sake hada kanmu sosai, manyanmu mu basu girmansu kanananmu mu jawo su jikinmu mu tafi tare da su, da neman shawara ga manyanmu domin sanin yadda zamu tafiyar da ayyukanmu inda suka ga mun yi kuskure su gyara mana, saboda kullum zamani canjawa yake kaga wataran wani sarki zai zo da iyalinsa kuma a al'adance bai kamata maza su yi ta mata hidima ba, mata yakamata a ce suna yi mata to kaga karkashin ofis dinmu za mu yin wannan aiki.
MENENE AYYUKAN SARAUTAR IYA A KANO?
To kamar  yadda gaya maka a baya ne cewa ayyukan wannan sarauta yana da yawa musamman harkokin mata da matasa da marayu, muna da bangarori har har guda hudu a wannan ofis na mu
don yin ayyukanmu bisa tsari kamar yadda muka tsara.
1.Akwai bangaren koyar da sana'o'i(Vocational)
2.Akwai bangaren kula da ilimin yara(Education)
3.Akwai bangaren koyar da wasanni da motsa jiki (Sport)
4.Akwai bangaren kula da lafiya(Health).
To wadannan ayyuka in sha Allah su ne manyan ayyukan da ofis sarautar Iya zai aiwatar.
YA KIKA JI DA AKA CE AN BAKI WANNAN SARAUTA?
IYA: Alhamdulillahi na ji dadi kwarai da gaske kuma na yi wa Allah godiya tare da mai martaba sarki, saboda ya bani dama in taimaka masa kuma dama ina sha'awar hakan don haka zan yi amfani da basirata in taimaka masa din don haka na ji dadi sosai da wannan nadi domin zan taimakawa dan uwana a harkar sarautarsa.
YA ZAKI BAYYANA MANA HALIN SARKIN KANO DANGANE DA ZAMAN DA KUKA YI DA SHI?
IYA: Sarki kano Muhammadu Sanusi II mutum mai hakuri da son jama'a sannan baya mantawa da mutane sai a dau shekaru da dama baku hadu ba amma kuna haduwa zai ambaci sunanka, kuma ko da ya zama sarki ni banga sarautar nan ta shiga kansa sosai ba, ko baki na zama sarki ni banga sarautar nan ta shiga kansa sosai ba, ko baki na kai masa kafin na gabatar masa dasu sai na ji ya ambaci sunansu, sannan shi mutum ne mai girmama mutane, akwai lokacin da muka shiga gidan sarki da daddare ba da niyar ganin sarki muka shiga ba domin lokacin wajen 11 na dare bayan mun gama gaisawa da mutane mun fito mun shiga mota sai aka kira cewa ga sarki ya fito saboda haka muka koma muka shiga muka yi hira wajen rabin awa kuma a lokacin shirin bashi sandar mulkin nan amma haka ya ba mu lokacinsa.
Saboda haka ina fata Allah yasa 'ya'yansa su yi ko da halayensa.
WANI KIRA ZA KI YI GA 'YAN UWA DA JAMA'AR GARI A MATSAYINKI NA IYAR GARI?
IYA: To Alhamdulillahi an riga an yi sarautar iya abinda zan ce shi ne jama'a su hada kai su so juna idan an taimake ka kaima ka taimaki wani domin za mu yi aiki tare kafada da kafada tare da jama'a, game da yan uwa kuma abinda zan ce shi ne Allah ya hada kawunanmu, Allah ya albarkace mu ya karfafemu da zumunci ya kara mana son junanmu.

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

TATTAUNAWA TA MUSAMMAN DA HAJIYA UMMA AMINU SANUSI (IYAN KANO)

No comments:

Post a Comment