Rikice-rikice na kara yawan zawarawa.
Sa'adatu Baba Ahmad
Yadda rikice-rikicen da ke faruwa a sassa daban-daban na kasar nan ke tasiri wajen kara yawan zawarawa da marayu da gajiyayyu da nakasassu. A bara kawai karkashin wani bincike an yi kiyasin an bar zawarawa dubu uku da dari biyar tare da marayu a k'alla dubu shidda. Ban da nakasassu bila adadin tare da gajiyayyu wadanda su ka rasa ma su tallafa musu.Irin wadannan rikice-rikicen sun had'a da na addini da na k'abilanci da na siyasa da sauransu, ko wacce tarzoma dai kan taso ne sakamakon rashin fahimta ko rashin adalci ko danniya da cin zali ko kuma dalilin son zuciya tare da gidadanci na zamantakewa.
Tun dai kafuwar wannan duniya da wacce ta gabaceta mutane ke ganin matakin zubda jini ne kadai hanyar kau da raini, da kuma cimma nasara. Tarihin musulunci ya nuna cewa an samar da duniyoyin da suka gabatane domin bautar Allah, amma sai halittun cikinta suka baude, yayin da su kai ta zubda jini a doron kasa wato su kai ta kisan juna wanda dalilin haka Allah ya
rushe su. Wannan da ma wasu dalilai na nuna cewa Allah na girmama halittarsa ba kamar mu 'yan adam da mu ke ganin kauda kara ba wuya ba ne.
In muka waiwayi sauran kasashen duniya sai mu ga cewa mu fa talauci da gidadanci ne kawai shimfidar kwananmu.
Ko nan jamhuriyar Nijar ma ai da wuya ka ji irin wadannan a na zubda jini haka duk da akwai kabilu daban-daban irin su zabarmawa da azbinawa da hausawa da Fulani da buzaye da sauransu. A duk wadannan kabilun da na lissafo ba wai rikice-rikicen ne da kashe-kashe ba a yi ba sai dai ba irin na Najeriya ba wanda ba doka ba ka'ida ba. Ba babba ba yaro.
Akasari dai rashin adalci da rashin hukunci yana jagorantar ma fi yawan munanan laifukan da mutane suke aikatawa, ba wai kawai wanda ya dauki bindiga ne ya ke barnar rayuka ba, har ma wanda ya dauki biro ya rubuta hukuncin rashin adalci da dokar tayar da zaune tsaye da kuma rahotannin k'arya wanda suke jefa zuciya a cikin tashin hankali tare da haddasa fitintinu.
Kamar yadda muka dubi al'amuran da ke kawo rikice-rikice wajibine mu dubi illar da su ke haifarwa a cikin al'umma, musamman ga rayuwar mata da yara, an kashe da yawan mazaje a sanadiyar rikice-rikicen nan, ko na baya-bayan nan irin rikicin zangon kataf, da shagamu da Kaduna da Kano da jos da Maiduguri da Damaturu da Gombe a kalla nazari ya nuna an kashe mazaje sama da dubu uku, wannan ba karamar asara ba ce a irin gudummowar da suke bawa al'umma, musamman ma iyalansu wanda suka dogara da su.
Na kan zauna kusan a lokuta da dama ina kukan tausayin marayu mata da maza
daga ko wanne jinsi ko yare ko kabila shin yaya su ke fafutukar rayuwarsu,
yadda al'ummar wannan zamani ta shagala da rashin temakawa mabukata ta yaya
matan da a ka bari da marayu su ke gwagwarmaya. Na taba jin labarin wata mata da 'ya'yanta marayu sun yi ciki gaba-daya da a ka sa ta a gaba sai tace tunda mujinta ya rasu ya barsu babu wani mutum da ya taba basu ko da kuwa tallafin hatsi ne wannan shi ya kaisu ga halakar da su ka samu kansu. Shin za mu iya tuna ko da maraya guda a unguwarmu ko a cikin danginmu da mu ke tallafawa da abin da mu ke da damar yi don ya samu ingantacciyar rayuwa?
Maraici wani abu ne mai ban tausayi, mai matukar tasirin raunana mutum ta hanyoyi da dama na rayuwa.
Rabe-raben kabilu ko yare ko addini a kullum mutane suke dubawa wajen cimma burin ransu na kashe-kashen juna amma ba sa tuntubar bangaren sakamakon abinda su ke yi, 'wai kaza da na yi mai ya ke haifarwa ga al'umma.
In har rayuwar wanda za ka kashe ba ta da amfani a gareka to, na tabbatar kashe shi ba zai amfaneka da komi ba sai dakon zunubansa wanda a kalla ya shafe Shekaru ya na yi, watakila ka bar shi ya amfanarwa iyalansa da 'yan uwansa zai fi maka daukar fansa ko huce fushin zuciya.
Kuma abin dubawa kashe wadansu mutanen a yayin da rikice-rikicen su ke tasowa su na tasirin dakushewar al'ummar ko addinin da a ke rigimar da su?, ko kuwa danniya da rashin adalci da zalunci da aikata munanan laifukan na raguwa?
Kashe-kashe ba sa maganin matsalolinmu kullum kara bude kofar matsaloli da rigingimu su ke yi. In kuma suna magani me su ka maganta mana?
In har wannan amsar a'a ce, to, gaskiya muna yaudarar kanmu wajen cutar da
juna ta hanyar kisa. Ya na da kyau mu bar kisan kai a kan wadanda Allah ya
umarta.
A zahiri irin kashe-kashen da a ke a kasar nan ya keta dokar mutuncin dan adam, ko a kwanakin baya na ga gawawwakin mace da yara da a ka kashe an kai wani asibiti, wannan ya fi komi ta'addanci da cin fuska a ganina,.
Mu sani gasar kashe-kashen rayuka da mu ke yi muna tozarta rayuwar matanmu
ne da 'ya'yanmu kuma ba zamu amfana da komai ba sai dakushewar al'ummarmu.
In muka dubi yawan yaran da a ka kashewa iyaye yadda su ke tasowa a cikin kunci da kadaici sai mu ga cewa lallai muna da hakki babba da watakila zai dinga bibiyarmu. Sannan a gefe guda muna kara haifar da yawan zawarawa duk da ko galibin mazajen ba aure su ke bisa tsari na taimakon al'umma ba, a ce yau namiji ya tausayawa macen da aka mutu a ka bari da marayu ya aureta ya rike 'ya'yan kamar nasa, ko ya dinga tallafa musu da abincin da za su ci don ya samu lada su kuma su ji dadin rayuwa, da wuya a samu haka. In kuwa a ka samu namiji zai auri matar mamaci ya rike mata 'ya'yanta galibi sai idan mamacin ya mutu ya bar dukiya mai tarin yawan gaske wacce zai zauna ya ci garabasa amma akasari in mace ta rasa mujinta in har ya barta da yara to, sai dai ta kaiwa iyayensa ko 'yan uwansa Sannan ta je ta yi aure, in kuwa ta
dage sai dai a aureta da 'ya'yanta don ta rike su ta basu kulawa da tarbiyyar da ta dace to, ba shakka zai wuya ba ta kare rayuwarta a gwauruwa ba.
Wahalar da muke gudu har yanzu ita ta ke bibiyarmu, yara da mata su na da rauni kuma su na bukatar tausayawa daga mazaje, lallai suna bukatar tallafi don mace komi girmanta yarinya ce a gun iyayenta da mujinta, ranar da ta rasa su kuwa tamkar mutum ne ba hannu ba kafa, shin ta yaya zai tallafawa kansa ba a tallafe shi ba.
A karshe ina kira ga:
Malamai,
Alkalai,
Sarakai,
Kungiyoyi.
A dubi Allah a tausayawa rayuwar mata da yara a kan duk wani hukunci da za'a zartar domin yana shafarmu ta fuskoki da dama, a kamanta adalci, sannan duk tsarin da ya kaucewa shari'a shi ke haifar da fushi tare da da-na-sani, a dinga aure don taimakawa addini da al'umma, kuma tallafawa marayu tallafawa baki dayan al'umma ne.
Sa'adatu Baba Ahmad
(Mrs Shehu Sanusi Bayero )
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.