0

Ma}alar da aka gabatar a taron Al'adun Hausa na {asa da {asa na Burkina Faso TAHAKA (karo na biyu), a Ouagadougou – Burkina- Faso, daga ranar 7th – 11th ga watan Disamba na 2018.

Gabatarwa

Waiwayen tarihin irin rawar da harshe da al'ada suke takawa ga ci gaba mai ]orewa, lamari ne da aka ayyana shekarun 1980 da kuma farkon 1990 a matsayin wani zango na baiwa mutane dama ta bayar da gudummawarsu a wajen ayyukan ci gaban al'umma. Taron duniya na Mexico a 1992 akan matsayin harshe da al'ada, ya jaddada nasarar samuwar ci gaban al'umma domin amfanin kansu. Da tafiya ta yi tafiya, sai hukumar raya ilimi da kimiyya da kuma al'adu ta Majalisar [inkin Duniya (UNESCO) ta }addamar da bukin shekara goma (1988-1998) na ci gaban harshe da al'ada a duniya. Sakamakon wannan gangami ne ya haifar da tanadin wasu ma'aunai na ci gaban rayuwar al'ummar duniya. A shekara ta 1990 kuma sai hukumar raya }asashe ta Majalisar [inkin Duniya (UNDP) ta yi amfani da wa]ancan ma'aunai ta wallafa rahoton irin ci gaban da ake samu. Haka dai lamarin ya ci gaba inda a shekarun (1992 -1996), hukumar inganta harshe da al'ada da kuma ci gaban al'umma ta Majalisar [inkin Duniya ta shirya rahoto akan yadda za a fa]a]a }umshiyar al'adun al'umma. 

Nan take taron }arawa juna ilimi na gwamnatocin }asashe da aka yi a Stockholm a 1998 ya amince da yalwata hurumin harshe da al'ada ga ci gaban al'umma. Daga nan  kuma sai wani taron }arawa juna ilimi na ha]in gwiwa tsakanin hukumar UNESCO da Bankin Duniya a 1999 akan matsayin al'ada ga bun}asa tattalin arzi}i. Sai kuma a 2001 da hukumar UNESCO ta ayyana harshe da al'ada a matsayin }ashin bayan tattalin arzi}i da zamantakewar al'umma. Da shekara ta 2005 ta zo sai UNESCO ta tanadi matakai na kariya da na bun}asa harshe da al'ada domin ci gaba mai ]orewa. A wannan ma}ala za mu yi tsokaci ne dangane da gudummawar harshe da al'ada ga bun}asa tattalin arzi}i da zaman lafiya da kuma ci gaba mai ]orewa. A sashe na farko da na }arshe, jawabin gabatarwa da kuma na kammalawa ne. Sashe na biyu ya kalli irin dangantakar da ke akwai ne tsakanin harshe da al'ada. Daga nan kuma sai sashe na uku inda muka kalli harshe da al'ada a matsayin madubin al'umma. A sashe na hu]u kuma muka taskace irin rawar da harshe da al'ada suke takawa wajen bun}asa tattalin arzi}i da kuma kawo zaman lafiya mai ]orewa ga al'umma.

2.0 Dangantakar Harshe da Al'ada

Kalmar dangantaka na iya ]aukar ma'anoni kamar ala}a da zamantakewa da }awance a tsakanin abubuwa biyu ko fiye. Saboda haka, ta ~angaren deangantaka, muhimmancin harshe da al'ada ga rayuwar al'umma ba abu ne ~oyayye ba. Trudgil (1974), wani masanin ilimin walwalar harshe ya bayyana }wararan ayyukan harshe da al'ada guda biyu: (a) na farko shi ne sadarwa ko isar da sa}o ta bayar da bayani (b) na biyu kuma shi ne tabbatar da ala}a da dangantaka tsakanin jama'a. Ita dangantaka tana wanzuwa ne a tsakanin ]ai]aiku da kuma tsakanin al'umma. Shi kuwa harshe shi ne hanyar furta ma'anoni da tunane-tunanen da suke ran ]an'Adam. Wato dai ita ce hanyar sadarwa tsakanin mutane. Ita wannan hanya kuma ba ganinta ake yi ba, jinta ake yi kawai, wato hanyar sadarwa ta ]an'Adam (harshe) saututtuka ne masu ma'ana da ake furta su, kunnen mai sauraro ya ji, kana basirarsu ta kama ta fahimta domin amfaninsa. Ita kuma al'ada ]abi'a ce da ]an'Adam yake ]aukar wa ransa, har a }arshe kuma ya ri}a ganin ta zame masa tilas (Gadanya, 1977). 

Hasali ma, ai kowace al'umma ta duniya tana da nata al'adu wa]amnda take ganin su ne mafi kyau ga duk sauran al'adun duniya. Wato dai yadda 'yan-Adam suka bambanta ta kowane fanni, haka ma suka bambanta ta fannin al'adu. Saboda haka, abu ne mawuyaci ka ga al'ummu guda biyu suna da al'adu iri ]aya, sai dai akan samu kamanceceniya, amma kuma harshe ne babban ginshi}in gina kowace  al'ada. Manazarta al'ada daga fannoni daban-daban kamar addini da kuma kimiyar kiwon lafiya suna kallon al'ada gwargwadon mizanin darussan nazarinsu. A fannin walwala musammanm ma cikin dangantaka da harshe, ana iya kallon al'ada ta hanyoyi biyu. Hanya ta farko tana iya nufin dukkan abubuwan da suka shafi ci gaban basirar ]an'Adam. Hanya ta biyu kuma (wadda masana kimiyar rayuwar ]an'Adam na }arni na ashirin suka fi }arfafawa) ita ce ta kallon al'ada a matsayin jimillar dukkan ilimi tare da hanyoyin cu]anyar yau da kullum na kowace al'umma (Nelson, 1960). 

Idan muka ]auki gundarin abin da wa]annan bayanai ke nunawa, sai mu ga cewa nuni suke yi da cewa al'ada dai kamar ita ce rumbun dukkanin tunne-tunane da falsafa da basira da kuma dukkan sauran ginshi}an rayuwar ]an'Adam (cf. Salim, 1985). Kenan idan aka yi la'akari da dangantakar da ke tsakanin harshe da al'ada, to sai a ga harshe a nan ya tashi a matsayin }ofar shiga da fita (wato ajiyewa da ]aukowa) daga cikin wannan rumbu. Wato dai ta wannan hanya ce kawai za mu san me ke cikin rumbun. Wannan shi ne ya sa cewa, da wuya a iya ware harshe daga al'ada. Haka kuma shi ne ka]ai mafi muhimmanci daga cikin dukkanin hanyoyin bayyanawa, da kuma gane sauran ginshi}an al'adar kowace al'umma (Lado, 1964). Saboda haka, dangantakar harshe da al'ada dangantaka ce  irin ta jini da tsoka. Wato yin nazarin harshe ba zai yi wu ba sai tare da sanin al'adar da wannan harshe ya ]amfaru gare ta. Rayuwar mutum ita ke shirya masa dukkan halayen zamansa a garinsa da kuma garin wasu. Hasali ma, har da irin abin da zai ce idan ya tashi yin magana da mutanen gida da waje. Ita wannan magana tana ginuwa ne a kan rayuwa gaba ]ayanta domin ita ce ma ke shiryawa mutum yadda yake magana da yara da tsara da mahaifa da kuma shugabanni. Harshe ba shi da ala}a da mutum, wato ba wai haihuwar mutum a awuri ke sa ya ji harshen su mutanen wurin ba, sai dai idan ya tashi da amfani da shi. Saboda haka, duk wanda ya tashi da wani harshe, to lallai harshen zai koya. Jinin mutum ba ya da ala}a da harshensa, domin sai a samu Baturen Ingila yana Larabci, ko kuwa Bafaranshe yana Hausa. Kenan furucin mutum ba ya nuna }abilarsa, domin furuci ba manunin }abila ne ba sai dai idan mutum ya fa]i }abilarsa, tun da duk inda mutum ya tashi, furucinsu zai koya ya kuma iya. Sai dai kuma furuci yana nuna matsayin mutum da iliminsa, amma ba asali da jini ba. An kuma yi amanna da cewa Bahaushe zai yi Hausa, Balarabe kuwa ya yi Larabci, Bafillace zai yi Fillanci da dai sauransu, amma ba dole ba ne.

3.0 Harshe da Al'ada a Matsayin Madubin Al'umma

Al'umma ita ce tarin ]ai]aikun mutane da suke zaune a gari guda ko yanki ko lardi ko jiha ko kuma }asa. Al'umma tana iya }unsar }abilu daban-daban. Wannan ya nuna cewa duk inda aka sami  fiye da ]an'Adam guda a wuri guda, to lalurar hul]a da mu'amala ta kama. Hul]a da mu'amala kuwa basa cika ba tare da magana ba. Kenan amfani da harshe da al'ada tilas ne a hul]a, kuma lalura ce. Tun da yake haka ne kuwa, to bukatar harshe da al'ada ga ]an'Adam ta kai }arfin bukatarsa ga abinci da ruwa, ko ma watakila har da iskar sha}a (Rufa'i, 1986).

Ta hanyar harshe, ana iya samun hasken tarihin al'umma. Wato ta harshen al'umma ne akan iya gane ci gabanta musamman dangane da tsarin mulki ko shugabanci da sharia da ilimi da tattalin arzi}i da addini da kuma al'ada. Sauran maganar kuma ita ce, idan aka yi dace cewa al'ummar tana da hanyar rubutu, to ta rubuce-rubucensu za a ga gacin da suka kai domin a ci gaba. Idan kuma babu hanyar rubutu, to ta hikimarsu ne kawai za a iya ganewa cikin mu'amala da su. Ta adabin al'umma ma ana iya gane irin }wazonsu cikin tarihi. Ta nan ne wayonsu zai bayyana da kuma }o}arinsu na kyautata rayuwarsu da irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban al'umma. Domin }ara tantance dangantakar harshe da al'ada, da kuma yadda sakamako ko kuma tasirin wannan dangantaka ke zama matsayin madubin al'umma, bari mu ]an yi nazarin jigogin rayuwar al'umma. Amfani ko kuma fa'idar yin nazarin shi ne fito da bayanan dangantakar a tsakaninsu. Da yake sadarwa tsakanin al'umma lalura ce wajiba, bukatun rayuwa za su matsa wa 'yan wata }abila su yi hul]a ko mu'amala da 'yan wata }abula daban. Hakan ya zama dole domin ita hul]a ko mu'amala ba ta yiwuwa sai fa ta amfani da harshe cikin dangantaka da al'ada. A ta}aice dai idan ana magana a kan matsayin harshe da al'ada na madubin al'umma, to wajibi ne batutuwa irin su koyar da harshe da ilimantarwa da tattalin arzi}i da tsarin zamantakewa da kuma nisha]antarwa su bijiro.

4.0 Nazarin Jigogin Rayuwa

Da yake al'umma ta }unshi ]ai]aiku, to ashe al'umma aba ce rayayyiya wacce take da farko da halin rayuwa da kuma }arshe, ko kuma a cikin hikima a iya cewa al'umma tana da jiya, tana da yau kuma tana da gobe. A ra'ayin Rufa'i (1986), idan aka juya ta wata hanya, to muna iya cewa al'umma tana da tarihi, kuma a cikin wannan halin wanzuwar tana ya}in rayuwa. Bugu da }ari kuma, tana faman tabbatar da kyawawan abin da zai je ya zo. Wannan ya nuna cewa al'umma kamar tilon ]an'Adam tana da alfahari da kuma buri. Alfaharin nan shi ne tarihi, buri kuwa shi ne kokawar rayuwa domin yau da kullum. Saboda haka, a fafutuka ta wanzuwa, akwai bukatar abubuwan nan da suka zama dole ga kowace al'umma domin rayuwa. Wa]annan abubuwa su ne: mulki da sharia da tattalin arzi}i da ilimi da addini da kuma al'ada.

Tsarin mulki a cikin kowace al'umma wajibi ne. Mulki shi ne ka]ai zai tabbatar da zaman lafiya yadda kowa zai sami damar yin harkokinsa na yau da kullum domin neman abinci da arzi}in duniya. Wato idan babu mulki a al'umma, to ru]ani da yamutsi da hargitsi da kuma cutar juna ne za su tabbata. Idan haka ya auku, sai al'umma ta kai ga halaka domin babu wanda zai sami sukunin neman abinci ballantana arzi}in }asa. Domin a sami cikakkiyar lumana da tabbatar da zaman lafiya, ya wajaba a sami fahimtar juna tsakanin masu mulki da wa]anda ake mulka. Mafi yawan kyawun hanyar fahimtar ita ce harshe wanda muka ce shi ne jigon sadarwa. Ga misali, kafin zuwan Tuarawa }asar Hausa, mutane ne daga cikinmu suke mulkin }asarmu. Wato harshenmu ]aya da su, kuma duk hanyoyin rayuwa ]aya ne tsakanin masu mulki da wa]anda ake mulka. Don haka, sadarwa take da sau}i, wanda hakan ya tabbatar da bin umurni da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali. Daga nan Nasara ya }wace mulki, amma kuma harshenmu da na nasara ba ]aya ba ne. Don haka sadarwa tsakaninsa a matsayinsa na mai mulki, da, mu a matsayin wa]anda ake mulka sai ta wuyata. Gaskiyar maganar ita ce, a yayin da aka rasa sadarwa tsakanin mai mulki da kuma wanda ake mulka, to babu yadda shi wanda ake mulka ]in zai sami damar sa baki a yadda ake mulkin nasa. Sauran maganar ita ce, zuwan Baturen ne dai ya kawo mana tsarin mulki na siyasa wanda hasken saninsa yana cikin harshen da ba namu ba. Haka kuma Bature ya bar mana gadon tsarin mulki wanda a kan rubuta shi da harshen da ba na 'yan }asa ba ne. Kasa fahimtar wa]annan abubuwa ya kawo matsala. Bayan tsarin mulki, kowace al'umma ba za ta gaza bukatar tsarin Sharia ba, da yadda za a tabbatar da adalci a mulki. To a nan ma harshe yana da rawar da za a gani. Wajibi ne ga jama'a su fahimci irin shariar da ake yi a }asarsu domin su tabbatar wa kansu adalci idan rigima ta same su. 

Mafi kyawun fahimta ita ce abu ya zama da harshen mutum ake yinsa, idan ba haka ba to wasu abubuwa za su shige duhu. Tun kafin zuwan Turawa, a }asar Hausa ana amfani da shari'ar Musulunci ne. Wannan tsari na sharia a cikin Larabci yake, wanda ba kowa da kowa ya iya fahimta ba. Don haka da wuya jama'a su san kanta sosai da sosai, musamman ma idan wata matsala ta taso. Da Bature ya zo, shi ma dai ba ta sake zani ba. Ita tasa shariar a cikin Turanci take, ko haifaffen harshen ma sai ya yi famar fahimta tasa, balle kuma ]an koyo. Duk a wa]annan halaye guda biyu, da wuya mutane da yawa su fahimci nau'in shari'un domin ba a cikin harshensu suke ba, ga shi da wuya koyon ba}on harshe.

Babu shakka ilimi babban jigo ne a rayuwar mutum da al'umma gaba ]aya. Hasali ma, ai ilimi wata hanya ce wadda mutum yake amfani da ita ya gane abubuwa, ya fahimce su ta yadda zai bun}asa sulukinsa a rayuwa (Gusau, 2010). Wani mutum, ilimi yakan daidaita tunaninsa ya zama mai tsiwurwurin rayuwa nau'i biyu, wato rayuwa ta duniya da kuma ta lahira. Wani kuma yakan gane sassan rayuwa ne wadda ta shafi duniya, ya zama mahiri, ya tumbatsa wajen samar da }ololuwar jin da]inta. Ta haka za a tabbatar da fahimta ita ce }ashin bayan ilimi wadda za ta yi jagora ga samun jin da]i ko muni, sannan a iya bambance abubuwa masu baragada ko baragurbi. Haka kuma shu]ewar kwanuka da yau da gobe a rayuwa wani }ari ne na daraja a ilimi (Bergery, 1934 da kuma Hornby, 1974). Don haka neman ilimi dole ne domin rayuwa ta yi armashi.

A ra'ayin Lepage (1964), a }asashe masu tasowa, ilimi mabu]i ne ga abubuwa guda biyu }warara: (a) mabu]i ne ga samun abinci. Ta hanyar ilimi ana iya kyautata noma da sana'o'i da fasaha da tattalin arzi}i da sauran abubuwa da suka ji~inci jin da]in rayuwa. (b) mabu]i ne ga kyautata al'adu da ha]a kan jama'a, da samar da manufa ko al'}ibla guda. Baya ga ilimin addini, ilimin zamani Bature ne ya kawo shi, don haka da harshen Bature ne wannan ilimi yake, duk da cewa ba duka muka taru muka iya Ingilishi ba. Masana sun ce harshen da yaro ya tashi da shi, to ya fi tasiri a kansa wajen gina basira da hankali da wayo da kuma }wazonsa. Wannan yanayi ya bambanta da halin da ake ciki, domin muna neman ilimi da ba}on harshe. Haka }arin wahala ne domin sai mun iya harshen sosai kafin mu koyi ilimin.

Duk da cewa Hausawa sun na}alci iya ciniki da safara da tajirci, to amma zuwan Bature ya kawo wani sabon salo dangane da tattalin arzi}i. Da yake babu }asar da za ta dogara da kanta kawai, to dole ne kafar hul]a da mu'amala ta bu]e musamman ma da wa]anda suka ci gaba. Sai dai kuma kash, hasken da ya kamata mu yi amfani da shi yana cikin harshen da ba namu ba. Saboda haka fahimtarmu da su sai an yi ]amara, musamman da yake ai rashin sanin sirrin tattalin arzi}in ne irin na zamani ya sa aka wawashe dukiyar  }asar a shekarun baya. Gaskiyar magana ita ce, idan ba ka fahimci abu ba, babu wuya a }ware ka a cikinsa. Wato dai idan kana mu'amala da mutum, ya fahimci ba ka na}alci sirrin abin da kuke mu'amala a kansa ba. to babu wuya a cuce ka. Rashin sanin sirrin tattalin arziki irin na zamani yana da illa, saboda haka babu makawa sai an rungume shi duk da kasancewa cikin ba}on harshe.

Kowace al'umma kan dogara da wani abu a matsayin mai wanzar da rayuwa. A al'umomin da suka waye akwai addinai da suka }udurce akwai ubangiji. A nan, addinin Musulunci ya da]e a }asar Hausa, sai dai mafi yawan jama'armu ba su fahimci addinin ba, saboda ba su san }a'idojin addinin da iliminsa ba. Hakan ya faru saboda kasancewar ilimin addinin a harshen da ba  namu ba, wato harshen Larabci. Tun da dukkaninmu ba mu iya Larabci ba, to da wuya kowa da kowa ya sami sukunin karanta littattafan addini. Don haka dole ne a dogara ga 'yan tsirarun mutanen da suka iya Larabci domin koyon addini ta kansu. Sauran maganar ita ce shin ko hakan zai wadatar? To a gaskiya ko da a harkar addini ba a rasa marasa gaskiya, wa]anda za su yi cuta su ribatu da jahilcin mutane. Saboda haka, maslaha ita ce fassare-fassare na littattafan addini zuwa harshenmu domin fahimtar addini sosai.    

Masana sun yi ittifa}i cewa al'ada ita ce tarin hanyoyin rayuwar jama'a, musamman hikimominsu da fasaharsu da wayewarsu da iliminsu da hul]o]insu da mu'amalarsu da ka]e-ka]ensu da raye-rayensu da kuma sauran irin su. Kafin zuwan Musuluni }asar Hausa, adabin Hausawa na baka ne, wato wa}ar baka da tatsuniyoyi da kuma labaru. Zuwan Musuluni ya sa wasu suka san Larabci har suka fitar da ajami a matsayin hanyar rubutu. Ta ]aya haujin kuwa, zuwan Turawa ya kawo mana iya rubuta Hausa da boko. Harshe shi ne abin furta ra'ayoyi da ma'anonin al'adu, saboda haka, dangntakar da take tsakanin harshe da al'ada }a}}arfa ce. Wato }arfin ya kai babu yadda za ka koyi wani harshe ko ka yi nazarinsa ba tare da ka san al'adar masu harshen da ladabin amfani da shi ba. Ga misali, saboda irin wannan ladabi na amfani da harshe, masana suke cewa koyon harshe da koyar da shi ba zai yiwu ba sai da fahimtar al'adar masu harshen. Tun da yake haka ne kuwa, to ta tabbata kenan cewa akwai dangantaka mai }arfi tsakanin harshe da al'ada.

5.0 Kammalawa

Daga abin da ya gabata dangane da matasayi da }imar harshe da al'ada, ta tabbata cewa ha]akarsu (wato harshe da al'ada), tana share fagen ci gaban al'umma mai ]orewa. Da farko dai akwai ]orewar tsarin zamantakewa, wato da harshe da al'ada ne  ake sarrafa muhimman batutuwan da suka gina tsarin zamantakewar al'umma. Irin wa]annan batutuwa sun ha]a da harshe da addini da ilimi da auratayya da kuma yin sulhu a tsakanin al'umma.

Akwai kuma ilimi na sarrafa tadoji da aka gada tun iyaye da kakanni, da suka ha]a da ilimin noma da tsarin cimaka da kiwon lafiya da rainon yara }anana da kayan gine-gine da kuma amfani da sarrafa muhalli. Wannan tsari da aka gada tun iyaye da kakanni, da harshe da al'ada ne ake tafiyar da su, saboda haka duk wani tasiri ma a bisa wannan tsari yake ci gaba da tafiya. Shi tasiri yanayi ne na ha]uwa da ba}in al'adu a sanadiyar hul]a ko mu'amala tare, daga nan kuma sai kwaikwayo da aro su bijiro a sanadiyar tasiri a kan juna.

Ta haujin al'adun gargajiya ma, da ha]akar harshe da al'ada ne ake sarrafa su. Wato da wa]annan ne (wa]anda sun ha]a da sana'o'i na samun abin ]awainiyar kai da kuma iyali gaba ]aya). A gaskiya ma, wa]annan hanyoyi na al'ada, na}altarsu ake yi kuma iliminsu na ]orewa tun daga iyaye daga kakanni. Akwai kuma batun wasu al'adu na musamman, wa]anda al'umma suka ]auka da matu}ar fa'ida da muhimmanci. Hasali ma, irin wa]annan al'adu na musamman (wa]anda kuma ake sarrafawa da harshe a cikin ma'auni na al'ada) suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al'umma. Ga misali, ]auki maganganun hikima da azanci da aka san a harsunan al'umma ne suke }umshe da kuma ]imbin al'adun da suke koyarwa. Akwai adabi (wanda ya }umshe zube da wa}a da kuma was an kwaikwayo) da zane-zane da raye-raye da wa}e-wa}e da labarum gargajiya da ayyukan hannu da kuma fina-finai. Bugu da }ari gudummawar harshe da al'ada ba a baya suke ba, dangane da ya]a ilimi, musamman ma irin wanda zai ha~aka basira da aiki da basira da hikima ta }ir}ira da kuma dabarun gina al'umma a matsayinsu na ]ai]aiku da kuma a }ungiyance. Ana kuma tace gur~atattun tadoji da al'adu, sannan a yi watsi da su domin kada su cutar da al'umma (musamman ma yara manyan gobe). Harshe a matsayinsa na hanyar furuci mai ma'ana, shi ne al'umma ke sarrafawa cikin magana domin isar da  sa}on da ke zukatansu na abin da ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum. 

Kenan tasirin harshe da al'ada ga al'umma tamkar rayuwa ce da ruhinta, wato harshe ba ya wanzuwa sai idan akwai al'ummar da ke amfani da shi. Haka kuma, al'umma ba ta iya gudanar da al'amuran rayuwarta sai ta yi amfani da harshe a cikin dangantaka da al'ada. Ashe kenan ]aya ba ya yin tasiri sai da ]ayan. A gaba ]aya dai harshe da al'ada ha]aka ce ta muhimman abubuwa guda biyu da suka zamo kafa wadda ]ai]aikun mutane (da kuma ma a }ungiyance) suke bayyana }wazo da hikima da kuma karsashinsu na gina kansu (da al'umarsu). Saboda haka, harshe da al'ada suna daga cikin ~angarorin ci gaban al'umma mai ]orewa.

                                  MANAZARTA

Gadanya, S. M. (1977): 'Salon Ta]i Tsakanin Hausawa', Unpublished B.A. Dissertation, Nigerian Languages Department, Bayero University Kano.

Gusau, S. M. (2010): 'Ilimi Garkuwar Al'umma', Takardar da aka Gabatar a Taron Kaddamar da Gidauniyar Bunkasa Ilimi a Masarautar Kaura Namoda, Zamfara.

Hymes, D. (1964): Language in Culture and Society, Harper and Row, New York

Lado, R. (1964): Language Teaching: A Scientific Approach, McGraw-Hill, New York.

Nelson, B. (1960): Language and Language Learning: A Theory and Pratice, Harcourt Brace and Co. New York

Trudgil, P. (1974): Sociolinguistics: An Introduction, Penguim Books Ltd, Harmondsworth.

Rufa'i, A. (1986): 'Dangantakar Harshe da Al'umma', Paper presented at the Hausa Week, School of Preliminary Studies, Kano.

Salim, B. A.(1985): Linguistic Borrowing as External Evidence in Phonology, Unpublished PhD Theses, York.

UNESCO (1953): The Use of Venacular Languages in Education, Report of the UNESCO Meeting of Specialists, 1951, Paris UNESCO

Yakasai, S.A. (2012): Jagoran Ilimin Walwalar Harshe, Sokoto: GARKUWA Media Services

Yakasai, S. A. (2000): Language Across Two Borders: A Sociolinguistic Study of Hausa in Konni and Illela Towns, Unpublished PhD Theses, Nigerian Languages Department, Bayero University Kano.

Yakasai, S.A. (2014): Language and Cultural Preservation: Hausa in the Face of Technological Advancement, Kano: Gidan Dabino Publishers.

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

Gudummawar Harshe da Al’ada ga Bun}asa Tattalin Arzi}i da Zaman Lafiya da kuma Ci gaban Al’umma Mai [orewa Daga Farfesa Salisu Ahmad Yakasai Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato syakasai2013@gmail.com (+234) 08035073537

No comments:

Post a Comment