0
MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU Tare da Dokta
Balbasatu Ibrahim (Mrs)
Tun da Allah ya halicci duniya ya jarabi dan adam
da abubuwa guda uku. Wadannan abubuwa kuwa
su ne yare, dukiya, da jinsi. Har yau da muke raye wadannan abubuwa na
ci gaba da ci wa Dan adam
tuwo a kwarya. Dalili kuwa shi ne a duk sanda aka
ce wannan shi ne yaren mutum, to zai yi kokarin
ganin cewa martaba da kwarjinin wannan yaren
nasa sun fi na kowa. Alal misali ja-in-jar da aka yi ta
yi tsakanin Turawa da bakar fata a kasar Afrika ta Kudu a shekarun
baya da kuma kisan gillar da 'yan
kabilar Hutu suka yi wa 'yan kabilan Tutsi a kasar
Ruwanda a shekara 1989, haka kuma rikicin da
ake ciki yin a halin yanzu tsakanin Larabawa da
bakar fata a Darfur ta kasar Sudan sun kasance
misalai na irin yadda yare ke tayar da takaddama tsakanin mutane.
Ita ma dukiya ko mulki kan haifar da zalunci da
danniya tsakanin masu hannu da shuni da
talakawa a cikin al'umma. Idan muka dubi irin
tsare-tsaren siyasar da aka yi ta yi a kasashen Turai,
kamar tsarin jari-hujja da na gurguzu da kuma na dimukradiyya da ake
ikirari a yanzu, sai mu ga har
yanzu ba su hutar da talakan ba, sai kara tsotse shi
ake yi, ana kara wa masu karfi, karfi.
Matsala ta uku kuwa ita ce wariyar jinsi, wadda
Jennifer (1985) ta yi bayanni cewa "ta wanzu ne a
sanadiyar ra'ayi ko akidar nan ta cewa "akwai bambancin fifiko
tsakanin namiji da mace a cikin
al'umma". Wannan matsalar ita ce take tashe a halin
yanzu a ko'ina cikin duniya. Tashenta kuwa ya
hada da fagen siyasa da na tattalin arziki da na
yanayin zamantakewa da fasaha da ilmi da sauran
su. A takaice babu bangaren rayuwar da matsalar wariyar jinsi ba ta
kutsa kai ba.
Shigowar wannan matsala ta haifar da ka-ce-na-ce
tsakanin manazarta ciki kuwa har da na adabi.
Ganin cewa bincikena ya shafi harkar bambancin
da ake iya samu tsakanin mace da namiji ta
bangaren rubuce-rubuce ko kuma adabi, na ya dace na soma da fahimtar
yadda wannan
takaddama ta samo asali da yadda take taimakawa
wajen ginawa da raya harkar nazarin ayyukan
mata.
Daga 'yan karance-karancen da na yi, sai na fahimci
cewa duk da cewa ana ta hayagaga kan wannan fage na wariyar jinsin ba
a cika aza tunanin fagen
bisa tafarkin da ya dace ba. Wannan na daga cikin
abin ya shiga cikin zuciyata a lokacin da na soma
tunanin wannan bincike. Shi ya sa ma na na ce a
zuciyata wai me zai hana in dauki fanni daya daga
cikin abubuwan da suka shafi mata in gudanar da zuzzurfan bincike a
kan sa, ta yadda ni ma zan iya
bada gudunmuwa game da irin gudunmuwar da
matan Hausawa ke bayarwa ta fuskar adabi.
Sai dai kafin na shiga cikin gonar aikin nawa ya
kamata mu san cewa wannan hayaniya ta wariyar
jinsi ba sabuwar aba ba ce, ta dade da kutso kai a tsakanin al'umma.
Wasu masana na ganin ewa ta
taso ne tun a wajajen shekarar 1960 har zuwa
shekara 1975 lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta
bullo da shirinta mai take "Shekarar Mata" da na
"Shekarun Mata"a shekarar 1985 aka yi taron
Majalisar na Nairobi, sannan aka yi babban taro wanda yake shi ne na
hudu irinsa da aka taba yi a
kan mata duk duniya, a birnin Beijing na kasar Sin.
Wannan taro an yi masa lakabi da " Taron
Beinjing" (Beinjing Conference), wanda shi a
shekarar 1995 aka gudanar da shi. Wannan taro ya
tattara mahalarta daga ko'ina cikin duniya, ya kuma yanke shawara a
kan sha'anin daidaita jinsi
na in-ba-ka-yi ba-ni wuri. Wato tun daga wannan
taro ne maganar daidaita jinsi take a bakin
kowa;'yan jarida ne ko masana ko manazarta ko
marubuta.
Kafin in ci gaba, na ga ya dace a san menene jinsi da kuma asalin ita
kanta matsalar a da, da kuma
yanzu a cikin al'ummomi daban-daban.
Jinsi kamar yadda aka sani shi ne bambancin da ke
tsakanin namiji da mace a halicce. Wanda kuma ya
shafi tsarin rayuwarsu ta zahiri da badini. Haka
kuma wadannan bambance-bambancen na canzawa da canjin zamani da rayuwar yau da
kullum, Graddol (1993) daga Kassam (1996).
Kodayake wasu masana suna ganin ma'anar jinsi
ba ta tsaya nan ba kawai, alal misali a ganin De
Beauvair (1973:301) "jinsi abu ne wanda mutum
ke iya zabar wa kansa". Ita a ganinta irin rayuwar da mutum ya zabar
wa kansa ita ce take nuna
jinsinsa, ba wai yadda aka halicce shi ba. Namiji na
iya daukar rayuwa irin ta mata, haka kuma mace na
iya zabar rayuwa irin ta maza, ko da kuwa al'umma
ta kyamaci wannan abu.
Haka su kuma Butler (1986.36)da Zimmerman (1991: 13-15) cewa suka yi
al'adu da dabi'un
mutum ko na al'ummarsa, su ne ke da alhakin
bayyana jinsinsa da kuma matsayinsa. Ita kuwa
Riley (1997; 2-6) tana ganin ma'anar jinsi ta wuce
bambanci halitta kawai, ta hada da bambace-
bambancen da ake samu ta bangaren abubuwan da al'umma ke shatawa a
al'adance a kan yadda ya
kamata mata ko maza su kasance. Haka kuma
wadannan ka'idojin sun shafi kowane bangare na
rayuwa, kamar yanayin zamantakewa na yau da
kullun da tattalin arziki da siyasa da neman ilmi da
makamantan su. Har wa yau kuma wadannan tsare-tsare na al'ada su ne
suke haifar da matsalar
daukakar wani jinsi a kan wani ko danniyar da ake
yi wa jinsin mata a cikin wata al'umma. Haka kuma
ana bayyana jinsi a matsayin tsare-tsaren al`umma
a kan da`bi`u da ayyuka da matsayin da ake ganin
ya dace da maza da wadanda suka fi dacewa da mata.
A fahimtata ana iya gwama wadannan ra'ayoyin na
masana a kan ma'anar "jinsi" a tayar da ma'ana
daya kamar haka, mai nufin bambancin halitta
tsakanin mace da maniji da kuma dukkan
sakamakon da wannan zai haifar ta fuskar rayuwar wadannan halitta guda
biyu a doron kasa ta fuskar
wadansu al'adu da ake shatawa ko gindayawa
domin a cimma wadansu manufofi na siyasa ko
zamantakewa.Bisa irin wannan tunani ne za mu
fahimci cewa wariya ko bambancin jinsi y hada
bambancin halitta da kuma bambancin rawar da kowane bangare zai taka
ta fuskar tattalin arziki ko
al'ada ko siyasa da dai duk wata fuska ta rayuwa.
Sai dai wannan bayani bai kasance an yi shi haka
nan sakayau ba, ya samu tubalin gina shi tun da
dadewa, kama daga addini ko siasa ko canjin
rayuwa ta yau da kullum. Saboda haka ya dace mu koma cikin tarihi
domin fahimtar yadda wannan
tunani ya ginu da kuma yadda ake daukar ko
kuma irin matsayin da ake ba wa jinsin mata cikin
al'ummomin daban-daban ta fuskoki daban-daban
.
MATA A ZAMANIN JAHILIYYA Bari mu koma cikin tarihi, mu kuma soma da nan
kusa, musamman wanda ya shafi addinin matan da
za mu yi nazari, wato Musulunci. Za mu ga tun a
zamanin jahiliyyar Larabawa8 ba a dauki mace a
bakin komai ba. Ana ganin an hallice ta kawai
domin ta yi wa maza hidima. Haka kuma ana iya sarrafa ta yadda aka ga
dama. Alal misali, zamanin
jahiliyyar Larabawa sun kasa halitta ga baki daya
zuwa gida uku, kaso na daya su ne mutane, kashi
na biyu kuwa su ba su kai matsayin mutane ba,
amma sun dara dabba, na uku kuwa su ne
dabbobi. Halittar da aka dauka ba ta kai mutum ba, amma ta fi dabba
ita ce mace. Saboda su a wurinsu
mata ba su da kima, ba su da wani zabi a rayuwa
sai yadda aka yi da su. Ana aurar da su yadda aka
ga dama ko kuma a saka su yin karuwanci ko aikin
wahala ba tare da an biya su lada ba. Har ma don
wulakanci gadonsu ake yi kamar dukiya. Wato idan mijin mace ya mutu,
idan yana da wani da
wanda ba nata ba sai ya gaje ta. A nan yana da
damar ya ajiye ta a matsayin matarsa ko baiwa ko
kuma ya sayar da ita. Haka kuma namiji yana da
damar ajiye mace ko nawa yake bukata ba tare da
wata ka'ida ba, saboda irin wulakanci da kaskanci da suka lika wa
mata, har ya kai suna binne
'ya'yansu mata masu rai tun suna jarirai idan ba su
bukata.
A tsohuwar daular Indiya kuwa a al'adar Hindu, an
dauki cewa namiji shi ne ubangijin matarsa (abin
bautarta). Idan ya mutu a tare za a kone gawarsu, alhali tana da rai.
Haka kuma har yanzu mata
mabiya addinin Hindu suna shiga halin kaka- ni-
kayi, idan mazansu sun mutu, sun bar su, domin
ana yi musu kallon "gawa", wato sun mace a
duniya, ba su da sauran jin dadin duniya. Mata da
suka shiga cikin irin wannan yanayi ba su kwalliya, ba su ma ko cin
abinci, mai kyau, ko mai dadi, sai
wanda aka zabar musu. Ba a hulda da su balle a
aure su. Sai dai dangin mijin maza su dinga yi musu
fyade (shige), idan suka ki ba su hadin kai sai a
kore su daga gidan. A halin yanzu mafi yawansu
suna gudun hijira zuwa wuraren ibada irin nasu, inda a can kadai suke
samu dan sauki. Haka kuma
a wancan lokaci a kasar Hindu akan yi matar iyali
wato idan da namiji goma ko kusa da haka a gida,
sai su dauko mace daya a matsayin matarsu su
duka.
Irin wannan ko makamancin haka ya faru a kasar Girkawa, inda aka dauki
mace tamkar dabba. Ana
iya kama ta a yanka kamar yadda ake yanka dabba
duk lokacin aka ga dama a matsayin horo. Misali
idan mace ta kuskura ta haihu ba a lokacin da ya
kamata ta haihu ba, ko ta rinka haihuwar 'ya'ya
mata zalla, to za a yanka ta. Idan kuwa ta rinka haihuwar 'ya'ya maza
kawai, to sai a rinka daukar
ta ana kai wa baye ga shahararrun baraden kasar,
kamar yadda ake kai dabba, wai don ta haihu
'ya'ya su biyo baraden a sami zaruman da za su
rinka yi wa kasa yaki.
A kasar Sin kuwa mace ita ce kasa da kowa wajen daraja, ko wajen cin
abinci ba a ba mata, sai an
tabbatar maza sun koshi. Haka ma waje bada
magani, amma kuma matan ne aka fi tura wa wajen
neman abinci.
A nahiyar Afrika ma haka lamarin ya kasance,
domin a nan ma maza ke jan ragamar al'umma a cikin kowane irin lamari.
Mace kuwa ba ta ma san
kanta ba balle ta sami bakin fada a ji cikin al'umma.
An dauki mata tamkar shanu, sai dai a debe su
zuwa gona ko nemo itace. Saboda raunin da ake
gani ga mata a kasar shi ya sa tun kafin su karbi
kowane addini suna da al'adar aure, wanda suke yi domin mace ta sami
galihu irin na maza wanda ake
ganin idan ba shi, tana iya fadawa cikin garari. Sai
dai wannan galihun da namiji ke ba mace yana da
tsada. Domin kuwa duk ita take aikin wahala,
kamar zuwa gona, nemo itace, dafa abinci, kula da
yara da dabbobi da kuma ayyukan gayya. A kasar Hausa da alama ba ta
canza zane ba, haka
aka dauki mata, har wata karin magana Hausawa
ke yi wanda suke cewa wai "namiji dutse, mace
sakaina", wannan maganar ta kara tabbatar da
matsalar jinsi kamar yadda Babba (1986) ta
bayyana. Kuma wannan ne ya kara dakushe armashin da ake ganin matan
Hausawa na da shi,
domin su ma kan su sun dauka cewa ba su iya yin
komi sai yadda jinsin ya tanada. Irin wannan
tunanin shi ya ne ya jawo koma bayan mata a cikin
al'ummar Hausawa. Haka kuma wannan ne ya sa
Hausawa suka fi kwadayin haihuwa 'ya'ya maza bisa ga mata. Har ya kai
ma aure na iya mutuwa
idan mace ba ta haihuwar 'ya'ya maza, wai babu
magaji.
Ko a addinin da suka yi tashe a duniya an sama irn
wannan tunani. Addinin Kirista na daya daga cikin
su. Domin kuwa a bisa tsarin addinin da kuma littafin da suke bi, cewa
ya yi mace ita ce uwar
zunubi, wadda ta yi dalilin fitar Annabi Adam daga
aljanna. Haka kuwa wannan addinin (na Kirista) ya
hana wa mace 'yanci kai da zarar ta yi aure, ba a
kiranta da sunanta ballantana na mahaifinta sai dai
na miji. A wani taro na Kiristoci da aka taba yi a shekarar 1856 domin
a gano mace 'yar Adam ce
ko dabba, bayan an tattauna sosai an yarda cewa
mace 'yar Adam ce, amma wadda aka halitta domin
ta bauta wa namiji. Haka kuma an sake yin wani
taro a zamanin Daular Romawa domin a gane ko
mace na da ruhi kuma ana iya sanar da ita addini. Haka dai al'amarin
mata ya kasance a mafi yawan
al'ummomin duniya, kafin zuwan addinin
Musulunci. Kuma addinin Musulunci shi ne ya
kwato wa mace "yancinta kamar yadda za mu gani
nan gaba.
MATA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI Addinin musulunci ya 'yantar da mata daga
kukumin da dan Adam ya sa musu tun shekaru
aru-aru da suka gabata. Addinin ne ya ba mata
dama da matsayin daidai da na maza a cikin mafi
yawan al'amurra. Misali a cikin Alkur'ani mai tsarki,
Allah (S.W.T) yana cewa: "Mun halicci mutane daga namiji da mace".(Hujrat
:13)
A wata sura kuma ya ce:
"Wanda ya yi kyakkyawan aiki namji ko mace alhali
shi yana mumuni, to lalle za mu raya shi rayuwa mai
tsarki, kuma za mu saka musu ladarsu da mafi kyau abin da suka kasance
suna aikatawa" (Nahl : 97)
Da kuma inda ya ce:
"Domin Allah ya azabantar da munafukai maza, da
munafikai mata, da mushirikai maza da mushirikai
mata. Ya kuma karbi tubar muminai maza da
muminai mata. Allah kuwa ya kasance mai gafara ne, mai jin kai"(Al-ahzab:73).
Duk wadannan ayoyin suna nuna cewa ubangiji da
kansa bai bambanta mace da namiji ba, domin duk
inda ya ambaci maza sai ya ambaci mata. Haka
kuma a wajen sakayya yana saka wa kowa da abin
da ya aikata ba wani bambanci. Haka kuma Musulunci ya ba mace wasu hakkoki da
aka danne a sakamakon al'adu da kuma zalunci
irin wanda aka saba wa mata tun a zamanin
jahiliyya. Misali a can da mace ba ta da iko a kan
abin da ta mallaka sai dai mijinta. Haka kuma ba ta
gado sai dai a gaje ta, ita kashin kanta da abin da ta mallaka, amma
Allah (S.W.T) ya ce:
"Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfata
(abin da suka nema domin amfanin kan su). Mata
ma suna da rabo daga abin da suka tsirfata.":32).
Game da gado kuma ayar farko da Allah (S.W.T) ya
fara saukarwa cewa ya yi: "Maza suna da rabo daga abin da iyaye biyu da
makusanta dangi suka bari, kuma mata suna da
rabo daga abin da ya karanta daga gare shi ko
kuwa ya yi yawa, a rabo yankakke."(4: 7).
Wannan ayar ta nuna muna cewa mace tana da
hakki gadon iyayenta da mijinta da 'ya'yanta da kuma 'yan uwan
haihuwarta, idan ba su haihu ba.
Bayan wannan kuma Musulunci ya ceto rayuwar
mace, ya ba ta damar rayuwa cikin al'umma tamkar
namiji, domin ya hana a bizne ta da rai. Inda Allah
(S.W.T) ke cewa:
"Kuma idan aka yi wa dayansu albishir da ('ya) mace sai fuskarsa ta yi
murtuk yana cike da
tsananin bakin ciki. Ya buya daga (idon) mutane
saboda mummunan abin da aka yi masa albishir da
shi. Shin zai riki ne a wulakance ko kuma zai binne
shi ne a cikin kasa, Na'am abin da suka hukunta
kam ya munana."(Nahl 58:59). Bagu da kari kuma addinin Musulunci ya ba mace
damar neman ilmi kamar yadda ya ba namiji. Akwai
hadisin Manzo (S.A.W) da ke cewa:
"Neman ilmi wajibi ne a kan kowane musulmi da
musulma. (Bukhari).
Mace ita ce kashin bayan al'umma, idan ta gyaru to al'ummar ta gyaru,
idan kuma ta lalace to al'ummar
za ta lalace."(Hadisi Nisa'i).
Haka kuma, Annabi (S.A.W) ya ce,
"Idan ka ilmantar da mace daya tamkar ka ilmantar
da al'umma ne ga baki daya". (Bukhari)
A nan mun ga Musulunci ya karfafa ilmin mata fiye da na maza domin
ganin cewa mace ita ke kula da
tarbiyar yaro, idan ba ta samu ilmi ba, ba za ta iya
tarbiyartar da 'ya'yanta ba balle su girma su gina
al'umma ta gari.
MATA A WANNAN ZAMANI
Da yake mun ga yadda ake kallon mata a wasu nahiyoyi tun a zamanin
jahiliyya da sauran lokuttan
da suka shige da kuma ceton da Musulunci ya yi wa
mata. Sai kuma mu leka yadda ake kallon su cikin
wannan zamani, musamman daga karni na sha-
tara zuwa na ashirin da daya. Daga abin da wannan
binciken ya samo dangane da matsalolin mata da yadda ake kallon su, a
iya cewa har yau da sauran
rina a kaba. Har yanzu al'adar nan ta daukar mata a
matsayin 'yan baya ga dangi tana nan sake cikin
zukatan al`umma duk kuwa da juyin da Musulunci
ya kawo da kuma canjin zamani. Domin ko a
kasashen Turai masu ikirarin ci gaba da wayewar kai, inda kuma ake ta
hayaniya kan 'yancin mata
har yanzu matsayin mace na mai rauni akan
kowane sha'ani, yana nan. Mata suna fuskantar
matsaloli da dama ta bangaren ilmi da siyasa da
fasaha da aure da aikin gwamnati da sauran su, a
ko'ina cikin duniya. Alal misali idan muka dauki bangaren ilmi wanda
shi ne mabudin arziki na
duniya da lahira, ta hanyarsa ne mutum ke fita
duhun jahilci, ya san addini da sauran al'amurran
rayuwar duniya. Da ilmi ne mutum ke iya samun
babban matsayi a cikin aikin gwamnati. Haka kuma
da ilmi mace za ta san kanta, har ta sami damar bada gudummawa a cikin
al'umma. Amma a mafi
yawan kasashe, musamman masu tasowa, mata ne
a baya, wajen samun ilmi. Misali a wata kididdigar
yawan jama'a da aka gabatar, an gano cewa a
kasashe Sin da Bangaladash yawan mazan da ke
da ilmi ya ribanya na mata sau uku. A Afirka kuwa matan da ke da ilmi
kalilan ne, kuma mafi yawanci
ilmin nasu ba mai zurfi ne ba33, Umar (1990).
A wata kididdiga ta "UNESCO" a shekarar 2000
yawan matan da ke cikin jahilci sai kara hauhawa
yake yi. Mangwat da Abama (1999) sun nuna cewa
a shekarar 1958 yawan mata marasa ilmi ya kai kashi hamsin da takwas
bisa dari, sai kuma kara
hauhawa da ya yi ta yadda a shekarar 1985 inda
yawan mata marasa ilmi ya kai miliyan 133. Har wa
yau wata kididdiga ta "UNESCO" ta karshen karni na
ashirin ta nuna cewa daga cikin yaran da suka
shiga makaranta a Nijeriya, kashi talatin da uku ne mata, sauran duk
maza ne. Saboda matan ko da
sun shiga akan janye su daga baya, saboda wasu
dalilai da masana da manazarta suka sha
bayyanawa.
A Arewacin Nijeriya ma tun kafin da bayan zuwan
turawan mulkin mallaka an maida mata baya a fagen ilmi. Domin ko da
Turawa suka ci Sakkwato
da yaki suka kwace mulki da karfi sun sami mata
masu ilmi da yawa wadanda suka gaji su Nana
Asma'u da 'yanuwanta da kuma takwarorinta,
wadanda suka yi ilmin addinin musulunci, suka
kuma yi rubuce-rubuce cikin harsunan Larabci, Fulfulde da kuma Hausa
don fadakar da al'umma,
ciki har da rubutatatun wakoki. Amma sai Turawa
suka yi biris da sha'anin ilmin mata har sai bayan
lokaci mai tsawo, a farkon karni na 20 da suka
bude makarantar maza a Kano ba su bude ta mata
irinta ba sai a shekarar 1933. Haka kuma Mulkin mallaka ya raunanar da
makarantun allo da ya iske.
Wannan ba karamin ci baya ya janyo wa Arewa ba
domi mata su ne asasin gyaran al'umma da son ci
gaba da samun ilmin addini kamar yadda aka
dauko a karni na 19. Da an yi hakan da alam aka
ba su ilmin zamani a lokacin da ya dace su same shi da Arewa ba ta
tsinci kanta a sahun 'yan baya ga
dangi ba a fagen ilmi da ci gaban al'umma. Daga
baya da aka sami makarantu don mata kuwa sai
aka yi rashin sa'a da cewa mutane na dari-dari da
ilmin boko, saboda addini da akidun wadanda
suka kawo shi. Dangane da wanna ga abin da Babba (1986) ke cewa :
iyaye na hana yaransu
mata karatu, domin kada su rasa miji. Saboda
al'umma, musamman ta Hausawa sun dauki cewa
boko ke sa yarinya ta hinjire wa mijin, saboda za ta
dauki kanta tana da wani matsayi cikin al'umma
tun da tana da ilmi, alhali kuwa a zahiri ba haka abin yake ba. Domin
mata da suka yi ilmi, su ne za a
same su masu tsabta da sanin ya kamata. Ga sanin
addini da kuma iya biyayya ga miji, ta hanyar kula
da shi da 'ya'yansa da kuma kayansa.
Haka kuma Congleton (1988) a cikin wata hira da
aka yi da shi, ya yi bayanin cewa, mutanen Arewacin Nijeria sun fi ba
wa tarbiyar da yaro ke
samu a gida muhimmanci a kan wadda za a ba shi a
makaranta. Har suna ganin cewa ana gurbata wa
yaransu, musamman mata tarbiya idan suka bar su
suka yi zurfi a cikin makaranta. Wanda kuma a dalili
haka maza ba su cika son su auri mata masu ilmi sosai ba. Babban
dalili kuwa bai wuce na akidar
nan ta cewa mace ta bi miji sau da kafa, ko da kuwa
yin haka din zai jawo mata cikas a rayuwarta. Suna
ganin cewa mace mai ilmi ta san hakkinta a kan miji
da kuma san hakkin miji a kan ta, ba za ta yarda a
tauye ta ba a cikin gida kamar dabba, ba kulawa ba wani abin yi.
Azare (2000) cewa ya yi babban dalili da ke sa ana
hana ko janye mata daga makaranta, shi ne rashin
isasshen kudin da za a dauki dawainiyar karatun
duka 'yaya, maza da mata ga baki daya, kuma
gudun lalacewar tarbiyarsu, wadda al'adar al'ummarsu ta tanadar musu.
Amma kuma sai abin
ya zan "an ki cin biri, an ci dila", domin sai a hana su
makaranta amma a tura su wajen kwadago ko
tallace-tallace, inda suke shiga cikin hadurra kala-
kala, kamar yin cikin shege ko kamuwa da cutar
kanjamau . Idan muka dubi matsalar ta fuskar siyasa kuma za
mu ga cewa a wannan fagen maza ne suka yi
kaka-gida, domin a yawanci kasashen duniya ba a
ba mata damar da ta kamance su a sha'anin siyasa
ballantana a ce su kai ga taka rawar gani a cikin
sha'anin mulki, Ashford (1995:17) ta yi bayanin cewa ana dai babatun
dimokuradiyya ne a baki
kawai, amma ayyanawar ba haka take ba. Da kyar
ne mace take kai ga shiga takarar mukamin siyasa.
Idan kuma ta samu shiga din, za ta fuskanci
tarnakin al'ada, wanda ke iya hana al'umma ta zabe
ta. Saboda idan aka dubi siyasar duniya a yau, mata irin su Margaret
Thacher ta Ingila, da Indira Ghandi
ta Indiya, da Komaratonga ta Sirilanka, da Benezir
Bhuto a Pakistan da wasu kalilan kadai ne
wadanda suka taba samun nasarar zama
zababbun shugabanin kasashe, wanda yake idan
aka kwatanta su da maza da suka taba shugabanci ba su kai ko kashi
biyar bisa dari ba. Haka kuma a
mafi yawan kasashe masu tasowa, musamman irin
su Mexico da Brazil da yawancin na nahiyar Afrika,
kujerin da ake ba mata a majilisar dokokin kasa ba
su taka kara sun karya ba. Har ma a kasashen da
suka ci gaba idan aka kwatanta maza da ke rike da mukamin siyasa da na
mata, za a sami bambanci
mai yawan gaske. A Arewanci Najeriya abin ma ya
fi muni, domin al'umma sun dauki cewa mata
karuwai kawai ke yin siyasa.
A lokacin da muka dubi matsalar shugabanci sai a
ga cewa a cikin matan da suka yi ilmi, kalilan ne ke samun yin aikin
gwamnati. Wadanda kuma suka
sami aikin, sukan fuskanci matsaloli ta fuskoki da
yawa. A kasashen duniya da yawa, har da
wadanda suka ci gaba, a kan nuna wa mata
bambanci ta fuskar matsayi ko makami da awoyin
aiki. Haka kuma akan nuna musu bambanci wajen biyan ladar aiki. A
kasar Amurka ga misali, Riley
(1997) ta yi bayanin akan tauye 'yancin mata ta
fuskar mayar da su saniyar ware a fagen siyasa. Ta
kai ga har shata wani tsari aka yi wanda yake
tabbatar da cewa matan da suke aikin gwamnati
ko na manyan kamfuna ba su rika manyan mukamai ba, wanda ya sa
bambanci tsakanin mata
da maza ya dade kafin a kawar da shi a kasar. Ta
kara da cewa ta kai ma ga albashin namiji ya fi na
mace yawa ko da kuwa aikinsu iri daya ne.
Wannan bambancin kuma ya kasance har a
kasashen Ingila da Kanada da kuma Siriya. Wannan akidar ba a can kadai
ta tsaya ba, ko a nahiyar
Afrika da kasar Nijeriya, har ma Arewa, mata sun
kasance a matsayin saniyar ware a fagen siyasa,
domin matan Arewa ba su fara ko jefa kuri`a ba sai
1976, ballantana su shiga takara a zabe su,
Dityavyar(1998;145). Matan da ke aiki ma ana yi musu kallon wasu
tsiraru ne, wadanda suka fi
karfin mazajensu a cikin al'umma. A wajen aikin
kuwa akwai mukaman da ake ganin cewa mata ba
su isa su rika su ba sai dai maza.
A fagen tattalin arziki mata na bakin kokarinsu,
domin kamar yadda Osunde and Imorayi (1999) suka bayyana, mata na yin
ayyuka da dama
wadanda ke taimaka wa wajen habaka arzikin
al'umma. Inda suka bada misalin cewa, mata na
noma, kiwo da kuma sana'oin hannu irin su saka,
har ma da fatauci, suna kuma yin ayyukan gayya.
Ita ma Riley (1997) ta yi bayani cewa A kasar Sin 'ya'ya mata ne ake
turawa gona ko wajen ga aiki,
domin su nemo wa iyaye da sauran 'yan uwansa
da suka hada da maza abin masarufi. Haka kuma
sanannen abu ne cewa a kasar Indiya mace ke
neman kudin biyan sadakin aurenta. A nahiyar
Afrika, har a arewacin Nijeriya mata na kokarin neman na kai. Inda
suke yin duk abubuwan da
aka ambata a sama, har ma da kari, domin sukan yi
`yan sana`oin hannu, suna dora wa 'yayansu
tallace-tallace, su kuma suna can suna yin wasu
sana'a wadanda suka hada har da kitso, dinki, da
sayar da abinci a wurare daban-daban. Mack (1992) ta yi bayanin har da
cinikin bayi matan
kasar Hausa suna yi a zamani da ake yin sa. Amma
abin mamaki shi ne duk da wannan gagarumar
gudumawar da mata ke bayarwa ta fannin tattalin
arziki, al'umma na ci gaba da yi musu kallon cima-
kwance wadanda komi sai an nemo an ba su. A yanayin zamantakewa na yau
da kullum, mata su
ne kashin bayan zaman lafiya da mu'amala mai
kyau cikin al'umma. Domin su ne aka fi sani da
kokarin sada zumunta da hulda da makwabta da
tarbiyar yara da kuma yin 'yan sana'o'in hannu,
masu taimakawa wajen gudanar da rayuwa cikin sauki. Haka kuma tarihi
ya nuna mata suna da
tausayi da kokari wajen kula da marasa lafiya,
musamman a zamanin da ake yawan yake-yake.
Ko a nan kusa lokacin jihadin su Shehu Usman
Danfodiyo, Boyd (1989) ta yi bayani akan irin
gudumawar da su Nana Asma'u da sauran matan zamaninta suka bayar, ta
hanyar kula da wadanda
aka ji wa rauni da kuma bada abinci da daukar
kaya da kula da yara lokacin yaki. A wannan
zamani da ake ciki mata na gudanar da kusan duk
abin da maza ke yi a kowane bangare na rayuwa
idan dai an ba su dama. A harkar aure mata suna samun matsaloli a ko ina
ciki duniya. Sai dai bayanin da zan yi a nan shi ne a
kan matan arewacin Najeriya, inda har yanzu a kan
yi wa yarinya aure ba tare da an nemi yardar ta ba,
kuma a nemi ta zauna da mijin nan bisa ga ladabi
da biyayya ko da kuwa ba ta son sa. A wani bayani na Callway and
Greevey (1994:84) cewa suka yi:
"A kasar Hausa ana yi wa yarinya auren wuri, kuma
zaba mata mijin ake yi (ba tare da yardarta ba)
kuma dole ta zauna da shi, ta bi shi sau da kafa, ta
kuma zauna tare da kishiyoyi, ko tana so, ko ba ta
so". Wannan auren da ake yi musu, na wuri yakan jawo
musu matsaloli iri-iri, musamman idan suka yi
saurin daukar ciki idan an zo wurin haihuwa, mafi
yawa yaran da ba su yi kwarin haihuwa ba, sukan
sami matsalar yoyon fitsari. Inda kuma daga
karshen mazan ke juya musu baya, sai dai iyayensu su yi ta wahala da
su. Wannan kuma ba a kasar
Hausa kawai yake faruwa ba, yana faruwa a
yawanci kasashe masu tasowa. Misali a kasar
Somaliya, musamman sai da wata baturiya ta kafa
asibitin taimakon irin wadannan mata da ke samun
matsalar yankan gishiri, kuma al'umma ta juya musu baya48.
MATA DA ADABIN BAKA
Shahararrun masana da yawa wadanda suka yi
rubuce-rubuce a tarihi da al'adun kasar Hausa,
kamar Clapperton da Lander (1829), da Jeroma
(1970,1972,1973), da Joseph (1973), da Palmer (1978) da Mark (1985) da
Boyd (1989) da Hill
(1972), da sauransu, duk sun yi bayanin cewa
kafin zuwan baki a kasar Hausa, matan Hausawa
sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen
ciyar da kasar da al'ummarsu gaba. Irin wannan
rawa tasu ta shafi bangaren tattalin arziki da siyasa, tarbiya da
fasaha da kuma ciyar da harshen Hausa
gaba, ta hanyar tatsuniyoyi da labarai da kacici-
kacici da karin magana da salon magana da badda-
bami da sauran su. Wadannan suna cikin
abubuwan da Fafunwa (1982) ya kira makarantun
farko na 'yan Afirika kafin su sami ilmin karatu da rubutu. Amma kuma
idan aka tashi bayani game da
irin wannan ci gaba sai ya zan gudummuwar maza
kadai ke fice.
Haka dai al'amarin mata ya kasance rayuwarsu na
cikin tawaya da rashin walwala wanda ba kome ya
hassada masu shi ba sai al'adu, wadanda ke ci da yawun addinai da
siyasa domin biyan bukatun
wani jinsin da ba mace ba. Wadanna al'adun sun yi
tasiri sosai cikin al'ummomi musamman a nahiyar
Afirika yadda har su ma matan an dasa wannan
akida ta namiji dutse, mace sakaina, har ya zan ba
su iya kalubalantar matsalolin da ke tattare da su, Remi(2003). Sai a
'yan shekarun baya –bayan nan
da aka sami mata kalilian masu matsawa, suka
tunkari wannan matsalar ta danniyar jinsin mata, ta
hanyoyi daban –daban.
MATA DA RUBUTACCEN ADABIN HAUSA
Daga abin da muka ga a sama mun fahimci abubuwa da dama. Da farko dai
matsalar nazari da
sharhi game da mata ba ta wuce irin mizanin da aka
dora batun ba, ko a adinance ko siyasance ko
kuma tafuskar ilmi da zamantakewa. Na biyu kuwa
shi ne duk da cewa an yarda mata na taka rawa a
gnuwar rayuwa ta kowace irin fuska, da alama akwai wadansu katangai da
ake jefawa a gabansu
domin kada su kai ga gaci.Na uku ga alama, yadda
ake kallon mata a kowane fage da irin rawar da
suke takawa da matsalolin da suke fuskanta su ne
suka yi katutu ko da a fagen nazarin ayyukan
adabin Hausawa. An fadi haka ne ganin cewa mata kamar
takwarorinsu maza su ma sun samu ilmin karatu da
rubutu bayan zuwan addinin Musulunci. Amma
duk da cewa Musulunci ya wajabta neman ilmi,
musamman na addini a kan kowane musulmi,
namiji ko mace, tarihi ya nuna cewa a kasar Hausa al'umma ta yi watsi
da sha'anin ilmin mata, wanda
shi ne ya haifar da barin mata cikin jahilci. Wannan
ya sa mata suka kasance tamkar dabbobi cikin
duhun jahilci. Abin da al'umma ta tanadar musu shi
ne aikin zaman gida. Da yake kuma rubutaccen
adabi ba ya samuwa sai da karatu da rubutu, dole rawar mata a wannan
fage ta takaita.
Rawa ba ta canza ba sosai, sai lokacin jihadin su
Shehu Danfodiyo da magoya bayansa, a karni na
19, Inda Shehu ya lura da wannan matsalar ya
kuma tashi tsaye domin kawar da ita. Ga abin da
Shehu ke cewa game da matan kasar Hausa a wancan lokaci:
Maza sun dauki matansu tamkar wasu rubabbun
kayan gida, wadanda aka gama amfani da su, sai
yar a shara. Kash wannan hali ya saba wa ka'ida.
Yaya za su bar su cikin duhun kai, bayan ga shi
kuwa suna ba dalibansu sani a waje." Shehu ya ci gaba da cewa fadar
nan ta Hausawa
mai cewa "aljannar mace tana karkashin kafafun
mijinta", ba ta da wani tasiri sai idan mace ta bauta
wa Allah yadda ya kamata. Bauta wa Allah ba ta
inganta sai da ilmin addinin Musulunci.
Wannan ne ya malamai da magidanta da 'yan uwan Shehu da kuma `ya`yansu
duk sun karbi kiran da
ya yi. Nan da nan sai makarantu suka budu a
gidajen mutanen da sassa a can cikin gidaje wurin
mata. Mafi yawan matan malamai suka zama
malamai su kansu. Alal misali matan Shehu da
'yanyansa da sarakunansa, kamar su Hadiza, Asma'u, 'yayan Shehu da
A'ishatu matar Aliyu Jedo,
da Maryam da Fatima, matan Sarkin Musulmi Bello
da Maryam 'Yar Shehu duk sun bude azuzuwan
karatun allo a cikin gidajen mazansu. Idan an
manta da rawar da wadannan suka taka to da kyar
ne za mu manta da rawar da Nana Asma'u ta taka. Dubi Boyd (1989),
wadda ta kawo bayanin `yan
taru, wadanda suka samo asali daga shirin ba mata
ilmi na Nana Asma'u. Haka kuma duk wadannan
mata sun yi rubuce-rubuce da suka hada har da
wakoki. A kan abubuwan da suka shafi rayuwar
al'umma dangane da addinin musulunci, Boyd (1989) ta yi bayanin cewa
Nana Asma'u kadai ta
rubuta wakoki da dama, amma kuma duk
wadannan ayyukan da mata suka yi, saboda su
mata ne, sai wannan ya kasance musu tarnaki
wajen yin fice da kuma samun shiga cikin
mashahuran marubuta. Ko Nana Asma'u idan ba domin bincike-binciken
Boyd da wasu ba da har
yanzu mutane da dama ba san irin gudumawar da
ta bayar ba. Domin ita Boyd ce ta yi kokarin binciko
wadannan ayyukan ta kuma buga cikin littattafai
da mujallu daban-daban. Amma kuma har yanzu
mutane kalilan ne a cikin wannan al`umma suka san ayyukanta. Wannan
dabi'ar ta rashin ba aiki
mata muhimmaci ba wai a ciki al'ummar Hausawa
kadai take ba, har ma da sauran al'ummomin
duniya. Misali kasar Ingila, tun a shekarar 1866
wata marubuciya mai suna Anne Evans ta yi rubutu
a kan matsalar mata, ta ce 'mace ba ta da zabi… sai dai ta dogara ga
duk abin da ta samu ko ya same
ta. Ta kuma tsaya iya dan matsayinta". Babban abin
takaici a nan shi ne ita wannan mata sai da ta lika
wa kanta sunan namiji wato "George Elliant' kafin
rubutunta ya sami karbuwa ga al'umma. Haka
kuma idan muka koma ga tarihi, za mu ga cewa daga cikin shahararrun
marubuta da suka yi suna a
duniya, wadanda aka yi ta nazarce-nazarce a kan
ayyukansu, da kyar ne idan za a sami mace. Misali
mun ga an yayata su Plato da Aristottle da
Shakesphere da Milton da Chaucer da Samuel
Johnson da T.S. Elliot da sauran su. Amma ba a damu da shahararrun
marubuta mata ba irin su
Austen da Broute, Woolf da Hurston da sauran su a
duniyar Turai da Amurka, ba domin komi ba sai
don suna mata.
Idan har hakan ya kasance dangane da su Nana
Asma'u da dangoginta a zamanin masu jihadi, ba abin mamaki ba ne idan
ba a ba mabiyansu wani
muhimmanci ba, duk kuwa da cewa an samar da
mata mashahurai da suka tashe a wannan fage.
Faga cikin irin wadannann an ci gaba da samun
mata da suka ci gaba da yin rubuce-rubuce cikin
Hausa da sauran harsunan Arewacin Nijeriya,musamman a fannin rubutattun wakoki
domin su ne suka fi saukin hardacewa ga matan da
ke daukar karatu da kuma dadin saurare ga
sauran jama'a. Amma saboda matsalar wariyar jinsi
da tarnakin al'adu wanda ya tauye mata ga samun
shawarwari daga kwararru game da rubuce- rubucen da kuma gudun
korafe-korafe a cikin
al'umma, sai aka kara samun dakushe aikace-
aikacen mata na rubutaccen adabin Hausa. Idan
kuma aka dubi bangaren maza ba haka abin yake
ba.
A halin yanzu ambaton Akilu Aliyu da Aliyu Namangi ko Abubakar Imam ko
Yusufu Kantu ko
Alkali Haliru Wurno ko Bello Kagara da dimbin
mazan da suka yi rubuce-rubucen cikin adabin
Hausa a shekarun baya, sai ka taras an san su. To
amma matan fa? Kodayake akwai su ba a ba su
damar fitowa su yayata kansu ba, ba a kuma taimaka aka yayata su ba.
Ko 'yan wadanda suka yi
fice, ba da yawun bakin maza suka yi shi ba. Domin
mata ne 'yan uwansu, suka yi kokarin da suka fito
da su. Wato mata irin su Baturiya Beverly Mark da ta
yi kokarin buga littafin "Alkalami a Hannun
Mata" (1983),wanda yake dauke da rubutattun wakoki na wasu mata a
Kano, wato Hajiya Hauwa
Gwaram da Hajiya 'Yar Shehu. Sai kuma Gambo U.
Babba, wadda ta rubuta kundin digirin farko a
Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, a kan wata malama
marubuciya a1986, wato Hajiya Hasana Sufi, sauran
matan da aka ji sunansu kuwa, su ne suka yi kokarin rubuta labaransu,
suka kuma buga abin su
da kan su. Wato irin Hafsat Abdulwaheed (1980)
da Yaya Hasana Umar (1980) da kuma marubutan
zamani, wato irin su Bilkisu Funtuwa da Balaraba
Ramat da Zuwaira Isah da sauran su. Inda kila za a
ga wannan aiki ya kankama shi ne littafin Ibrahim Yaro Yahaya
(1988),wato Hausa a Rubuce, shi ma
rubuce-rubucen maza ya fi yawa, kila saboda
rubuce-rubucen mazan ne ya fi yawa, ga abin da
yake cewa game da wannan batu:
Mata su ma ba a bar su a baya ba wajen ciyar da ilmi
gaba ta yin rubuce-rubuce da ajami ko boko, a buga a littattafai.
Harsashin da nana Asma'u 'yar
Shehu da Maryama 'yar Shehu suka aza a kan ilmin
mata ya samu kafuwa sosai, har ma ana ta dora gini
a kansa tun daga wancan karni har zuwa wannan
zamani namu, domin ana samun mata a ko'ina a
kasar Hausa suna neman ilmi a makarantun allo da na Islamiyya da ilmin
zamani ma. Wasu daga
cikinsu in an yi musu aure, suna gudanar da
azuzuwan koyarwa a gidajen mazajensu.
Akwai mata da dama irin wadanda Yahaya (1988)
ya ambata, wadanda suka nemi ilmi har suka zama
malamai, kuma marubuta cikin ajami da boko. Haka kuma rubuce-rubucen
nasu sun tabo fannoni da
dama, sai dai saboda kasancewar mafi yawansa
matan aure ne ko kuma 'yan matan da ke
karkashin kulawar iyayensu ba su da damar zuwa
wasu wurare don nuna fasaharsu, kamar yadda
maza ke samun yi, ya sa ba a san da zaman mafi yawansu ba, wannan
matsalar ta fi shafuwar
marubuta wakoki, kila shi ya sa mazan suka fi
tashe fiye da matan. Lallai akwai marubuta mata
kamar yadda aka sha fada, amma ga nawa tunanin
ba wai fadar cewa akwai matan ne kawai da ke
rubuce-rubucen ajami ke da muhimmanci ba, a'a, a ga ayyukan nasu a
zahiri. Wannan shi ne kashin
bayan wannan tunani, a nemo matan marubuta
wakoki da kagaggun labarai da kuma wasan
kwaikwayo, domin kafa hujja ta fasalce-fasalcen
ayyukan adabi na mata a kasar Hausa. Ta haka ne
za a ga irin rawar da suka ko suke ko za su bayarwa a raya kasa da al'umma.

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

MARUBUTA MATA: JIYA DA YAU

No comments:

Post a Comment