Na fara son Alhaji Shata da waqoqinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Sa'ilin ban wuce shekaru 6 da haihuwa ba. Tun lokacin son da na ke ma Mamman Shata na musamman ne. Tun iyaye na ba su fahimta har su ka gane. Ko a Telebijin aka nuno shi ya na waqa na kama murna kenan, da zaran kuma an xauke wuta kafin ya ida waqar, to har kuka na ke yi kuma na dinga fushi kenan har safe.
Ni babana ba ya da wata alaqa da Shata, amma ganin ina son sa ya kan zaunar da ni ya bani labarin sa, na zuwan da ya ke yi a RTK Kaduna (watau BCNN da kuma daga bisani NBC) a tsakanin 1969 da 1972 lokacin mahaifin nawu na aiki a can, da kuma ziyarar da ya kan kai ma amininsa Alhaji Hamza Qanqara har Musawa lokacin ya na aiki a gonar mahaifin Shata Malam Ibrahim Yaro.
Sai cikin 1975, watarana da babana za ya tafi Katsina, ya ce in shirya in bishi tunda a sannan ban shiga firamare ba, a sa'annan ya na da wata mota Morris Marina. Ba zan manta ba mun shiga Funtuwa a tsakanin mangariba da isha'I, har mu ka bi santar gidan Shata. A daidai qofar gidan Shatan mun zo wucewa sai babana ya ce da ni: 'Ali Gadanga, ga gidan Shata, ga shi can ma zaune qofar gida'. Ya faxi mani hakane saboda sanin da ya yi ina matuqar son makaxin. Sai na ce masa 'mu tsaya in gan shi' Sai ya ce : 'a'a, saboda mu na sauri'. Amma gab da za mu wuce Allah Ya jiye mani muryar Shatan, na ji ya na cewa 'a zo a kwashe kwanonin abincin nan'. Wannan kenan.
A tsakanin 1976 da 1978 an kai ni riqo Daura wajen wana Ahmed Ibrahim Qanqara, lokacin ya na aiki a can. To a can mu kan ga wasan Shata a qofar fada in ya ziyarci Sarki, da kuma Neja Club da ke kan hanyar Zangon Daura. Har ma nine Shatan Islamiyya Firamare inda na yi karatu. Idan an gama shara da marece, sai a zo bakin ofishin Hedimasta a yi wasan kwaikwayo, to nan ni kan xan yi waqoqin Shata 'yan ajinmu na yi mani amshi. Sunan Hedimasta xin mu Hamisu Famili, wanda daga baya ya zama Matawallen Daura.
Cikin 1979 ina aji 5 na Firamare a Qanqara (bayan babana ya bar Kaduna, mai riqo na kuma na bar Daura) sai Shata ya zo kamfe na GNPP a cikin tawagar 'yan siyasa a Qanqara, nan mu ka yi ta bin motar sa da gudu aka zagaya gari da mu, shi kuma ya na waqa. Wannan ta sa wanshekare ni da abokina Garba (Abubakar) Suleiman Qanqara (yanzu yana aiki a Xakin Awon Jini na Asibitin Tarayya ta Katsina) mu ka sawo littafi mai warqa 40 mu ka fara rubuta tarihinsa, har ma mu ka samu shuwagabannin GNPP na yankin Qanqara su ka bamu abinda su ka sani gameda makaxin. Amma a lokacin ana ta yarinta, ba mu xauki abin da gaske ba, sai dai mi? abin da yaro ya ke so kuma ya girma da abin nan a zuciyar sa watarana sai ya tabbata, to ashe Allah Za Ya tabbatar da abin a gaba.
A tsakanin 1986 da 1994 ina karakaina, in kai gwauro in kai mari a tsakanin Daura, Malumfashi, Dutsinma, Qanqara, Funtuwa da Katsina, duk samari masoya Shata sun sanni kuma inda duk na je ana maraba da ni ana kuma son in zauna in bada labari sabo na Shata da na kalato. Sai da ta kai ma a Malumfashi da Daura mun kafa Qungiya ta masoya Duna na Bilkin Sambo. Cikin 1987 na fara zuwa gidan Shata kuma mu na haxuwa da shi a Zariya (a Magume gidan Sani Gadagau, Bakatoshi) da Kano da Funtuwa da Katsina (Nasara Guest Inn, gidan Sa'in Katsina). Ba wanda ya fara kai ni ya gabatar da ni wurin sa, ni na kai kaina, musamman saboda dalilan can na sama. Cikin 1990, ina tammanin ma ran Lahadi 3/9/1990 ne lokacin na kammala karatu a Kwalejin Ilimi mai zurfi (CAS) Zariya na tafi Funtuwa na samu Shata na kai masa wani littafi da na rubuta mai suna Karon Battar Qarfe (na yaqi ko hikaya ne), na kwana har da safe ni da shi da Mati Bomber mu ka tafi ofishinsa na kan hanyar Zariya, lokacin ya na shugaban Jam'iyyar SDP, nan mu ka wuni. Na gabatar masa da littafi, na kuma buqaci ina so ya biya kuxi a wallafa littafin. Amma ban samu nasara ba, don bai ce ya amince ba, bai kuma ce ba ya yi ba. Na yi waqoqin Shata a CAS Zariya a qungiyar mu ta Hausa, a matsayi na na Shatan CAS, sannan da ina Jami'ar Ahmadu Bello na zama Shatan ABU na qungiyar Hausa, duk don dalilin soyayya ta da Shata, mai benen-bene na Izzatu Musawa. Ka ga kenan wanda duk za ya bada labarin ko nuna son Shata baya na ya ke. Wanda duk ya sha wuta baran tsire ne, kuma labarin dare a tambayi kura.
Mafarin Tunanin Wallafa Littafin Tarihin Shata, 1992
A cikin 1992, lokacin ina karatun Digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello, aji biyu (300 Level) Allah Ya haxa ni da wani yaro a Jami'ar mai qwazo mai ilimi ana ce masa Kabiru Husaini Gwangwazo, kuma lokacin ya na karanta Digiri akan harshen Turanci. Mun fara haxuwa da shi a taron OUA na wasan kwaikwayo na xaliban Turanci, inda ya fito a matsayin Shugaban Zaire watau Mobutu Sese Sekou. Sha'awar da ya bani ta sa na nemi mu yi abotaka, ya amince. Muna nan, mu na nan, ya zo wuri na, nima in je wurin sa. Sai rannan na xauki littafi na na Hausa da na rubuta mai suna Saqo Daga Birni Al-Shabdad (na hikaya ne) na ba Gwangwazo domin ya duba mani. Bayan kwanaki, sai wani xan rikici ya sanya aka rufe Jammi'ar. Ina gida Qanqara, sai na yi amfani da wannan damar na tafi Kano wajen sa domin in amso littafin. Sai na tarar an tsare shi a Ofishin 'Yan sanda na Bompai saboda littafin Xanmasanin Kano da ya rubuta, aka qaddamar, amma a baya ya ranci kuxaxen mutane saboda hidimar bai biya su ba, sun sa an kama shi.
To, a unguwar Takuntawa inda ya ke da zama sai aka kai ni wajen abokan hulxar sa, to su su ka kai ni wajen sa a Bompai. Sai na tarar suna da wata qungiya mai suna Young Writers Club (YWC) Kano, wadda Kabirun ma mamba ne. To nan su ka riqe ni na yi kwanaki a wajen su, su ka yi mani abin arziki, nan kuma na riqa kwana wajen su. Kuma su ka bani fam na cika na zama xan qungiya. Ina tuna cikin su akwai Suleiman Gezawa, Rabi'u Kura, Rabi'u Mohammed, Mohammed Garzali, da sauransu. A cikin shirye-shiryen qungiyar ana rubuta tarihin mutanen da su ka shahara ko na garuruwa. To sai su ka bani shawara mi za ya hana in tafi Funtuwa in nemo izinin rubuta tarihin Shata daga wajen sa ? Tunda dama sun yi tunanin hakan tun kafin in baqunce su. Sai na amince. Na tafi Funtuwa, na yi sa'a na samu Shata a gida, na bashi labarin abinda ake ciki da qudurin wannan qungiya, da abin da ta sanya ni in yi mata. Ya yi murna. Har na ce masa : 'sun ce ka faxi mani ranar da ka ke a gari, don mu zo tare da su'. Ba zan manta ba har ya kama faxa ya na ce mani 'ai yanzu na girma, na daina yawon zage, bare a ce a za a zo ba a same ni ba, saidai fa ko in kun ji ana wani buki a Rediyo, watakila zan je, to sai ku dakata sai randa ku ka ji ba a yin wata sabga ko naxin sarauta'. Mu ka rabu a haka. Na koma Kano na shaida masu. Su ka bani dama da in rubuta littafin. Na fara rubutu, wanda ya kai ni har cikin 1994 (bayan shekara 2 kenan) Na kammala. Sai mu ka kai littafin ga Ahmed Mohammed wani mai kafanin buga littattafai a Gidan Goldie kusa da Singer, Kano. Ana ta cuku-cukun ya za a yi a samu kuxi a buga shi, sai na tafi bautar qasa a Legas. Ran da ma zani tafi, na biya ta Funtuwa na yi bankwana da Shata (ran Lahadi 13/11/1994) har ma na bashi kofin littafin, ya amsa ya riqa ya duba. Har ya na cewa 'yanzu nan wannan duk aikin tarihi na ne? Na ce masa 'e'. Ya yi fatar Allah sa albarka. Sannan ya ce idan na dawo daga Ikko za mu zauna. Ya kuma lissafa mani wasu a Legas da in na je in yi ma intabiyu, mutanen sa kamar su Alhaji Na'Allah Xan Ibrahim da Alhaji Salmanu Agege, shugaban 'Yan Daudu na Afirka, da sauran su. Kuma na yi hakan.
Shirya Littafin Shata Ikon Allah
Na dawo daga bautar qasa cikin 1995. Sai kuma abokan aiki na na Kano su ka nuna gazawa ga buga littafi na jan qafa. Waje xaya kuma na samu labarin Ibrahim Sheme daga Ya'u Wazirin Shata da wani abokina Kabir Xan'azumi Qanqara wanda mazaunin Kaduna ne, bil hasali ma gida xaya su ke zaune da Sheme xin a unguwar Badikko. Kafin Ya'u waziri ya qara tunkara ta da maganar Sheme, sai kwaram rannan Shata ya yi ma ni bayanin sa. Ya ce mani na san shi? Na ce masa 'ban san shi ba, ba mu tava haxuwa ba'. Shata ya ce mani ya kamata mu haxu, abinda ba ni da shi ya taimaka mani da shi, shi ma abinda ba ya da shi, da ni ni ke da shi sai in bashi'. Amma bai nuna ya na so mu haxe ba, amma ni a fahimta ta haka Shata ke nufi. A waje xaya Ibrahim Malumfashi (wanda ya zama Farfesan Hausa daga bisani) ma ya tava yi mani maganar sa, amma ba shi ya kai ni wurin sa ba. Ni na kai kai na wurin Sheme a gidan san a Badikko xin nan da dare, ina kuma zaton cikin 1995 xin ne, don lokacin ban ma gama bautar qasa ba. Sheme ya yi murna da gani na, cewa ya daxe ya na jin labari na amma sai rannan mu ka haxu. Ya zaunar da ni, ya xauko mani aikin san a littafin Shata na gani, na kuma yaba. Tun daga rannan bamu qara haxuwa ba sai cikin 1997 da na koma Kwalejin Ilimin Kimiyya ta Kaduna da aiki. Ya tava samu na a ofis, ya nunaya kamata idan zamu haxe ayyukan mu wuri xaya mu yi haka, idan kuma ba mu yi to kowa ya kama gabansa. Matata Habiba ('yar mutanen Mangu)ta na sheda cewa Sheme, ban da ofis (tunda wannan ba ta gani ba) ya tava zuwa gida na a nan Kwanar PRP kusa da Angwan Sanusi duk akan zancen yiwuwar haxewar mu. Da, da farko Sheme na zawarci na amma na so in noqe saboda halin rayuwa a gaba, amma sai matata ta nuna tunda ya nuna yana so mu haxe in xauki aiki na in bashi, ta ce ta tabbata a gaba abin alheri za ya zama. Ta kuma tabbatar mani da cewa duk da ya ke ba ta tava ma ganin sa ba, ta san ba za ya cuce ni ba. Na rantse da girman Allah abin da ya faru kenan. Sai na aminta. Ran wata Asabar da safe Ibrahim Sheme ya zo waje na ya ce in xauko masa littafi na ya gani. Ba musu na shiga na xauko littafi gaba xaya na bashi, don ni ba na iya tsallake maganar matata. Na yarda da ita. Mu na nan mu na nan, sai ya tura ni in yi intabiyu da wasu mutanen Shata, don shi ayyukan ofis sun sha masa kai. Kuma ina ta yi masa biyayya saboda ko ba komi akwai tazarar shekaru kimanin 2 ko 3 ma kuma ya na gabana a makaranta. Gashi a lokacin ya na 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatun Digiri na Biyu daga Ingila, ya na ta bani sha'awa. Inda duk ya tura ni ba gardama sai in tafi, watau a nan Kaduna. Sannan kuma na kan xauke shi in kaishi ga wasu da Shatan ya yi ma waqa da shi bai ma san su ba, misali: Malam Na Gwandu mai nama, wanda ta hanyar Ahmadu Doka na san a Kaduna ya ke da zama. Sannan na xauke shi na kaishi ga Hauwa 'yar Bori matar marigayi Sarkin Bori Sule a Titin Vashama Tudun Wada Kaduna. Dole ne in fi Ibrahim Sheme sanin mutanen da Shata ya waqe sabili da a kullum ina tare da Ahmadu Doka (unguwa xaya mu ke zaune) da sauran makaxa da mawaqa da su ka sha yin kwaramniya da Shatan, su ke bayyana mani mutanen Shatan. Ni da Doka, kuluyaumin ba mu da wani labari sai na Shatan.
Cikin 1998 sai Sheme ya tafi Funtuwa, ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano. A nan ya samu labarin wasu 'yan Kano su 2 su na rubuta tarihin sa daga bakin Shatan, don sun ma same shi aasibiti sun nuna masa aikin da su ka yi. Saidai su Sarkin Daura ya sanya su. Saboda haka Shata ya ce ma Sheme ya tafi Kano ya nemo su ya ce su zo Funtuwa ya na kiran su, don ya sanya su haxe da mu. Amma Shata ya yi ma Sheme kashedin kada ya bayyana masu cewa buqatar sa a haxe. Sheme ya dawo Kaduna ya same ni gidan marigayi Adamu Yusuf BBC ya bayyana mani abinda ke faruwa. Har na vata rai sai ya bani haquri y ace haka Allah Ya so kuma mu yi fatan Allah sa abin ya zama alheri. Mu ka sa ranar tafiya Funtuwa, watau Asabar mai zuwa ta ran 19/9/1998. Tun ran Juma'a Sheme ya xauke ni, tare da wani abokinsa Aimana Datti Usman mu ka tafi mu ka kwana Funtuwa. Wanshekare da safe mu ka haxu da baqi daga Kano a gaban Shata. Nan da nan Shata ya nuna da za a haxe da ya fi, amma mu je mu yi shawara. Mu ka fito garejin motar sa mu ka yanke cewa mu 4 mu zama xaya ga wannan tafiya. Mu ka koma mu ka shaida masa.
Amma cikin ikon Allah sai Allah Ya mantar da Shata ya tuna ma Sheme da sauran baqin nan wancan zancen littafin sa da na ke yi da qungiyar YWC ta Kano su ka sanya ni. Ni kuma, saboda kawaici sai Allah Ya rufe mani baki, saboda ma ina ganin ga wani sabon shafi an buxe, to mi za ya sanya in kawo zancen abin da ma ya wuce?
Mu kwana nan, za mu xora a gaba insha Allahu.
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.