0

                             Na
             Alhaji Ibrahin Muhammad
       Ɗanmadamin BirninMagaji
  Inkiya, Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin-Magaji (Ɗan Alin Birnin-Magaji),
         Jahar Zamfara. 08149388452, birninbagaji4040@gmail.com

              Takardar da aka gabatar a taron Ƙasa da Ƙasa  Kan
                           Makaɗa Ibrahim Narambaɗa  Tubali
            A Jami'ar Bayero Kano Ranar 15-17 ga Watan Satumba ,2019

Makaɗa Ibrahim Narambaɗa a Fadojin Ƙasar Hausa

Tsakure
Wannan takarda ta ƙuduri niyyar fayyace irin matsayi da rawar da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taka wajen kyautata al'amuran sarauta da hanyoyin samunta, da na gudanar da ita a wasu fadojin ƙasar Hausa. Domin cimma wannan manufa an saurari waƙoƙin makaɗa Narambaɗa sama da guda goma da nufin tsinkayen irin yadda sarauta take a ƙasar Hausa da yadda ake kokuwar nemanta idan ta faɗi da kuma yadda mu'amaloli sukan kasance a cikin masarautun ƙasar musamman a dauri. Ƙasar da Ibrahim Narambaɗa ya fito ƙasa ce mai yalwar arzikin ƙasa da na ma'adanai da kuma tsarin sarautu masu biyayya ga ɗabi'u da al'adun gudanarwa mabambanta. Wannan yanayi ya yi tasiri sosai wajen yadda ake gudanar da mulkin  sarautar gargajiya  a cikin Hausawa kamar yadda yake cikin waƙoƙinsa na fada. Daga wasu waƙoƙin Narambaɗa  da aka yi nazari an samu tarihin garuruwa da sunayen sarautar ƴaƴan sarki da na barori da yanayin ƙasa da kuma wasu al'adun sarakuna kamar a ƙasar Isa da Zazzau.

Gabatarwa
Ko da Bahaushe ya zo ƙasar Hausa ya samu al'ummar ƙasar Hausa da tsarin mulkinsu  ta wasu tsarrarun hanyoyi da suka zaɓa don tafiyar  da al'umma cikin linzami. "
Allah ya albarkaci wannan ƙasar ta Hausa da  wadatacciyar ƙasa ta noma da tudu da gangare da ƙoramu waɗanda suka ba da dama ga mazauna cikinta su yi noma da kiwo da sana'oin hannu da kuma fatauci" Adamu (1997:3-4).  Wannan arziƙi ya haifar da zaman al'ummar waje guda tare da tilasta musu samar da shugabanci don tafiyar da al'umma cikin mizani na bin dokoki da kiyaye duk wasu sharuɗɗa da tsarin mulki da al'adun da suka tanada.
Birnin magaji (2018:174) ya bayyana makaɗan fada da cewa sun zama wani kundi na adana tarihin masarautu da sarautun ƙasar Hausa da zamantakewa da faɗi-tashi da gwagwarmayar da ake yi a fada." Yadda makaɗan  fada ke kallon sarauta da masarauta abu ne mai faɗin gaske, har ta kai sarki kan ji sarautarsa da ikonsa ko darajarsa basu cika ba in har ba shi da mawaƙi na nuna wa sa'a.  Narambaɗa yana cikin mawaƙa da suka kalli fadar ƙasar Hausa da tsarin sarautunta daki-daki kamar yadda za mu gani a wannan takarda mai taken "Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Fadojin qasar Hausa". Narambaɗa ya kalli masarautun ya yi musu waƙa inda ya kwarzanta wasu masarautun har ya kai darajarsu ta ɗaukaka. Ire-iren masarautun da ya kalla akwai ta Ubangidansa sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa ( Amadu I) da Masarautun Dagatai na yankin Zamfara, kamar Shinkafi da Jangeru da Kuryad Dambo sai kuma masarautar Zazzau wajen sarki Malam Jafaru Isyaku da sarkin Zazzau Muhammadu Aminu. A ƙarshe an kawo kammalawa da manazarta.

Taƙaitaccen Tarihin Ibrahim  Narambaɗa
Zai yi wuya a iya tantance haƙiƙanin shekarun da aka haifi Narambaɗa saboda dogon lokaci ko kuma rashin wayewar hanyar karatu da rubutu a ƙasar Hausa a wancan lokaci. Amma a hasashe, Gusau ya bayyana an haifi Narabaɗa a shearar 1875 amma shi Bunza ga na shi hasashen cewa ya yi an haifi Narabaɗa a shekarar  1890. Sunan Narambaɗa na Gaskiya Ibrahim. Ya samo laƙabin Narambaɗa ne daga sunan karyarsa Rambaɗa. Sunan mahaifinsa Maidangwale wanda shi kuma ya sami sunan ne daga  sana'ar sayar da alewa amma sunansa na Gaskiya Buhari. Mahaifin Narambaɗa fitaccen ɗan kokawa ne wanda ya shahara a lokacinsa. Asalin mahaifinsa mutanen Nijar ne, yawon karatu ne ya kawo su lardin Sakkwato don haka Narambaɗa a ɓangaren uba karatu ya gada. Amma mahaifiyar Narambaɗa mutuniyar Badarawa ce mahaifanta makaɗa ne don haka Narambaɗa Karen makaɗa ne, kenan a nono ya sha kiɗa. In ana batun ƙabila kuwa daga uba da uwa duk Bare-bari ne.
Tun tasowar Narambaɗa mutum ne mai kazar-kazar don haka ma ya shiga harkar wasan samartaka sosai musamman wasan yara na lokacinsa ya yi wasan tashe da wasannin dandali na motsa jiki. Da ya ɗan tasa sai ya shiga wasan kokawa da na tauri. Narambaɗa ya yi karatun allo har ya kai ya sauka a hannun malaminsa mai suna Malam Shu'aibu, ya sa karatun sani har ya yi zurfi a cikinsa. Narambaɗa ya yi aure kuma ya samu zuriya.
    A ɓangaren kiɗi kuwa ya shahara kwarai mutum ne mai hazaƙar gaske yana da mu'amala da kyakkyawar dangantaka da hulɗa da jama'a wannan ya ƙara masa soyuwa a wajen mutane musamman Sarakai da Dagatai da ma Fadawa. Narambaɗa ya shiga harkar kiɗi da girmansa, wannan ya sanya kamalarsa da dattakunsa da ya sa  ake mutunta shi sannan shi ma a ɓangarensa ya ja girmansa . Duk da waƙar noma Narambaɗa ya fara har ya shahara a cikinta, ya yi suna musamman a ƙasar Gobir da Zamfara kuma wannan ne silar da ya sa manoma suka rinƙa kai masa gayyatar hira. An ce farkon fara kiɗansa a fara shi ne lokacin da Galadima ya gayyace shi  a matsayin mai kiɗan fada ba kiɗan noma ba, kuma shi Galadima shi ya yi wa fadar sarkin Gobir tallarsa.
    Narambaɗa bai samu shiga fadar Gobir ba sai a shekara ta 1927 da aka naɗa Tudu Muhammadu Na'ammani sarautar sarkin Gobir na Isa. Daga nan ya ajiye kiɗan noma ya shiga fada. Ubangidansa na farko shi ne sarkin Gobir Tudu Muhammadu Na'amani (1927-1935).
Bayan rasuwarsa aka naɗa sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935-1975). Ahmadu Bawa ya shekara goma sha biyu bayan rasuwar Narambaɗa ba tare da  neman wanda zai gaji Narambaɗan a fada ba. Narambaɗa ya rasu ranar 30 ga watan janairu 1963. Bunza (2009:8-30)

Makaɗan Fada Ga Al'adar Gidajen Sarautar Qasar Hausa
Kowane gidan sarauta na da makaɗinsa na gado idan za a yi wani gagarimin biki ko naɗin sarauta shi zai zo ya yi hira. Mawaƙan baka na kallon sarauta da faɗin gaske kuma hukuma ce mai cin gashin kanta . Makaɗan fada suna waƙa ne cikin ilimi ba sa yin kowacce irin waƙa ta sarauta sai sun san  masarautar cikinta da wajenta saƙo da lungunta, domin su burge waɗanda suka gaji sarautar.
Gwarzo ( :58)  Ya ce "makaɗan fada sune makaɗan da kurum sarki suke yi wa waƙa"  Ɗanmadami (2018:187 ) Ya bayyana makaɗan fada da sune suke aiwatar da waƙoƙinsu ga wani basarake guda a matsayin ubangida ba tare da sun haɗa shi da wani ba, in kuwa sun haɗa ɗin to sai da izininsa ko na wani amininsa kuma da sharaɗinsa."
Sarauta da Kokawar Neman ta a Ƙasar Hausa a Bakin Narambaɗa
Bahaushe yana da ƙasa mai suna ƙasar Hausa'. Kowace al'umma ta zo, nan ta tarar da su da sunansu. Ƙasar Hausa babbar farfajiya ce mai dauloli manya-manya zagaye da manyan tsofaffin dauloli maƙwabta irin su Daular Nupe da Daular Songhai da Daular Borno da Daular Oyo da Daular Azbin. Jigajigai daga cikin daulolin ƙasar Hausa su ne: Daular Kano da daular Katsina da daular Zazzau da daular Kabi da daular Gobir da daular Maraɗi daular da Damagaram da daular Zamfara .
Waɗannan daulolin da gundumomin da garuruwa da ƙasashen da ke ƙarƙashin riƙonsu su ne ƙasar Hausa, kuma a nan ne ƙasar Bahaushe take. Mutanen da ke ciki su ne Hausawa, wanda ya baƙunce su ya rikiɗe a cikinsu ya zama Bahaushe.

A Ƙasar Hausa Sarki shi ne jagora a Fada. Yana da ikon gudanar da mulki a hannun sa, yana zartas da kowane irin hukunci a Ƙasar sa. Gaya (2010: 15) ya nuna cewa samun zama Sarki ya ta'allaƙa ne akan gado da nuna jaruntaka da zaɓen cancanta dangane da tsoron Allah da sanin ilmin addinin Musulunci da adalci".
Sarauta wani matsayi ne da wanda ya gada ko wanda ya cancanta ko kuma wani dalili na daban zai iya kai Mutum ga wannan gado. Sarauta ita ce mulki da sukuni da bayar da umurni na aikatawa ko hanawa ga Talakawa waɗanda ke ƙarkashin tutar mai mulki (Alasan da Musa, 1980: 17). Hanyoyin zaɓen Sarki sun bambanta daga Masarauta zuwa Masarauta. Wasu Masarautu gida ɗaya garesu tak na sarauta, kamar Sakkwato. Wasu garuruwan kuma suna da fiye da ɗaya kamar Zazzau. Sarauta tana da matuƙar tasiri a Ƙasar Hausa. Gusau (1988:21) ya bayyana Sarauta da ita ce shugabanci, musamman na  gargajiya dake sanya hura hanci ko girman kai ko fadin rai.
A cikin Waƙar babban Ubangida sa, wato Sarkin Gobir na Isa, Amadu Bawa, Ibrahim Narambaɗa ya nuna cewa Sarauta dai gadon ta ake yi, bayan cika sauran sharruɗa, domin a cikin Bakandamiyar shi ya na cewa "
JAGORA:  Ummaru Ɗan Alu gida nai na Isa

ƳAN AMSHI: Yayi Sarki kuma ga diyan da yay haihwa nan sun yi,

                       Kuma yau ga gadon sa dan jika nai ya hau,

                       Dangi sai ku hanƙure shina ham mahdi,

(Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa, Baban Dodo ba a tamma da batun banza).

A ciki dai ya nuna jaruntakar Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa, domin ya ce

JAGORA: Bai san tsoro ba zucciyatai bata kammai ba

ƳAN AMSHI: Yaro bai kai garai ba ko ga uwaye mata.

                        ( Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa, Baban. Dodo ba a tamma da batun banza).

Wato gado da jaruntakar dai sun fito ƙarara, domin ban da gadon Sarauta daga gefen Mahaifinsa , har ma a gefen Mahaifiyarsa ya yi gadon Sarauta domin kuwa Mahaifiyar shi  Aminatu ƴar Sarkin Gabas na Goronyo Abdulkadir ce. Makaɗa Ibrahim Narambaɗa ya nuna cewa Sarauta dai duk da gadon ta ake yi, to akwai amincewar Allah. Kamar yadda ya faɗa a cikin wannan waƙar "

   JAGORA:     Ai Sarauta ban da nuhin Allah ce,

                        Da dibat ta akan yi da ƙarhi,

                        Waɗanga da nag gaza ganewa,

ƳAN AMSHI: Da sun gane ana hakanan da sunyi.

( Gogarman Tudu jikan Sanda, Maza suji tsoron Ɗan mai Hausa)

Faɗuwa da Samun Sarauta a Waƙoƙin Narambaɗa
Kamar kowane irin abu na duniya da ake gasa akan shi, haka sarauta take, ana iya shiga wajen neman ta, a yi sa'a a samu, ko kuma a samu akasin haka wato a rasa. Narambaɗa ya bayyana irin haka a cikin Waƙoƙin shi. A cikin Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alh Abubakar Garba (1952-1960) Narambaɗa ya nuna waɗanda ko da sun tafi neman Sarauta ba za su samu ba saboda wasu dalilai, kamar dai yadda yake cewa

JAGORA:  Gidan ga mutum huɗu ba su Sarauta,

                  Da sambalko da satoto,

                  Shi wanga na ukku ƙazami,

                  Na cikon na hudunsu azuji,

                  Shiri Bajinin Mamuda,

                 Abu na Namoda shirarre

(Shirin Bajinin Mamuda, Abu na Namoda Shirarre)
                                                                 
A Masarautar Zazzau ma ya ƙarfafa wannan kamar haka:-

   JAGORA:      Sardaunan Kaduna yayi jawabi dug ga Zage-zagi zamne,

                        Ya ce ku bar hushi da dangin ku,

                        Sarauta tana ga Allah,

                        Kun ga gidan Alu gidan Sarauta na,

                        Gidan Yaro gidan Sarauta na,

                       Shi wannan da kun kaso a naɗa Allah bai yi mai Sarauta ba.

ƳAN AMSHI: Mijin Nana Yalwa Ɗansanda,

                       Gulbi ka wuce kwalfewa.

                       ( Mijin Nana Yalwa Ɗansanda, Gulbi ka wuce Kwalhewa).

A cikin Waƙar Dagacin Shinkafi, Ibrahimu Naguraguri (Ibrahimu Naguraguri, Mai Shinkahi Bajinin Zagi mu dai Allah ya bar muna kayaa) ya na cewa :-

JAGORA:       Duk ɗan Sarki son ya kai ya zan Sarki,

                        Sai in bata samuwa,

ƳAN AMSHI: Ta tabbata ko ban hwaɗi ba,

                       in gandu ya samu ya hi gamana.

                      Ibrahimu na Guraguri,
 
                      Mai Shinkahi Bajinin Zagi,

                      Mu dai Allah ya bar mana  kaya.

(Ibrahimu na Guraguri,Mai Shinkahi Bajinin  Zagi, Mudai Allah ya bar muna kaya)

Ya na ƙara jaddada cewa Sarauta dai gasa ce kamar gasar kokawa

JAGORA:    Waɗanga da Kak kayas,

                   Gasu an faɗa man wai an ce da ni suka hushi

( Ibarahimu na Guraguri, Mai Shinkahi bajinin Zagi, mudai Allah ya bar muna kaya)

ya ci gaba da nuna rashin iyawar su (Ƴan Sarkin da suka yi takarar Sarauta da Ibrahimu Naguraguri)

JAGORA:        Bamin kokuwa koda yaushe shi aka shammata,

bai iya ba.

ƳAN AMSHI: Ga wata kokuwa an wuce dashi,

                       Karsanai kakkabe mashi Ƙasa,

                   Ibrahimu na Guraguri,

                   Mai Shinkahi bajinin zagi,

                   Mudai Allah ya bar muna kaya.

(Ibrahimu na Guraguri, Mai Shinkahi Bajinin Zagi, mudai Allah ya bar muna kaya)

Narambaɗa a Da'irar Masarautun Ƙasar Hausa
Kamar yadda Makaɗa Sani Sabulu Kanoma ya faɗa a cikin wata waƙar sa "Bani rena Mutan ƙauye, don nasan jama'ar birni", haka Makaɗa Ibrahim Narambaɗa bai rena Masarautun Ƙauye ba duk kuwa da karɓuwa da ɗaukakar da ya samu a fadojin manyan Sarakunan Ƙasar Hausa. Ya leƙa fadodin Dagatai da Hakimai/Uwayen Ƙasa daban-daban, a Gundumomi na Masarautun Ƙasar Hausa domin yaɗa fasahar sa.
A wajen irin wannan leƙe -leƙen ne ya ziyarci Dagacin Kuryad Dambo/ Sarkin Rwahin Kuryad Dambo, da Dagacin Jangeru/Sarkin Bazai da kuma Dagacin Shinkafi/Magajin Shinkafi, waɗanda a wancan lokaci duk yankunan Dagatai ne a Gundumar Isa da ke tsohuwar Masarautar Sakkwato (Saboda a halin yanzu dukkan su Gundumomin Hakimai ne a cikin Masarautar Shinkafi da ke Jahar Zamfara) Haka ma ya ziyarci Masarautar Zazzau da ke Jahar Kaduna, baya ga ƙoƙarin sa na fitar da sunan Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar sa, da Ƙasar Isa a idon duniya. Misalin irin wannan masarautu sun hada da:-
Narambaɗa a Fadar Dagacin Shinkafi, Jahar Zamfara
Magajin Shinkafi Ibrahim
Wasu Fulani ne da suka fito daga yankin Gwandu a farko-farkon ƙarni na 18 suka fara yada zango a Ƴankuzo da ke Masarautar Tsafe ta Jahar Zamfara, daga baya suka zauna a cikin Masarautar Bunguɗu ta Jahar Zamfara kafin daga bisani su cimma wani wuri a tsakanin Kogunan Bunsuru daga Gabas da Gagare daga yamma, sun ƙirƙiri wani gari da ake kira Badarawa a ƙarƙashin Jagorancin Shugaban su, Muhamman Bello, wanda ya fara Sarautar garin da laƙabin Magaji. Badarawa ta kasance hedikwatar su har zuwa 1940s lokacin da  Magaji (1939-1950) Amadu Lamiɗo ya maido da hedikwatar a sabon wurin da suka kira Shinkafi, kuma ya yi Sarauta har zuwa rasuwar sa a Shekarar 1950. An naɗa magadin shi, wato Magaji Ibrahim (Ibrahimu Naguraguri) Wanda shi ne Dagacin da Narambaɗa ya yi ma wannan waƙar, "Ibrahimu Naguraguri, Mai Shinkahi Bajinin Zagi mudai Allah ya bar muna kayaa", Shekarar 1950, ya yi mulki har zuwa rasuwar shi a Shekarar 1990. Wannan Waƙa ta na cike da batutuwa irin n a mulki . A wani ɗan Waƙar, Narambaɗa na zano wasu masu riƙe da sarautu a ƙarkashin wannan Dagaci,

JAGORA:    Na Arɗo, na Shehu, na Sarkin Ruwa,

ƳAN AMSHI: Ibrahimu buƙatak ka ta biya,

                       Baban Ɗan Inna kayi ƙoƙari,

                       Ibrahimu na Guraguri,

                       Mai Shinkahi Bajinin zagi,

                       Mudai Allah ya bar muna kaya.

Ya cigaba ya na cewa:-

JAGORA:   Kowayyi sarauta gidan ga,

                   Dag ga Kakanni haz zakkuwa Uwaye

ƳAN AMSHI: Ba ga na yau ba,

                       Ko mazan na hwarko,

                       Ba ay naɗi da yahhi wanga ba.

Domin ya kammale wannan zancen sai ya ƙara da cewa

JAGORA: Wada Mainasara yayyi ƙoƙari,

                 ko Ibrahimu yayi ƙokari,

ƳAN AMSHI: Sun ɗebi ƙasa zamanin sa,

                        Ibrahimu sa'akka an gameta dut.

(Ibrahimu na Guraguri, MAI Shinkahi Bajinin Zagi, mudai Allah ya bar mana kaya)

Domin ya nuna cikar burin Magaji Ibrahimu, Narambaɗa ya na cewa

JAGORA:   Kai aa Ummaru,

                   Kai aa Abubakar wan Mani,

                   Kai am Magaji Dango,

                   Kai ash Shiggaban gidan ga dut.

Magajin Shinkafi Ummaru (Magaji na 5, 1889-1903), Shi ne Magajin Shinkafi Abubakar/Bube (Magaji na 4, 1874-1889) Shi ne kuma Magajin Shinkafi Dango(Magaji na 8, 1925-1939), wato tunda ya zamo Magajin Shinkafi to shi ne  Jagoran gidan Malam Muhamman Bello (1835-1845).

Narambaɗa a Fadar Dagacin Kuryad Dambo, Jahar Zamfara
Sarkin Rwahin Kurya
Ƙauyen Kuryad Dambo wasu Fulani ne daga jinsi Alibawa da suka zauni Zurmi da Ƙaura Namoda da Moriki da ke Jahar Zamfara a halin yanzu suka ƙirƙire ta, bayan kammala Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a ƙasar Hausa. Wa da ƙane ne, wato Gatari da Makaru, suka fito daga yankin Zurmi, Gatari ya ƙirƙiri ƙauyen Kware ya cigaba da mulki da laƙabin sarautar sarkin yaƙi, ƙanen shi Makaru ya zarce  zuwa Kudu maso gabashin Kware, ya ƙirƙiri wannan Ƙauyen da ake kira Kurya, wacce daga baya ta cigaba da ansa sunan Kuryad Dambo, saboda wani mashahurin jagora da ya gadi Makauru, wanda ya ƙirƙiri Ƙauyen bayan rasuwar shi. Kamar Shinkafi, duka da Kware da Kuryad Dambo sun kasance a cikin Gundumar Hakimi/Uban Ƙasar Isa a Masarautar Sakkwato har zuwa Shekarar 1996  da aka ƙirƙiiro Jahar Zamfara, aka haɗe su a Gundumar Shinkafi. Narambaɗa ya leƙa Fadar Dagacin Kuryad Dambo ne a cikin 1940s zuwa 1950s, a lokacin mulkin Sarkin Rafi Ibrahim, wanda shi ne ya waƙe sosai kamar yadda zamu gani a cikin ɗaya daga irin waɗannan Waƙoƙin.
Narambaɗa ya yi ƙoƙarin fitowa da jaruntakar wannan Dagaci na Kurya da kuma na zuriyar su, tun a lokacin Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ya na cewa:-

JAGORA:        Ko dauri gidan gabas,

ƳAN AMSHI: Mazan Gabas gidan Rahwawa an kasani,na Sakkwato,

                       Ko can ga sa'ag gaba,

                      Hawo da shirin yaƙi,

                      Ha Dambo marinjayi.

(Hawo da shirin ƴaƙi, Na Dambo Marinjayi)

Ya ƙara bayyanawa "Ku baku ku cin amanas Sarki (Sarkin Gobir na Isa/Sarkin Musulmi) gidan ku Rahwawa nan Kun kayi hakimai". Ya sanar damu wasu daga cikin ƙauyukkan da Sarkin Rafin ke mulki.

JAGORA:        Na Magatakarda mai Ɗakwarawa,

                        Mai Bagare na Daudu,

ƳAN AMSHI: Kai haɓe suke tsoro.

Ya ƙara nuna cewa dai Sarkin Rafi Ibrahim ke da Ƙasar Kurya

JAGORA: Sarkin Rwahi mai Ƙasak Kurya,

ƳAN AMSHI: Ya kwan da shirin gaba.

(Hawo da shirin yaƙi , na Dambo Marinjayi)

Domin  ya nuna zuriyar su Mayaƙa ne sai ya buɗe wannan waƙar da " Hawo da shirin yaƙi na Dambo marinjayi". Sun yi duniya sosai tare, Narambaɗa ya fito da Sarkin Rafi Ibrahim na Kuryad Dambo ta hanyar Waƙoƙi, shi kuma ya samu gwargwadon alheri daga wannan Dagacin.
Narambaɗa ya yi ƙoƙarin fitowa da jaruntakar wannan Dagaci na Kurya da kuma na zuriyar su, tun a lokacin Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio inda ya ke cewa:-

JAGORA:        Ko dauri Mazan Gabas.

ƳAN AMSHI:  Gidan Rahwawa an ka sani Sakkwato,

                        Ko can ga sa'ag gaba,

                        Hawo da shirin yaƙi,

                        Na Dambo Marinjayi,

                        Ya ƙara bayyanawa.

JAGORA:       Su basu ku cin amanas Sarki

ƳAN AMSHI: Gidan ku Rahwawa nan Kun ka hi hakimmai.

(Hawo da shirin yaƙi, na Dambo Marinjayi)

Narambaɗa ya  sanar damu wasu daga cikin ƙauyukkan da Sarkin Rafin ke mulki " Inda yake cewa:-

JAGORA:  Magatakarda  mai Ɗakwarawa,

                  Mai Bagare,

                  Kai haɓe suke tsoro.

(Hawo da shirin yaƙi , Na Dambo Marinjayi)

Jagora: Sarkin Rwahi mai Ƙasak Kurya.
Narambaɗa ya sanarda jama'a a kan zumuncin da ke tsakanin gidan Sarautar Kware da Kuryad Dambo inda ya fito da abin ƙarara kamar haka:_

  JAGORA:      Na taho biɗad Doki,

                        Na shiɗa Kware,

ƳAN AMSHI: Sarkin Yaƙi ya biya Doki ya bani sule sittin.

(Hawo da Shirin Yaƙi, Na Dambo Marinjayi)

Wato kenan ya fara tsayawa a wajen Wa (Gatari)  da ke Kware kafin ya isa Kuryad Dambo wajen Ƙane (Makauru), duk da ba su ne ya tarar ba, ya iske magadan su ne, Sarkin Yaƙin Kware Mainasara da Sarkin Rwahin Kuryad Dambo, Ibrahim.

Narambaɗa a Fadar Hakimin Masarautar Baji/Bazai/Jangeru ta Jahar  Zamfara.
Ana kyautata zaton Ƙasar Baji (wadda ta ƙunshi garuruwan Baji da Jangeru da Birnin Yero da sauransu) da ke cikin Masarautar Shinkafi a Jahar Zamfara ta samu ne a Shekarar 1787, tun daga Malam Muhammadu Woni wanda ya ƙirƙiro Ƙasar. Muhammadu Woni, Bafulatani ne da ya shigo wannan yanki daga Tsohuwar Daular Borno, kuma shi ne ya ƙirƙire ta bayan ya zauna wurare irin su Tsohuwar Wonaka(a Masarautar Gusau ta yanzu) da wani Gari da ake kira Duhu (a Masarautar Zurmi ta yanzu). Da ya zo dai-dai inda garin Baji ya ke a halin yanzu,  ya lura da yalwar wurin kiyo da noma da ruwa,  sai ya ce ma Jama'ar shi "Mu Baje a nan", ance ta haka wannan gari na Baji ya samo sunan sa.
Daga cikin Ƴaƴan shi akwai Badambo da Muhammadu Yero. Bayan samuwar Jangeru da Birnin Yero, sai Badambo ya zo Jangeru a matsayin Sarki, shi kuma Muhammadu Yero ya je Birnin Yero(Ciki) a matsayin Sarki. Da wannan ne sai Jangeru ta zamo sabuwar hedikwatar Ƙasar Baji, yayin da aka naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Malam Muhammadu Woni a matsayin Sarki a Baji da laƙabin Magaji, laƙabin Sarautar Ƙasar kuma ya kasance Sarkin Bazai, a Jangeru.
Makaɗa Narambaɗa ya shaƙu da Masarautar Bazai/Baji sosai, wannan ne dalilin da yasa ya waƙe Sarkin Bazai, Suleman Dikko ( 1945 -1955) wanda kuma shi ne Sarki na 15 a tsarin Sarakunan Ƙasar Bazai/Baji/Jangeru. Ya yi mashi Waƙoƙi masu dama, ɗaya daga cikin su ita ce wadda ya ke cewa

JAGORA:    Sarki yahi wargi,

                    Na Malam Dara Dodo,

                    Na Ummaru ci Maraya.

( Sarki yahi wargi, Na Malam Dara Dodo na Ummaru Ci Maraya)

A cikin wannan Waƙar, ya na bayyana Sarkin Bazai Dikko a matsayin muzzakkarin basarake, wanda bai yarda da reni daga talakawa da masu jagorancin da ke ƙarƙashin ikon shi ba

JAGORA:        Bai taɓa wargi ba,

ƳAN AMAHI: Kuma baya tare da masu wargi.

Ya ƙara da cewa:-

JAGORA:        Dikko Magajin Buhari

ƳAN AMSHI: Ya murɗe wuyan Maza,

                       Ya riƙa wada Woni yayyi.

                       Sarki yahi wargi,

                       Na Malam Dara,

                       Dodo Na Umaru Ci Maraya.

(Sarki yahi wargi, Na Malam Dara Dodo, na Ummaru ci Maraya)

Domin ya sanar da Jama'a wuraren da Sarkin Ba zai ke iko da shi ba, sai Narambaɗa ya ce:-

JAGORA:        Na tafi Jangeru in ga Sarki,

ƳAN AMSHI: Sai an kace man ya na Baji, Ciki yay yi.

(Sarki yahi wargi, Na Malam Dara Dodo, Na Ummaru ci Maraya)

Ga kyauta ga Sarkin Bazai inji Makaɗa Narambaɗa
JAGORA:  Ai komi nab biɗa,

                  Ga Dikko Magajin Buhari,

                  Ai ya da kure ba,

                  Ɗansanda ba wada bai yi ma ba.

Narambaɗa a Fadar Zazzau, Jahar Kaduna
JAGORA:        Sarkin Gobir na Isa Amadu,

                        Shi yak kira ni, na ji jawabin da yay Mani,

                        Ban zamna ba, na shigo jirgi,

                        Sai hwadin nikai jirgi kai ni Zariya,

                        Kai dai kai mu Zariya, kai dai kaimu lahiya,

ƳAN AMSHI: Bisa yardar Ubangiji, in mun shiɗa,

                      Mun ga Jafaru, mun ɗebe arkane,

                      Ɗan Isiyaku makaye,

                     Jafaru mai halin mazan jiya zauna da lahiya.

(Ɗan Isiyaku Makaye, Jafaru mai halin Mazan Jiya, Zauna da Lafiya)

Wannan na cikin maganganun da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa da ya yi a lokacin da ya isa Fadar Zazzau a lokacin Mulkin Sarki na 16 a Daular Fulani ta Masarautar, wato Sarkin Zazzau, Malam Jafaru Isiyaku (1937-1959). Sarkin Zazzau, Malam Jafaru ya fito daga Gidan Sarautar Bare-Bari ne na Daular Fulanin Masarautar Zazzau wanda Sarki Yamusa ya assasa tsakanin 1821-1834. Shi Ɗan Malam Isiyaku ne, Shi kuma Malam Isiyaku Dan Abdullahi ne, Shi Kuma Abdullahi Ɗan Hammada ne, Shi Kuma Hammada Sarki Yamusa ne mahaifin shi. Sarki Malam Jafaru Isiyaku shi ne Mahaifin Gimbiya, daya daga cikin Matan Sarkin Gobir na Isa, Amadu Bawa, wato maigidan Makaɗa Ibrahim Narambaɗa. Kenan dai babu mamakin zuwan shi Zariya domin kiɗa da Waƙa a Fadar Masarautar, kamar yadda ya bayyana a cikin waɗan nan ɗiyan Waƙar.
Narambaɗa ya nuna cewa tun kafin ya isa Zariya ya na da labarin ta  a Sarauce.
JAGORA:     Tun ban zo nan ba,

                      Na ji labarin Audu yayi Sarki,

                      Ya Kyauta duniya,
 
                      Har Yaro naji yayi Sarki,

                      Ya Kyauta duniya,

                        Ibrahimu yai Sarauta,

                        Ya Kyauta duniya,

JAGORA :      Jafaru kai ag gidanga,

                        Kai ab babban su kahi kowa,

ƳAN AMSHI: Wada nit taho kamad Ɗanyamusa ni ishe,

                       Ɗan Isiyaku Makaye,

                       Jafaru mai halin mazan jiya,

                       Zamna da lafiya.

Domin tabbatar da maganar gemu da gemu game da zuwan sa Zariya, Narambaɗa ya na cewa"
JAGORA:        Kowac ce ya gane ni Zariya,

                        Domin ka yag gamu,

ƳAN AMSHI: In ba kai ba,

                        Babu mai iya kawo mu Zariya,

                        Ɗan Isiyaku Makaye,

                        Jafaru mai halin mazan jiya,

                        Zamna da lahiya.

( Ɗan Isiyaku Makaye, Jafaru Mai halin Mazan Jiya Zauna da Lafiya).

Kenan dai Sarautar Sarki Malam Jafaru ce sanadiyar zuwan sa Zariya har ya haɗu da wanda ya gaji Sarkin Zazzau Malam Jafaru Isiyaku. Bayan rasuwar shi a Shekarar 1959, ma'ana Iyan Zazzau,  Muhammadu Aminu, wanda ya yi Sarauta daga Shekarar 1959 zuwa Shekarar 1975. Tun Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya na Iyan Zazzau , Hakimin Sabon gari ne suka haɗu da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa, lokacin da Narambaɗa ya shiga Fadar Zazzau kenan. Ya yi mashi waƙoƙi da dama tun yana Iyan Zazzau, wannan ya nuna a cikin 'ya'yan Sarki, Narambaɗa ya riƙe shi a matsayin wanda ke da niyyar gadon gidan su , ga abin da yake cewa a cikin wata Waƙa.

JAGORA:     Ɗan Sadauki kak kaji tsoron Maza,

                      Iyan Zazzau Ɗan Bubakar,

                      Yanzu na gane halin Iya,

                      Abinda ad daidai duk ya sani,

                      Abinda ak kyawon Ɗan Sarki,

                      Ya zanka lura da manyan duniya,

                      Ƙoƙarin da shi kai bai hwasa ba,

                      Swahe duk aikin girma ya kai.

(Iyan Zazzau Ɗan Bubakar, Ɗan Sadauki Kak kaji Tsoron Maza)

Wato a nan yana yi wa Iya Muhammadu Aminu hannunka mai sanda ne cewa ya tsare aikin Mulki da kyau, ya kuma kulla hulɗa da muhimman Mutane domin sabo da maza jari, ya fara shirin zaman sa Sarki kenan. Bayan Iya Muhammadu Aminu ya zamo Sarkin Zazzau a Shekarar 1959, sun cigaba da duniya tareda Makaɗa Ibrahim Narambaɗa. Domin ya nuna abin nema ya samu, sai ya ce
JAGORA:       Taka sannu - sannu,

                        Banda garaje uban Iya,

ƳAN AMSHI:  Indon birnin Zariya ta samu,

                        Ya tankwashe maza,

JAGORA:        Mamman ya ci garin gaba,

                        Mai ya kamata na birnin Zariya Ɗansanda.

(Mijin Nana Yalwa Ɗansanda)
Domin ya bayyana daga Gidan Sarautar da Sarki Muhammadu Aminu ya fito sai ya cigaba yana cewa:-

JAGORA:       Ba kokwanto ba Sambona,

                        Kuma Abdulkarimi na,

ƳAN AMSHI: Gogarman Magaji,

                       A samu ya riƙa dangi nai.

( Ya Tankwashe Maza, Maman ya ci garin gaaba, Mai ya kamata na Birnin Zariya Ɗan Sanda)

Kyautatawa na cikin abubuwan da ke sanya Makaɗin Fada riƙe wuta a wajen Basarake. Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya kyautata wa Makaɗa Ibrahim Narambaɗa har ma ya nuna da kan shi cewa idan dai ba a same shi a Isa ba, to ya koma Birnin Zazzau

JAGORA:        Ai haƙon ga Mai akwai maza,

                Ya zarge mai kwaɗai,

ƳAN AMSHI: In dai ba ni Birnin Isa,

                        Zazzau ni ka komawa.

Ɗan Malam Abubakar Kwasau,
Jikan Iyan Zazzau Malam Usman D
Ɗan Sarki Malam Abdulkarimi,
Mai Martaba Sarkin Zazzau. Muhammadu Aminu shi ne Sarki na 17 a Daular Fulani ta Masarautar Zazzau. Ya fito ne daga gidan Sarautar Katsinawa na Masarautar, gidan da Sarki Malam Abdulkarimi (1834-1846) ya assasa, ya kuma yi Sarauta daga Shekarar 1959 zuwa Shekarar 1975.
Narambaɗa a Fadar Uban Ƙasar/Hakimin Isa (Sarkin Gobir na Isa), Jahar Sakkwato
Tun daga farko mun bayar da labarin lokaci da kuma yadda Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya isa Fadar Sarkin Gobir na Isa dake Jahar Sakkwato. Ya tarad da Sarkin Gobir na Isa Muhammadu Na'ammani, wanda yayi Sarauta daga Shekarar 1925 zuwa 1935. Ya samu nashi rabo daga taskar Waƙokin Narambaɗa, ciki kuwa har da wadda yake cewa
JAGORA:        Toya matsafa Sadauki na Abdu,

ƳAN AMSHI: Baban Isah baban Buwai,

                         Indon na ka gama lahiya.

(Toya Matsafa Sadauki na Abdu, Baban Isah Baban Buwai, in don na ka gama lahiya)

Bayan wafatin Sarkin Gobir Muhammadu Na'ammani, sai aka naɗa Amadu Bawa (Amadu I) a matsayin Sarkin Gobir na Isa na 10) a Shekarar 1936.  Ɗan Sarkin Gobir Basharu (Sarki na 8), shi kuma Ɗan Sarkin Gobir na 5 ne, watau Sarkin Gobir Ummaru , wanda ya zamo Sarkin Musulmi tsakanin 1881 zuwa 1891, shi Kuma Sarkin Gobir /Sarkin Musulmi Ummaru Ɗan Sarkin Musulmi Aliyu ne, Sarkin Musulmi Aliyu Ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Dan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullahu birahamatihi ne. A wajen Mahaifiya kuwa, Sarkin Gobir Amadu Bawa Ɗan Aminatu ne ɗiyar Sarkin Gabas na Goronyo Abdulkadir, wanda shi ma Batoranke ne, kamar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio.
An haifi Sarkin Gobir Amadu Bawa a Shekarar 1898 a Garin Isa, ya yi Sarauta daga Shekarar 1936 har zuwa 1975. Ya rasu a Shekarar 1982.
Zaman Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali da Sarkin Gobir Amadu Bawa, zama ne na amana da mutunci da kyautatawa a tsakanin su. Taren su ta yi nisa sosai har ta kai saboda tsare lalura da karimci da mutuntawa, Makaɗa Narambaɗa baya iya barin Isa da sunan zuwa wata Masarauta domin yayi kiɗa da waƙa ba tare da amincewar Maigidan sa, Sarkin Gobir Amadu Bawa ba. Hasali ma Manazarta na kallon kusan duk fasahar Narambaɗa ta ƙare ne akan Sarkin Gobir Amadu Bawa. Anan muna iya kawo misali da wata Waƙa da ya yi mashi wadda ya yi wa laƙabi da "Uwar Waƙa", Bakandamiya, kamar yadda wasu Makaɗan ke kiran irin wannan Waƙar. A ciki ya zayyano manya -manyan Mawaƙan Ƙasar Hausa na lokacin, ya na nuna cewa tunda dai sun yi irin wannan Waƙar shi ma ga ta sa  ya shirya.

JAGORA:         Kwaz zaka kallo ya karkaɗe kunne nai.

ƳAN AMSHI:  Ga Makandamiya zani yi cikin manyan waƙoƙi.

                        Gwarzon Shamaki na malam toron giwa.

                Baban dodo ba a tamma da batun banza

JAGORA:        Na jiya Jankiɗi,

ƳAN AMSHI: Ya yi tai uwar Waƙar sai nai tau,

JAGORA:        Na jiya Zamau,

JAGORA:         Na jiya Gurso,

ƳAN AMSHI: A yi tai uwar Waƙar sai nai tau,

JAGORA:         Na jiya Akwara,

JAGORA:         Na jiya Ɗandawo,

JAGORA:         Na jiya Nagaya,

ƳAN AMSHI:   A yi tai uwar waƙar sai nai tau,

JAGORA:         Dodo malamin waƙa kundumi Magajin ɗan Ɓaidu,

ƳAN AMSHI:   Ya yi tai uwar Waƙar sai nai tau

                          Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa,

                          Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

(Gwarzon Shamaki na Malam Toron Gowa, Baban Dodo ba a tamma da Batun Banza)

Kusan dukan abin da yakamata ya gaya wa Sarkin Gobir Amadu Bawa na sassala da dattaku da kamala da karimci da iya mulki da Kambamawa da Yabo da Kwarzantawa da Kirari da Roƙo da Habaici da Zambo da Zuga babu abinda Makaɗa Narambaɗa ya rage. Misali :

JAGORA:          Ai ba tun yau ba tun ya na can Sardaunanai,

ƳAN AMSHI:    Har yak kai wurin da an ka nada mai Sarki,

                          Bai ci amana ba bai yi shawagin banza ba,

                          Don ya san uban da yaz zana mai suna.

(Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa, Baban Dodo ba a Tamma da batun Baza)

Irin mutuntawa da karimci da tsaron lalura da Sarkin Gobir Amadu ke yi wa Makaɗa Ibrahim Narambaɗa, ta sanya tilas ya nuna duk duniya babu wanda yake ƙauna kamar Sarkin Gobir Amadu. Kamar yadda ya faɗa a cikin waɗannan ɗiyan waƙa.
JAGORA:             Amadu naf fiso,

ƳAN AMSHI:       Don waɗanga mazaje na yau bani son kowa,

JAGORA:             Faifa nissani,

JAGORA/YARA: Zamanin baban Rwahi ban san sulalla ba.

(Amadun Bubakar Gwarzon Yari Dodo na Alkali)

Yadai kammale da nuna cewa sarkin Gobir Amadu Bawa shi ne kowa da komi a ƙasar Isa Kwata kamar yadda ya faɗa a cikin wannan waƙa
JAGORA:         Amadu ganɗon Ƙasar Isa,

                         Ban Sarkin Ƙasar Isa,

                         Hakimman Ƙasar Isa,

                         Ƴan Sarkim Ƙasar Isah,

                         Dud da ɗiyan dud da ƙanne,

                         Ku bi shi ku bar kissa,

ƳAN AMSHI:  Wallahi in ganɗon yah hwashe baku ji daɗi,

                        Amadun Bubakar gwarzon yari dodo na Alƙali.

(Amadun Bubakar Gwarzon Yari Dodo na Alƙali)

Kammalawa
Wannan takardar ta yi tsokaci ne kan  matsayi da rawar da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taka wajen kyautata al'amuran sarauta da hanyoyin samunta, da na gudanar da ita a wasu fadojin ƙasar Hausa. Yayin gudanar da wannan bincike an saurari waƙoƙii fiye da  goma sha biyar don bibiya da zaƙulo fasahar makaɗa Ibrahim Narambaɗa da yadda ya fito da sarauta a Ƙasar Hausa da tanade-tanadenta.  A cikin waƙoƙin an kawo yadda ake  gudanar da mulkin  sarautar gargajiya  a cikin Hausawa .
Daga wasu waƙoƙin Narambaɗa  da aka yi nazari a cikin wannan Muƙala, an samu tarihin garuruwa da sunayen sarautar ƴaƴan  sarki da na barori da yanayin ƙasa da kuma wasu al'adun sarakuna kamar a ƙasar Isa da Zazzau. Binciken ya gano tabbas Narambaɗa ya zauni fada kuma ya ba wa fada gagarumar gudummawa. Daga cikin masarautun da Naramdaɗa ya ziyarta wanda binciken ya laluba sun haɗa da Dagacin Kuryad Dambo/ Sarkin Rwahin Kuryad Dambo, da Dagacin Jangeru/Sarkin Bazai da kuma Dagacin Shinkafi/Magajin Shinkafi, waɗanda a wancan lokaci duk yankunan Dagatai ne a Gundumar Isa da ke tsohuwar Masarautar Sakkwato (Saboda a halin yanzu dukkan su Gundumomin Hakimai ne a cikin Masarautar Shinkafi da ke Jahar Zamfara) Haka ma ya ziyarci Masarautar Zazzau da ke Jahar Kaduna, baya ga ƙoƙarin sa na fitar da sunan Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar sa, da Ƙasar Isa a idon duniya. Lallai ƙoƙari da fasaha irin ta makaɗa Ibrahim Narambaɗa ta kamanci killacewa da nazarta a matakan ilimi daban-daban.

Manazarta
Adamu, M.T (1997)  Asalin Hausawa da Harshensu , Kano: Ɗansarki Publishers.

Alhassan,H.da Wasu (1982) Zaman Hausawa.Islamic Publications Bureau, Zariya.

Bunza, A.M (2009)  Narambaɗa Lagos: Ibrash Islamic Publishers.

Bunza, A .M( 2019) "Hausa da Hausawa a Duniyar Ƙarni na Ishirin da Ɗaya (Amsa kiran  Majalisar Ɗinkin Duniya (UN)" ga Ranar Hausa ta Duniya  Majalisar Ɗinkin Duniya ta  Kebe a Ranar Litinin , 26 ga Ogusta, 2019, Jami'ar Bayero, Kano.
Birnin Magaji, I.M (2018) "Duniyar Makaɗan Fada Jiya da Yau." A Cikin  Taguwa  Multi-   Disciplinary Journal of Humanities Katsina: Umaru Musa
Dalhatu, U & Hassan, M. (2000)  Alhaji Shehu Idris CFR, The 18th Fulani Emir of Zazzau, Books Africana.
Ibrahim A. Tambuwal, Fascinating of The Emirates in Zamfara State (Unplished)
Gaya, A M. ( 2010) "Aladun sarauta a Ƙasar Hausa"  Takardar da aka gabatar don tattaunawa a Tsakanin Malamai da Ɗalibai Don Cikasa Wani Ɓangare na Neman Digiri na Uku a  Fannin Al'adun Hausa, a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero, Kano.
Gusau, S M (2002) "Saƙo a waƙoƙin Baka: Tsokaci Kan Turke da Rabe - Rabensa: a Cikin  Tsarin Takardun da aka gabatar a Babban Taron Ƙarawa Juna Ilimi na Biyar Kan Harshe da Adabi da Al'adun Hausa a Jami'ar Bayero, Kano.
Gusau, S M (2014) "Waƙa Baka Bahaushiya" Takardar da aka Gabatar a Jerin Laccoci na Bayan Samun Matsayin Farfesa a Jami'ar Bayero, Kano.
Gwarzo, ST( ND)  Asalin Hausawa daga Kaɗe-kaɗen su.

MUTANEN DA AKA TATTAUNA DA SU

Alh. Aliyu Mohammed Moyi (Ɗanmadamin Shinkafi), A Gidansa  da ke Shinkafi,  Ranar 12/6/2018.
Alh.Kabiru Isah (Ɗanmasanin Jangeru. A gidansa da ke Jangeru,  Ranar 18/08/2019
Tattaunawa da Malam Abdullahi Mohammed Birnin-Magaji (Dangulun). A gidansa da Birnin Magaji, ranar 21/08/19

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

MAKADA IBRAHIM NARAMBADA A FADOJIN KASAR HAUSA

No comments:

Post a Comment