0
SABANI GAME DA WASU KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA. SABANI GAME DA WASU KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA.

DAGA Nasir G Ahmad, ZUWA GA FARFESA MALUMFASHI: Kamar yadda aka ba da shawara, za mu so jin ra'ayin Malam, da ma sauran malamai kan s...

0
YUNKURIN 'YAN KASUWA WAJEN KAFA MULKIN DIMOKARADIYA A NIJERIYA. YUNKURIN 'YAN KASUWA WAJEN KAFA MULKIN DIMOKARADIYA A NIJERIYA.

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya +2348065025820 abuhidya3@gmail.com GABATARWA Wannan shi ne kundin kudiri na gamayyar tunanin kafar tur...

0
AN YI NADIN SABON SARKI A MASARAUTAR BANDE AN YI NADIN SABON SARKI A MASARAUTAR BANDE

Daga Rabi'u Muhammad Abu Hidaya Masarautar Bande wadda ta kasance masarauta mai dadadden tarihi cikin masarautun kasar Nijar ta samu ...

0
ALMARA KO GASKE ALMARA KO GASKE

ALMARA KO GASKE? Daga Rabi'u Muhammad Abu Hidaya Al'ada ta ce duk karshen mako na kan kai ziyar...

0
Sabon Injin Sarrafa Kankana Sabon Injin Sarrafa Kankana

SABANI GAME DA WASU KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA.

DAGA Nasir G Ahmad, ZUWA GA FARFESA
MALUMFASHI:
Kamar yadda aka ba da shawara, za mu so jin
ra'ayin Malam, da ma sauran malamai kan sabanin da ke akwai a halin
yanzu game da wani bangare
na ka'idojin rubutun Hausa, musamman 'yar
mallaka da zagagen aikatau na lokaci mai ci.
Yayin da mu daliban Hausa muka kankame abin da
ke rubuce cikin littafai dangane da wadannan
ka'idoji muke hadewa mu rubuta: GIDANMU, GUDUMMAWARMU, AYYUKANMU;
akwai ra'ayi na
biyu (Darikar Malam Sheme) da ke cewa raba 'yar
mallakar da kalmar abin da aka mallaka za a yi,
wato a rubuta, GIDAN MU, GUDUMMAWAR MU,
AYYUKAN MU.
Haka nan akwai masu raba zagagen aikatau na lokaci mai ci, wato suna
rubuta TA NA, MU NA, KA
NA, KI KE, YA KE, SU KE, ds., maimakon hade su da
mu muke yi.
*Ina jin zafin wannan sabani da ke akwai, domin
zai raba hankalin matasan marubuta, su rasa
wanne za su dauka, ko kuma abin ya zama "Hamiyya," wato ya zamo mutum
na zabar ra'ayi
kaza ne, saboda shi wane ke bi, don haka shi ne
dai dai.
*Mene ne mafita game da wannan sabani?
*** *** ***
Malumfashi Ibrahim: "Salamu alykum. Ina jin kamar an amsa tambayar
ma kafin ni na shigo. Aminu Garba Ingawa ya ce;
mafita a nan Malam ita ce: shehunan Malaman da
muke da su su yi zama na musamman don samar
mana mafita kan wannan matsalar. Hauwa Lawan
Maiturare kuma ta ce, shawarar Aminu ita ce abin bi, domin kuwa
ba'arin malamai tun daga
sakandare zuwa jami'o'i har yau suna koyarda
had'e mallaka ne, memakon raba su, amma idan
aka shirya zama aka buga masa stamfi sai ya zama
kar'ba'b'be bai d'aya, memakon wannan nabin
d'arik'ar wane, wance na bin ta wance. Ni na kara da cewa harkar
dabbaka ka'idojin
rubutu a kowane harshe na duniya a fagen nazarin
kimiyyar harshe yake shimfide, ba adabi ko al'ada
ko wani abu makamancinsa ba, duk kuwa da cewa
masana kimiyyar harshen ba sa aiwatar da komi sai
sun yi la'akari da adabi da al'adu da addini da sauran ire-iren su
wajen kai ga matsaya.
Ba wani abu ya sa haka ba, sai ganin cewa dukkan
ka'idojin suna tafiya da ginuwar nahawun harshe;
shi ya sa za ka ji ana maganar DOGUWA da
GAJERIYAR MALLAKA, da kuma TSIGALAU da
WAKILIN SUNA ko ZAGIN AIKATAU ko AZUZUWAN AIKATAU da LOKUTTAN HAUSA da
wasu da dama
irin su.
Wannan ne ya sa ko a fagen tsara rubutu da
ka'idojinsa ake tattaruwa da mutane mabambanta
domin a samar da matsaya. Duk wata matsala da a
yanzu ake fama da ita ta rarrabuwa da dagewa a kan wani abin da ake
gani shi ne daidai, to an bar
tsayayyar ka'ida ne an shigo da son rai ko wani
abu makamancin haka.
Alal misali, a duniyar rubutun Hausa yanzu za ka ga
ana samun takaddama kan: Ba da za a rubuta ko
Bada. Akan zo ne za a ce ko A kan zo. Bayar da ne daidai ko Bayarda.
Namu, naku, nasu ne gaskiya
ko na mu, na ku, na su. Wane ne daidai ko Wanene.
Mene ne ko kuwa Menene ko Minene, Allah ne ko
kuwa allah Allah ya ce ko kuwa Allah Ya ce.
Akwai misalai da yawan gaske da ake ta fama da
su tsakanin masana da manazarta da dalibai. A nawa tunanin ba abin da
ya jawo haka face rashin
bin diddigin yadda lamurra suke a nazarce, da
kuma rashin ilmin Rubutun Ka'idojin Rubutu da
yawancinmu ba mu da shi, sa'annan uwa-uba
rashin takarkarewa wajen koyar da wadannan
ka'idoji a makarantun Firamare da Sakandare da Kwalejoji da Jami'o'inmu.
Ba a ba wannan darasi muhimmanci ba, shi ya sa
muke wa harkar ka'idojin rubutu labarin cin
kanzon kurege. Abin da na sani shi ne, a yanzu
mutum daya ko biyu ko uku ko ma fiye ba su da
ikon canza ka'idojin da aka amince da su tsakanin masana da goyon bayan hukuma.
Muna da dama mu ki amincewa da dukkan abin da
aka taru aka amince kan sa, a matsayin 'yan tsiraru,
amma a kullum tarbacen taron masana ake aiki da
shi ba na 'yan tsirarun ba.
Saboda haka a halin yanzu MALLAKA a rubutun HAUSA a hade take, kamar
yadda malam Nasir G
Ahmad ya nuna: GIDANMU, GUDUMMAWARMU,
AYYUKANMU ake rubutawa a gajera, alhali a
doguwa GIDAN NAMU, GUDUMMAWAR TAMU,
AYYUKAN NAMU. Haka kuma TANA, MUNA, KANA,
KIKE, YAKE, SUKE, da sauransu ake rubutawa, maimakon rabawa da wasu ke yi.
Wannan ita ce tsayayya, amsassa kuma karbabbar
ka'ida. Sai in nan gaba an sake yin wani taro an
canza wadannan ka'idoji, sa'annan za mu iya
amincewa da sabon alkawari."
*** *** *** Ibrahim Sheme: "RA'AYIN "TSIRARU" KAN RABA MALLAKA.
Oh, ikon Allah! Malam ya ce: "Abin da na sani shi ne,
a yanzu mutum daya ko biyu ko uku ko ma fiye ba
su da ikon canza ka'idojin da aka amince da su
tsakanin masana da goyon bayan hukuma. Muna
da dama mu ki amincewa da dukkan abin da aka taru aka amince kan sa, a
matsayin 'yan tsiraru,
amma a kullum tarbacen taron masana ake aiki da
shi ba na 'yan tsirarun ba."
Amma na yi mamakin yadda Farfesa ya gina
kafewar sa a kan AL'ADA, wato kunne ya girmi
kaka. Ban da nuna mana cewa "haka ake yi" ko "haka mu ka gani," babu
wata kwakkwarar hujja
da ya kawo mana mai nuna dalilin da ya sa za mu
hade mallaka.
Malam bai kawo mana sabon abu ba; ai da ma mun
san cewa an ce "haka ake yi." Abin da mu ke so shi
ne: me ya sa? Don me za a yi hakan? Bisa wace hujja?
Ni, da yawa an san ni da cewa ina daga cikin tsiraru
(ko ma jagoran su) masu yekuwar lallai sai an raba
mallaka. Kuma tuni na kawo kwararan hujjoji na a
wannan dandalin na DM (koda yake na ga babu
wanda ya tuno da su, ciki kuwa har da shi Mal. Nasir).
Ni ina ganin maganar da Farfesa ya yi ta farko kafin
ya yanke hukuncin sa cikin garaje ita ce ya kamata
ya zauna a kai, wato inda ya ce:
"Ina jin kamar an amsa tambayar ma kafin ni na
shigo. Aminu Garba Ingawa ya ce; mafita a nan Malam ita ce: shehunan
Malaman da muke da su su
yi zama na musamman don samar mana mafita kan
wannan matsalar. Hauwa Lawan Maiturare kuma ta
ce, shawarar Aminu ita ce abin bi, domin kuwa
ba'arin malamai tun daga sakandare zuwa jami'o'i
har yau suna koyarda had'e mallaka ne, memakon raba su, amma idan aka
shirya zama aka buga
masa stamfi sai ya zama kar'ba'b'be bai d'aya
memakon wannan nabin d'arik'ar wane wance na
bin ta wance."
Wannan na nuna cewa har yanzu ba a yanke
hukunci kan batun nan na mallaka ba. Ba mallaka kurum ba, har ma wasu
kalmomin masu tarin
yawa. Farfesa Malumfashi ya yanke nasa a nan, ba
tare da ya kawo mana wata madogara da za mu
zauna a kai ba.
Sannan batun nan ba fa na "son rai" ba ne ko
"rashin ilmi" kamar yadda Malam ya nuna. Batu ne na nazari da bincike
inda ake kafa hujja. Ni kam ba
ni da PhD ko farfesanci, to amma ba shakka zan ja
da ko waye da zai ce ba ni da ilmi ko ba ni da sani
kan nahawu. Na karanta shi matukar karantawa, a
cikin aji (ni dalibin Farfesa Sani Zaria ne), na mallaki
littattafan nahawu, na fahimci dukkan inda duk wani masani mai cewa a
hade mallaka ya dosa.
Tuni na kasance daya daga cikin marubutan Hausa
da su ka san harshen Hausa da yadda ake rubuta
shi. Wannan ba cika baki ba ne, dahir ne.
A da can, ina bin waccan darikar ta masu cewa a
hade kalma. Littattafai na na farko-farko, irin su "Kifin Rijiya"
(1991) da bugun farko na
"'Yartsana" (2003) da duk wasu rubuce-rubuce da
na yi lokacin ina aikin jaridar Hausa (Nasiha, Rana,
Gaskiya Ta Fi Kwabo) a bisa waccan darikar na yi
su, to amma tuni kai na ya waye, na gane cewa
masana sun dulmiyar da mu cikin wannan dokar ba tare da sun ba mu dalilin su ba.
Daga nan na zama "tsiraru" ko "dan tawaye" - har
na ke jagorantar su. A cikin farin sani na sauya
sheka, ba wai duhun sani ba.
Na so a ce Malam Malumfashi ya kawo mana hujja,
misali: ga dalilin da ya sa ake hadewa, ba wai kawai a ce taron masana
ne su ka ce a yi hakan ba. Ai
mun san me su ka ce tun tuni.
Da masanan su ka taru, me su ka gindaya a
matsayin hujja? Idan an shanya mana hujjar su a
faifai, to sai mu dube ta mu gani: karbabbiya ce ko
a'a? Dalili shi ne: ilmi kogi ne. Malam ya fi ni sanin hakan.
Ina so ni da Farfesa mu zauna in jera masa hujjoji
na daki-daki (idan na kai minzalin zama da farfesa).
Na tabbatar a matsayin sa na mutum wanda ya
dade da kin karbar abu ba tare da ya ga hujja ba,
zai amince da nawa uzirin, kuma ya dawo cikin mu "tsiraru".
*** *** ***
Nasir G Ahmad:
"Allah ya ja mana da Malam (Sheme)! Ina sha'awar
irin wannan dagewa taka, amma fa ni ba zan bi
wannan sabuwar darika ba. Ga Farfesa ka fuskantar da bayananka. Duk da
haka ga ra'ayin
almajirinku:
Ka yi watsi da ijma'i, wato haduwar ra'ayin
manazarta kan hade gajerar mallaka, wannan
ra'ayinka ne. Amma ijma'i ya fi karfin a ce ba abin
dogaro ba ne. A musulunce ma, shi ne mataki na uku wajen samar da
hukunce-hukuncen shari'a.
Wanda ya bijire wa ijma'i, ya zama mu'utazili ke nan,
wato dan tawaye, kamar yadda ka ce ka yi wa
ra'ayin manazartan Hausa.
Kamar dai yadda na taba fada, zan yi amfani da
abin da nake da madogara kansa a hannuna ne. Wanda aka yi
wallafe-wallafe kansa, ake kuma kan
yi. Aka amince da amfani da shi, da koyar da shi a
dukkan matakan ilimi.
Kamar yadda kuma na taba fada, ni da nake
malamin makaranta mai koyar da dalibai Hausa da
ka'idojin rubuta ta, da wace hujja zan dogara in na ce zan sauya
alkibla rana tsaka, na nemi koyar da
dalibaina ka'idojin rubutun Hausa na sabuwar
darikar Shemiyya, alhali ga abin da ke cikin littafan
manhaja da aka umarce ni na yi amfani da su? Ba
ma ta fuskar aiki ba, ni a karan kaina, ba zan iya ba
da hujjojin da Malam ke rike da su a matsayin madogarata ba, domin ni
kaina ba su gamshe ni ba
(ta yiwu saboda karamin sanina).
Kamar yadda kuma na taba fada, ya kamata Malam
(Sheme) ya fito da wata wallafa ta littafi, ko a
matsayin makala ga irin taron masana Hausa da
akan yi, inda zai fito da wannan sabon ra'ayi nasa ga 'yan uwansa
manyan masana don tattaunawa.
Idan aka amince, aka yi ittifakin yin amfani da su,
mu dalibai ba abin da ke kanmu sai run gumar su
da fara dabbaka su a rubuce-rubucenmu. In ba
haka ba, to muna nan bisa darikar 'yan mazan jiya,
babu gudu babu ja da baya." *** *** ***
Malumfashi Ibrahim:
"Alhamdu lillah, na karanta jawabin Ibrahim
Sheme, amma kamar ya yi mani mummunar
fahimta, 'son rai' da 'rashin ilmin' da na yi magana
ba da shi nake ba, da dukkanmu nake da ke da matsala da ka'idojin
rubutun Hausa. Ba wai shi
kadai ba ne ke cikin 'tsirarun' da na yi magana, ni
ma ina ciki. Kuma na sha korafi game da haka a
wuraren tarurrukan ilimi da kara wa juna sani.
Na dade ban yarda a raba /ba da/, misali /na ba da
kudi/ ni fi yarda da a hade su, domin a tawa fahimtar /bada/
cikakkiyar kalma ce, amma in
muka raba, / ba/ na matsayinta daban da /da/ ke
nan, wato dukkansu za su iya zama da gindinsu su
bada ma'ana.
Na kuma kafa hujja da abu guda, idan muka koma
ga ita kalmar /ba/ za a ga ta samo asali ne daga / bayar/, wato misali
/na bayar da/. A bisa ka'idar
nahawu, duk inda aka yanke wani abu daga wata
kalma, abin da ke bin wannan kalmar hade shi ake
da wanda ya biyo masa, ya koma kalma guda mai
ma'ana guda. Ke nan /bayar da/ idan ka ka debe /
yar/ zai zama /ba/, ita kuma /da/ da ke biye sai ta koma ta
saje da /ba/ ya zama / bada/. Wannan shi aka koya
mana a nahawun, amma daga baya masu nazarin
nahawu suka ce, ai nan ba kalmomi yau da kullum
ba ne, kalmomin fannu ne na aikatau, kuma tun
azal bayar/ da /ba/ kalmomi biyu masu zaman kansu , wato kana iya cewa
/bayar da/ ko kuma /
ba da/, domin ita/bayar/ da /ba/ duk abu daya ne
a kalmomin fannun aikatau, aji ne kurum ya
bambanta su, ba wai gutsire / yar/ aka yi ba, ke
nan dole a bar su a rabe. Har yau a rubuce-
rubucena raba su nake yi, sai in na tuna da cewa ai an yi ittifaki,
kan rabawa sai na
gyara na koma ga wanda aka amince da shi. Ko a
aji, nakan bayyana wa dalibai rashin amincewa ta
da wasu ka'idoji da yawa, amma in mun gama
tattaunawa, tambayar da aka yi man ita ce, 'to
malam wane za mu dauka mu yi aiki da shi,' ni kuma a kullum nakan ce,
wanda aka amince da shi,
ko da kuwa bisa kuskure ne.
Saboda me? Idan aka bar harshe yana gudana bisa
son rai ko rashin sanin tushen abu, yana iya jawo
rugujewar abin da aka riga aka gina, ta yadda za a
zo a kare ba wan ba kanen. Sheme da duk wani mai irin wannan ra'ayi nasa ba
za mu taba samun galaba ba sai an kuma yin wani
taro na bitar ka'idojin, mun je wurin an kwafsa da
mu, ba mun bayar da hujjojinmu, an karba, an
buga, an watsa ga sauran al'umma, ana kuma
karantar da su don na baya su sami abin karaswa. Ba yadda za ka yi
jayayya da abin da taron
daidaitawa ya zo da su, yin haka barna zai jawo ga
harshen."

YUNKURIN 'YAN KASUWA WAJEN KAFA MULKIN DIMOKARADIYA A NIJERIYA.

Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya
+2348065025820
abuhidya3@gmail.com

GABATARWA
Wannan shi ne kundin kudiri na gamayyar tunanin kafar turakun siyasar
'yan kasuwa a jihar Kano wanda ya dunkule yadda za a gabatar da tsari
da manufofin kudirin wannan tafiya bisa aminci da yarda.

TARIHIN KASUWANCI A KANO DA ZUWAN 'YAN KASUWA LARABAWA DA WASUN SU.
Kafin bayyana waccan tsari da aka fada a sama yana da kyau a dan dubi
tarihin kasuwan a wannan babbar jiha ta Kano. A shekara ta 1453
miladiyya, a zamanin Sarkin Kano Yakubu dan Abdullahi Barja, Sarkin
Kano na goma sha shida(16)a mulkin kanawa, wadansu Larabawa mutanen
kasar Gadamus masu fatauci, suka zo daga Turabulus(Libya), suka sauka
a birnin Kano, su ne Larabawan da suka fara zuwa Kano. Da saukar
wadannan fataken Larabawa, suka je wurin sarkin Kano Malam Yakubu, a
jujin 'Yan Labu, a lokacin ba a gina gidan sarautar Kano na yanzu ba,
Shamakin Kano Korau, yana shigar da su gaban sarki, suka ce da Sarki a
cikin harshen Larabci su fatake ne, suna so su zauna a Kano, domin su
yi ciniki.

A wannan Lokaci kuwa, limamin Kano Muhammadu Hashimu, shi ne yake
fassara wa Sarkin Kano abin da wadannan Larabawa suke fada cikin
harshen Hausa. Daga nan Sarkin Kano Yakubu ya yi farin ciki kwarai da
gaske da wadannan larabawa, sannan yace da Shamakin Kano, ya kai su
sararin nan na yamma da Unguwar Garke wato Dandali, su yi gidaje su
zauna a can. Saboda wadannan Larabawa suna da jar fata, sai mutane
suka sa musu suna Turawa. Ya yin da wadannan Fatake Larabawa suka yi
gidaje a wannan wuri suka zazzauna, sai Kanawa suka sa wa wannan
unguwa suna Dandalin Turawa, dalilin sunan Dandalin Turawa ta yanzu ke
nan, tun shekarar 553.

A waccan zamani, sarkin Kano yana da shekara daya a kan gadon sarautar
Kano. A zamaninsa Kano ta karu da arziki mai yawa da kuma garuruwa
ko'ina, a kowane gari, akwai makarantu na Al'kur'ani Mai Girma Har Ila
yau, kuma a kowane gari, akwai karofi da Mabugai da Masaku da Makera
da Dukawa, (Wato wurin Dukanci) da majema,(Wato wurin yin jima) da
kuma masassakan turmi da akusa, ko'ina sun yawaita a kasar Kano.
Tun daga waccan zamani Larabawa suka ci gaba da zuwa Kano, kamar
Yamalawa(Mutanen Yaman) da Larabawan Tunis, amma kowane da nau'in
kasuwancinsa. Su Larabawan Libiya duk kayan da suke sayarwa kayan
alatu ne(Suturu da kayan kamshi da kayan zaki).
Da wahala a ce ga lokacin asalin samuwar Kasuwanci a Kano. A zamanin
da, mutanen da ke Kano ba su san wata harka ta Kasuwanci ba, sai dai
sun fi mayar da hankali a kan aikin gona da aikin lambu. Amma an sani
cewa sana'o'inmu na Hausa wato sana'o'in gargajiya kamar su rini da
jima da kira da saka da sauransu, su suka haifar da ainihin samuwar
kasuwanci, domin kuwa a wancan zamanin mutum zai yi abu ya sayar don
amfanin jama'ar kasarsa, ko da yake lokacin da ba a fara amfani da
kudi a Kano ba, ana yin amfani da wata hanya ta ba ni gishiri in baka
manda (cinikin furfure ) don cinikayya.

Daga baya ne lokacin da fatake Larabawa ko Asbinawa da Agalawa suka zo
Kano, Kasuwanci ya fara Kankama. Haka kuma lokacin fataucin Kasar
Hausa, wato lokacin da abubuwan zirga-zirga na zamani ba su iso kano
ba, za mu iya cewa Kasuwanci ya samu kwarai a Kano, dangane da tawayen
da fatake suka yi wa kasar Katsina, suka dawo kasar Kano da sha'anin
Kasuwanci, kamar yadda aka fada a cikin littafi mai suna (Kano Civil
War and the Britshi Over Rule 1882-1940) na Muhammad F.A wannan ya
kawo mu har lokacin zuwan Turawa, wato lokacin da suka zo mana da
farin kudi a shekarar 1930, har aka fara amfani da shi a harkar
cinikayya ta Kano. Wannan ya sa kasuwanci ya dada samuwa kwarai a
Kano, ta hanyar bude ido da abin da Turawa suka zo da shi a sha'anin
kasuwanci, wanda ya kai jama'ar Kano suka san mene ne kasuwancin ma
kansa, har su tafiyar da sha'anin kasuwanci kansa, ba tare da wasu
Turawa sun ja musu gaba ba. Samuwar wannan kasuwanci a Kano ya fito
da Kano a idanun duniya baki daya, wanda har ta kai ga yi mata kirari
kamar haka, "Kano tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika".

TASIRIN 'YAN KASUWA A NIJERIYA
Idan mun lura za mu ga ne cewa yan kasuwa suna da tasiri kwarai da
gaske a jihohin Nijeriya da kasa baki daya, musamman jihar Kano wadda
ake yi wa kirari da cibiyar kasuwancin afrika. Kuma manyan yan kasuwar
da suke baiwa kasa kayan masarufi da al'muran yau da kullum daga Kano
suke, dukkan wani kasuwanci a yau baya samun karbuwa matukar babu shi
a jihar Kano, duba da bayanan da suka gabata a baya za mu yarda da
cewa Kano ta zama tumbin giwa komai ka nema akwai a ciki.
'Yan kasuwa masu sha'awar kasuwa daga sassa daban-daban na duniya a
kullum shiga jihar Kano suke don tallata hajarsu, a saboda haka muna
iya cewa kano ta 'yan kasuwa ce.

YUNKURIN 'YAN KASUWA WAJEN KAFA MULKIN DIMOKARADIYA A NIJERIYA.
A yau idan ka raba mutanen Nijeriya kaso goma to kaso shida duka 'yan
kasuwa ne, ragowar kashin ne za a rabawa ma'aikatan gwamnati da sauran
sassa. Bisa kididdiga ko bincike da mu ka yi mun samu nasarar gano a
duk unguwa a Nijeriya cikin kowane gida matukar mutanen cikin sun
haura biyar sai ka samu dan kasuwa a ciki, kama daga masu sana'ar
sayar da Kosai, kitso, mai, Kanti, Shayi, shagunan kayan gyara da na
masarufi da suturu da sauransu.
Har ila yau wadannan mutane su ne suke tururuwa lokacin gudanar da har
zabe don zabar shugabanni 'yan boko wadanda za su jagorance su don
kawo musu ci gaba a har kasuwancinsu da bunkasarsa amma a wasu lokaci
harkar su ba ta cimma ruwa, wani sa'in ma sai a biyo su da neman su
biya haraji bayan ba su samu ribar zaben da suka yi ba, haka kuma
lokacin zabe wadannan yan siyasa za su sake wanke rigunansu su shigo
cikin al'ummar da ta zabe su wadanda mafi akasarinsu 'yan kasuwa ne su
ce a kara zabarsu karo na gaba, haka dai za su kara komawa bisa
matsayinsu ba tare da kawo wani babban ci gaba ba a harkar kasuwancin,
wanda kuma shi ne yake rike da kasar ma baki daya.

KAFA TSARIN SHUGABANCIN 'YAN KASUWA NA JIHA DA KANANAN HUKUMOMI.
A saboda wadancan dalilai na rashin samun tagomashin ribar romon
dimokaradiya da 'yan kasuwa ba sa yi ya sanya suka ga dacewar su kafa
gwamnatin da za su ji koken junansu da na sauran al'umma don ci gaban
kasuwanci da masana'antu a jiha da kasa baki daya.

Ga Yadda tsarin zai kasance
idan har kowani mai karamin sana'a zai iya aje wani abu daga cikin
abin da yake samu don bunkasar kasuwancinsa da goyon bayan wannan
tafiya, misali a ce ko wani mai sana'a a jihar kano zai a je Naira
dari(100) a wata don bayarwa a yankin da yake a matakin karamar hukuma
zuwa jiha to za a samu adadin abin ake so na kafa gwamnati da sauran
hidindimun da za su sanya kowa ya fahimci cewa "Daminar bana ta dara
ta bara"
don haka a wannan tsari za a kafa ofishi da zai kula da adadin 'yan
kasuwar da suke a kowacce karamar hukuma kuma za a yi wa kowa rijista
wacce za ta game duka yan kasuwar jihar Kano a inuwa daya yadda ko
wani tsunsu zai yi kukan gidansu.
Ta yadda za a zama tsintsiya madaurinki daya.

MATAKIN DA ZA A SANAR DA TSARIN
1-Za a yi amfani da kafafen yada labarai don sanar da wannan yunkuri.
2- Za a radawa tsarin suna yadda amonsa zai mamaye jiha da kasa baki daya.
3- Za a kafa tsarin shugabanci tun daga jiha har kananan hukumomi.
4-A karkashin wannan tsari za a fitar da shugabanin ta za su yi
takarar kujerun da ake bukata don biyan bukatar al'ummar kasa.

KARSHE
Ana fata wannan tsari ya zama kawo ci gaban da zai mayar da kasar
Nijeriya sama da kasashen da ake ganin sun taso tare amma sun fita ci
gaba.


On 11/23/17, Rabiu Muhammad Abu Hidaya <abuhidya3@gmail.com> wrote:
> Daga
> Rabi'u Muhammad Abu Hidaya Masarautar Bande wadda ta kasance masarauta
> mai dadadden tarihi cikin masarautun kasar Nijar ta
> samu sabon sarki bayan rasuwar tsohon sarkin
> garin,
> sarkin dai mai suna Abubakar Yahaya Lushe ya
> kasance shi ne sarki na bakwai a jerin sarakunan da suka mulki kasar
> ya kuma matashi ne jami'i a
> aikin Soja mai mukamin Kanal wanda ya bar aikin
> sojan don maye gurbin mahaifinsa domin shi
> mutum ne mai son ci gaban al'ummar kasarsa, ya
> samu zama sarkin ne bayan da masu ruwa da tsaki
> suka zabe shi a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa da ya rasu kwanaki
> kadan baya, wannan zabi da
> aka yi masa dai ya faranta ran mafi yawa daga cikin
> jama'ar garin Bande da na masarautar, inda
> dukkansu su ka yi maraba da shi, domin sun
> tabbatar da cewa sabon sarkin na su yana da halin
> girma da dattako irin na mahaifinsa. A lokacin da sarkin yake jawabi
> game da kudirin
> da zai gabatar a masarautar da ya gada daga
> mahaifinsa ya ce "zai fi mayar da hankali ne game
> da abin ya shafi Ilimi a kasar da kuma harkar
> kasuwanci tare da wasannin gargajiya wadanda ya
> ce an yi musu nisa a sauran gurare. Ya kuma ce zai karfafa alaka da
> sauran masarautun
> da suke sauran kasashen da suke makotaka da
> masarautarsa"
> har ila yau da yake ci gaba da jawabi ya ce
> masarautarsa tana maraba da duk wani da yake da
> son ci gaban al'umma kuma zai yi hadin gwiwa da duk wanda da yake da
> harkar kasuwanci, haka
> kuma yace game da abin da ya shafi noma kiwo
> gami da kiwon lafiya nan ma ba za a bar kasar
> bande a baya ba, lallai a karkashin masarautarsa za
> a samu ci gaba sosai, babban burin wannan sabon
> sarki dai ya ce bai wuce ya samu hadin kan jama'ar kasarsa ba sannan
> yana fatan a ce ya fi mahaifinsa
> kokari.
> A nasa jawabin wani malamin Makaranta kuma na
> kusa da masarautar ya ce" lallai suna alfahari da
> wannan sarki wanda suke ganinsa tamkar
> mahaifinsa domin mahaifinsa ya zauna da kowa lafiya da ya kuma kaunaci
> talakawansa tamkar a
> 'yayan cikinsa shi mutum ne mai son talakawan
> kasarsa, kuma ya tabbatar da cewa wannan sarki
> zai kawo ma kasar Bande gagarumin ci gaba.
> A karshe mafi yawa daga cikin jama'ar kasar suna
> ta tururuwa domin yin mubaya'a ga sabon sarkin na su Abubakar Yahaya
> Lushe har ila yau kuma
> mutane da dama suna ta fatan ganin ranar da za a
> yi bikin ba shi sandar mulki domin su nuna masa
> soyayya da kauna.
>
> On 11/23/17, Rabiu Muhammad Abu Hidaya <abuhidya3@gmail.com> wrote:
>> ALMARA KO GASKE?
>>
>> Daga
>> Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
>>
>>
>> Al'ada ta ce duk karshen mako na kan kai ziyara garinmu, domin gaishe
>> da iyaye, 'yan'uwa da
>> abokan arziki.
>> A garin akwai wata kasuwa da
>> ta ke ci duk ranar juma'a, kasancewata mutum ne mai son shan fura, don
>> haka duk ranar kasuwar garin na kan shiga kasuwar domin sayan fura,
>> akwai wata budurwar bafulatana, mai suna Hajjo, Hajjo tana da kirki
>> kwarai don haka ne ma, babu furar wadda da nake sha kaf
>> kasuwar sai ta ta, mun saba da Hajjo matukar sabo, domin idan na je
>> gurinta sam ba ta iya sakewa
>> saboda tsananin jin kunya.
>> So! shu'umi ya kan shiga zuciya ba tare da ya yi sallama ba. A kwana a
>> tashi sai na fara jin son Hajjo mai fura ya shiga zuciyata, domin har
>> ta kai idan na dawo kano bana iya sakewa in yi ayyukana yadda ya
>> kamata, haka zan ta fatan karshen mako ya yi na je garin, ban samu
>> nutsuwa ba sai da na bayyanawa Hajjo abin da yake raina, na ci sa'a
>> domin a karon farko Hajjo ta amince da ni a matsayin saurayinta.
>> Watarana ina kasuwa a cikin rumfar da Hajjo take sayar da fura muna
>> hira ina shan furar da ta dama min, sai nake
>> tambayarta Hajjo ya kamata a ce nasan gidanku
>> domin in zo mu yi maganar aure, shiru ta yi na 'yan
>> mintoci gami da aje ludayin furar da ke hannunta tare da sunkuyar da
>> kai kasa na dan wani lokaci, kana daga bisani sai ta ja wani dogon
>> numfashi! Gami da kallon wata yarinya da ke zaune a gefenta bisa wani
>> dutse tana sayar da mandako. Ko ba ki son in zo gidan ku ne? A'a kawai
>> dai ina wani dan tunani ne. Wai don Allah da gaske ka ke
>> kana so na?
>> (Dariya) ina sonki mana Hajjo. Amma me ya sa kika
>> min wannan tambayar?
>> Ai gani na yi kai dan birni
>> ne, me za ka yi da 'yar kauye iri na?Dariya na sake yi sannan na ce
>> mata kar ki damu Hajjo
>> ko ma ya ki ke ina sonki a haka kuma aurenki zan yi.
>> A karshe Hajjo ta kwatanta mini
>> rugar su, ranar Asabar ranar ce mu ka yi da Hajjo zan je rugar su.
>> Da misalin hudu da rabi na
>> yammacin ranar Asabar na shiga rugar su Hajjo, ban sha wata wahala ba
>> wajen neman gidansu ba, domin rugar ta su ba ta da girma sosai. Hajjo
>> tana gani na ta yi ta murna kamar ta rungume ni don tsananin jin dadi,
>> kusan duka mutanen gidan su Hajjo sai da suka zo muka gaisa tare da
>> nuna farin cikinsu da gani na.
>> Fura da nono mai kyau Hajjo ta kawo min, na kuma ji dadin furar
>> gaskiya kauye akwai dadi musamman rugagen fulani ba ruwansu ga yanayi
>> mai dadi ga kuma nono mai kyau ka sha iya shanka ba ka da damuwa.
>> Abu ka ga garinmu kauye ko?
>> Hajjo kenan, ai garin nan naku ina ganin bayan mun yi aure a nan za mu
>> zauna saboda ya min kyau.
>> Cikin jin dadi Hajjo ta rufe fuska da hannayenta tana murmushi alamun
>> jin kunya, kana ta ce haba dai ashe za ka iya zaman kauye?
>> Bayan na hadiye wani gayan fura tare lashe baki kai da ka gan ni kasan
>> ina jin dadin furar da nake sha, sai na bata amsa na ce ban da abin ki
>> Hajjo ai ko shugaban kasa zai so zama a nan ko don shan fura da nonon
>> da ke rugar nan.
>> Wannan karon dariya Hajjo ta yi har da kyakyatawa kana ta ce" gaskiya
>> Abu furar nan ta kama ka da kyau har da santi haka.
>> A ranar mun yi hira sosai kuma hira mai dadi da ita, sannan a karshe
>> mu ka yi bankwana tare da alkawarin kwanaki kadan masu zuwa zan sake
>> dawowa.
>>
>> KARO NA BIYU A RUGAR SU HAJJO
>> Daga ina ka ke?
>> Wa kake nema?
>> Yanzu ba mu da Hajjo a wannan gidan, Hajjonmu yau kimanin shekarunta
>> bakwai da rasuwa. Abin da aka shaida min kenan
>> bayan na koma rugar su Hajjo a karo na biyu.
>> Ikon Allah sai kallo, abin da ya fi bani mamaki shi ne duk mutanen
>> gidan su Hajjo babu wanda ya nuna ya ta6a ganina balle
>> mai kamata, na yi musu bayanin kamanin Hajjo sun tabbatar min ita ce
>> hasalima sun kawo min
>> hotunanta inda ni ma na tabbatar musu cewa ita din ce.
>> Cikin tsananin mamaki da kaduwa haka na baro rugar su Hajjo duk jiki
>> na ya yi sanyi.
>> Tun daga wannan ranar idanuna ba su sake tozali
>> da Hajjo ba balle mai kamarta. Kuma har yanzu zuciyata na cike da
>> matsananciyar kaunarta...
>>
>

AN YI NADIN SABON SARKI A MASARAUTAR BANDE

Daga
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya Masarautar Bande wadda ta kasance masarauta
mai dadadden tarihi cikin masarautun kasar Nijar ta
samu sabon sarki bayan rasuwar tsohon sarkin
garin,
sarkin dai mai suna Abubakar Yahaya Lushe ya
kasance shi ne sarki na bakwai a jerin sarakunan da suka mulki kasar
ya kuma matashi ne jami'i a
aikin Soja mai mukamin Kanal wanda ya bar aikin
sojan don maye gurbin mahaifinsa domin shi
mutum ne mai son ci gaban al'ummar kasarsa, ya
samu zama sarkin ne bayan da masu ruwa da tsaki
suka zabe shi a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa da ya rasu kwanaki
kadan baya, wannan zabi da
aka yi masa dai ya faranta ran mafi yawa daga cikin
jama'ar garin Bande da na masarautar, inda
dukkansu su ka yi maraba da shi, domin sun
tabbatar da cewa sabon sarkin na su yana da halin
girma da dattako irin na mahaifinsa. A lokacin da sarkin yake jawabi
game da kudirin
da zai gabatar a masarautar da ya gada daga
mahaifinsa ya ce "zai fi mayar da hankali ne game
da abin ya shafi Ilimi a kasar da kuma harkar
kasuwanci tare da wasannin gargajiya wadanda ya
ce an yi musu nisa a sauran gurare. Ya kuma ce zai karfafa alaka da
sauran masarautun
da suke sauran kasashen da suke makotaka da
masarautarsa"
har ila yau da yake ci gaba da jawabi ya ce
masarautarsa tana maraba da duk wani da yake da
son ci gaban al'umma kuma zai yi hadin gwiwa da duk wanda da yake da
harkar kasuwanci, haka
kuma yace game da abin da ya shafi noma kiwo
gami da kiwon lafiya nan ma ba za a bar kasar
bande a baya ba, lallai a karkashin masarautarsa za
a samu ci gaba sosai, babban burin wannan sabon
sarki dai ya ce bai wuce ya samu hadin kan jama'ar kasarsa ba sannan
yana fatan a ce ya fi mahaifinsa
kokari.
A nasa jawabin wani malamin Makaranta kuma na
kusa da masarautar ya ce" lallai suna alfahari da
wannan sarki wanda suke ganinsa tamkar
mahaifinsa domin mahaifinsa ya zauna da kowa lafiya da ya kuma kaunaci
talakawansa tamkar a
'yayan cikinsa shi mutum ne mai son talakawan
kasarsa, kuma ya tabbatar da cewa wannan sarki
zai kawo ma kasar Bande gagarumin ci gaba.
A karshe mafi yawa daga cikin jama'ar kasar suna
ta tururuwa domin yin mubaya'a ga sabon sarkin na su Abubakar Yahaya
Lushe har ila yau kuma
mutane da dama suna ta fatan ganin ranar da za a
yi bikin ba shi sandar mulki domin su nuna masa
soyayya da kauna.

On 11/23/17, Rabiu Muhammad Abu Hidaya <abuhidya3@gmail.com> wrote:
> ALMARA KO GASKE?
>
> Daga
> Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
>
>
> Al'ada ta ce duk karshen mako na kan kai ziyara garinmu, domin gaishe
> da iyaye, 'yan'uwa da
> abokan arziki.
> A garin akwai wata kasuwa da
> ta ke ci duk ranar juma'a, kasancewata mutum ne mai son shan fura, don
> haka duk ranar kasuwar garin na kan shiga kasuwar domin sayan fura,
> akwai wata budurwar bafulatana, mai suna Hajjo, Hajjo tana da kirki
> kwarai don haka ne ma, babu furar wadda da nake sha kaf
> kasuwar sai ta ta, mun saba da Hajjo matukar sabo, domin idan na je
> gurinta sam ba ta iya sakewa
> saboda tsananin jin kunya.
> So! shu'umi ya kan shiga zuciya ba tare da ya yi sallama ba. A kwana a
> tashi sai na fara jin son Hajjo mai fura ya shiga zuciyata, domin har
> ta kai idan na dawo kano bana iya sakewa in yi ayyukana yadda ya
> kamata, haka zan ta fatan karshen mako ya yi na je garin, ban samu
> nutsuwa ba sai da na bayyanawa Hajjo abin da yake raina, na ci sa'a
> domin a karon farko Hajjo ta amince da ni a matsayin saurayinta.
> Watarana ina kasuwa a cikin rumfar da Hajjo take sayar da fura muna
> hira ina shan furar da ta dama min, sai nake
> tambayarta Hajjo ya kamata a ce nasan gidanku
> domin in zo mu yi maganar aure, shiru ta yi na 'yan
> mintoci gami da aje ludayin furar da ke hannunta tare da sunkuyar da
> kai kasa na dan wani lokaci, kana daga bisani sai ta ja wani dogon
> numfashi! Gami da kallon wata yarinya da ke zaune a gefenta bisa wani
> dutse tana sayar da mandako. Ko ba ki son in zo gidan ku ne? A'a kawai
> dai ina wani dan tunani ne. Wai don Allah da gaske ka ke
> kana so na?
> (Dariya) ina sonki mana Hajjo. Amma me ya sa kika
> min wannan tambayar?
> Ai gani na yi kai dan birni
> ne, me za ka yi da 'yar kauye iri na?Dariya na sake yi sannan na ce
> mata kar ki damu Hajjo
> ko ma ya ki ke ina sonki a haka kuma aurenki zan yi.
> A karshe Hajjo ta kwatanta mini
> rugar su, ranar Asabar ranar ce mu ka yi da Hajjo zan je rugar su.
> Da misalin hudu da rabi na
> yammacin ranar Asabar na shiga rugar su Hajjo, ban sha wata wahala ba
> wajen neman gidansu ba, domin rugar ta su ba ta da girma sosai. Hajjo
> tana gani na ta yi ta murna kamar ta rungume ni don tsananin jin dadi,
> kusan duka mutanen gidan su Hajjo sai da suka zo muka gaisa tare da
> nuna farin cikinsu da gani na.
> Fura da nono mai kyau Hajjo ta kawo min, na kuma ji dadin furar
> gaskiya kauye akwai dadi musamman rugagen fulani ba ruwansu ga yanayi
> mai dadi ga kuma nono mai kyau ka sha iya shanka ba ka da damuwa.
> Abu ka ga garinmu kauye ko?
> Hajjo kenan, ai garin nan naku ina ganin bayan mun yi aure a nan za mu
> zauna saboda ya min kyau.
> Cikin jin dadi Hajjo ta rufe fuska da hannayenta tana murmushi alamun
> jin kunya, kana ta ce haba dai ashe za ka iya zaman kauye?
> Bayan na hadiye wani gayan fura tare lashe baki kai da ka gan ni kasan
> ina jin dadin furar da nake sha, sai na bata amsa na ce ban da abin ki
> Hajjo ai ko shugaban kasa zai so zama a nan ko don shan fura da nonon
> da ke rugar nan.
> Wannan karon dariya Hajjo ta yi har da kyakyatawa kana ta ce" gaskiya
> Abu furar nan ta kama ka da kyau har da santi haka.
> A ranar mun yi hira sosai kuma hira mai dadi da ita, sannan a karshe
> mu ka yi bankwana tare da alkawarin kwanaki kadan masu zuwa zan sake
> dawowa.
>
> KARO NA BIYU A RUGAR SU HAJJO
> Daga ina ka ke?
> Wa kake nema?
> Yanzu ba mu da Hajjo a wannan gidan, Hajjonmu yau kimanin shekarunta
> bakwai da rasuwa. Abin da aka shaida min kenan
> bayan na koma rugar su Hajjo a karo na biyu.
> Ikon Allah sai kallo, abin da ya fi bani mamaki shi ne duk mutanen
> gidan su Hajjo babu wanda ya nuna ya ta6a ganina balle
> mai kamata, na yi musu bayanin kamanin Hajjo sun tabbatar min ita ce
> hasalima sun kawo min
> hotunanta inda ni ma na tabbatar musu cewa ita din ce.
> Cikin tsananin mamaki da kaduwa haka na baro rugar su Hajjo duk jiki
> na ya yi sanyi.
> Tun daga wannan ranar idanuna ba su sake tozali
> da Hajjo ba balle mai kamarta. Kuma har yanzu zuciyata na cike da
> matsananciyar kaunarta...
>

ALMARA KO GASKE

ALMARA KO GASKE?

Daga
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya


Al'ada ta ce duk karshen mako na kan kai ziyara garinmu, domin gaishe
da iyaye, 'yan'uwa da
abokan arziki.
A garin akwai wata kasuwa da
ta ke ci duk ranar juma'a, kasancewata mutum ne mai son shan fura, don
haka duk ranar kasuwar garin na kan shiga kasuwar domin sayan fura,
akwai wata budurwar bafulatana, mai suna Hajjo, Hajjo tana da kirki
kwarai don haka ne ma, babu furar wadda da nake sha kaf
kasuwar sai ta ta, mun saba da Hajjo matukar sabo, domin idan na je
gurinta sam ba ta iya sakewa
saboda tsananin jin kunya.
So! shu'umi ya kan shiga zuciya ba tare da ya yi sallama ba. A kwana a
tashi sai na fara jin son Hajjo mai fura ya shiga zuciyata, domin har
ta kai idan na dawo kano bana iya sakewa in yi ayyukana yadda ya
kamata, haka zan ta fatan karshen mako ya yi na je garin, ban samu
nutsuwa ba sai da na bayyanawa Hajjo abin da yake raina, na ci sa'a
domin a karon farko Hajjo ta amince da ni a matsayin saurayinta.
Watarana ina kasuwa a cikin rumfar da Hajjo take sayar da fura muna
hira ina shan furar da ta dama min, sai nake
tambayarta Hajjo ya kamata a ce nasan gidanku
domin in zo mu yi maganar aure, shiru ta yi na 'yan
mintoci gami da aje ludayin furar da ke hannunta tare da sunkuyar da
kai kasa na dan wani lokaci, kana daga bisani sai ta ja wani dogon
numfashi! Gami da kallon wata yarinya da ke zaune a gefenta bisa wani
dutse tana sayar da mandako. Ko ba ki son in zo gidan ku ne? A'a kawai
dai ina wani dan tunani ne. Wai don Allah da gaske ka ke
kana so na?
(Dariya) ina sonki mana Hajjo. Amma me ya sa kika
min wannan tambayar?
Ai gani na yi kai dan birni
ne, me za ka yi da 'yar kauye iri na?Dariya na sake yi sannan na ce
mata kar ki damu Hajjo
ko ma ya ki ke ina sonki a haka kuma aurenki zan yi.
A karshe Hajjo ta kwatanta mini
rugar su, ranar Asabar ranar ce mu ka yi da Hajjo zan je rugar su.
Da misalin hudu da rabi na
yammacin ranar Asabar na shiga rugar su Hajjo, ban sha wata wahala ba
wajen neman gidansu ba, domin rugar ta su ba ta da girma sosai. Hajjo
tana gani na ta yi ta murna kamar ta rungume ni don tsananin jin dadi,
kusan duka mutanen gidan su Hajjo sai da suka zo muka gaisa tare da
nuna farin cikinsu da gani na.
Fura da nono mai kyau Hajjo ta kawo min, na kuma ji dadin furar
gaskiya kauye akwai dadi musamman rugagen fulani ba ruwansu ga yanayi
mai dadi ga kuma nono mai kyau ka sha iya shanka ba ka da damuwa.
Abu ka ga garinmu kauye ko?
Hajjo kenan, ai garin nan naku ina ganin bayan mun yi aure a nan za mu
zauna saboda ya min kyau.
Cikin jin dadi Hajjo ta rufe fuska da hannayenta tana murmushi alamun
jin kunya, kana ta ce haba dai ashe za ka iya zaman kauye?
Bayan na hadiye wani gayan fura tare lashe baki kai da ka gan ni kasan
ina jin dadin furar da nake sha, sai na bata amsa na ce ban da abin ki
Hajjo ai ko shugaban kasa zai so zama a nan ko don shan fura da nonon
da ke rugar nan.
Wannan karon dariya Hajjo ta yi har da kyakyatawa kana ta ce" gaskiya
Abu furar nan ta kama ka da kyau har da santi haka.
A ranar mun yi hira sosai kuma hira mai dadi da ita, sannan a karshe
mu ka yi bankwana tare da alkawarin kwanaki kadan masu zuwa zan sake
dawowa.

KARO NA BIYU A RUGAR SU HAJJO
Daga ina ka ke?
Wa kake nema?
Yanzu ba mu da Hajjo a wannan gidan, Hajjonmu yau kimanin shekarunta
bakwai da rasuwa. Abin da aka shaida min kenan
bayan na koma rugar su Hajjo a karo na biyu.
Ikon Allah sai kallo, abin da ya fi bani mamaki shi ne duk mutanen
gidan su Hajjo babu wanda ya nuna ya ta6a ganina balle
mai kamata, na yi musu bayanin kamanin Hajjo sun tabbatar min ita ce
hasalima sun kawo min
hotunanta inda ni ma na tabbatar musu cewa ita din ce.
Cikin tsananin mamaki da kaduwa haka na baro rugar su Hajjo duk jiki
na ya yi sanyi.
Tun daga wannan ranar idanuna ba su sake tozali
da Hajjo ba balle mai kamarta. Kuma har yanzu zuciyata na cike da
matsananciyar kaunarta...