ALMARA KO GASKE?
Daga
Rabi'u Muhammad Abu Hidaya
Al'ada ta ce duk karshen mako na kan kai ziyara garinmu, domin gaishe
da iyaye, 'yan'uwa da
abokan arziki.
A garin akwai wata kasuwa da
ta ke ci duk ranar juma'a, kasancewata mutum ne mai son shan fura, don
haka duk ranar kasuwar garin na kan shiga kasuwar domin sayan fura,
akwai wata budurwar bafulatana, mai suna Hajjo, Hajjo tana da kirki
kwarai don haka ne ma, babu furar wadda da nake sha kaf
kasuwar sai ta ta, mun saba da Hajjo matukar sabo, domin idan na je
gurinta sam ba ta iya sakewa
saboda tsananin jin kunya.
So! shu'umi ya kan shiga zuciya ba tare da ya yi sallama ba. A kwana a
tashi sai na fara jin son Hajjo mai fura ya shiga zuciyata, domin har
ta kai idan na dawo kano bana iya sakewa in yi ayyukana yadda ya
kamata, haka zan ta fatan karshen mako ya yi na je garin, ban samu
nutsuwa ba sai da na bayyanawa Hajjo abin da yake raina, na ci sa'a
domin a karon farko Hajjo ta amince da ni a matsayin saurayinta.
Watarana ina kasuwa a cikin rumfar da Hajjo take sayar da fura muna
hira ina shan furar da ta dama min, sai nake
tambayarta Hajjo ya kamata a ce nasan gidanku
domin in zo mu yi maganar aure, shiru ta yi na 'yan
mintoci gami da aje ludayin furar da ke hannunta tare da sunkuyar da
kai kasa na dan wani lokaci, kana daga bisani sai ta ja wani dogon
numfashi! Gami da kallon wata yarinya da ke zaune a gefenta bisa wani
dutse tana sayar da mandako. Ko ba ki son in zo gidan ku ne? A'a kawai
dai ina wani dan tunani ne. Wai don Allah da gaske ka ke
kana so na?
(Dariya) ina sonki mana Hajjo. Amma me ya sa kika
min wannan tambayar?
Ai gani na yi kai dan birni
ne, me za ka yi da 'yar kauye iri na?Dariya na sake yi sannan na ce
mata kar ki damu Hajjo
ko ma ya ki ke ina sonki a haka kuma aurenki zan yi.
A karshe Hajjo ta kwatanta mini
rugar su, ranar Asabar ranar ce mu ka yi da Hajjo zan je rugar su.
Da misalin hudu da rabi na
yammacin ranar Asabar na shiga rugar su Hajjo, ban sha wata wahala ba
wajen neman gidansu ba, domin rugar ta su ba ta da girma sosai. Hajjo
tana gani na ta yi ta murna kamar ta rungume ni don tsananin jin dadi,
kusan duka mutanen gidan su Hajjo sai da suka zo muka gaisa tare da
nuna farin cikinsu da gani na.
Fura da nono mai kyau Hajjo ta kawo min, na kuma ji dadin furar
gaskiya kauye akwai dadi musamman rugagen fulani ba ruwansu ga yanayi
mai dadi ga kuma nono mai kyau ka sha iya shanka ba ka da damuwa.
Abu ka ga garinmu kauye ko?
Hajjo kenan, ai garin nan naku ina ganin bayan mun yi aure a nan za mu
zauna saboda ya min kyau.
Cikin jin dadi Hajjo ta rufe fuska da hannayenta tana murmushi alamun
jin kunya, kana ta ce haba dai ashe za ka iya zaman kauye?
Bayan na hadiye wani gayan fura tare lashe baki kai da ka gan ni kasan
ina jin dadin furar da nake sha, sai na bata amsa na ce ban da abin ki
Hajjo ai ko shugaban kasa zai so zama a nan ko don shan fura da nonon
da ke rugar nan.
Wannan karon dariya Hajjo ta yi har da kyakyatawa kana ta ce" gaskiya
Abu furar nan ta kama ka da kyau har da santi haka.
A ranar mun yi hira sosai kuma hira mai dadi da ita, sannan a karshe
mu ka yi bankwana tare da alkawarin kwanaki kadan masu zuwa zan sake
dawowa.
KARO NA BIYU A RUGAR SU HAJJO
Daga ina ka ke?
Wa kake nema?
Yanzu ba mu da Hajjo a wannan gidan, Hajjonmu yau kimanin shekarunta
bakwai da rasuwa. Abin da aka shaida min kenan
bayan na koma rugar su Hajjo a karo na biyu.
Ikon Allah sai kallo, abin da ya fi bani mamaki shi ne duk mutanen
gidan su Hajjo babu wanda ya nuna ya ta6a ganina balle
mai kamata, na yi musu bayanin kamanin Hajjo sun tabbatar min ita ce
hasalima sun kawo min
hotunanta inda ni ma na tabbatar musu cewa ita din ce.
Cikin tsananin mamaki da kaduwa haka na baro rugar su Hajjo duk jiki
na ya yi sanyi.
Tun daga wannan ranar idanuna ba su sake tozali
da Hajjo ba balle mai kamarta. Kuma har yanzu zuciyata na cike da
matsananciyar kaunarta...
Tsangayar Adabin Hausa. Powered by Blogger.
Home
»
»Unlabelled
» ALMARA KO GASKE
ALMARA KO GASKE

Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.