0
DAGA Nasir G Ahmad, ZUWA GA FARFESA
MALUMFASHI:
Kamar yadda aka ba da shawara, za mu so jin
ra'ayin Malam, da ma sauran malamai kan sabanin da ke akwai a halin
yanzu game da wani bangare
na ka'idojin rubutun Hausa, musamman 'yar
mallaka da zagagen aikatau na lokaci mai ci.
Yayin da mu daliban Hausa muka kankame abin da
ke rubuce cikin littafai dangane da wadannan
ka'idoji muke hadewa mu rubuta: GIDANMU, GUDUMMAWARMU, AYYUKANMU;
akwai ra'ayi na
biyu (Darikar Malam Sheme) da ke cewa raba 'yar
mallakar da kalmar abin da aka mallaka za a yi,
wato a rubuta, GIDAN MU, GUDUMMAWAR MU,
AYYUKAN MU.
Haka nan akwai masu raba zagagen aikatau na lokaci mai ci, wato suna
rubuta TA NA, MU NA, KA
NA, KI KE, YA KE, SU KE, ds., maimakon hade su da
mu muke yi.
*Ina jin zafin wannan sabani da ke akwai, domin
zai raba hankalin matasan marubuta, su rasa
wanne za su dauka, ko kuma abin ya zama "Hamiyya," wato ya zamo mutum
na zabar ra'ayi
kaza ne, saboda shi wane ke bi, don haka shi ne
dai dai.
*Mene ne mafita game da wannan sabani?
*** *** ***
Malumfashi Ibrahim: "Salamu alykum. Ina jin kamar an amsa tambayar
ma kafin ni na shigo. Aminu Garba Ingawa ya ce;
mafita a nan Malam ita ce: shehunan Malaman da
muke da su su yi zama na musamman don samar
mana mafita kan wannan matsalar. Hauwa Lawan
Maiturare kuma ta ce, shawarar Aminu ita ce abin bi, domin kuwa
ba'arin malamai tun daga
sakandare zuwa jami'o'i har yau suna koyarda
had'e mallaka ne, memakon raba su, amma idan
aka shirya zama aka buga masa stamfi sai ya zama
kar'ba'b'be bai d'aya, memakon wannan nabin
d'arik'ar wane, wance na bin ta wance. Ni na kara da cewa harkar
dabbaka ka'idojin
rubutu a kowane harshe na duniya a fagen nazarin
kimiyyar harshe yake shimfide, ba adabi ko al'ada
ko wani abu makamancinsa ba, duk kuwa da cewa
masana kimiyyar harshen ba sa aiwatar da komi sai
sun yi la'akari da adabi da al'adu da addini da sauran ire-iren su
wajen kai ga matsaya.
Ba wani abu ya sa haka ba, sai ganin cewa dukkan
ka'idojin suna tafiya da ginuwar nahawun harshe;
shi ya sa za ka ji ana maganar DOGUWA da
GAJERIYAR MALLAKA, da kuma TSIGALAU da
WAKILIN SUNA ko ZAGIN AIKATAU ko AZUZUWAN AIKATAU da LOKUTTAN HAUSA da
wasu da dama
irin su.
Wannan ne ya sa ko a fagen tsara rubutu da
ka'idojinsa ake tattaruwa da mutane mabambanta
domin a samar da matsaya. Duk wata matsala da a
yanzu ake fama da ita ta rarrabuwa da dagewa a kan wani abin da ake
gani shi ne daidai, to an bar
tsayayyar ka'ida ne an shigo da son rai ko wani
abu makamancin haka.
Alal misali, a duniyar rubutun Hausa yanzu za ka ga
ana samun takaddama kan: Ba da za a rubuta ko
Bada. Akan zo ne za a ce ko A kan zo. Bayar da ne daidai ko Bayarda.
Namu, naku, nasu ne gaskiya
ko na mu, na ku, na su. Wane ne daidai ko Wanene.
Mene ne ko kuwa Menene ko Minene, Allah ne ko
kuwa allah Allah ya ce ko kuwa Allah Ya ce.
Akwai misalai da yawan gaske da ake ta fama da
su tsakanin masana da manazarta da dalibai. A nawa tunanin ba abin da
ya jawo haka face rashin
bin diddigin yadda lamurra suke a nazarce, da
kuma rashin ilmin Rubutun Ka'idojin Rubutu da
yawancinmu ba mu da shi, sa'annan uwa-uba
rashin takarkarewa wajen koyar da wadannan
ka'idoji a makarantun Firamare da Sakandare da Kwalejoji da Jami'o'inmu.
Ba a ba wannan darasi muhimmanci ba, shi ya sa
muke wa harkar ka'idojin rubutu labarin cin
kanzon kurege. Abin da na sani shi ne, a yanzu
mutum daya ko biyu ko uku ko ma fiye ba su da
ikon canza ka'idojin da aka amince da su tsakanin masana da goyon bayan hukuma.
Muna da dama mu ki amincewa da dukkan abin da
aka taru aka amince kan sa, a matsayin 'yan tsiraru,
amma a kullum tarbacen taron masana ake aiki da
shi ba na 'yan tsirarun ba.
Saboda haka a halin yanzu MALLAKA a rubutun HAUSA a hade take, kamar
yadda malam Nasir G
Ahmad ya nuna: GIDANMU, GUDUMMAWARMU,
AYYUKANMU ake rubutawa a gajera, alhali a
doguwa GIDAN NAMU, GUDUMMAWAR TAMU,
AYYUKAN NAMU. Haka kuma TANA, MUNA, KANA,
KIKE, YAKE, SUKE, da sauransu ake rubutawa, maimakon rabawa da wasu ke yi.
Wannan ita ce tsayayya, amsassa kuma karbabbar
ka'ida. Sai in nan gaba an sake yin wani taro an
canza wadannan ka'idoji, sa'annan za mu iya
amincewa da sabon alkawari."
*** *** *** Ibrahim Sheme: "RA'AYIN "TSIRARU" KAN RABA MALLAKA.
Oh, ikon Allah! Malam ya ce: "Abin da na sani shi ne,
a yanzu mutum daya ko biyu ko uku ko ma fiye ba
su da ikon canza ka'idojin da aka amince da su
tsakanin masana da goyon bayan hukuma. Muna
da dama mu ki amincewa da dukkan abin da aka taru aka amince kan sa, a
matsayin 'yan tsiraru,

shi ba na 'yan tsirarun ba."
Amma na yi mamakin yadda Farfesa ya gina
kafewar sa a kan AL'ADA, wato kunne ya girmi
kaka. Ban da nuna mana cewa "haka ake yi" ko "haka mu ka gani," babu
wata kwakkwarar hujja
da ya kawo mana mai nuna dalilin da ya sa za mu
hade mallaka.
Malam bai kawo mana sabon abu ba; ai da ma mun
san cewa an ce "haka ake yi." Abin da mu ke so shi
ne: me ya sa? Don me za a yi hakan? Bisa wace hujja?
Ni, da yawa an san ni da cewa ina daga cikin tsiraru
(ko ma jagoran su) masu yekuwar lallai sai an raba
mallaka. Kuma tuni na kawo kwararan hujjoji na a
wannan dandalin na DM (koda yake na ga babu
wanda ya tuno da su, ciki kuwa har da shi Mal. Nasir).
Ni ina ganin maganar da Farfesa ya yi ta farko kafin
ya yanke hukuncin sa cikin garaje ita ce ya kamata
ya zauna a kai, wato inda ya ce:
"Ina jin kamar an amsa tambayar ma kafin ni na
shigo. Aminu Garba Ingawa ya ce; mafita a nan Malam ita ce: shehunan
Malaman da muke da su su
yi zama na musamman don samar mana mafita kan
wannan matsalar. Hauwa Lawan Maiturare kuma ta
ce, shawarar Aminu ita ce abin bi, domin kuwa
ba'arin malamai tun daga sakandare zuwa jami'o'i
har yau suna koyarda had'e mallaka ne, memakon raba su, amma idan aka
shirya zama aka buga
masa stamfi sai ya zama kar'ba'b'be bai d'aya
memakon wannan nabin d'arik'ar wane wance na
bin ta wance."
Wannan na nuna cewa har yanzu ba a yanke
hukunci kan batun nan na mallaka ba. Ba mallaka kurum ba, har ma wasu
kalmomin masu tarin
yawa. Farfesa Malumfashi ya yanke nasa a nan, ba
tare da ya kawo mana wata madogara da za mu
zauna a kai ba.
Sannan batun nan ba fa na "son rai" ba ne ko
"rashin ilmi" kamar yadda Malam ya nuna. Batu ne na nazari da bincike
inda ake kafa hujja. Ni kam ba
ni da PhD ko farfesanci, to amma ba shakka zan ja
da ko waye da zai ce ba ni da ilmi ko ba ni da sani
kan nahawu. Na karanta shi matukar karantawa, a
cikin aji (ni dalibin Farfesa Sani Zaria ne), na mallaki
littattafan nahawu, na fahimci dukkan inda duk wani masani mai cewa a
hade mallaka ya dosa.
Tuni na kasance daya daga cikin marubutan Hausa
da su ka san harshen Hausa da yadda ake rubuta
shi. Wannan ba cika baki ba ne, dahir ne.
A da can, ina bin waccan darikar ta masu cewa a
hade kalma. Littattafai na na farko-farko, irin su "Kifin Rijiya"
(1991) da bugun farko na
"'Yartsana" (2003) da duk wasu rubuce-rubuce da
na yi lokacin ina aikin jaridar Hausa (Nasiha, Rana,
Gaskiya Ta Fi Kwabo) a bisa waccan darikar na yi
su, to amma tuni kai na ya waye, na gane cewa
masana sun dulmiyar da mu cikin wannan dokar ba tare da sun ba mu dalilin su ba.
Daga nan na zama "tsiraru" ko "dan tawaye" - har
na ke jagorantar su. A cikin farin sani na sauya
sheka, ba wai duhun sani ba.
Na so a ce Malam Malumfashi ya kawo mana hujja,
misali: ga dalilin da ya sa ake hadewa, ba wai kawai a ce taron masana
ne su ka ce a yi hakan ba. Ai
mun san me su ka ce tun tuni.
Da masanan su ka taru, me su ka gindaya a
matsayin hujja? Idan an shanya mana hujjar su a
faifai, to sai mu dube ta mu gani: karbabbiya ce ko
a'a? Dalili shi ne: ilmi kogi ne. Malam ya fi ni sanin hakan.
Ina so ni da Farfesa mu zauna in jera masa hujjoji
na daki-daki (idan na kai minzalin zama da farfesa).
Na tabbatar a matsayin sa na mutum wanda ya
dade da kin karbar abu ba tare da ya ga hujja ba,
zai amince da nawa uzirin, kuma ya dawo cikin mu "tsiraru".
*** *** ***
Nasir G Ahmad:
"Allah ya ja mana da Malam (Sheme)! Ina sha'awar
irin wannan dagewa taka, amma fa ni ba zan bi
wannan sabuwar darika ba. Ga Farfesa ka fuskantar da bayananka. Duk da
haka ga ra'ayin
almajirinku:
Ka yi watsi da ijma'i, wato haduwar ra'ayin
manazarta kan hade gajerar mallaka, wannan
ra'ayinka ne. Amma ijma'i ya fi karfin a ce ba abin
dogaro ba ne. A musulunce ma, shi ne mataki na uku wajen samar da
hukunce-hukuncen shari'a.
Wanda ya bijire wa ijma'i, ya zama mu'utazili ke nan,
wato dan tawaye, kamar yadda ka ce ka yi wa
ra'ayin manazartan Hausa.
Kamar dai yadda na taba fada, zan yi amfani da
abin da nake da madogara kansa a hannuna ne. Wanda aka yi
wallafe-wallafe kansa, ake kuma kan
yi. Aka amince da amfani da shi, da koyar da shi a
dukkan matakan ilimi.
Kamar yadda kuma na taba fada, ni da nake
malamin makaranta mai koyar da dalibai Hausa da
ka'idojin rubuta ta, da wace hujja zan dogara in na ce zan sauya
alkibla rana tsaka, na nemi koyar da
dalibaina ka'idojin rubutun Hausa na sabuwar
darikar Shemiyya, alhali ga abin da ke cikin littafan
manhaja da aka umarce ni na yi amfani da su? Ba
ma ta fuskar aiki ba, ni a karan kaina, ba zan iya ba
da hujjojin da Malam ke rike da su a matsayin madogarata ba, domin ni
kaina ba su gamshe ni ba
(ta yiwu saboda karamin sanina).
Kamar yadda kuma na taba fada, ya kamata Malam
(Sheme) ya fito da wata wallafa ta littafi, ko a
matsayin makala ga irin taron masana Hausa da
akan yi, inda zai fito da wannan sabon ra'ayi nasa ga 'yan uwansa
manyan masana don tattaunawa.
Idan aka amince, aka yi ittifakin yin amfani da su,
mu dalibai ba abin da ke kanmu sai run gumar su
da fara dabbaka su a rubuce-rubucenmu. In ba
haka ba, to muna nan bisa darikar 'yan mazan jiya,
babu gudu babu ja da baya." *** *** ***
Malumfashi Ibrahim:
"Alhamdu lillah, na karanta jawabin Ibrahim
Sheme, amma kamar ya yi mani mummunar
fahimta, 'son rai' da 'rashin ilmin' da na yi magana
ba da shi nake ba, da dukkanmu nake da ke da matsala da ka'idojin
rubutun Hausa. Ba wai shi
kadai ba ne ke cikin 'tsirarun' da na yi magana, ni
ma ina ciki. Kuma na sha korafi game da haka a
wuraren tarurrukan ilimi da kara wa juna sani.
Na dade ban yarda a raba /ba da/, misali /na ba da
kudi/ ni fi yarda da a hade su, domin a tawa fahimtar /bada/
cikakkiyar kalma ce, amma in
muka raba, / ba/ na matsayinta daban da /da/ ke
nan, wato dukkansu za su iya zama da gindinsu su
bada ma'ana.
Na kuma kafa hujja da abu guda, idan muka koma
ga ita kalmar /ba/ za a ga ta samo asali ne daga / bayar/, wato misali
/na bayar da/. A bisa ka'idar
nahawu, duk inda aka yanke wani abu daga wata
kalma, abin da ke bin wannan kalmar hade shi ake
da wanda ya biyo masa, ya koma kalma guda mai
ma'ana guda. Ke nan /bayar da/ idan ka ka debe /
yar/ zai zama /ba/, ita kuma /da/ da ke biye sai ta koma ta
saje da /ba/ ya zama / bada/. Wannan shi aka koya
mana a nahawun, amma daga baya masu nazarin
nahawu suka ce, ai nan ba kalmomi yau da kullum
ba ne, kalmomin fannu ne na aikatau, kuma tun
azal bayar/ da /ba/ kalmomi biyu masu zaman kansu , wato kana iya cewa
/bayar da/ ko kuma /
ba da/, domin ita/bayar/ da /ba/ duk abu daya ne
a kalmomin fannun aikatau, aji ne kurum ya
bambanta su, ba wai gutsire / yar/ aka yi ba, ke
nan dole a bar su a rabe. Har yau a rubuce-
rubucena raba su nake yi, sai in na tuna da cewa ai an yi ittifaki,
kan rabawa sai na
gyara na koma ga wanda aka amince da shi. Ko a
aji, nakan bayyana wa dalibai rashin amincewa ta
da wasu ka'idoji da yawa, amma in mun gama
tattaunawa, tambayar da aka yi man ita ce, 'to
malam wane za mu dauka mu yi aiki da shi,' ni kuma a kullum nakan ce,
wanda aka amince da shi,
ko da kuwa bisa kuskure ne.
Saboda me? Idan aka bar harshe yana gudana bisa
son rai ko rashin sanin tushen abu, yana iya jawo
rugujewar abin da aka riga aka gina, ta yadda za a
zo a kare ba wan ba kanen. Sheme da duk wani mai irin wannan ra'ayi nasa ba
za mu taba samun galaba ba sai an kuma yin wani
taro na bitar ka'idojin, mun je wurin an kwafsa da
mu, ba mun bayar da hujjojinmu, an karba, an
buga, an watsa ga sauran al'umma, ana kuma
karantar da su don na baya su sami abin karaswa. Ba yadda za ka yi
jayayya da abin da taron
daidaitawa ya zo da su, yin haka barna zai jawo ga
harshen."

Post a Comment

Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.

SABANI GAME DA WASU KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA.

No comments:

Post a Comment