(Ci gaba daga inda aka tsaya)
Bayan Yarjejeniyar Rubuta Littafin Shata Sai Me,
Wacce Rawa Aliyu Qanqara Ya Taka a Littafin ?
A nan take mu ka sasanta kawunanmu mu ka kuma sanya Sheme ya jagoranci wannan tafiya. Amma ko a sannan xin yawan littattafan da na wallafa na Hausa sun fi na Sheme yawa; ba wai akan littafin Shata na fara rubutu ba. Mun aminta ya zama jagoran mu saboda shi ke da Komfuta don haka a kyauta ya ce za ya sanya a buga littafin kafin a kai shi maxaba'a, kuma sannan ya gwanance wajen rubutu tare da basirar rubuta littafi. Mu ka xauki hotunan tarihi tare da Makaxa Shata har kala 12.
Sauran hirarrakin da abokan mu su ka yi da wasu jama'a a cikin kasasuwan rikoda da ba su kai ga rubuta ko fassara su ba, su ka tattara su ka bamu. Shi kuma Sheme ya bani su, tare da bani umurnin in zauna in rubuta su in bashi. Na himmatu na yi aikin na kai masa. Daga cikin hirarrakin akwai ta Sidi mijin Hotiho da Hauwa mai tuwo. Shima Sheme, hirarrakin da ya yi a kaset-kaset ya bani in dai rubuta, a ciki akwai ta Laila Dogonyaro, Musa Musawa da Bawa Dungun Mu'azu. Tun daga ran da mu ka bar gidan Shata su biyu su ka sakam mana aikin, su ka zare jikin su.
A Kaduna, Sheme ya ke faxa mani cewa 'Aliyu ka ga mutanen nan sun bar mana aikin nan, sun daina yin intabiyu da mutanen Shata'. Idan mu ka yi masu qorafin haka sai su ce 'kun kira mu kun ce ga aiki kun ga mun qi amsa'? Sai ni da shi mu ka duqufa don nemo sauran hirarraki daga mutane, amma ni nawu aikin ya fi nashi faxaxa da nauyi, shi ma ya san haka. Don shima kan sa ba ya da lokaci, kullum aikin Edita na New Nigerian N ewspapers ya sha masa kai. Kuma galiban duk ni na ke bashi bayanan wasu da Shatan ya yi ma waqa da kuma waqoqin su, don bai sansu ba. Watau al'amarin sa na Shata bai yi nauyi kamar nawu ba.
Kwaram tun ma ba a je ko'ina ba bayan watanni 9 sai Allah Ya yi ma Shata rasuwa ran Juma'a 18/6/1999. Hakazalika Sheme ya qirqiri wallafa mujallar FIM a cikin Mayun 1999. Ga kuma aikin wallafa tarihin Shehu Musa 'Ya'aduwa da sabuwar gwamnatin Obasanjo ta bashi. Duk abubuwa su ka rincave masa. A lokacin an sallame ni daga Kwalejin Kimiyya ta Kaduna ta hanyar rage ma'aikata, saboda haka ina zaune a Kaduna ba ni aikin komi (na zama abin tausayi) saidai rubuce-rubucen da ba za a rasa ba. Ganin haka, sai na duqufa, kuma muka shirya ni da Sheme, ina ta nemo labaru daga jama'a. Kuma ya kan tura ni ya bani kuxin mota da na abinci zuwa Musawa. Dama tun cikin Maris 1998 ya tura ni Gombe da Bauchi don ganawa da mutanen Shatan na can wajen. A taqaice ba a gama aikin littafin nan ba sai ina da kashi 65 na aikin littafin. Sheme ya bada gudunmuwar kashi 25, sauran abokan mu daga Kano sun bada gudunmuwar kashi 10. Allah Shi ne shaida ta, idan na yi masu qarya zan haxu da Allah. Ni fa xalibin kimiyya ne ina da ilimin qididdiga ko statistics. Tuni na yi wannan lissafin na fitar da sakamakon.
Game da waqoqin Shata da na bada shawarar a tattara su a vangare xaya na qarshen littafin, shi da kan sa Sheme ya bani aikin nemo su. Gaba xayan waqoqi 638 da aka sanya duk ni na bada su. Yanda aka yi na tattara su shi ne: da na ji wata waqa ta Shata sai in rubuta ta a takarda in ofishin sa in bashi, koda ban tarar da shi ba sai in tura takardar a 'yar kafa ta qarqashin qofa. Shi kuma da ya zo ya buxe qofa sai ya gani. Sai ya xauka ya rubuta a kundin littafin.
A littafin mu mai xauke da shafuka 604 ga dai gudunmuwar da na bada, watau wasu daga cikin waxanda na gana da su a lokuta daban-daban (kafin, da kuma bayan mun haxe da sauran abokan aikin littafin):
Hakimin Musawa, Inde Magajin Musawa, Sa'in Katsina Amadu Na-Funtuwa (oga kwata-kwata a zancen Shata), Wasu dattawan Musawa, Hauwa matar Sarkin Bori Sule, Babba Qofar Gabas, Maigarin Sayaya Yahaya Salmanu, Tijjani Hashim Kano, Walin Kano Mahe, Ada tela Daura, Ali Scorpion, Walin Kano Mahe, Dagacin Falgore, Shu'aibu Bada-Bada, Alaramma Sulen Shata, Ali Xanqane Musawa da Mamman Tsalahu Musawa (da matan su), Hajiya Safiya Qumbula qanwar Shata, Xanbaba makaxi Musawa (makaxin sa na farko), Balan Guzun qanen Shata, Bilkin Sambo, Sani Bakatoshi, Inuwa Xalibi, Uwawu Kano, Mairo Munari, Indo Musawa, Indon Xanbaqi, Garba Xan Ammani, Musa Xan Amare Musawa, Ayuba mai nama Musawa, Bala Abdullahi Funtuwa, Halle Jani, Garba Ja, Abba Na Titi, Sabo Dogarai Kano, Ahmed Kari Garkuwan Bauchi, Bappa Ahmed Gombe, Musa Usman tsohon gwamnan NW, Hajiya Indo 'Yar Mamman Gombe, Magaji Mai Ido Xaya, Amadu Doka mai kukuma, Alhaji Mayau Kaduna, 'Yayan Qungiyar makaxa da mawaqa ta Qasa, Ali Xan Saraki 'Yankara, Musa Xanbade, Sarkin Damben Haxejiya, Sanqira Isiyaku Usman Galo, Abashe Yaro maihoto, Dauda Mani da Garba (Yaro) Na-Gwandu mai nama, Ado Kankiya, Garba Kwagira, Salisu Bangul Xandaudu, Yahaya Xandaudu, Shehu Tsatso, Abubakar Kashe-kura na qofar Qaura.
Waxanda kuma su ka rasu, na tattauna da iyalan su, kamar su: Sarkin Katsina Nagogo, Haruna Qasim, Maude Tabako, Ali Bagobiri, Mati 'Yammama, Xan Lagai-Lagai, Sani Audi, Sule Xan Wazifa, Sani Stores, Mamman Xa, Garba 'Yammama, Alhaji Abdulwahabu Malumfashi, Sani Xanqwara Malmfashi, Ahmadun Gaya, Ciroman Gombe Umaru, Adamun Pankshin (Ladi), Garba Sarkin malamai.
Na kuma ziyarci RTK sau da yawa na yi hira da ma'aikatan su kamar su: Ofishin kasuwancin su, Xakin ajiye faya-fayi, Lawal Yusuf Saulawa, Nasiru Maiwada Malumfashi, Ahmed Aja, Rashida Bello, Shafi'u Zangon Aya, Yakubu Gombe, Ladan Kontagora, Ibrahim Baqo, Ahmed Girei (Xan uwan Xahiru Modibbo) Nine kuma na yi hira da wasu 'ya'ya da matan Shata kamar su: Binta Mami, Magaji, Salisu, Sanusi, Amina, Mamuda, Binta Iya, Asabe (Zuwaira), Hurera Yamai, Hadiza Falgore, Amina Dikke, Nasara Musawa, Yalwa, Binta Qanqara, Hajiya Kulu Kaduna, Halima, Jamila.
Wasu ma mutanen da na gana da su na manta da su. Amma duk aikin nan da aka yi, na rantse da Allah ko kwabo ban samu ba, na tashi a tutar asara. An qaddamar da littafi, amma bisa ga amana, ya dace mu zauna mu 4 mu kasafta xan abin da aka samu, kowa a bashi ko da a hannu ne. Sai ba a yi haka ba. Shi dai Sheme shi ne shugaba na, su kuma su biyu daga Kano sai Tijjani ya ke wakiltar su. Kuxin da ba a amso ba daga mahalarta taro da su ka yi alqawari sai Sheme ya ce ya ranci gudunuwar Sarkin Zazzau ta N200, 000 ya gyara mota. Ganin haka, sai Shima Albasu, da ya amso kuxin Badaru Vavura (gwamnan Jigawa na yanzu, N100, 000) ya ranta shima ya gyara mota. Amma da Albasu ya faxa mani sai ya ce Sheme ya kwave shi ya ce kada ya faxa mana, mu sauran biyun. Zancen kenan har yau ba a qara tada shi ba. Ni kuma na sa masu hajar mujiya. Gudunmuwar Alhaji Xahiru Mangal ta N250, 000 na ke tababa ko sun amsa koko ba su amsa ba? Tunda na ji shiru itama ba a rasa amsar ta.
A lokacin wannan hidima ta tarawa da kuma kasafta kuxin ina can Daudawa, wani lungu cikin daji ina koyarwa a Makarantar 'Yammata, su kuma abokaina su na Kano da Abuja a inda waxanda za a amshi kuxn daga wurin su su ke. Haka su ka yi qumuiniyar su ta kuxin ni ban sani ba. Sai daga baya xaya daga cikinsu ke faa mani. Har inda yau ta ke ban yi masu magana ba saboda kawaici da haquri.
Sannan mu duka 4 mun yi alqawari wanda duk aka ba kofin littattafai ya kai wasu garuruwa, idan an sayar an bashi kuxin to ya turo a asusun da aka buxe ma littafin, kuma Sheme da Albasu kaxai ke da sa hannun ko ikon fitar da kuxi daga banki.
Ni, na tafi Sokoto na kai littattafai, amma don tsoron kada a ce na sava alqawari, waxanda na sayas sai na tafi banki na aiko da kuxin. Waxanda na kai Funtuwa kuma, da ba a samu kasuwa ba sai Sheme ya umurce ni da in kai su Kano in ba Ali Malami don ya kai BUK, haka kuma na yi. To tsakanin kuxin qaddamarwa da na ciniki wallahi summa tallahi ban samu ko kwabo ba. Sai daga baya na fahimci kuxaxen an yi wani waje da su, bayan an sayar da littattafan. Yanzu an shirya mani gaskiya kenan? Kada fa ka manta kashi 65 na aikin littafin duk qoqari na ne.
Don saboda wahalar da na sha a littafin lokacin shirya shi, ranar da zamu tafi Arewa House bukin qaddamarwa, na kwana gidan marigayi Adamu Yusuf BBC, amma da mu ka zo za mu shiga motar sa, sai ya kada baki ya ce: 'za mu tafi qaddamar da littafin da Aliyu Qanqara ya rubuta, ba su Ibrahim Sheme ba, domin su Sheme ba wata wahalar da su ka yi'.
Na rantse da girman Allah abinda ya faxi kenan. Ya na lafira, na san zan bishi watarana. In na yi masa qarya na san zamu haxu a gaban Allah.
Dalilan Da Su Ka Sanya NaWare Na Sake Rubuta Littafin Shata Ni kaxai Guda 8:
Duk da asarar da na yi na 'yan uwana sun rabe kuxin littafi sun manta da ni, ban damu ba, don babana ya bani haquri ya ce 'ba rabo na ba ne, rabon na nan tafe a gaba'. Na ce su zo a sake buga wani, sai su ka ce su sun gaji, idan ni ina da sarari in tafi in ci gaba. Kafin wannan lokacin, mun haxu a magana xaya cewa kowannen mu na iya xaukar littafin ko wani sashen sa ya rubuta wani abu game da Shata a gaba. Na rantse da Alkur'ani abinda Sheme ya bamu umurni kenan, kuma kowa ya yarda. Daga baya sai su ka yi mani gardamar maganar don sun ga ba rubutawa mu ka yi ba, ga kuma wani littafi ina ta qoqarin fitarwa. Don sun ga littafin ne ya sa su ka canza magana. Ka ga hassada ta shigo ciki kenan.
Amma dalilan da su ka sanya na ware na haxa runduna ta ni kaxai su ne:
Na sha wahalar Sheme a littafin farko. Bai cika xaukar shawara ba, abin da kuma ya ga dama shi ya ke sanyawa ko ya ke cirewa ko da kuwa mu ba mu so hakan ba, alhali an ce tafiya ce ta mutum 4. Ai don ana so a samu idea ta kowa shi ya sanya aka game. To minene amfanin haxewar? A ce cikin mutum 4, mutum xaya shi kaxai za a xauki ra'ayinsa dole ? Ka ga ko tafiya ta tafi watarana sai an samu savani. Duk labarin da na kawo masa sai ya tace ya zubar da fiye da rabi, sannan ya sanya sauran. Vangaren tarihin Shata da ya fi garxi da gishiri da nuna, sai na ga Sheme ba ya son nan wajen. Alhali abubuwan da ya zubda suma masu amfani ne. Mahaifin Shata mahalbi ne kuma gagararre, duk hatsabibancin sa Shata ya gaje su. Don haka komin iya yin mutum ba ya raba Shata da wannan hatsabibanci don gadon sa ne, saidai in ba ya son gaskiya, kamar kwatsam a ga ya vace ko a ganshi cikin fili ba tare da an ga isowar sa wurin ba.
(Idan ana taron aikin gayya ko na mahalba, ba a ganin lokacin da mahaifin Shata za ya iso wurin, saidai a ganshi a tsakiyar fili, to shima Shata ya sha saidai a ganshi a fili ba a ga ta inda ya zo ba. Da mutum ya cire wannan a tarihin Shata to ya vata shi, kuma zancensa ya tashi daga tarihin makaxin ya koma wani abu daban. Ka na iya raba mutum da abin da ya gada? An tabbatar Ibrahim Yaro ya na vacewa (ba mamaki ba ne saboda mahalbi ne) kuma ya na iya shiga cikin kukar gidan su ya kwana 2 bai fito ba. Ko kuma in ya shige ta sai a ga ya vulla a cikin tafkin Musawa. Daga gida kuma ya na kiran namun daji su zo wajen sa. Tsohuwar matar Shata da su ka zauna da shi a Musawa ta shaida mani haka, ta ce an yi abin a gabanta ba sau xaya ba, ba sau biyu ba.Ya na kuma ba mahalba asirin kama dabba. Don na faxi tarihin mutum ai ba aibata shi na yi ba. To don dai labarin daga gare ni ya fito saboda hassada da kushe sai a qaryata ni? Saboda ba'a qaunata ? Af, ba hatsabibancin su ka sanya shi ya yi kiwon kadoji har daga baya Shatan ya gaje su daga hannun sa ba? Tsofaffin da su ka bani labarin wasun su na nan da rai. Vangaren hatsabibancin Shata, Sheme babu ruwan sa da wannan, ni kuma vangaren da na fi so kenan. Ya ce wai babu scientific proof. To Sheme ya je Musawa ya nemo tarihin Babu ya sha mamaki. In kuma an yi musun hakan, to a ce kiwon kadojin ma bai yi ba mana)
Tun farko, yakamata a ce ra'ayin mu da aqidar mu da tunanin mu, mu marubutan sun zo iri xaya, sai aka samu akasin haka.
A vangaren abubuwan da Sheme ke rubutawa akan Shata, akwai tawaya, saboda na rantse da Allah bai san Shata ba, ba ya kuma son ya san ko wanene shi. Tun a littafin farko, na jawo hankalin sa a kan matattun waqoqi da basu samu gatancin da aka naxe su a faya-fayin garmaho da Telbijin ba, cewa sun fi rayayyun waqoqin sa (waxanda aka xauka a Rediyo da Telbijin) garxi da azanci da hikima tunda su ya riga yi, har ya zuwa tsakiyar shekarun 1960. To duk waqoqin Shaa dodon hoto ne, ma'ana: su na da qanne ko yayye. Wadda duk ya yi, to watarana sai ya wanke ta ya yi samfurin wata irin ta. Amma Sheme bai yarda da wannan ba. Misali, Bakandamiya kala 130 ce, a cikin littafi na. Shi a wurin sa Bakandamiya ba ta fi kala 10 ba. A nan ma mun sha bambam. Da za a yi wa tarihin Sheme na Shata gwagwa za a gane cewa zunzurutun tarihin Shatan da ya sani ba wani abin a zo a gani ba ne.
Irin fasalin intabiyu da Sheme ke yi ma mutanen Shata ya taqaita su kurum ga waxanda ya yi wa waqa. Shi ko wanda Shata ya yi wa waqa bai san Shata ba kamar maroq ko makaxin Shata, don shi da shi ake yawo. Shi wanda aka yi ma waqa ai zaune ya ke wuri xaya sai randa aka iske shi. Ni kuma a intabiyu, na fi son in karkata ga maroqa da Adamusawa ('ya amshin Shata) don su ke da tarihi. Su, sun yi ma Sheme nisa saboda a karkaru su ke zaune, su ko waxanda ya yi ma waqa ga su nan ko'ina birjik har cikin Abuja. Don haka Sheme ya huta ba sai ya wahala ya tafi karkaru ba. Shi ya fi jin daxin ganawa da su akan Adamusawa.
Dama ni na yi wahala na shiga lunguna-lunguna da qauyuka na nemi zancen Shata daga hannn Adamusawa da waxanda ya yi zama da su. Na yi imanin cewa Sheme ba za ya iya yin wannan wahalar ba.
Sannan intabiyun Sheme ba mai nauyi ba ce, kuma ba ta ba da wani abin kirki da ake son a samu, duk da ya ke shi Xan Jarida ne. Misli, mun je Zariya tare da shi wurin A'isha Yalwar Yakubi Shandam, amma saboda nawar sa da rashin yi mata allurar zaqulo labarin dangantakar ta da Shata sai ma ta ce mana aiki ta ke yi kuma ta na da baqi. Qarshe mu ka tashi aka yi asarar hira da ita. Sheme ya cika nuna lallashin mutum in ya je intabiyu, ni kuwa da zafi zan afka ma mutum, wannan zafin shi za ya sanya mutum ya zabura ya ga lallai da gaske na ke. Shi Shatan, ba da zafi-zafi ya kai ga shaharar ba? Da ya nuna son jiki ko nawa ko lallashi da ya samu xaukaka da shaharar da ya samu? Shi ya sanya ni ke da ideas masu yawa; idan na fara bayani mutane ba su so in daina, kuma sun a da tabbacin abin da duk aka tambayeni san bada gamsassar amsa, don na samo ta. Ina kua allurar yi a duk wanda na je wurin sa hira, ko bai so yin hirar ba dole ya tsaya ya saurare ni. Misali, Alasan Abdallah Dunu, da na same shi a Kano, da farko sai ya ce mani ba ya da lokaci. Amma ina ce masa 'ranka ya daxe da Kwastan qwara ne ya zo da kan sa da ka ce ba ka da lokaci ?'Sai ya yi znnbur ya tashi zaune ya ce 'yaro ina ka samo labarin Kwastan ? Ai kawai sai ya ce mani zauna, na zauna, sannan mu ka dosa hira, ya shiga bani labari tun lokacin da ya yi tuqi a gidan Kwastan xin a Malumfashi, shi da su Bawa Janke. Wasu mutanen da barkwanci-barkwanci, allura-allura ake kamo su da zaren labari, amma shi Sheme ba ya da wannan salon. Shi ya sanya hira ta ta fi ta kowa yawa. Bugu da qari, wanda duk zan je wurinsa, dama na haddace waqar sa a bisa kai, da na je saidai in yi ta rero masa baituttukan ina yi masa tambayoyi a kansu. Jin ina yin waqarsa za ta say a qara bada azama.
Gaba xayan aikin, Sheme na da jan qafa, ba ya da sauri. Ga shi ayyuka sun yi masa yawa. Ba ya da lokacin aikin littafin Shata. Ya na wallafa mujallar FIM, don haka ya na da ofis a Kano da Kaduna, daga baya ya buxe wani a Abuja. Ga aikin littafin Shehu 'Yar'aduwa. Kuma kullum ya na hanya, ba ya Kano ba ya Kaduna, ba ya Abuja. Gashi duk watan Duniya sai mujallarsa ta fito, kuma shi ke shirya ta yanda ya ke so, iyakaci ma'aikatan sa s nemo masa labaru. Amma saboda qwararren mai aikin jarida ne, kuma a Ingila ya yi kwas akan maxaba'ar littafi, shi ke tsara yanda mujallar za ta kasance don ta fito da kyau da inganci, kuma haka ta ke xin. Don haka, ya kasa zama ya tattara hankalinsa wuri xaya ya gama mana aikin mu. Shi kuma ya qi yarda ya bamu aikin mu tama shi, ya tattara ya riqe. Har ta kai an kai matsayin da ba mu ma san halin da ake ciki ba. Wannan ya sanya mu duka ukun mu ka ma vata da shi. Mun daxe ba mu magana ma. Sauran biyun su ka riqa lallashi na su na cewa 'mu rabi da shi, watarana in Allah Ya so ai dole ya gama aikin ya fiddo shi a buga'. A haka mu ka yi ta lallava shi har 2006 da aka buga littafin.
Wasu Abubuwan Takaici ma su ne:
A. wasu hirarrakin da na fassara a takardu na bashi na Hajiya Yalwa (matar) Shata da ta Musa Musawa da Laila Dogonyaro da Sidi Mijin Hotiho su ka vace ko salwanta a tsakanin kayansa saboda takardun sa sun yi yawa, kuma bai maida hankali ga aikin ba; ga na FIM ga na Tarihin 'Yar'aduwa. Saidai ni na dawo na sake rubuta wasu na bashi tunda su na cikin kai na na haddace su.
B. Hotunan da mu ka xauka da Shata lokacin wannan ziyara ta tarihi kala 12, da kyamarar Sheme mu ka xauke su, wadda ya sawo a Ingila. Amma an kai wata 3 ina fama da shi ya kai ta a zare dodon hoton a wanke mana hotunan nan, kada mu yi wasa da su don a tarihi ne. Har na ke kwatanta masa cewa kyamara sumatsi ke gare ta. Qarshe ya qi, har abinda ba a so ya faru ya faru. Rannan ya shigo Kaduna daga Zariya, a daidai NDA wani mutum ya tsayar da shi, ya xauko shi, jikkar da kyamarar ke ciki ta na a bayan mota (tunda da ita ya ke yawo) Wannan tsinannen mutumen ya zage jikkar ya xauke kyamarar, duk da fim xin da ke ciki na hotunan mu da Dodon waqa. Su na kai wa junction na Unguwar Sarki mutumin ya sauka. Sheme na qara gusawa gaba sai ya tuna, ya tsaya ya duba jikka ya ga mutumin nan ya sace wannan kyamara. To ka ga duk sakaci da nawar Sheme ta jawo mana haka. Yakamata Sheme ya bamu haquri akan wannan abin da ya yi mana. Nan dai wauta ce da sakaci.
To tunda an rabu da qyar kai ka yi karambanin koma ma mutum a yi wani littafin tare ? Idan ka koma ka sake haxewa da mutum, duk abinda ya biyo baya kai ka ja ma kan ka kada ka yi kuka da wani.
C. Lokacin da na tafi Katsina, bayan rasuwar Shata da wata 5, watau cikin Nuwamba 1999 sai na zarce Daura don in gana da Sarkin Daura, kan zancen yiwuwar xaukar xawainiyar bugawa. Tunda a lokacin babbar matsalar mu ita ce kuxin buga littafin. A fadar Sarki, aka ce mani ya na ciki ba za ya fito ba. Na gabatar da abin da ya kawo ni ga fadawa. Amma wani dogari ya ce mani idan na san wani mutum babba a Daura in je in samo takarda daga gare shi in kawo za su kai ma sa. Ana cikin maida magana sai su ka ji na ambaci Qanqara (gari na). Sai wani daga cikin su ya ce 'ai kuwa xazu da safe Ibrahim Tukur Qanqara manajan (tsohon almajrin mahaifi na ne a Qaramar Firamare ta Qanqara) Bankin Union na Daura ya zo su ka gaisa da Sarki, don mutumin sa ne. Sai su ka bani shawarar in tafi in same shi ofis. Na ruga na same shi, mu ka gaisa. Da na faxa masa abinda ke tafe da ni, wallahi summa tallahi,na rantse da Alkur'ani mai tsarki nan take ba vata lokaci ya xauko wayar teburi ya buga ma Sarkin Daura Bashar. Su ka yi magana, ya gabatar da ni ya kuma ce ina son inga Sarki akan littafin, Sarki ya ce ya faxa mani in zo ranar talata mai zuwa da qarfe 12 na rana in kuma zo da littafin, don Litinin ya na da taro a Kano. Ibrahim Tukur kuma ya tabbatar mani cewa shi za ya sanya Sarki ya biya kuxin buga littafin. Tunda na bar Daura (ran Alhamis ne) na tafi Kaduna, ba zullumin da na ke shi ne yanda zan raba Sheme da littafin nan, don na san da qyar za ya yarda ya bani littafin. Kuma haka ta faru, don da na je na bshi labarin yanda mu ka yi da Sarkin Daura, amma wallahi summa tallahi ya hana ni littafin. Na ce masa ran Lahadi na ke son in koma Katsina, in kwana ran Litinin in tafi Daura, wanshekare in tafi in ga Sarki. Da ya xauki zancen har zucci da ya bani shi tun Lahadin. Amma har Litini bai ba ni ba, ina ta da lallashin sa.
Ran Talata da safe na yi sammako na tafi gidan sa, na daxe a falo bai tashi barci ba. Matarsa ta shaida masa na zo. Sai da na daxe sannan ya fito ya bani littafin; don ya san bata yiwuwa. A lokacin qarfe 9 na sfe ta yi kuma ina a Kaduna, yaushe na gane Daura a cikin awa 3 ?
Abinda Sheme ke nufi shi ne; duk wani yunquri daga xayan mu a wurin sa aikin banza ne, ba mu isa ba, don ya raina mu. Ya na gani taimakon da za ya taso daga vangaren sa shi ne taimako, ba namu ba. Wai shugaban mu kenan a tafiyar Shata. Wallahi tallahi nan zance ya tsaya don ban ma tafi ba. Watarana nag a Ibrahim Tukur a Qanqara, ya tambaye ni mi yasa ban koma ba? Na faxa masa dalili. Ya ce 'Allah Shi kyauta'.
D. Cikn Maris 2000, sannan dangantaka ni da Sheme ta yi yami, sai na same shi a gidan Shehu Musa 'Yar'aduwa da ke kusa da gidan gwamnati na Katsina, na same shi da dare. Ni na je ne don idan akwai rashin jituwa mu gyara varakar, mu ba juna haquri, sannan a ga minene kuma za a dosa a gaba don a ci nasarar fitar wannan littafi. Amma sai Sheme ya same ni ya yi mani kaca-kaca, ya wulaqanta ni ya ce 'littafi ba a baka, ka tafi duk inda za ka kai ni qara ka kai ni, kuma ni da kai har abada, kada ka qara zuwa inda na ke, ko ka ganni a wuri kada ka nuna ka sanni. Har ya na buga mani misali, ya ce a rayuwarsa mutum biyu ya tava yi ma haka saboda sun harzuqa shi. Daga wani abokin sa (ya faxa mani sunan sa, na manta) sai ni. Ya kuma ce:' littafi, idan Alla Ya hukunta za a wallafa shi, to sai a wallafa, idan kuma Bai nufa ba to. Ina fita kuma sai ya zo ya wuce ni a mota ya tafi cikin gari, ni ina ta tafiya qasa. Yanzu saboda Allah, mai karatu ka na ganin Sheme ya yi adalci a nan ?. Wai shugaba kenan. Shi shugaba, na yi tsammanin ya kamata a ce ya na da haquri akan wanda yak e yi ma shugabanci, kuma idan an smu masala, ya kamata shi za a fara gayyatar mutane don a gyara, to ban da Sheme. Da haka ya yi mana shugabancin tafiyar Shata. Idan na yi masa qarya kada Allah Ya bani abinda na ke nema Duniya da lafira.
Ko an samu kuskure ko gyara, misali: a kan shekaru na faruwar wani abu, Sheme ba za ya gyara ba, ko da mun lurar da shi akan hakan. Ga hujja amma sai a yi ta gardama da shi. Da na fahmci haka, ko da na ga kuskure sai in yi shiru in qyale shi. Misali, a bukin 'Yan Sarki na su Ado Bayero, na ce Disamba 1952 ((tunda Galadiman Kano da Walin Kano da Sabo Dogarai da Inuwa Xalibi duk sun tabbatar mani haka) ne aka yi, shi kuma Sheme sai ya tsaya akan dole 1954 ne wai don ya ji Shatan na cewa '… a zamanin Sanusi Mamman' Na ce masa ai sannan Sanusi bai kai ga zama Sarki ba, ya na Ciroman Kano, amma shi ya yi hidimar bukin, shi ko Shata babu ruwansa, wanda ya ga ya na karakaina a buki shi a wurinsa shi ke da zamani. Misali na biyu shi ne ba Garba Goga ya fara kai Shata Funtuwa ba, don ya faxi haka a waqa ba dole ba ne a ce daidai ne, shi ya san abinda ya ke nufi da Kalmar. Bature makaxi Bakori shi ya fara kai Shata Funtuwa cikin Yuli 1943, sannan bai kai ga sanin Goga ba ma. Ba yanda ban yi ba da Sheme ya canza wannan zancen amma ya qi.
Tarihin da Sheme ya fi so na Shata shi ne gama-gari wanda kowa ya sani. Ni kuma tarihin Shata da na fi so ya fito a littafin mu shine voyayye, wanda ya yi nisa, wanda Duniya ba ta san da shi ba. Ka ga nan dole mu raba gari. Don abinda mutanen Duniya ba su sani ba game da Shata shi su ka fi son su ji. Shi ya sanya ake matuqar son hirarraki na na Rediyo da Telbijin fiye da kowanne mai bada tarihin Shata. Wannan ya sanya Idan Sheme bai san mutum ba ko bai tava jin labarin sa ba, ko na yi masa intabiyu na kawo masa ba ya sanyawa sai ya zubas. Kada Sheme ya manta, tarihin Shata ya fi karkata ga waxannan qasqantattun mutane maroqa da makaxa (tunda karkara ya tashi) da ya ke ganin shi ya raina.
Ina son idan za a yi hira da mutum, to a yi hira mai zafi, doguwa. Saboda ni mutum ne mai zafin hannu, mai azama, kamar dai yanda Shatan ya ke, watau tsaitsaye askin doki. To duk hirarrakin da abokaina su ka yi ba su gamsar da ni ba, don ba masu nauyi ba ne. Sabili da haka, galiban duk sai da na koma daga baya na sake hira da mutane, ba ma dai a nan qwaryar Kano. A baya kafin mu haxe, abokanmu sun yi hira da su Umaru da Uwawu da Hassan sarkin Dogarai, da Liman 'Yalleman, da sauran su, amma da ban gamsu ba sai da na bi su na sake ganawa da su, saboda ni abin na cikin jini na. Dama a rayuwata na fi son zama cikin dattawan mutane ba yara ba, shi ya sanya in na yi magana a rediyo sai a yi ta mamaki, ana cewa 'mun xauka tsarar Shata ne ma ashe ma yaro ne'. To zama da tsofaffi ya kawo haka. Kuma hira xaya tilo da wanda Shata ya yi ma waqa wallahi ba ta isa, sai an yi da yawa don a samu abinda ake so. Ta yiwu shi wanda ka je wurinsa tsoho ne, ya manta wasu abubuwa da yawa, to in ka koma sai ka qara samun abin da ya tuna kuma. Su abokaina da sun yi hira sau xaya shikenan, ni kuma naci ke gare ni, yawan zuwa na wurin mutum ke sanyawa mu ma zama kamar 'yan uwa ma.
Saboda wannan takardar yarjejeniya da mu ka rubuta shi ya sanya Sheme za ya yi ta yi mani cin kashi, kuma in yi ta haquri ba zan valle in samu 'yanci na ba? Ba zan yarda takarda ta tauye ni in rasa 'yanci na ba.
Za mu xora a gaba insha Allahu.