0
Alakar Mawaki da Al’umma: Tsokaci Cikin Shafukan Zumunta a Kafar Sadarwa ta Intanet Alakar Mawaki da Al’umma: Tsokaci Cikin Shafukan Zumunta a Kafar Sadarwa ta Intanet

                                      Daga                 Farfesa Salisu Ahmad Yakasai                Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya    ...

0
Bitar Ma’anar Kalmar ‘Hausa’ A Qarni Na 21: Al’umma; Harshe; Azanci; Qasa; Nazari Bitar Ma’anar Kalmar ‘Hausa’ A Qarni Na 21: Al’umma; Harshe; Azanci; Qasa; Nazari

Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' A Qarni Na 21: Al'umma; Harshe; Azanci; Qasa; Nazari Tsakure:  Masana sun yi ta yunquri a baya ...

0
HABAICI A WAQOQIN MATA NA DAVE DA NIQA A BAHAUSHIYAR AL’ADA HABAICI A WAQOQIN MATA NA DAVE DA NIQA A BAHAUSHIYAR AL’ADA

                                                               NA                                                 ZAINAB UMAR SALEH AMINU KA...

0
TASIRIN WAQA A YAU: TSOKACI DAGA WASU WAQOQIN GASA NA RANAR MAWAQAN HAUSA NA SHEKARAR 2017-2018. TASIRIN WAQA A YAU: TSOKACI DAGA WASU WAQOQIN GASA NA RANAR MAWAQAN HAUSA NA SHEKARAR 2017-2018.

            DAGA                      A. S. BELLO            (08033551751)                  SASHEN HAUSA KWALEJIN ILIM...

Alakar Mawaki da Al’umma: Tsokaci Cikin Shafukan Zumunta a Kafar Sadarwa ta Intanet



 

                                    Daga



                Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
               Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
          Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
                    syakasai2013@gmail.com
                        (+234) 08035073537









Makalar da aka gabatar a taron DANGIN JUNA MASOYA ALA FOUNDATION (karo na farko), a ranar Asabar, ashirin da uku (23rd) ga watan Yuni 2018, a É—akin taro na  Gidan Mambayya Kano, da }arfe goma.
Gabatarwa           

Harshe shi ne babbar kafa ko kuma hanya ta sadarwa tsakanin al'umma na duniya daban-daban. Ita kuwa al'umma É—aukacin mutanen da ke zaune ne a wuri ]aya, kuma suke da al'adu da É—abi'u iri É—aya (Yakasai, 2012). Wato da harshe ne ake aiwatar da mu'amala a magance (kamar waÆ™a) ko kuma a rubuce, musamman ma a wannan zamani na }auyantar da duniya (wato gulobalazeshin). Ko shakka babu, muhimmancin sadarwa ne ya haifar da samuwar hanyoyin isar da saÆ™onni ta kafar sadarwa babba ta duniyar Gizo (wato intanet). Mafi yawa daga cikin waÉ—annan hanyoyin sadarwa a kafar intanet sun yi tarayya cikin siga, wato a magance ta buga waya kai tsaye ko barin saÆ™o ta magana ko ta rubutu mai yawa ko saÆ™o kaÉ—an ko hotuna ko bidiyo ko kuma waÆ™oÆ™i ta sigogi daban-daban. 

Saboda haka, gudummawar harshe a sadarwa tana bijirowa ta hanya biyu, wato a magance ko kuma a rubuce. Ita hanyar magana domin sadarwa da]a]]iya ce kamar shi harshen kansa, wato kafa ce da kowa na iya amfani da ita la'alla ko ya iya karatu ko kuma bai iya ba. Ita kuwa hanyar rubutu ta bun}asa ne sannu a hankali a lokuta mabambanta cikin tarihi. Saƙo ta sigar waƙa (a magance ko kuma a rubuce), kamar yadda yake tasiri a mu'amalar al'umma shi ne al}iblar wannan ma}ala mai taken Alaƙar Mawaƙi da Al'umma: Tsokaci Cikin Shafukan Zumunta a Kafar Sadarwa ta Intanet.

Domin cimma wannan manufa, an karkasa ma}alar zuwa sassa biyar, É—auke da gabatarwa da kammalawa a sashe na farko da kuma na Æ™arshe. A sashe na biyu mun waiwayi ma'anar wa}a ne  da kuma yun}urin sanin ko wane ne mawa}i a mahangar masana. Daga nan kuma sai muka le}a kafar sadarwa ta intanet a sashe na uku. Sashe na hu]u kuma tsokaci ne dangane da ala}ar mawa}i da al'umma a shafukan sada zumunta. Ita kuwa wa}a (ta baka ko rubutacciya) ana rera ta ne ko aiwatarwa domin jan hankali ko isar da sa}o na musamman ga al'umma da ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum. Wannan ma}alar tana ]auke da wasu kalmomi wa]anda a kan su za a maida hankali kamar haka: wa}a da mawa}i da al'umma da kuma shafukan zumunta. Bibiyar wa]annan kalmomin zai taimaka sosai wajen warwarar zaren ma}alar.

2.0 Tsakanin Wa}a da Mawa}i          

Kowane lokaci a cikin al'umma akan samu wasu ba'adin mutane ]ai]aiku da sukan bayar da gagarumar gudummawa iri daban-daban domin ci gaban rayuwarsu. Daga cikin wa]annan mutane akwai mawa}i. Masana adabin Hausa sun raba wa}o}in Hausa zuwa gida biyu, wato akwai wa}o}in baka na gargajiya wa]anda maka]a ke ha]awa tare da ki]a. Irin wa]annan wa}o}i an da]e ana yin su a }asar Hausa, kusan ma ana iya cewa tare suka ginu da al'ummar Hausawa. Kaso na biyu kuwa shi ne na rubutacciyar wa}a, ita wannan ta samu ne a sakamakon cu]anyar Hausawa da wasu ba}in al'ummu musamman Larabawa da Turawa. To idan haka ne (wanda kuma haka ]in ne), to mece ce ma'anar wa}a?

Ra'ayoyi mabambanta na masana da manazarta adabi, sun yi ta karo da juna wajen tsayar da ma'ana guda ]aya dangane da wa}a. Sai dai kuma abin sha'awa, dukkan ma'anonin da aka gabatar za a same su suna magana ne da siga iri ]aya. Ka]an daga cikin su sun ha]a da: Umar (1980) yana ganin "Wa}ar baka a Hausa kamar sauran harsuna tana zuwa ne a rere cikin sautin murya ko rauji". Wato rerawar da ake yi wa wa}a ya sa ba ta zuwa a shimfi]e gaba ]ayanta, sai dai ta zo gunduwa-gunduwa tare da amshi a tsakaninsu. Shi kuwa [angambo (1982) cewa ya yi "Wa}a wani sa}o ne da ake gina shi kan tsararriyar }a'ida ta baiti da ]ango da rerawa da kari (bahari) da amsa-amo (}afiya) da kuma sauran }a'idojin da suka shafi daidaita kalmomi da za~insu da amfani da su a cikin sigogin da ba lallai ne haka suke ba".

Haka kuma Yahaya (2007) cewa ya yi "Wa}a tsararriyar magana ce da ta }unshi sa}o cikin za~a~~un kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba fa]uwa kurum ba". Da wannan ne kuma {amusun Hausa ya jaddada cewa "Wa}a wata tsararriyar magana ce da aka yi a kan kari ko rauji" (CNHN, 2006). Wa]annan bayanai sun nuna cewa wa}a wata manufa ce da akan bayyana a rere ta hanyar amfani da amsa-amo ko kuma rerawa ta zama ta sautin murya mai za}i, wata sa'a kuma da ha]awa da ki]a da sauran salon jin da]i ga mai sauraro domin jawo hankalinsa ga manufa. Haka kuma wa}a ta sha bamban da maganar baka ta yau da kullum da zube da kuma wasan kwaikwayo (Auta, 2001). A gaba ]aya dai wa}a ta bambanta daga ta]i ko magana ta yau da kullum. Hasali ma, ita aba ce wadda ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna }warewar harshe. Saboda haka, harshen wa}a a bisa kansa cikakke ne, duk da cewar ya kauce wa wasu }a'idojin nahawu (Gusau, 2000).

Wa}o}in da aka tsara a ka, aka adana a ka, aka kuma rera su da baki (wato wa}o}in baka na Hausa) wa}o}i ne da ke da tarin yawa kuma kullum suke }aruwa a }asar Hausa, musamman ma a wannan }arni na ashirin da ]aya ({21). Duk da yawan da suke da shi, idan aka dubi nazarce-nazarcen da aka gudanar a kansu, sai a ce har yanzu da sauran aiki a gaban maza. Dangane da lokacin da aka fara nazarin wa}o}in baka kuwa, ko shakka babu za a iya cewa an fara ne tun a farko-farkon }arni na 20, wato lokacin da Turawa kamar su Prietze (1916, 1918, 1930) da Greenberg (1949) da Smith (1957) da Kirk-Green (1961) da  Ames (1965, 1973) da King (1969) da Richard (1972) da Hoftsad (1973) da Besmer (1973), sannan kuma su Gidly (1975) da Kraft (1976) da Furnis (1977, 1978, 1982) da sauransu suka nazarci wasu wa}o}i ko kuma wani abu da ya shafe su kai tsaye.

Bayan shu]ewar wa]annan manazarta ne, sai aka samu shigowar 'yan }asa a cikin fagen, duk da cewa an ci gaba da samun 'yan tsirarun Turawa da suka ci gaba da nuna sha'awarsu a lamarin nazarin, wato ba su watsar da harkar gaba ]aya ba. 'Yan }asa da suka fara sa hannu a lamarin sun ha]a da Abdul}adir (1975) da Bichi (1985) wa]anda suka yi digiri na uku, sannan sai manazarta da suka yi digiri na biyu da na ]aya. Har ya zuwa yanzu ana samun masu sha'awa a jami'o'in gida da na waje, wato Hausawa da Turawa. A fagen nazari, ana iya gane wa}a ta baka ko rubutacciya ta duban ma'aunan da Jackman (1977) ya kawo kamar haka:
Rashin tsayin magana
Za~a~~en amo da rauji mai nanatuwa
Harshen musamman
Za~in kalmomi da ma'anoni
Rerawa          

Ta ]aya haujin kuma, mawa}i mutum ne da Allah (SWT) ya horewa hikimar za~en kalmomi da iya sarrafa su a cikin azanci da basira, wato ya tsara baitukan da suka }umshi zantuka masu ma'ana. Mawa}i mutum ne mai hangen nesa da hasashen gaba, mutum ne mai lura da al'amuran yau da kullum cikin hikima. Ga misali, idan ka ]auki wa}ar Sa'adu Zungur ta Arewa Jumhuriya ko Mulukiya, sai a ga kamar yanzu aka tsara ta, saboda  marubucin nata ya hango wa Arewa halin da za ta iya shiga a cikin shekaru da yawa masu zuwa. Wannan shi ne hasashe kan hangen nesa. Ke nan mawa}i kamar garkuwa ne ga jama'arsa da ke kare mutuncinsu, ya kare tarihin al'ummarsa, ya kare 'yancin jama'arsa. Mawa}i ke kare shugabanni masu adalci, sannan ya zaburar da mutanensa a kan aikata aiki nagari. Hasali ma, shi ne ke fa]akar da su a kan su farka daga barci su kuma san ciwon kansu.

A ra'ayin Gusau (2001:30-4) akwai hanyoyi uku wa]anda da wuya marubucin wa}a ya kasa fa]awa a cikin ]ayansu. Wa]annan hanyoyin kuwa su ne na jibilliya da koyo da kuma lalurar rayuwa ko tsananin wata bukata. Jibilliya kalmar Larabci ce da ke nufin hanya ta ]abi'a wadda ake haihuwar mutum da ita. Mutum zai tashi da hikima da basirar tsarawa da rubuta wa}a, shi kansa ma zai ji wa}a tana zo masa ne kawai. Koyo kuwa hanya ce ta zama da wani wanda ya iya wa}a, musamman idan yana yi masa hidima wadda ta shafi wa}a kai tsaye. Shi ma irin wannan mutum sannu a hankali yakan kasance mawa}i. Lalurar rayuwa ko tsananin wata bukata kuwa, wannan ma wani dalili ne da yakan sa mutum ya tsara wa}a a rubuce. Ga misali, bege ko ciwon soyayyar wani abu ko tsoron wani abu kamar talauci da sauran abubuwa na juye-juyen zamani za su iya haifar da rubuta wa}a. Daga cikin halayen da mawa}i ke iya siffantuwa da su kuwa, akwai zama mai wadataccen ilimin rayuwar ]an'Adam, ko ya zama mai tambaya ko mai bincike ko mai lura da harkokin rayuwa. Haka kuma, tattare da wannan mawa}i ya zama mai hikima da basirar zayyana abubuwa dalla-dalla.
 
3.0 Mu Le}a Kafar Sadarwa ta Intanet

Samuwar kafafen sada zumunta da muhawara a 'yan shekarun nan, ya taimaka matu}a gaya a matsayin kafa ta sadarwa mafi inganci da ]an'Adam ya }ir}iro. Ida ana maganar shafukan zumunta, to ana magana ne a kan abubuwa irin su imel da waz'af da fesbuk da istagiram da biba da nimbiz da jobaman da kakatak da sikayif da badoo da yutub da sauransu. Amma da alamun babu wanda zai yi jayayya idan aka ce duk rawar da shafukan zumunta suke takawa da bazaar intanet suke ta}ama. Idan haka ne (wanda haka ]in ne), to akwai bukatar mu waiwayi intanet.

A wannan zamani da muke ciki, amfanin da ke tattare da intanet yana da yawa. A }asashen da suka ci gaba (kamar Nahiyar Turai da Asiya da kuma wasu }asashe na Afirka), ana amfani da intanet wajen tafiyar da kasuwanci da siyasa da ha~aka ilimi ta hanyar bincike da nazari da kuma tattaunawa. Haka kuma ana aiwatar da hira ko musayar ra'ayi, ana kula da lafiya da tsaro da dai ayyuka da dama da suka shafi ci gaban rayuwa na yau da kullum. Don haka, har kullum ana ci gaba da inganta hanyoyin amfani da fasahar intanet. {ididdiga ta shekarar 2011 ta nuna cewa a}alla kashi 35% na al'ummar duniya ke amfani da intanet a wancan lokaci. Idan aka kwatanta wannan adadi da kashi 18% da ke amfani da intanet a shekarar 2006, za a ga cewa an sami ci gaba sosai. Wannan ya nuna irin kar~uwar da intanet take da]a samu a fa]in duniya. Haka abin yake ko a Nijeriya, duk da yake intanet ba ta da]e da samun wajen zama ba, hasashen }ididdigar Ayo da wasu (2011) da aka gudanar a shekara ta 2010 ya nuna cewa kimanin mutane miliyan arba'in (40,000,000) ke amfani da intanet a Nijeriya.

A ta}aice dai, intanet ita ce babbar hanyar sadarwa ta duniya baki ]aya. Wato matsayinta ya zarce a kwatanta shi da duk wata hanya ta sadarwa, musamman ma idan aka yi la'akari da yadda lamarin intanet yake da]a samun kar~uwa da tagomashi a duniya. Gudanar da wannan kafa ta sadarwa ya ta'alla}a ne ga amfani da harshe. Masana irin su Crystal (2001) da Rumsiene (2004) da Muhammad (2004) da Amfani (2007) da kuma Kurbalijia (2010) sun tabbatar da cewa harshen da ake amfani da shi wajen sadarwa a intanet shi ne harshen Ingilishi. Kasancewar intanet ana tafiyar da ita ne da Ingilishi, shi ya sa ta zamo sinadarin gulobulazeshin (wato shirin game duniya). Tun a shekarun 1995 ne, shugaban kamfanin Microsoft Bill Gates ya yi hasashen dun}ulewar duniya ta yadda kowa zai iya sarrafa bayanai da ilimin da ya shafi fannonin rayuwa mabambanta cikin sau}i da lokaci. A dalilin haka ne intanet take da]a kutsawa cikin kowane sha'ani na rayuwar ]an'Adam na yau da kullum.

 Kasancewar harshen Hausa Mahadi mai dogon zamani, ko bayan zamansa harshen sadarwa ga kimanin mutane miliyan talatin da biyar (35,000,000) a }asashen Yammacin Afirka in ji Newman (2000) da Schuh (2001), harshen Hausa ya yi kaka-gida ga al'ummai da dama a }asashen Afirka. Amfani (2005) ya ce Hausa ita ce harshen farko ga mutane fiye da miliyan ashirin a }asar Nijeriya kawai. Ya kuma }ara da cewa akwai kimanin mutane miliyan hamsin (50,000,000) Hausawa wa]anda ke jin Hausa. Wannan }ididdiga tana nuna mana irin martabar Hausa da har ta sami kasancewa ]aya daga cikin manyan harsunan }asa a Nijeriya, kuma wani yaro da gari abokin tafiyar manya a duniyar sadarwa ta intanet. Tambayar a nan ita ce, wace irin rawa ce Hausa ke takawa cikin ala}ar mawa}i da al'umma a shafukan zumunta na intanet? Domin amsa wannan tambaya, bari mu juya akalarmu zuwa ga amfani da wa}a a shafukan sada zumunta.

4.0 Amfani da Wa}a a Shafukan Sada Zumunta      

Masana ilimin walwalar harshe sun yi ittifa}i dangane da hanyoyi daban-daban da ]an'Adam yake amfani da harshe domin biyan bukatunsa. Wato baya ga abin da ya shafi tsarin sauti da nahawu da }irar kalmomi na harshe, to akwai kuma abin da ya ta'alla}a ga sarrafa ainahin ita kanta magana (Fasold, 1984). Irin wa]annan maganganu (a wa}e ko a rubuce) sukan bambanta dangane da yanayi da wuri da kuma matsayin masu wa}ar ko rubutun da kuma wa]anda aka yi wa}ar ko rubutun a kan su. Ke nan, lamarin ya dace da tsarin nan na la'akari da abubuwa uku da kan zo a zuciya, a duk lokacin da za a fa]i wani zance ko bayar da umurni ko kuma yin wa}a. Wa]annan abubuwa guda uku, wa]anda sauyawar ]aya daga cikinsu ke sauya jigo sun ha]a da:
Darajar masu saurare a idanun mawa}i
Abin da ake wa}a a kansa
Wuri ko muhallin da ake gudanar da wa}ar (Yakasai, 2012).

A wannan sashe, za mu kalli yadda ma'abuta kafar sada zumunci ta intanet suke amfana da wa}a cikin mu'amala. Mawa}a suna amfani ko sarrafa kalmomi ta hanyoyi akasin yadda aka saba domin bayyana ma'ana da tunani da kuma sosuwar rai (jin zuciya) ga mai karatu ko sauraron wa}o}insu. Irin wannan yanayi, wata dama ce da mawa}i ke amfani da ita wajen sarrafa adon harshe (ko adon magana) domin inganta wa}a. Galibi mawa}a suna yin haka ne a wani yun}uri na adana ]orewar hawa da sauka na murya (Abdulsalam, 2013). A ra'ayin Mukarovsky (1964), shi kansa harshen wa}a yana }unshe da nasa kalmomi da sassan jumla da kuma uwa-uba tsarin nahawu. Dalili kuwa shi ne mawa}a sukan karya dokokin nahawu ta hanyar sassa}a sassan harshe cikin za~in kalmomi da hawa da sauka na murya da ma'ana da kuma daidauta sahun kalmomi domin dacewa. Wannan ne ha}i}anin abin da Bierwisch (1965) ya jaddada da cewa harshe da kuma nahawun wa}a wani tsari ne na musamman da ke aiki a bisa nahawun kowane harshe. Wannan tsari ya ha]e har da akasin hanyoyin nahawu na amfani da harshe da suka ji~anci azuzuwan kalmomi da nahawu domin daidaitawa da kuma dacewa (Leech da Short, 1981).

Sai dai kuma batun da yake karakaina a duniyar sadarwa ita ce ta yadda wa]annan shafukan sada zumunta da muhawara sukan yi tasiri cikin tunanin al'umma. Harshe ya }unshi abubuwa da yawa kuma masu muhimmanci ga rayuwar ]an'Adam kamar tunaninsa da kuma addininsa, kai da ma dukkan al'amarin da ya shafi rayuwar kowace al'umma. A kowane lokaci, kana iya ganin mutane a wuraren bukukuwa ko tarurrukan }arawa juna ilimi sun maida hankali ga wayoyinsu na tafi-da-gidanka suna amfani da shafukan sada zumunta da muhawara irin su fesbuk da waz'af da istagiram da tiwita da sinafsho. Wa]annan shafukan sada zumunta suna ba da dama ga mutane su aika da sa}onni da hotuna da bidiyo da kuma uwa-uba musayar ra'ayi. To shin wa]annan shafuka suna biyan bukatar aikin da aka tanade su dominsa ko kuwa suna tasirantar da tunanin al'umma?

Da yake  wa]annan hanyoyi suna ]amfare ne da fasaha da kimiyar zamani, to ba su da kwatankwacin sunaye a bahaushiyar al'ada, kuma wannan ne dalilin da ya sa bayanin yadda suke aiki yake tabbatar da wanzuwarsu. Gaskiyar maganar ita ce, a yanzu ana iya samun kowane irin bayanin ilimi a cikin intanet. Masarrafar da ke taimakawa mai bincike wajen nemo bayanai kuwa ita ce ta matambayi ba ya ~ata. Wannan wata manhaja ce da take nemo nau'o'in bayanai da ke ma}are a intanet ta hanyar shigar da kalma ko kalmomin da suka shafi irin bayanin da ake so (Almajir, 2008). Akwai hanyoyin neman bayanai iri biyu: (a) shigar da kalma ko kalmomi da suka shafi irin bayanin da ake nema kai-tsaye zuwa masarrafar nemo bayanai, sannan a ba ta umurni ta nemo. (b) samun kalmomin da suka shafi fannoni daban-daban a jere a jikin allon kwamfuta, domin za~in wadda ake bukata. Saboda haka ana iya samun dukkan bayanan da ake nema kama daga }ere-}ere da fasaha da kimiyya da siyasa da adabi da al'adu na kowane lungu da sa}o na duniya.

Babu shakka samuwar wa]annan shafuka na sada zumunci da muhawara sun kawo ci gaba a fannin sadarwa. Ko ba komai dai, an sami hanyar sadarwa kai tsaye wadda ta }ara }arfafa zumunci da kuma taimakawa wajen cinikayya da siyasa da addini da kuma zamantakewa. Amma kuma kash, wa]annan shafuka na sada zumunci da muhawara suna kuma haifar da wasu matsaloli masu gur~ata al'umma, kamar }arya da fankama da son-iyawa. Sauran wa]annan matsaloli sun ha]a da sauya tunani da ~ata tarbiyya da nuna hotuna da bidiyon batsa da wa}e-wa}en banza da kuma uwa-uba satar fasaha ta hanyar zamba cikin aminci. Da yake a cikin ido ne ake tsawurwa, bari mu karkata ga yadda ala}ar mawa}i da al'umma take wanzuwa, da kuma irin sakamakon dake bijirowa ta irin wannan ala}a har al'umma gaba ]aya ta fa'idantu.

Da farko dai shafukan sada zumunta sun share fagen shimfi]a ko kuma }ulla zumunta tsakanin mawa}a da al'umma. Irin wannan zumunta ita ce ta ke ci gaba da yau}a}a cikin soyayya da kuma }aunar juna. Ga misali, assasa hurumin ha]uwarmu a rana irin ta yau a }ar}ashin Al-mutahibbuna fillahi (wato Dangin Juna Masoya ALA Foundation) ya samo tushe ne daga gudummawar wa]annan shafuka na sada zumunta. Ta wa]annan shafukan ne kuma mu'amala take gudana tsakanin mawa}in da masoyansa, da kuma su masoya ALA a tsakaninsu. A wani sa}o ta shafin waz'af, ga sa}on ALA ga masoya:

                  Masoyana ku yi subscribing channel ]ina idan
                  kun shiga, daga rana irin ta yau zan fara saka
                  wa}o}ina cikakku na bidiyo masu }ayatarwa,
                  ku sami abin kewa da ilimi ta wannan hanya da
                  halali ba da hululi ba.

Domin tabbatar da ]orewar irin wannan ala}a tsakanin mawa}i da kuma al'umma, kafin ka ce kwabo har sa}on ALA ya kai ga wa]anda ya tanada dominsu (wato rukunin mutane daban-daban daga cikin al'umma). Daga cikin irin wannan rukuni na al'amma akwai sarakuna, kuma ga abin da Mai Martaba Magaji Galadiman Mai Tsidau ya amsa daga wancan sa}o na ALA:

                   MashaAllah! Godiya sosai sosai kuma Allah
                   ya }ara basira da hikima da ]aukaka da kuma 
                   kariya alfarmar Rasulullahi Sallallahu Alaihi 
                   Wasallam. Sannu hukuma mai zaman kanta.

Wani muhimmin lamari kuma mai ala}a da wannan da ya gabata shi ne, mawa}i yana samun dama ta renon masoya da magoya baya daga rukunin al'umma daban-daban (da suka ha]a da maza da mata da ]alibai da ma'aikatan gwamnati da sarakuna da sauransu) a shafukan sada zumunta. Da yake rukunin jama'a ya }unshi ]ai]aikun mutane wa]anda suka yi tarayya ta fuskar zamantakewa ko tattalin arzi}i (Yakasai, 2012), to ta hakan ne kuma su ma al'umma suke zama abokai da 'yan uwan juna na har abada. 

Ta hanyar amfani da wa]annan shafuka na sada zumunta, mawa}i yana bun}asa sana'arsa ko kuma kasuwancinsa, su kuma al'umma suna samun bayanai dangane da sana'ar mawa}i (musamman sababbin wa}o}i da kuma hanyoyi ko wuraren da za a same su). Ga misali, mawa}i kan tallata hajarsa ta kusan dukkan wa]annan shafuka na sada zumunta, wa]anda a cikin lokaci }alilan su isa ga al'umma. Su kansu al'umma sukan yi ta bibiyar mawa}i ta irin wa]annan shafuka kamar istagram da tumbula da yutub ko tiwita domin samun bayanai game da mawa}i da wa}o}insa da ]umi-]uminsu. Ta haka kasuwanci ke wanzuwa tsakanin mawa}i da al'umma, kuma sannu a hankali har ya samu ]orewa.

Da yake yau da gobe ba ta bar komai ba, mawa}i da al'umma suna tasirantuwa da juna, musamman ta hanyar sauraron wa}o}insa da kuma ba da shawarwari da martani. Ta haka ne ala}ar take samar da yanayin gyara kayanka (wanda masu hikimar magana suke cewa baya zama sauke mu raba). Wato mawa}i yana isar da sa}onni daban-daban zuwa ga al'umma wa]anda ke da tasiri ga inganta rayuwarsu. Shi kuma mawa}i yana tasirantuwa da shawarwari da martani dangane da yadda zai inganta sana'arsa ta samar da wa}o}i da suka dace da bukatar al'umma.

Shafukan sada zumunta sun zamo hurumin da kan samar da sha'awa da ba da }arfin gwiwa, domin gudanr da nazarce-nazarce da kuma bincike-bincike na ilimi. Sau da yawa masana da manazarta a jami'o'i da sauran manyan makarantun ilimi suna samun wa}o}i daban-daban da suke gudanar da nazari ko bincike a matakai daban-daban (digiri na ]aya da na biyu da kuma digirgir). Sakamakon irin wa]annan nazarce-nazarce da bincike-bincike suna fa'idantar mawa}i da kuma al'umma gaba ]aya. Ga misali, an tanadi bayanan sakamakon irin wa]annan nazarce-nazarce a tarukan }arawa juna ilimi a shafin www.amsoshi.com Shi kuma mawa}i yana samun }arin }arfin gwiwa da karsashi na ci gaba da yin wa}o}i da za su fa'idantu ga al'umma.

Ta fuskar nuni cikin nisha]i, mawa}i na jefe tsuntsaye da yawa da dutse guda ]aya. Hasali ma, ai rayuwa cikin farin ciki da annashuwa, ita ce garkuwa daga damuwa da ba}in ciki. Da farko dai mawa}i yana samar da wa}o}i daban-daban domin nisha]antar da al'umma. Da yake rai dangin goro ne (wato yana bukatar a ba shi iska), to yakan nisha]antu daga sauraron wa}o}i daban-daban, da yake ji da gani da kuma sauraro a irin wa]annan shafuka na sada zumunci. Ta ]aya haujin kuma, mawa}i kan yi amfani da wa}o}i wajen nusar da al'umma wasu muhimman al'amura, da suke ]amfare da zubi da tsarin rayuwarsu. A sanadiyar irin wa]annan wa}o}in kuma sai al'umma ta ilimantu.

Ta fuskar tarihi kuwa, gaskiya ne cewa duk a'ummar da ba ta da  tarihi, to al'ummarta na tafarkin salwanta da ~acewa. Daga tarihin kowane harshe ne ake samun tarihin al'ummar da ta yi amfani da shi a zamanin da ya shu]e. A nan harshen mawa}i wani sinadari ne na zayyano muhimman al'amura da suka auku a cikin rayuwar al'umma. Sau da yawa mutane ba su da cikakkiyar masaniya game da irin wa]annan al'amura da aukuwarsu a tarihance. Ga misali, ]auki wa}ar ALA ta mashigan Kano ko sarakunan Fulani ko tagwayen-masu da ]imbin tarihin da ke cikinsu. Ta haka ne mawa}i yake tunasar da al'umma tarihinsu domin fa'idarsu gaba ]aya.

Tarihi ya kuma tabbatar da kasancewar mawa}i mai adana harshe da al'adun al'umma. Saboda haka ne ma yake amfani da wa}a a matsayin wani makami na zaburar da al'umma da kuma wayar masu da kai. Da yake mawa}i mutum ne da kowa ya yi ittifa}i cewa ya na}alci amfani da harshe, to mawa}i yana amfani da basirarsa cikin wa}o}insa domin fa]akar da al'umma abubuwan da ka iya kawo cikas ko na}asu ga rayuwa. Wannan ya nuna cewa mawa}i mutum ne da a kowane lokaci yake la'akari da harshensa da kuma wa}o}insa domin bayyana duniyar da yake rayuwa a cikinta. Da irin wannan mu'amala ta cu]e-ni-in-cu]e-ka ne mawa}i da al'umma suka zamo abokan juna.

Shafukan sada zumunta na kafar sadarwa ta intanet suna samar da hurumi na samun fahimtar juna ko akasin haka nan take. Da yake kowa yana da dama ta bayyana ra'ayinsa dangane da shu'unan rayuwa, to nan da nan al'umma kan bayyana fahimtarsu ko kuma rashin fahimtarsu. A nan addini ne zakaran gwajin-dafi, wato sanin muhimmancin addini ya sa rawar da mawa}i yake takawa wajen nusar da al'umma ba }arama ba ce. [auki wa}ar ALA ta shugaban halitta ganganko ko ta azumi ko kuma bu}u}uwa.  Haka ma lamarin yake ta fuskar siayasa, wato mawa}i na wayar da kan al'umma dangane da siyasa (wato zubi da tsarin shugabanci da yadda ya kamata al'umma ta gudanar da shi). A nan ma wa}o}in ALA na farfaganda da sambarka da wa}ar Buhari sun isa misalai.
   
5.0 Kammalawa            

 Abin da ya gabata a wannan ma}ala, tsokaci ne cikin ala}ar mawa}i da al'umma a shafukan sada zumunta na kafar sadarwa ta intanet. A kullum mawa}a cikin rera wa}o}i suke a kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al'umma. Ta haka ne ma irin wa]annan wa}o}i suka zamo madubi na kallon rayuwar al'ummar. Daga cikin irin ala}ar da ke akwai tsakanin mawa}i da kuma al'ummar da yake yin wa}a domin ingantawa, akwai }ulla ita kanta zumuntar a tsakaninsu. Da sannu a hankali ne ita wannan zununtar take bun}asa har a narke a zamo abu ]aya. Ta haka kuma mawa}i yana samun dammar renon masoya da magoya baya daga sassa daban-daban a shafukan sada zumunta. Ana kuma samun fahimtar juna nan take, kuma shafukan na kasancewa hurumi na tabbatar da so da }auna ga mawa}i da kuma al'umma. Mawa}i yana samun damar bun}asa sana'arsa ta samun ]imbin magoya baya da ke bubiyarsa a istagram da yutub da tiwita, a yayin da al'umma ke samun gamsuwa cikin mu'amala da mawa}in ba tare da wata matsala ba. Bugu da }ari, mawa}i da al'umma duka suna tasirantuwa da juna cikin wa}o}i da shawarwari da kuma martini. Sai dai kuma duk da ]imbin wa]annan alhairai, akwai kuma wasu abubuwa na akasi da akan samu a cikin irin wannan dangantaka a shafukan sada zumunta (wato masu gur~ata al'umma) da suka ha]a da }arya da fanklama da son-iyawa da ~ata tarbiya da nuna hotuna da bidiyon batsa da wa}e-wa}en banza da kuma uwa-uba satar fasaha.


                               MANAZARTA

Abubakar, A. L. (2015): Shahara: Alfiyar Alan WQa}a, Kano: TASKAR ALA GLOBAL.

Amfani, A. H. (2005): '{amusun Hausa Cikin Hausa", Ma}alar da aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato.

Amfani, A. H. (2012): "Hausa da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe", Cikin Champion of Hausa (A Festschrift in Honour of [alhatu Muhammad, Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Barista, M. L. (2011): Wa}o}in Aminu Ladan Abubakar, Kano: Iya Ruwa Publishers.

CNHN (2006): {AMUSUN HAUSA na Jami'ar Bayero, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

[angambo, A. (1984): Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company Ltd.

Gusau, S. M. (2001): Wasu Sanabe-Sanaben Rubuta da Nazarin Rubutattun Wa}o}i na Hausa, Kano: Rock Castle.

Gusau, S. A. (2003): Jigon Nazarin Wa}ar Baka, Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Halilu, S. (2015): Jigon Fa]akarwa a Wa}o}in Aminu Ladan Abubakar, Unp. M. A. Thesis, Nigerian Languages Department, Usmanu Danfodiyo University.

Illigworth, V. (1996): Oxford Dictionary of Computing, New York: Oxford University Press.

Jackman, M. (1997): Introtopoetry.htm

Sar~i, S. A. (2007): Nazarin Wa}o}in Hausa, Kano: Samarib Publishers.

Woolger, D. (1978): Images of Impression: An Oxford Senior Poetry Course, Oxford University Press,

Yahaya, A. B. (2007): Jigon Nazarin Wa}a, Kaduna: Fisbas Media Services. 

Yakasai, S. A. (2012): Jagoran Ilimin Walwalar Harshe, Sokoto: Garkuwa Media Services.

Yakasai, S. A. (2014): "Some Major Themes in Hausa Responsorial Songs in Aminu Ladan Abubakar's Performance" in Current Perspective on African Folklore (A Festschrift for Professor [andatti Abdul}adir), Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Yakasai, S. A. (2015): Hausar Mawa}a: Yadda Take da Kuma Yadda ake Amfani da Ita a Wa}a, Taron Ranar Mawa}a ta Duniya, Jihar Kaduna.

Yakasai, S. A. (2016): Sa}on Yau Domin Gobe: Mawa}i a Rigar Malanta Cikin Wa}ar KUSHEWA ta Aminu Ladan Abubakar, Ranar Mawa}a ta Duniya, Jihar Jigawa.











 

Bitar Ma’anar Kalmar ‘Hausa’ A Qarni Na 21: Al’umma; Harshe; Azanci; Qasa; Nazari

Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' A Qarni Na 21:
Al'umma; Harshe; Azanci; Qasa; Nazari
Tsakure: 
Masana sun yi ta yunquri a baya wajen rawaito asalin kalmar Hausa sai dai har yanzu ba a cimma wata qwaqqwarar matsaya game da inda tushen kalmar ya tusgo ba. Domin tarihin Hausawa da na samuwar kalmar ta Hausa al'amari ne da zai yi wuya a iya haxuwa bisa matsaya xaya sakamakon rashin tabbataccen rubutun da za a iya dogara da shi wajen sanin haqiqanin yadda qasar Hausa ta kafu da bayanin mazauna cikinta na farko da yadda al'amura suka cigaba da wakana daga zamani zuwa zamani; illa iyaka a cigaba da kintatowa har zuwa sa'ar da bincike zai tabbatar da gaskiyar yadda al'amarin yake. Amma idan aka jingine batun asalin kalmar to za a iya kallon ma'anar Hausa ta mabambantan fuskoki kamar yadda Ibrahim (1978) da Vavura (2008) suka kalle ta a matsayin kalma mai iya xaukar ma'anar harshe da mutanen da suke magana da harshen da kuma qasar da ake amfani da harshen. Bisa irin waxannan bayanai ne aka qara da cewa: Hausa kalma ce mai faffaxar ma'ana da take wakiltar Hausawa da harshensu da azancinsu da qasarsu da kuma nazarin al'amuransu. Wato kalma ce da ta qunshi mabambantan ma'anoni a qalla guda biyar masu alaqa ta qut da qut da junansu, musamman ta fuskar jama'a da yaren da suke magana da shi a matsayin harshensu da dabarun sarrafa tunani cikin harshen nasu da qasar da suke tutiya da ita a matsayin mazauninsu na dindindin da harkar nazari a fagen ilimin harshe da adabi da al'adu na Hausawan a makarantu da kwalejoji da jami'o'i a faxin duniya. 
Mahimman Kalmomi: Bita; Hausa; al'umma; harshe; azanci; qasa; nazari; qarni na 21 

Revisiting the Term 'Hausa' in the 21st Century:
Society; Language; Wisdom; Motherland; Studies
Abstract:
The research reported in this article is a review about the 'Hausa' term as it is employed over centuries by the Hausa natives to represent their homeland, language and the wisdom attributed to the usage of the language. However, a number of varied narrations have been put forward by scholars at different occasions in an endeavor to account for the origin of the term as well as early inhabitants of the present day Hausaland but never reach consensus due to lack of documented evidence. As an alternative to revisiting the history of the word, this paper focuses on the meaning of the term 'Hausa' as it is continually used in modern-days within the outline of Ibrahim (1978) & Vavura (2008), as they described it as a word which entails the Hausaland, people and their language. Additionally, the research elaborated that the term can be used to refers to the Hausa society, their language as a means of communication, the wisdom manifested in their language, their motherland and a field of studying the linguistic system, literature and cultural aspects of the people commonly found in Northern Nigeria, Niger and the diaspora.  
Keywords:  Revisiting, Hausa, society; language; wisdom; motherland; studies
Yusuf Nuhu Inuwa, BA, PGDE, MA, (PhD)
School of Languages, College of Arts, Sciences and Remedial Studies, Kano
+2348060444074/yusufnuhu84@gmail.com
Gabatarwa
Masana sun yi ta yunquri a mabambantan lokuta wajen rawaito asalin kalmar Hausa sai dai har yanzu ba a cimma wata qwaqqwarar matsaya game da inda tushen kalmar ya tusgo ba. Saboda asalin Hausawa da tarihin samuwar kalmar ta Hausa al'amari ne da zai yi wuya a iya haxuwa a kan matsaya xaya jal sakamakon rashin tabbataccen rubutun da za a iya dogara da shi wajen sanin haqiqanin yadda qasar Hausa ta kafu da bayanin mazauna cikinta na farko da kuma yadda al'amura suka cigaba da wakana zamani bayan zamani; illa iyaka a cigaba da kintatowa har zuwa lokacin da bincike zai tabbatar da haqiqanin yadda al'amarin yake. Amma idan aka jingine batun asalin kalmar ta Hausa to za a iya kallon ma'anar ita kanta kalmar ta mabambantan fuskoki kamar yadda masana suka kalle ta a matsayin kalma mai iya xaukar ma'anar harshe da mutanen da suke magana da harshen da kuma qasar da ake amfani da harshen. Bisa irin waxannan bayanai ne aka qara da cewa Hausa, kalma ce mai faffaxar ma'ana wadda take wakiltar Hausawa da harshensu da azancinsu da qasarsu da kuma nazarin al'amuransu. 
A taqaice, Hausa kalma ce wadda ta qunshi mabambantan ma'anoni a qalla guda biyar waxanda suke da alaqa ta qut da qut da juna musamman ta fuskar jama'a da yaren da suke magana da shi a matsayin harshensu da dabarun sarrafa tunani cikin harshen nasu da qasar da suke tutiya da ita a matsayin mazauninsu na dindindin da kuma harkar nazari a fagen ilimin harshe da adabi da ma al'adu na Hausawan a makarantu da kwalejoji da jami'o'i a faxin duniya. Sai dai kuma ba an rubuta wannan takarda ne da burin bibiyar tarihi ko asalin kalmar Hausa ba domin tarihin Hausawa da na samuwar kalmar ta Hausa abu ne da zai yi wuya a iya haxuwa bisa matsaya xaya duba da rashin wanzajjen rubutun abin dogara game da kafuwa da mazauna cikin qasar Hausa na farko da kuma yadda lamura suka cigaba da faruwa tun daga lokacin zuwa yau. Saboda haka waiwaye adon tafiya kawai aka yi game da ma'anar kalmar ta Hausa domin cimma manufar rubuta wannan maqala wanda a dalilin haka ne ma ba a tsaya waiwayen asalin samuwar kalmar ba; illa iyaka dai bibiyar ma'anar da kalmar take da shi a wurin Hausawa da ma majivantansu wajen yi wa maqala kyakkyawar gabatarwa.
Bitar Ayyukan Bincike
Idan aka ajiye maganar asali ko farkon samuwar kalmar Hausa to za a iya kallon ma'anar kalmar ta mabambantan fuskoki kamar yadda masana harshe da adabi da al'adun Hausa a mabambantan lokuta suka yi rubuce-rubuce da gabatar da takardu a wurare dabam-dabam domin yin qarin haske a kan ma'anar kalmar, musamman ma matsayin kalmar a idon Hausawa da majivantansu na kusa da na nesa. Kusan za a iya cewa Bargery (1934) yana xaya daga cikin masanan da suka fara bayyana ma'anar kalmar Hausa a cikin ayyukansu. Ya shigar da Hausa cikin jerangiyar kalmomin qamus xinsa a matsayin kalma mai iya wakiltar harshen Hausa da dukkan wani harshe wanda Hausawa ba sa ji ko zancen da suka kasa ganewa a cikin Hausa da kuma azancin da yake cikin maganganun Hausawa, musamman masu sauqaqa fahimta. Baya ga ma'anar harshe da Hausa take iya xauka, harwayau, kalmar tana wakiltar qasar Hausawa ta gado, wato yankin da aka fi amfani da harshen Hausa a matsayin harshen uwa a ban qasa. Xoriya a kan ma'anar Bargery ita ce ma'anar da Abraham (1962) ya ba wa kalmar a cikin qamusunsa, inda ya bayyana ma'anar Hausa da kalma ce wadda take iya wakiltar harshe da qasar Hausa ta gado da dukkan wani yare da Bahaushe ba ya ji da kuma zancen da malam Bahaushe zai kasa fahimta yayin da ake magana cikin harshen nasa na Hausa. 
Daga baya ne kuma aka fara samun manazarta Hausawa, waxanda su ma suka fara tofa albarkacin bakinsu game da ma'anar kalmar ta Hausa. Ibrahim (1978) da Vavura (2008) su kuma sun bayyana Hausa a matsayin kalma mai iya xaukar ma'anar harshe da mutanen da suke magana da harshen a matsayin harshen uwa, wato Hausawa da kuma qasar da ake amfani da harshen, wato qasar Hausa. Yayin gabatar da maqalarsa, Bunza (2004) ya dunqule harshen Hausa da kaxaitacciyar kalmar Hausa da al'adun Hausawa domin ambatonsu da suna 'Hausa', musamman a wannan qarni na ashirin da xaya. Daxin daxawa, Bunza (2015) ya sake kallon ma'anar kalmar ta Hausa a matsayin harshen da Hausawa suke sadarwa da shi sai kuma yankin qasashe da garuruwan da suke mamaye da xabi'u da al'adun Hausawa (masarautun qasar Hausa) sannan sai kuma fasahar (azancin) da yake xamfare cikin harshen, wato zalaqar iya amfani da harshen na Hausa yayin sadarwa. Ta fuskar karatu kuwa, marubucin ya kalli Hausa a matsayin wani wagegen fage da ake nazarin tsari (nahawu) da yadda ake amfani da harshen Hausa da fannonin adabin Hausa da kuma al'adun zamantakewar Hausawa tun daga zamanin zamunna.
Junaidu (2011) ma ya yi bayanin amfani da kalmar Hausa a matsayin wani fage na nazari da ake karanta da karantar da harshe da adabi da kuma al'adun Hausawa a sassa dabam-dabam na Nazarin Harsunan Najeriya a jami'o'i da Sashen Harsuna a manyan makarantu da kwalejojin ilimi a Najeriya da kuma sasannin koyar da Kimiyyar Harshe da ma Harsuna ko Al'amuran Afirka da ake samu cikin manyan jami'o'i da cibiyoyin ilimi a Afirka da Qasar Amurka da kuma na qasashen Turai. Bisa haka ne ma Aldul-Qadeer (2011) ya bibiyi tarihin Hausa a matakin nazari inda ya gano cewar Turawa ne malaman farko da suka fara koyar da Hausa a makarantu da jami'o'i, waxanda suka yi nazarinta cikin harsunan Turanci kafin daga bisani Hausawa su ma suka tsunduma cikin harkar koyar da Hausar cikin harshensu ta hanyar fassara kalmomin fannu daga harsunan Larabci da Ingilishi da Faransaci domin amfanin masu koyo da koyarwa. Saboda haka, qarqashin bita da fahimtar irin waxannan ayyuka na magabata ne wannan takarda ta sake kallon Hausa a matsayin kalma mai iya xaukar mabambantan ma'anoni guda biyar masu alaqa ta qut da qut da junansu. Wato kalma ce wadda take wakiltar jama'a da yaren da suke magana da shi a matsayin harshensu da dabarun sarrafa tunani cikin harshen nasu da qasar da suke tutiya da ita a matsayin mazauninsu na dindindin da kuma harkar nazari a fagen ilimin harshe da adabi da ma al'adu na Hausawan a manyan makarantu da kwalejojin ilimi da jami'o'i a duniya.         
Tattaunawa 
Duba da qoqarin da masana suka yi wajen gabatar da bayanai kan ma'anar kalmar Hausa, inda kusan babu wani daga cikin manazarta da ya tava dunqule ma'anoni har guda biyar da kalmar take iya xauka, wanda hakan ne ya sa wannan qasida ta qara fitowa da kalmar qarin ma'anoni kamar yadda za a tattauna a qasa.    
Hausa a Matsayin Al'umma
"Hausa karambani ka jan su, Bakambare nake" Muhammadu Gambu 
Ana yi wa tushen kalmar Hausa –Haus- qari da xafa-goshi na qwayar ma'anar ba- a gabanta da sauya baqin qarshe na tushen kalmar daga s > sh tare kuma da canja wasalin qarshe na kalmar daga a > -e / -iya a lokaci guda domin samar da wata kalmar ta dabam daga ta farko, wadda zata wakilci mutumin da ake alaqanta asalinsa/ta da Hausa; wato a samar da kalmar Bahaushe (namiji, tilo) ko kuma Bahaushiya (tamata, tilo). Yayin da kuma ake son a gina wata kalma wadda za a danganta wasu mutane masu alaqar tarihi da al'adu da kuma qasar Hausa to sai a yi wa tushen kalmar Haus- xin qari na xafa-qeyar –awa a qarshenta a samar da kalmar Hausawa. Kenan Hausawa al'umma ce ko tarayyar mutane ne da suke yin hulxar furuci da Hausanci ko abin da ake cewa harshen Hausa. Haka kuma, su ne jama'ar da qasar Hausa ce mazauninsu tun daga kaka da kakanni waxanda kuma harshen Hausa ne yarensu na asali ta yadda a sanadiyyar haka ne ma ake kiran mutanen da suka shaqu da al'adun ko suka taso cikin xabi'un Hausa da Hausawa. Irin wannan dalilin ne ma ya sa Hausawan suke yin amfani da kalmar Hausa wajen kiran kansu da ma harshensu da ita. Daxin daxawa, wasu maqwabtan qabilu kamar Yarbawa suna kiran Hausawa da Gambari, Bare-bari su kira su da Afno, Jukunawa kuwa su kira su da Mgbakpa kamar yadda Jukun xin suke kiran tsatsonsu Jukunawa waxanda suka musulunta har ta kai ga sun fara sajewa cikin al'adun Hausawa da Abakwariga, su kuwa Fulani sukan ambaci Hausawa ne da kalmar Kaxo ko Have (Mukhtar, 2014).   
Duk da yake cewar ana samun ximbin Hausawa da masu magana da harshen a ciki da wajen Afirka, musamman ma a yankin Afirka ta Yamma, sai dai an fi yin amfani da harshen na Hausa a Arewacin Najeriya da kuma Kudu maso Yammacin Jumhuriyar Nijar. Domin nan ne ya kasance tabbatacciyar farfajiyar qasar Hausa sannan kuma inda Hausawa da takwarorinsu suka fi yin amfani da harshen fiye da ko'ina a faxin duniya. Wuraren da ake samun tarin Hausawa da suka yi kaka-gida har ma suka zama 'yanqasa baya ga qasarsu ta Hausa kuwa akwai Qasar Gana, Cadi, Kamaru, Binin, Saliyo, Sudan, Togo, Mali, Burkina Faso, Sanigal, Gini, Kwadebuwa, Masar, Libiya, Afirka ta Tsakiya, Gabon, Maroko, Aljeriya, Saudi Arabiya da sauransu da dama. Cikin haka ne ma Yusuf (2011) ya qiyasta cewa akwai kimanin al'ummar da suke magana da Hausa a matsayin harshen uwa ko harshen farko kimanin mutum miliyan tamanin zuwa xari (80–100) kamar yadda ake samun aqalla mutane miliyan xari (100) zuwa sama waxanda suke amfani da harshen a matsayin harshe na biyu ko na uku ko kuma ma harshen hulxa a duniya bakixaya. 
Irin wannan tsarin zamantakewa da cuxanyar al'adu da sadarwa tsakanin Hausawa da majivantansu ne ya ja hankalin Paden (1968) ga raba masu magana da Hausa a Arewacin Najeriya da sauran wurare zuwa rukuni uku. Da farko dai akwai Hausawa, waxanda ba su da wani asali ta fuskar harshe da tarihi da xabi'u face na Hausa. Kaso na biyu kuwa, su ne waxanda suka zama Hausawa sakamakon sajewa da suka yi cikin zamantakewa da xabi'un Hausa ta yadda har tarihi da harshensu na asali yake neman vacewa vat ko ma sun narke gabaxaya a cikin na Hausa; saboda haka ba su da wata makama face rungumar Hausa a matsayin madogararsu. Irin waxannan mutane ne Kwakwaci (2010) yake ganin su ma za a iya kiran su da Hausawa, saboda na-ji-daxi ne gari ba na-saba ba ta sa sun bar yarensu na gado sun kuma riqi Hausa a matsayin harshensu sakamakon auratayya ko zaman tare duk kuwa da cewar har yanzu suna danganta kansu da wata qabila. Rukunin qarshe su ne mutanen da suke da harshe da tarihi da al'adu daban da na Hausawa amma kuma suke amfani da Hausa a matsayin harshe na biyu ko na uku yayin gudanar da hulxoxinsu na yau da kullum; waxannan su ne irin qabilun da suke iya amfani da Hausa haxe da harshensu na uwa kuma suke magana da su a cikin harkokinsu na sadarwa. Wannan ne ya tabbatar da cewa akwai ximbin majiya-harshe biyu, waxanda Hausa ne harshensu na biyu a Arewacin Najeriya da kuma a wasu vangarori na ciki da wajen qasar (Smirnova, 1982); kamar yadda shi ma Gambu ya tabbatar da haka a cikin waqarsa. 
Arna ka giya arna ka shan ta,
Hausa karambani ka jan su,
Bakambare nake,
                                          Mu ad da giya mu munka gaje ta.    (Waqar Inuwa Xanmaxaci)
A cikin xiyan wannan waqa Gambu ya ambaci Hausa a matsayin qabila kamar kowace, wadda daga bisani tasirin maqwabtaka da cuxanyar al'adu da yawan jama'a ya mayar da ita al'umma. Kenan Gambu ma da mutane irinsa suna daga cikin waxanda suka rungumi Hausa a matsayin harshen farko duk da dai cewar har yanzu yana tabbatarwa da kuma alaqanta asalinsa da qabilar Kambari, a lokaci xaya kuma yake ambaton Hausa a matsayin qabila ko al'umma. Shi kuwa Muhammadu Sarkin Taushin Sarkin Katsina alaqanta Hausa da garuruwansu guda bakwai na asali ya yi, waxanda kusan xaukacin Hausawa suke danganta tarihinsu da garuruwan a matsayin tushensu, a inda yake cewa:
Darajjar Shehu tun da bayyana ce,
Ba sai an faxi ba Hausa Bakwai,
Ko da Ikko ce mutum ya ji alama,
Bubakar Sadauki na Mu'azu,
Kai ag gidan Shehu da Bello           (Sarkin Musulmi Abubakar).  
Hausa Bakwai kalma ce da take nufin cibiyar qabilar Hausa tun daga kaka da kakanni, musamman garuruwan Daura da Rano da Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da Garun Gabas (Biram), waxanda tun fil azal ba su da wata kalmar da suke danganta tarihinsu da ita face Hausa, waxanda kuma su ne qabilun da babu wani yare wanda suke alaqanta kansu da shi sama da harshen Hausa a doron qasa. 
Hausa a Matakin Harshe
"Na ji Hausawa suna faxi cikin Hausanci" Sani Sabulu
Ma'ana ta biyu da kalmar Hausa take iya xauka ita ce ta harshe, wanda shi ne yaren da Hausawa da maqwabtansu suke amfani da shi wajen sadarwa cikin zamantakewarsu ta yau da kullum. A taqaicen taqaitawa, Hausa shi ne Hausanci, wato yaren da Hausawa suke amfani da shi a matsayin harshen uwa ko harshen farko, wanda kuma suke tashi da shi tun daga quruciya har zuwa qarshen rayuwarsu. Su ma da kansu Hausawa suna kiran harshen nasu da Hausa; ta yadda zaka ji idan an yi wa mutum maganar da bai gane ta ba sai ya nuna cewar 'ban ji/gane Hausar ba'; wato bai fahimci abin da aka faxa ba. A wani lokacin akan ji Bahaushe ya ce 'na ji ana wata Hausa' a duk sanda ya ji ana magana da wani yare ko gwalangwalantun da bai laqanta ba (Adamu, 1997). Har ila yau, Hausa tana zamantowa harshe na biyu ko na uku ga wasu mutane waxanda ba Hausawa ba ne, wanda suke sadarwa da shi a tsakaninsu cikin mu'amalolinsu na rayuwa. Akwai aqalla irin waxannan qabilu guda xari huxu a cikin Tarayyar Najeriya waxanda mafi yawa daga cikinsu suke cuxanya da Hausa ta mabambantan fuskoki irin na hulxatayyar harshe da kuma zaman haxaka a qarqashin tuta xaya. Cikin haka ne ma ake samun kaso da yawa cikin qabilun da suke da harshensu na gado musamman a Arewacin Najeriya suke sauqin koya da fahimta har ma a kai ga sun iya magana da harshen na Hausa wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ba komai ne ya ba Hausa wannan matsayi ba face yaxuwar Hausawa da bunqasa da kuma cigaban da harshen ya rinqa samu daga zamani zuwa zamani. 
Alhaji Musa Xanqwairo ma da jama'arsa yana xaya cikin mutanen da suka tabbatar da cewar ana amfani da kalmar Hausa a matsayin harshe yayin da ya amsa gayyatar Bare-bari domin rerawa Shehu Umar Alkanemi waqa da Hausa a fadar Shehun na Barno a garin Maiduguri. A cikin waqar ya bayyana cewa duk da Shehun bai ba shi amsar gaisuwar da ya yi masa cikin harshen Hausa ba amma an samu masu jin Hausar da suka gaya masa cewa ai Shehun ba ya yin magana da Hausa ko wani yare na dabam da ba Barbanci ba yayin zaman fada. Ga abin da yake cewa game da Hausa a matsayin yare a cikin xiyan waqar tasa:  
Xanqwairo na je Barno, 
Can Bare-bari sun yi kirana, 
…………………………….., 
Na ko je na iske Shehu,
Sai nic ce ranka ya daxe,
Sai yaq qyale bai tanka ba,
Sai nac ce mai Allah sabbunani,
Kuma yaq qyale bai tanka ba,
Na tambayi Zanna Yawudima,
Ko Shehun ba ya jin Hausa?
To in dai ba ka jin Hausa,
Bari in gaisai da yarenai.                                 (Waqar Shehun Barno)
Bisa irin waxannan bayanai ne ma wani daga cikin Turawan Kamfani da ya tava ziyartar qasar Hausa a wajejen qarshen Qarni na sha tara (Q.19) ya bayyana Hausa a matsayin harshen da ya samu tagomashin gwamnatin Ingila kamar yadda ya rawaito a cikin littafinsa "A bara ne Gwamnati ta zavi Hausa a matsayin xaya daga cikin harsunan da suka dace a rinqa fassarar al'amuran soji da shi" Robinson (1897:2). A taqaice, ana amfani da kalmar Hausa a matsayin yare ko harshen xaukacin mutanen da suke amsa sunan Hausawa ne su a faxin duniya, musamman ma waxanda suka sha Hausar a mama. Qarqashin haka ne ma Aqilu Aliyu a matsayinsa na Bahaushe kuma mai rajin kishi da kare harshensa a wasu daga cikin baitukan waqarsa ya qara tabbatar da cewar Hausa fa, harshe ne kuma yaren dukkan wani mai kiran kansa da suna Bahaushe ne a ban qasa. Wanda harwayau kuma ya kyautu ga Hausawa da su zage dantse wajen bunqasa harshen nasu ta yadda zasu ma iya yin taqama da shi a duk inda suka tsinci kansu a sararin duniya. Ga abin da yake cewa: 
Qwazo ya kyautu da mu, mu nuna kuzarin,
Inganta harshen namu, shi ne Hausa.
……………………………………..
Ni dai Aqilu Aliyu nai waqena,
Ba don a ce mini na fi kowa Hausa. (Hausa Mai Ban Haushi)
Daxin daxawa, harshen Hausa shi ne babba kuma fitaccen harshe a yankin Afirka ta Yamma, wanda yake tafiya kafaxa da kafaxa da harsunan Larabci da Siwahila a xaukacin Afirka. Qarqashin wannan bayani zamu gane cewa Hausa babban harshe ne mai farin jini a tushensa, wato a Najeriya mai kimanin harsuna xari huxu (400) da Jamhuriyar Nijar mai kusan harsuna (150) da kuma a faxin Afirka inda ake da kimanin harsuna dubu biyu (2000) da ma kuma a duniya bakixaya mai mabambantan harsuna aqalla sama da dubu shida (6000) waxanda ake amfani da su a matsayin hanyoyin sadarwa. Hausa bayan haka, harshen gidan Cadi ne wanda tushensa ya tusgo daga cibiyar harsunan Afrosiya. Baya ga harshen na Hausa ana samun harsuna iyalan Cadi a jihohin da suka mamaye Arewa Maso-yamma da Arewa Maso-gabas da Arewa ta Tsakiya cikin Tarayyar Najeriya da kusan Xaukacin Arewacin Jamhuriyar Nijar da kuma wasu vangarori na qasar Cadi da Jamhuriyar Kamaru. Irin waxannan harsuna 'yan'uwan Hausa da ake samun su a gefen tafkin Cadi da kewayensa sun haxa da harshen Bura, Vacama, Margi, Kilba, Higi, Kotoko, Mandara, Tere, Badanci, Bolanci, Kare-kare, Ingizim, Angas da sauran harsuna da qabilun da binciken ya kai kansu da ma waxanda nazarin masana bai kai gare su ba a yankin na Afirka da ma a wasu wurare a duniya bakixaya. Bayan haka, binciken masanan zamani a kwanan nan ya tabbatar da makusanciyar dangantakar da ta wanzu tsakanin harshen na Hausa da takwarorinsa na cikin rukunin Afrosiya, musamman ma harsunan Larabci da Hiburu da Ibramiyanci da Amharik da sauran dangogin harsunan da ake samu a cikin rukunin. 
Kenan harsunan duniya rankatakaf xinsu yaruka ne da suka tofo/toho daga tushe xaya, waxanda daga baya ne suka watsu zuwa dangogi sannan kuma suka zama iyalai mabambanta (Fromkin & Rodman, 1974). Zuri'ar Afrosiya na xaya daga cikin waxannan dangogin na harsuna, wanda yake da 'ya'ya da yawa a Gabas ta Tsakiya da kuma a Nahiyar Afirka. Bisa haka ne ma aka raba zuri'ar harsunan na Afrosiya zuwa gida biyar wanda kuma kowane kaso daga cikin biyar xin nan ya qunshi wasu daga cikin manyan harsunan duniya waxanda mabambantan mutane masu bin addinai da tsarin al'adu da kuma tarihi dabam-dabam suke magana da su a doron duniya. Daga ciki akwai iyalan Samawa (Semitic), wanda ya qunshi harsunan Larabci da Hiburu da wasu daga cikin tsirarun harsunan da ake samu a yankin tsohuwar Habasha (Ethiopiya da Jibuti da Eritiriya) da kuma a Sudan ta Kudu. Baya ga wannan sai harsunan gidan Babar waxanda aka fi samun masu yin amfani da harsunan a Aljeriya da Maroko da kuma wasu vangarori na qasashen Libiya da Mauritaniya da Mali da Nijar. Akwai kuma 'ya gidan Kushitik, harsunan da aka fi samun masu magana da su a qasar Somaliya, wanda harshen Somali yake xaya da cikinsu da kuma a Habasa, inda harshen Amharik da ragowar wasu harsunan da ake samu a qasashen biyu da ma a Sudan ta Kudu suke zamanto 'yangida a cikin wannan kaso. 
Harshen Misiranci, wanda Qibxanci (Coptic) da Larabci suka maye gurbinsa a Masar ta yanzu su ma suna xaya daga cikin harsunan da suka tusgo daga cikin zuri'ar Afrosiya. Baya ga waxannan gidajen na harsuna guda huxu sai cikon na biyar da aka fi samun 'ya'yansa a tsakiya da kuma a yammacin Afirka, wanda harshen Hausa yake jagorantar xaukacin harsunan ciki ta fuskar yaxuwa da yawan majiya; ba kowane gida ba ne wannan face harshen Cadi. Ana samun waxannan harsuna na gidan Cadi a jihohin Barno da Yobe da Taraba da Adamawa da Nasarawa da Bauci da Filato da Gwambe da xaukacin jihohi da garuruwan Hausa Bakwai da 'Yan'uwa (Banza) Bakwai suka faxa cikinsu a Najeriya. Daga cikin harsunan da suka fito daga cikin wannan gida kuwa akwai Margi da Kare-kare da Bura da Angas da Tangale da Bade da Hausa da kuma Gwandara, wanda ya samo asali daga harshen na Hausa, musammam ma Kanonci.  
Hausa a Maimakon Azanci/Tuntuntuni
Hausa ba dabo ba ce – Hausawa 
Ma'ana ta uku da ake jinginawa ga kalmar Hausa ita ce ta tuntuntunin da ake ganin nasonsa a cikin azancin maganar Hausawa, waxanda suke maqare a cikin harshen nasu. Tuntuntuni dai shi ne abin da ake kira da falsafa, wato zurfafa tunani domin warware matsala ko don kyautata magana, wato qawata zance. Azanci kuwa shi ake ambato da hikima, wato dabarun sarrafa tunani cikin zantuka da ma a rayuwa gabaxaya. Ana iya gane zurfin tunanin al'umma ne a virvishin azancin da ake iya tsinkaya a cikin adabinsu da tarsashin zantukan hikimarsu, wanda harshen Hausa cike yake da irin waxannan dabaru na sarrafa harshe. Kamar yadda bayani ya gabata, Hausa suna ne da aka laqabawa harshe da kuma al'ummar da za a iske suna zaune a qasarsu ta gado cikin yankin Afirka ta Yamma in aka tashi lalubensu a taswirar duniya, musamman ma mutanen da suka sha harshen a mama, wato masu amfani da harshen a matsayin harshen uwa. A saboda haka ne ma su da kansu Hausawa suke kiran harshensu da Hausa kamar yadda suke alaqanta azancin da ya dabaibaye adabi da tuntuntuninsu da kalmar ta Hausa a cikin al'amuran zamantakewarsu. 
Bisa haka ne zaka ji in aka yi arashi da wani ya kasa warware wata sarqaqiya ko surqullen zance sai ka tsinkayi Hausawa suna cewa 'wane ba shi da Hausa'; a sakamakon gazawar mutumin wajen yin bayani tarwai yadda kowa zai fahimci maganar cikin sauqi. A irin haka ne ma suke alaqanta Hausa da ragon azancin da mutane suke tsintar kansu a ciki wajen warware sarqaqiyar zance, musamman ma abin da ya shafi lissafi ko kwatance ko iya bayani xoxar cikin harshen na Hausa. Cikin haka ne ma Hausawa suke kurara harshensu da cewar 'Hausa ba dabo ba ce', a wani lokacin ma su ce 'Hausa mai ban haushi'; ba domin komai ba kuwa sai don zamantowar azancin da yake xamfare cikin tuntuntunin harshen, musamman ma cikin al'amuran adabi da iya saqa zantuka. Azancin da Hausawa suke kira Hausa kan gagari 'ya'yan harshen kansu a wani lokacin ballantana kuma 'yan'uba ko baqi, waxanda suke amfani da harshen a matsayin harshe na biyu ko na uku ko ma harshen hulxa kawai. Musa Xanqwairo ma ya tafi a kan wannan fahimta a cikin waqarsa, inda ya ambaci Hausa a matsayin azanci, wato dabarar sarrafa tunani cikin Hausanci domin warware matsala ko kyautata magana, a inda yake cewa:
Raggo mai hanta hauni, 
Dubaratai ai ba ta his sai,
Don na san ba shi da Hausa.      (Mai Tcahe Sannu da Daga) 

Hausa a Madadin Qasa
Wata ma'anar da kalmar Hausa ta qunsa ita ce wadda ake jingina ta ga farfajiyar qasar Hausa. Abin nufi da qasa kuwa shi ne mazaunin da aka tabbatar a nan Hausawa suke zaune tun tali-tali a cikin garuruwa da biranen da suka yi wa yankin qawanya. Gusau (2008) ma ya tafi a kan cewar qasar Hausa ita ce farfajiyar da Hausawa suke zaune a cikinta, wadda kuma take cike da manyan garuruwa da kuma fitattun birane. Kenan ana yin amfani da kalmar Hausa a matsayin mazaunin da kaso mafi yawa na Hausawa suke zaune a ciki, inda kuma nan ne ragowar Hausawan da suka watsu a duniya suke alaqantawa a matsayin tushensu na asali. Har ila yau kuma, Qasar Hausa ta qunshi dukkan da'irar da ta zamanto mafi yawan mutanen cikinta suke furuci da harshen Hausa a matsayin hanyar sadarwa. Qasashen Hausawa na asali su ake kira da "Hausa Bakwai", waxanda suka haxa da Gobir da Katsina da Daura da Kano da Rano da Garun Gabas (Biram) da kuma Zazzau. Waxannan yankuna na qasar Hausa a yanzu sun faxa cikin jihohin Kano da Sakkwato da Kabi da Zamfara da Bauci da Jigawa da Katsina a Tarayyar Najeriya, sai kuma wasu manyan garuruwa da jihohi irin su Maraxi da Madawa da Filinge da Gaya da Birnin Qwanni da Dogon Dutci da Damagaram da Tsibiri a cikin Jamhuriyar Nijar. A cikin waxannan garuruwa da birane ne tushen Hausa yake, wanda kuma daga nan ne Hausawa da al'adunsu da harshensu suka watsu zuwa sauran wurare a ban qasa. 
Mu'azu (2014) ya tabbatar da cewar qasar Hausa a qarnukan baya kafin zuwan Turawan mulkin mallaka a haxe take wuri xaya, duk da cewar kowace qasa qarqashin babban sarkinta cin gashin kanta take yi; amma sakamakon mulkin mallakar da ya ci Hausa da yaqi sai qasar ta dare zuwa gida biyu. Inda aka samu Hausawan da suka tsinci kansu a Nijar qarqashin ikon Faranshi yayin da wasu kuma suka samu kansu a Najeriya qarqashin mulkin Ingilishi. Babban misalin da za a iya bugawa game da wannan al'amari na raba qasar Hausa da Turawa suka yi shi ne na qasar Katsina wadda garin Maraxi yake a qarqashinta a baya kafin a tsaga su zuwa gida biyu, a inda Maraxi ta faxa Nijar ita kuma qasar Katsina ta zama jiha a cikin Najeriya ta yanzu. Qarqashin wannan rabo ne za a gane cewa gurbin qasar Hausa dai farfajiya ce da take a tsakanin dazuzzukan da suka maqwabci gavar Tekun Atilantika daga varin Kudu a Najeriya da kuma Hamadar Sahara daga sashen Arewa na Nijar. Irin wannan alaqa ta mulkin mallaka tsakanin Turawa Ingilishi da qasar Hausa ce ta ja hankalin Salihu Jankixi a cikin waqarsa ta Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya kwatanta Kano da Birnin Landan na Qasar Ingilia a matsayin garin Kanon na bunqasasshe kuma fitaccen birni, musamman ta fuskar noma da harkokin kasuwanci da ma na masana'antu a qasar Hausa da duniya bakixaya. Bisa haka ne ma kalmar Hausa a xiyan waqar ta zo da ma'anar qasar 'Yanhausa (Hausawa) mai manyan biranen da har ta kai za a iya kamanta Kano da Birnin Landan saboda qasaitarta; kamar yadda ya rera waqar: 
Dole qarhi ka sa ai komai,
Rani an mai sai damuna,
Ga ruwa na gudana bisa ga qasa,
Ga shuke-shuke can cikin gida,
Baturiya Gwamna shi yac ce mata,
Ga Kano Ingilar 'Yanhausa (Hausawa),
Nan akan saqa kayan yabqi,
Martabar Shehu na yas samo.     (Qi-sake Sadauki Na Bubakar). 
Baya ga tsaunuka da kogunan da suka ratsa ta cikin qasar Hausa, shimfixaxxiyar jigawa ce mai mayalwacin sarari wadda qasarta take da daraja da albarka wajen noma da kiwo (Adamu, 1997). A yau qasar Hausa mai iyakoki ta kowace fuska, a taswirar duniya tana cikin yammacin Afirka ne a Arewacin Najeriya da kuma Kudancin Nijar. A vangaren Gabas Hausa ta yi iyaka da Daular Barno ne, daga sashen Yamma kuwa da garuruwa ko da qabilun bakin kogin Kuwara (Kwara) ta yi iyaka savanin a shiyyar Kudu inda qasar ta yi iyaka da Gwarawa (Gbagyi) ne da kuma sauran qabilun kudancin Zariya da ma na kudancin Bauci; a inda kuma a sashen arewa ta yi iyaka da qabilun Azbinawa (Buzaye) da sauran yarukan da ake samun qabilun da suke magana da su a Jamhuriyar Nijar a yanzu. Saboda haka, qasashen Hausa a yau su ne xaukacin garuruwan Kano da Rano a Jihar Kanon Dabo da Jihar Jigawa da Katsina da Daura a Jihar Katsinan Dikko da Masarautar Zazzau a Jihar Kaduna da Gobir da Sakkwato a Jihar Sakkwato Birnin Shehu da Jihar Zamfara da Birnin Kabi da Argungun da Gwandu da Birnin Yawuri a jihar Kabi da Masarautar Kwantagora da ta Suleja a Jihar Neja da Yankin Guddiri da Arewacin Jihar Bauci da Masarautar Kafi a Jihar Nasarawa waxanda dukkansu suke a cikin tarayyar Najeriya. Garuruwan Maraxi da Tsibiri da Damagaram da Adar da Birnin Qwanni da Filinge da Dogon Dutci da Madawa da sauransu, wurare ne da suka haxu suka gina qasar Hausa a duniyar yau. 
Daxin daxawa, Hausawa da kansu sukan kira garuruwan da suka fito ko kuma yankin qasashensu rankatakaf da sunan Hausa kamar yadda Alasan Xantata ya rawaito labarin haxuwarsa da wani dattijo, wanda ya umarce shi da siyan wani dutse kafin ya wuce zuwa qasar Hausa a kan hanyarsa ta zuwa Legas daga Birnin Akara na qasar Gana, al'amarin da ya yi sanadiyar xaukakarsa kamar yadda ya maimaita maganar mutumin a cikin tarihinsa: "In ka isa Legas ka da ka wuce Hausa, ka nemi irin dutsen nan ka siyo shi da duk abin da ka mallaka" (Kano Sate: Jiya da Yau: 39). Daga wannan lokaci da ya bi umarnin maganar mutumin nan ne kuma Allah ya cigaba da sanya albarka cikin tushen dukiyarsa. A cikin littafin Shaihu Umar kuwa kalmar ta Hausa aka yi amfani da ita a matsayin qasar ko yankin Sakkawato: "Yanzu na yi niyyar zuwa Hausa in ziyarci kabarin babban waliyyi, Shaihu Usmanu Xanhodiyo" (Tafawa Balewa: sh.36); kamar yadda su ma Sakkwatawa suke yin amfani da kalmar ta Hausa a mafi yawancin lokuta a matsayin Qasar Sakkwato ko yankin tsohuwar jihar Sakkwato (garin Sakkwato da yankin Gobir da Jihar Kabi da Jihar Zamfara) kamar yadda a wani lokacin suke nufin qasar Hausa gavadaya da kalmar. Misali, Xan Qwairo a cikin waqar da ya rerawa Ahmadu Bello Sardauna yana cewa:
Amadu ya zo Hausa (Sakkwato),
Ga shi gidanai rannan……             (Mai Dubun Nasara Garnaqaqi)
             
Hausa a Gwadaben Nazari  
Yayin da ake maganar kalmar Hausa a mahangar nazari to ana batu ne game da nazartar Hausa a matakai dabam-dabam na ilimi da ake koyo da koyar da Hausa a duniya bakixaya. Idan aka waiwayi tarihin Hausa musamman in aka qyallaro lokacin da aka fara rubutu da harshen har ta kai ga ya zama wani tangamemen fage na ilimi cikin abin da ya jivanci nazarin harshe da adabi da kuma al'adun Hausawa za a iske cewa masana sun xebe kusan shekara xari biyu suna yi ba qaqqautawa. Wannan al'amari ne ya ja hankalin Junaidu (2011) ga bayanin Hausa a matsayin wani fage na nazari da ake karanta da karantar da harshe da adabi da kuma al'adun Hausawa a sassa dabam-dabam na Nazarin Harsunan Najeriya a jami'o'i da Sashen Harsuna a manyan makarantu da kwalejojin ilimi a Najeriya da kuma sasannin koyar da Kimiyyar Harshe da ma Harsuna ko Al'amuran Afirka da ake samu cikin manyan jami'o'i da cibiyoyin ilimi a Afirka da Qasar Amurka da kuma na qasashen Turai. Qarqashin haka ne ma gwamnati a Najeriya ta warewa Hausa gurbi a manhajar karatu ta makarantun firamare da sakandire a Najeriya domin nazartar harshe da adabi da ma al'adu na Hausawa a kowane mataki na koyo da koyarwa a cikin waxannan makarantun kamar yadda gwamnati a Jamhuriyar Nijar ita ma ta bi sawu. 
Malaman farko a duniya da suka fara koyar da Hausa a makarantu da jami'o'i su ne Turawa, waxanda suka yi nazarinta cikin harsunan Turanci kafin daga bisani 'yanqasa Hausawa su ma suka tsunduma cikin harkar koyar da Hausar cikin harshensu ta hanyar fassara kalmomin fannu daga harsunan Larabci da na Ingilishi (ko Faransaci) domin amfanin masu koyo da koyarwa (Aldul-Qadeer, 2011). Bugu da qari, irin wannan yunquri da Turawa suka fara assasawa cikin harkar nazarin Hausa a matsayin wani fage na ilimi ta hanyar wallafa littattafai da gabatar da takardu a taruka ne ya cusa kishi a zuqatan Hausawa masana Hausar yin hovvasa wajen samar da littattafai da maqaloli a vangarorin nazari na Hausa guda uku, wato harshe da al'adun Hausawa da adabinsu cikin Hausa domin amfanin xalibai da manazarta. Bisa haka ne ma Bunza (2004) ya bugi qirji da cewar a rankatakaf xin harsunan da ake da su a Afirka babu wani harshe da yake da tarin masana kwatankwacin na harshen Hausa kamar yadda kuma ake da ximbin talifai na mujallu da jaridu da maqalu da littattafan nazari waxanda aka wallafa cikin al'amuran rubuce-rubuce game da nazarin Hausa da ma sauran vangarorin ilimi da na rayuwa gabaxaya. A waqar da Aqilu Aliyu ya rera ta xungurungum ga Sashen Koyar da Hausa, mawaqin yana cewa:  
Sa mini hattararka, ka kimsa,                      Sarki, kar ka sa in kasa,
Sa kusa kar mu kai ta a nesa,                       Sashen Hausa ya bunqasa,
Sosai, ya xarar wa waninsa. (Harshen Hausa)
Kammalawa 
A qarshe, wannan takarda ta qara faxaxa ma'anar Hausa daga al'umma da qasa da harshe kawai zuwa kalma mai ma'ana wadda take iya wakiltar Hausawa da harshensu da azancinsu da qasarsu da kuma nazarin rayuwarsu. Kenan kalma ce mai faxaxan ma'anoni a qalla guda biyar masu alaqa junansu ta fuskar jama'a da yaren da suke amfani da shi da dabarun sarrafa tunani cikin harshen da qasar da suke yin tutiya da ita a matsayin tushensu na asali da fagen nazarin harshe da adabi da al'adu na Hausawan a makarantu da kwalejoji da jami'o'i a faxin duniya. 
Manazarta  
Abraham, R. C. (1959). The language of the Hausa people. London: University of London Press.
Abraham, R. C. (1962). Dictionary of the Hausa language. London: University of London Press.
Adamu, M. T. (1997). Asalin Hausawa da harshensu. Kano: Xansarkin Kura Publishers Ltd. 
Amfani, A. H. (2011). Four decades of language and linguistic studies in Hausa (1960-2000). In Yalwa, L. D., Bichi, A. Y. & Sani, S. (Eds.), proceeding of Studies in Hausa Language, Literature and Culture (pp. 96-112). Kano: CSNL – Bayero University.  
Bavura, H. S. (2008). Hausa a Hausa. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Vol. 1(5), pp. 1-17. 
Bunza, A. M. (2004). Hausa a idon duniya (Qaqa tsara qaqa). Takardar da Aka Gabatar a Taron Qarawa Juna Sani Na Sashen Koyar da Harsunan Najeriya. Sakkwato: Jami'ar Usmanu Xanfodiyo.   
Bunza, A. M. (2015). Bitar karatun Hausa a qarni na ashirin da xaya: wurin da babu qasa nan ake gardamar kokawa. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Vol. 1(1), 17-46. 
Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya–Jami'ar Bayero, Kano. (1981). Rayuwar Hausawa. Lagos: Thomas Nelson (Nigeria) Limited.
Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya–Jami'ar Bayero, Kano. (2006). Qamusun Hausa na Jami'ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero.
Fromkin, V. & Rodman, R. (1974). An introduction to language. New York: Holt, Rinehart & Winston. 
Fuglestad, F. (1978). A reconsideration of Hausa history before the Jihad. The Journal of African History, Vol. 19 (3), pp. 319-339.
Furniss, G. L. (1991). Hausa language studies: The present. In A. Rufa'i (Ed.), Nigerian Languages: Yesterday, Today and Tomorrow, pp. 19-25. Kano: Center for the Studies of Nigerian Languages, Bayero University.
Gusau, S. M. (2008). Waqoqin baka a Qasar Hausa: Yanaye-yanayensu da sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.  
Ibrahim, M. S. (1978). Are-aren kalmomi cikin Hausa. In Yahaya, I. Y. & Abba Rufa'i (edc.), proceeding of Studies in Hausa Language, Literature and Culture (pp. 94-116). Kano: Center for the Studies of Nigerian Languages, Bayero University. 
Ikara, B. (1991). Hausa language studies: A projection of the future. In A. Rufa'i (Ed.), Nigerian Languages: Yesterday, Today and Tomorrow, pp. 26-51. Kano: Center for the Studies of Nigerian Languages, Bayero University.
Inuwa, Y. N. (2014). A sociolinguistic analysis of Hausa-English code switching. Germany: Lambert Academic Publishing.
Jinju, M. H. (1985). Asalin Hausawa da harshensu. Cikin Rufa'i, A., Yahaya, I. Y. & Bichi, A. Y. (Edc.), Tarin Zavavvun Takardun Nazarin Harshe da Adabi da Al'adu Na Hausa (sh. 1-10). Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero.
Jinju, M. H. (1990). Garkuwar Hausa da tafarkin cigaba. Kaduna: Fisbas Media Services Publishers. 
Junaidu, I. (2011). Funding research in Hausa studies: A multidimensional and protective approach. In Yelwa, L. X., Bichi, A. Y. & Sani, S. (eds.), Proceeding of Studies in Hausa Language, Literature and Culture (pp.-.). Kano: Center for the Studies of Nigerian Languages, Bayero University.  
Kwakwaci, H. K. (2010). Asalin Hausawa. Kano: Harsashin Ltd. 
Mamman, M. (2012). Essays on Hausa grammar and linguistics. Zaria: Ahmadu Bello University Press. 
McIntyre, J. A. (1991). Lexical innovation in Hausa (Niger, Nigeria). In Gleich, U. & Wolff, H. E. (eds.) Symposium on Language Standardization, pp.11-20; Hamburg: UNESCO Institute for Education.
Mu'azu, A. (2014). Ceto Hausa a qasar Hausa. In Gusau, S. M. et al (edc.) a Festschrift in Tribute to Abdulqadir Xangambo, pp. 1-10.  
Muhammad, Y. M. (2011). Hausa a yau. Zaria: Maxaba'ar Jami'ar Ahmadu Bello.
Mukhtar, I. (2014). Jagoran nazarin qagaggun labarai. Kano: Usman Al-Amin Publishers.
Newman, P. (1991). A century and half of Hausa language studies. In A. Rufa'i (Ed.), Nigerian Languages: Yesterday, Today and Tomorrow, pp. 1-18. Kano: Center for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.   
Newman, P. (2000). The Hausa Language: An encyclopedic reference grammar. London: Yale University Press.
Paden, J. O. (1968). Language problems of national integration in Nigeria: The special position of Hausa. J. Fishman, C. Ferguson & J. Das Gupta (Eds.), pp. 199-213.  
Robinson, C. H. (1897). Hausaland or fifteen hundred miles through the central Soudan. London: Sampson Low, Marston and Company.
Sarvi, A. S. (2011). Yaxuwa da mahimmancin harshen Hausa a duniya. Himma Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol. 3, pp. 20-31. 
Skinner, N. (1977). A grammar of Hausa for Nigerian secondary schools and colleges. Zaria: The Northern Nigerian Publishing Company.
Skinner, N. (1977). Qamus na Turanci da Hausa. Zaria: The Northern Nigerian Publishing Company.
Smirnova, M. A. (1982). The Hausa Language: A descriptive grammar. London: Routledge & Kegan Paul.
Wolff, H. E. (1991). Standardization and varieties of written Hausa (West Africa). In Gleich, U. & Wolff, H. E. (Eds.) Symposium on Language Standardization, pp. 21-32. Hamburg: UNESCO Institute for Education.
Xangambo, A. (1985). Qa'idojin rubutu a Hausa: Matattakala zuwa ga harshen qasa. Cikin Rufa'i, A., Yahaya, I. Y. & Bichi, A. Y. (Edc.), Tarin Zavavvun Takardun Nazarin Harshe da Adabi da Al'adu Na Hausa (sh. 17-31). Kano: CNHN – Jami'ar Bayero.
Yahaya, I. Y. (1988) Hausa a rubuce: tarihin rubuce-rubuce cikin Hausa. Zaria: The Northern Nigerian Publishing Company.
Yakasai, S. A. (2014). Language and cultural preservation: Hausa in the face of technological advancement. Kano: Gidan Dabino Publishers.   
Yunusa, Y. (1985). Yanayin yaxuwar Hausa a duniya. Cikin Rufa'i, A., Yahaya, I. Y. & Bichi, A. Y. (Edc.), Tarin Zavavvun Takardun Nazarin Harshe da Adabi da Al'adu Na Hausa (sh. 32-38). Kano: CNHN – Jami'ar Bayero.
Yusuf, M. A. (2011). Hausa grammar: An introduction. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

HABAICI A WAQOQIN MATA NA DAVE DA NIQA A BAHAUSHIYAR AL’ADA








                                                               NA 

                                               ZAINAB UMAR SALEH

AMINU KANO COLLEGE OF ISLAMIC AND LEGAL STUDIES, KANO NIJERIYA




TAKARDA DA AKA GABATAR A HAUSA CULTURE INTERNATIONAL FASTIVAL OF BURKINA FASO IN CONJUCTION WITH NATIONAL MUSEUM OF BURKINA FASO


                                          15 ZUWA 17 AFRILU, 2017
 
TSAKURE

 
1.0 GABATARWA 

Wannan takarda za ta yi bayani ne a kan wani kaso na waqoqin baka na Hausa wato waqoqin manyan mata. Wannan aiki kenan zai kalli yadda mata suke yin habaici a lokacin da suke yin aiki musamman na niqa da aka da kuma dave. A cikin wannan aiki da farko za mu kalli ma'anar al'ada da waqa da rabe-raben waqoqin baka na Hausa da kuma bayani a kan cewa an samu yawaitar amfani da Habaici cikin waqoqin Hausa ta hanyar manyan mata. Za kuma mu kalli ma'anar Habaici daga masana daban -daban. To daga nan sai mu tsunduma cikin aikinmu wato habaici a waqoqin aiki na mata a Bahaushiyar al'ada.  
2.0 Ma'anar Al'ada
Kalmar al'ada tana da ma'ana ta lugga da kuma ma'ana ta fannin ilmi. 
Qamus na Bargery ya bayyana al'ada da tada ko xabi a ko hanya ko haila wato fashin salla ko jini ko bin wata ko wanki (Bagery, 1934:16)
Shi kuma qamusun Hausa (2006:9) cewa ya yi al'ada ita ce, hanyar rayuwar al'umma ko jinin haila ko ingani ko tsafi ko wani irin hali daban na mutum. Akwai kuma ma'anonin al'ada na lugga da suka haxa da sabo da tafarki da kuma gwadabe. 
Masana da yawa sun ba da ma'anoni na kalmar al'ada bisa fannin ilmi. Alalmisali, Ibrahim (1982: iii) yana ganin al'ada dangane da wani ilmi da ta kevantu da shi, ta haka al'ada ta shafi yanayin rayuwar al'umma da harkokin da take gudanarwa na yau da kullum. 
Kamar yadda bayanai suka gabata za a yi cewa al'ada ta qunshi tafarki wadda wata al'umma take rayuwa a cikinta dangane da abinci da tufafi da muhalli da rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulxoxin rayuwa kamar maqwabtaka da sana'o'i da shugabanci da bukukuwa da waqoqi da sauran abubuwa waxanda suke da alaqa da haka. Funtua da Gusau (2010:2)
2.1 Ma'anar Waqa
Gusau, (1998) ya ce "Akwai wasu matakai wato kalmomi muhimmai da za a iya amfani da su wajen fito da ma'anar waqa su ne kamar haka: rerawa, hawa da sauka na murya da ke saka zuciya jin daxi da daidaita sautin murya (zaqin murya) azanci da naqaltar harshe, hikima da fasaha, kixa da amshi (karvi) da gaxa da tafi da zabiyanci da kuma saqo".
Xangambo (1973) ya ce "Waqa wani furuci (lafazi ko saqo) ne cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko qa'ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi".
Masana sun fito da ra'ayoyinsu akan ma'anar waqa da rabe-rabenta inda suka yi tarayya da cewa waqa ta kasu ka so biyu watau waqar baka da rubutacciya amma mu ba za mu dubi rubutacciya ba, zamu dogara aikinmu a kan waqar baka. Waqar baka ta kasu kasha-kashi har kashi huxu, waxanda sun haxa da: waqoqin makaxan fada da makaxan jama'a da makaxan sana'a, makaxan sha'awa, makaxan gama gari da sauransu. Sai waqoqin tatsuniya da waqoqin yara maza da mata. Da waqoqin manyan mata waxanda sun haxa da waqoqin cikin aiki kamar na niqa da daka da dave da reno da makamantan su. A bisa ka so na qarshe za mu yi nazari. 
2.2 Ma'anar Habaici 
Kamar yadda bincike ya nuna asalin kalmar habaici ba za a danganta ta da wani harshe ko wata qabila ba, ban da ta Hausa abin nufi kalmar asalinta ta Hausa ce. Ita kalmar an gina ta ne daga abin da ake yin sa bayan wani abu ya faru.
Xan Hausa (2012:13) ya bayyana habaici da cewa magana ce da ake yi cikin hikima da nufin gaya wa wani sa qo amma ba kai tsaye ba, a fakaice wato a voyayyar manufa, akan yi magana da nufin wai abu da ake yi domin shi.
Haka ma Gusau (2011) ya bayyana cewa Habaici wasu maganganu ne da ake faxa a fakaice don vata wa wani mutum rai ba tare da bayyana mutumin da ake nufin vata wa quru-quru ba. Amma shi wanda ake nufi wani lokaci da wuya ya gane abin da ko wanda ake nufi da shi. Ya daxa fayyacewa "Habaici shi ne yi wa wani mutum wata magana ta cin mutunci ba tare da an bambaci sunansa ba qiri-qiri. Idan bai san tarihin abubuwan da suka gudana da tsokacin masu gabar guda biyu ba zai iya hasashen wanda ake ma habaicin ba. 
Xangambo (1984:8) ya ce "Habaici magana ce mai voyayyiyar manufa. Akan yi magan da niyyar nufin wani abu ga wanda aka yi maganar dominsa.
Amma shi habaici idan ba mutum ya san kan zancen ba, ba kasafai yake gane wanda aka yi wa Habaicin domin shi ba. 
Domin shi habaicin ana alqanta shi da wani abu ne da ya faru da wani mutum da ya aikata wani aiki mara kyau. Misali.
Idan ana zargin mutum da sata, ko an kama shi yayi sata, idan magana ta tashi wani yana soya yi masa habaici yana iya cewa, "Kai shegun varayin garin nan sun dame mu da satar tsiya, wani da ke gefe sai ya qara da cewa a jiya an harve yan fashi a Kano.
2.3 Dalili da Masu Yin Habaici 
Bisa waxannan ma'anoni da suka gabata za mu iya cewa Habaici saqo ne na taqaice don tunatarwa ko tsokana ko mayar a magana ko huce haushi da sauransu, musamman ga wanda wani abu ya haxa su. Akwai dalilan da suke sawa ake yin habaici waxanda suka haxa da Hassada da Rowa da Huce takaici da tsokanar faxa ko cusgunawa da ramuwar gayya da gargaxi da uwa ubansasu kishi. Masu yin habaici kuwa sun haxa da manyan mutane, da maza da mata da maroqa da mawaqa sannan akan samu ga yara. Amma mata sun fi yin habaici da 'yan daudu da mawaqa. 
2.4 Yadda ake yin Habaici a Waqoqin Dave da Niqa da Lugude
Idan aka yi maganar dave, za a iya cewa ita ce ta tun fil-azal, sannan ita kan ta waqar baka daga cikin ra'ayoyin na masana sun ce yana daga cikin hanyoyin samuwar waqa daga wajen mata, kuma an samu cewa, waqar da ta fi daxewa a wajensu ita ce waqar da suke yi a dutsen niqa. An kuma ce yawancin waqoqin habaici ne tsakanin kishiya da kishiya. Amma yawanci waqoqin ba ana tsara su ba ne, amma kusan kowanne xiya yana cin gashin kansa. Kuma za a iya farawa da kowanne a kuma qare da  hakan akan kuma samar da ita ta hanyar yin lugude.
Da farko za mu xauki waqar dave in muka ce dave ba muna nufin irin na zamani da ake yi da siminta ba, a irin na iyaye da kakanni tun kafin zuwan Turawa. Ana saura kwana uku ko huxu a yi dave za yi gayya in mace na da 'yan'uwa a nesa tun saura kwana bakwai zata aika dangi da qawayen arziqi ko ta je da kanta ta shaida musu tana gayyatarsu dave. Kafin ranar za ta tanaxi kayan aiki da kuma abincin da za a ci za ta tanadi wake da gero domin in an gama a ci, sai kayan aiki wanda sun haxa da madavi ita ce ne ake daidaita gindinsa, sannan ana yin shi kala uku na farko na kisan tsakuwa na biyu kwantar da hannu na uku xan karami mai faxi mai laushi. Ana gauraya birji da garin xorawa, makuba kuwa ana jiqa ta ta kwana da safe sa a xige ta ana dave ana yayyafa ta. Kuma faba xaya ake xaga madavai a saukar gaba xaya daga gefe kuma ga masu kixa kwarya  ana waqa masu dave ma suna bayar da amshi.

2.5 Waxanda ake yi wa Dave
Ba sai lallai a xakin amarya ake dave ba ko da mace za tai sabon gida ita da mijinta sai a taya ta dave. Yawanci matan da suke dave a matsayin sana'a wataqila shi ya sa mugun baki (batsa) ya yi yawa a cikin waqoqin dave wanda duk yawancin su ruhin su al'ada ce ta samar da su ta hanyar yin habaici.
2.5.1 Dave
Manyan mata na da al'dar yin dave ne a yayin da suka samu goron gayyata daga uwar amarya ko uwar ango al'ada ta amince da a gyara xakin amarya ta hanyar yi mata dave da jere da kwalliya domin a qawata mata xaki. Ga wasu daga cikin misalan waqoqin dave da mata ke saka habaici domin mayar da martini ga wani abu da ya tava faruwa. Ga misali waqar mai jigida. 
Rawar jigida
Ku dava mana kai, 
Yara jigida 
Manya jigida
Kowa jigida 
'Ya'ya jigida 
Jigida za tai arha
Ka ce babba
Ke ce qarama 
A she ke ce babbar shegiya
Abin kirki bai karve kiba
Ana murna fara ta tafi 
Ashe xango na bayan gari. 
(Hira da Hajiya Umamatu Gaida)

Idan muka duba za mu ga cewa wata na yi wa wata habaici ne tsammanin ta fita ashe ta na nan. Ta yiwu qawar kishiya ta yi habaici ko qanwar miji ko maqwabciya da ita kanta kishiyar a wurin dave. Misali  Iye mairowa tana dave.
Ta ka ba ku tow? Ba ta ba mu ba, 
Wa ta mijinta, 
Mijin ma ba ta ba shi ba,
Ku dave mata ba don halinta ba. 
(Hira da Hajiya Umamatu Gaida)

A nan ma wani turke na habaici ya fito wato rowa in bamu ba tana cikin al'adun da suke sakawa ake wa kishiya habaicin don ta na da rowa. Ga wani misalin kuma: 
Kukan kurciya, 
Na yi gudun ruwa a kwai,
Na tarad da rava, 
Na garba jikan garba,
Kwaxo ya danne maciji, 
Ke ba ki zo ba, 
Ke ba ki ce ba zaki zoba, 
Ke ba ki barni, 
Na je cikin jama'a ba, 
Ku kan kurciya…..

Wannan qawa ce take yi wa qawar ta habaici saboda ta gayyace ta dave bata ba je ba. Saboda haka tana yar mata da habaici cewa ko ta zo ko bat a zo ba za ai daven kunga a nan in ba kasan dalilin ba ko labarin ba za a ga ne ba ta na nufin kuma da ta gayya ce ta ta yi zaven tumin dare.
Xan jiniya 
Ana neman shege a duniya,
Ga babban shege a gida, 
Ana zagin kwarto a gari,
Masu mata na varna ya na tallan shuci a gari, 
Dakin uwata san a yoyo,
Allah kai yaro matatsayin babba,
Da ikon Allah kututture sai yai ganye,
Ashe haka yake uban laraba, 
Ashe haka ake tsiyace da shi, 
Kura ta shigo gari akuya kya ci uwaki, 
Gani baba na tsoron 'yan jiniya. 

Sai kuma waqar A rayye lole a sha ruwa,

Mai goyo ba mace ce ba, 
Mai goyo ta shi ki hau gado, 
Kada xana yai mini kuka, 
Ga taro nan bashi yai sha ruwa. 

A nan kishiya c eta ke yi wa kishiyarta habaici saboda ta na goyo ita ba ta yi saboda haka ta na nunawa ita ce da miji da sauransu. 
2.5.2 Niqa
A nan ma za mu ga yadda ake nuna burgewar harshe da nuna gwaninta wajen zuquklo wasu kalmomi don gardaxi ko tsokanar faxa ko ramuwar gayya da sauransu a cikin niqa ta Bahaushiar al'ada. 
Wadda ita ce ake ganin ma tafi daxewa a waqoqin aiki na mata. Kuma yawancin duk tsohuwar da ka tambaya za ta yi maka waqar niqa ba kamar ta dave ba su ma na samo waxannan waqoqin daga bakin tsofaffi da dama da suka haxa da Amina Gaida Kaka Ja'en da sauransu.
Ana amfani da dutsen niqa babban da xan dutsen niqa na sama da matari (ja baya) qananan guda biyu yayin da aka zo yin niqa ana fita da kalmomi na habaici a cikin waqa kamar yadda suka shaida mana. Ga misalign waqar niqa ta Dodorido.
Mu riqo Allah haxari ya koma gabas daidai. 
Santarove namijin da baya zuwa hira, 
Sharvo-sharvo xayen tuwo, 
Maganin namijin sai ya rage saura, 
Idan da Allah sai na yi auran mutan birni,
Ga katifa ga lalube ga gidan sauro, 
Ga turare xangoma ga sabulun wanka.

Ita wannan wani abu ne yahaxa ta nda mijinta ta roqeshi wani abu ya hana ta shi ne ta saka shi a dutsen niqa har kuma da yi masa sharri cewa ba ya rage saura a tuwi saboda haka za yi xanyen tuwo duk tsiya ya fita har ma kuma tana fatan ta yi auran birni wai dai duk dan ya ji haushi. Saboda haka in muka luta a nan ma Bahaushiar al'ada ta mata ce ta fito ta yiwa miji Habaici idan wani abu ya haxasu. Bayan miji a kan sa kishiya saboda waqa in an xauka bata qarewa har a gama niqa saboda haka za a yi ta salo-salo duka a cikin al'adun Hausawa na mayar da martini ga kishiya a cikin waqa. Bara mu ji xaya salon kishiya. 
A gayan dalili da na sha kunu ban ji gaya ba, 
'Yar bodara ga tusa ga xan karan wari, 
Uwar kwanika gindin gyaxa mai yawa 'ya'ya, 
Kaza uwar iyali ni ba za ki roron gyaxa ta, 
Gari da lalle ta bar qafa shi ka ce garwa, 
Ba ta kitso ba ta sukola abin mata,
Ta ji kotso ta xura 'ya'ya a gajirani,
Uwar gumaida dinga yi kina waiwayen baya.

Wannan al'ada ce ta yi wa mata Habaici a cikin niqa saboda kishiyarta wato uwar gida ta na da yawan 'ya'ya shi ne a ke yi mata sharri ko habaici da cewar xakinta yana wari haka ko da 'ya'yanta ne su ka yi tusa sai a ce ita ce ta yi. Kuma a nan an yi amfani da gwanancewa da iya zaqulu kalmomi in da aka siffanta ta ko kamanta ta da gindin gyaxa saboda in an cisgo gyaxa akan sami 'ya'yan da yawa. Haka an ce baza ta rore gyaxa ba ana nufin duk dai yawan haihuwarta ba za ta haifi xan da ba nata ba. An kuma kwatan ta ta da qazama kuma marowaciya uwar haxin faxa saboda duk abin da a kai miji in ya zo ita yake tambaya. A nan in muka duba za mu ga an zage ta a fakaice kuma in ba ka san tarihin zancan ba za ka san ai ake nufi ba a cikin niqa ta rama inda aka ce ta dinga yi tan a waiwaye in ta na gulma. Misali 
Na waiwaya gaba, baya ni banga kowa ba,
Idan da Allah bana jibgiya zan yi gona ta ita xayar sai ta ce….
Allah sa ki jibge da shagaxi. 

Wato gyaxa mara kyau tun da ta ce bana ma haihuwar da yawa za tai ana nufin tayi ma duk su mutu ko marasa lafiya da sauransu. Mata suna da al'adar saka mazajensu cikin waqar tare da yi musu habaici musamman idan basa adalci tsakanin matansu. Misali cikin waqar soriyo.
Sakkwato sototon mata, 
Baran mace bawan mata,
Ni ban san maza sun a tsoron mata ba, 
Wai ta saka shi a bayan kyaure, 
Ya ce in ya daxa a bakin rayinai. 

Bayan miji Hausa ba su bar facalolinsu ba, idan muka koma kan facala ita kuma ta na yi wa matar wan mijinta wanda ya tafi birni ya barta shi kuma bai yi noma ba.
Ko kunsan katagalle mu ba mu
San wannan ba cin ranin da ba 
Miji shi ake kataggale ko kusan 
Faxa zurun a'a ba mu san
Wannan ba rumbun daba hatsi 
Shi a faxa zurum

Hatta uwar-mijii ba a bar ta a baya ba ita ma ana sa ta a niqa in ta sami suruka marar kunya ko ita uwar mijin in ta matsa mata wannan al'ada ce irin ta Hausawa ga misalin irin habaicin da ake yi wa uwar miji a niqa. 
Zagin uwar miji tauhidi,
Zagin uban miji ma'ana
Inna bari wa zai biya mani
Uwar miji sakainar kuka
In ta fashe wata zan bangara

Anan za mu iya cewa wasu baitocin akwai tasiri na addni har an dangata ta da tauhidi ana nufin ya zamo tilas.
A waqar lalaiyon dai an yiwa miji inda a ke cewa:
Kar ka tsane ni kar ka samin tsama
Goron kwabo sai na saya maka.

Wato a wannan jerin kalmomin an yi amfani da al'adar maza ta sayawa mata goro wajen jera kalmomin  don fito da  baitin ta amfani da kwarewa wajen nuna muhimmancin da al'ada ke takawa ga rayuwar Hausawa ta harkar zamantakewar aure. Ga wani misali kuma a cikin waqar Lilo.
Ya raye iye sama lilo, 
Ba ado ba ne ya yi ne,
Kin wuce ki na mana kwambo,
Ca muke xiyar sarki ce,
Ashe ashe xiyar gwauroce.

A nan habaici ake yiwa kishiya a cikin waqar ana nuna kishi da kuma Hassada da ake wa kishiya don ta yi ado har ana cewa wai xiyar gwauro ce domin a vata mata mutuncin ta.


2.5.3 Lugude
Amma idan muka koma wa lugude ko daka, za muga can ma dai ba ta sake xan ba don ba wacce a ka kyale. Idan aka yi maganar daka mace xaya ce ke yi cikin gida ko mata biyu. Amma lugude shi ne wanda mata kan haxu su yi a gidan biki wajan daka cukuxi da sauransu. Ana yi ana cika tavarya sama ana cefewa ana tafi ana kuma dukan bakin turmi da tavarya don qara wa waqar armashi. Anan al'adun Hausawa na nuna qwarewa ko da a wajen lugude ma za a iya cewa ba a barsu a baya ba wajen fito da habaici qarara. Ga misalign habaici cikin lugude.
Idan za ki rafi
Tambayi mijinki
In ya hana ki
Kwakwale idonsa
Gibe ya hana ki?
Ko jibi ya hana ki?
Ta aro zani ya qone
In ga ta yanga.

Anan ma miji da kishiya ake wa wai ta aro zani ga shi ya qone kaga anan ma a fakaice an mata gargaxi da ta dena aro.
Ta ji kullule
Ta rugo baqar tsohuwa
Ba dawo bane
Tashi ne.

Anan habaici ake yi wa uwar miji wai taji ana daka ta xauka fura ce ta taho. To wai wannan furar da suruka ta ke ba uwarmiji. Shi ta ke wa baqin ciki shi ne take mata habaici a cikin luguden ta.
Anan  kuwa uwargida ce take wa kishiyar ta habaici akan tan a son ta gaya mata ta san qulle-qullen da take yi wai don ta kore ta tana yi mata gargaxi cewar bata isa ba ba ita ta kafu. In da take cewa.
Tashi bari gidanga,
'Yar baya bari gidanga,
Ni ce kututturen qirya
Mai wuyar cire wa
A cire ba a iyawa.

Ita ko wannan kishiya ita ma take cewa.
Ashe xiyar 'yar ubbo
Ta qi zama xakinta
Da arziqinka ka tashi ka auro tsinanniya
Kwananta uku ta kasha tukunyar masu gida.

Anan sharri kishiya ake yi wa cewa ba ta kwana gida ranar da ba girkinta ba sannan daga zuwa ta fashe tukunya, wannan ma al'ada ce ta nuna kishi.
Hausawa sun ce waiwaye adon tafiya saboda haka muma zamu xan waiwaya baya domin mu yi tafiyar mu ado, mu xan koma kan waqar niqa ida wata dattijuwa sunan ta Hajiya Amina kaka ita tar era min ita tarera da bayaninta.
An mata kishiya tana watsi da hatsin tuwo,
Ada ba ta da guru ada, ba ta da laya.
Ada bata wanka, ada ba ta wanki

A yanzu ko sai guru ta ke kamar yar kamun kura
A yanzu ko sai wanka take-kamar kado a cikin ruwa 
Sassafe-sammakon sa hoda xakinta toka mangala bakwai.

Anan ma in muka duba al'ada ce cikin waqa kishi ne yasa kishiya ta hau tsafta amma sai ta nuna cewa duk da tsaftar da take saboda ba ta saba yi sa ba bata iya tsaftace xakinta.
Ita ma uwargidan ba ta kyale batun da ta gane da ita ake da ta hau niqa sai ta rama mai aka ce mata ta nuna cewar duk wani gwallinta a yawon dandi ta koyo shi da ta ga ba riba shi ne ta daqo ta yi aure.
Ga wata ta fito dandi
Allah bai bat a sa a ba
Koa lade bai fi ta muni ba 
Tanda ba ta fito maqo ba
Hadarin kudu ba ruwa ya ke ba
Sai dai zirnaniya ta sauka 
In da hadari ya taru ta nan ruwa ke zuba.
Kammalawa
Idan mu ka duba abubawan da muka zayyano za mu ga yadda mata suke ba da gudummawar su wajen havvaka al'adun Hausawa amma cikin waqa kuma munga cewar tun a wancan zamani yin 'yan waqoqin don dave kewa da xauke hankali daga gejiyar aiki. Kuma waqa tana rage damuwa don mutum ya kan bayyana damuwarsa a Bahashiyar al'ada. Daga cikin al'adun da Hausawa suke aiwatarwa an yi magana akan dave idan an yi sabon gini ko za a yi amarya da yanayin da suke nuna kishi a fili cikin Habaici idan an vata musu.
Har wa yau kuma an nuna Hausawa suna da al'adunsu na asali waxanda ake ambata da al'adun na gargajiya waxanda suke gudanarwa a yayin daka da niqa da cikin lugude daga nan ne matan Hausawa manya suke iya isar da saqonsu cikin Habaici ga faccalolinsu ko uwar miji da danginsu da uwa uba kishiya.




 
MANAZARTA

Xan gambo, A. (1973) Shata da Waqoqinsa. Kundin Digirin Farko, Kano Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.
Xangambo A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimsa ga Rayuwar Hausawa. Kano Trium Publishing Company.
Xanhausa, A.M. (2012) Hausa mai Dubun Hikima Century Researeh and Publishing Company Kano – Nigeria.
Gusau, S.M. (1988) Waqoqin Makaxan Fada: Sigoginsu da Yanaye-yanayensu. Kunin Digiri na Uku, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.
Gusau, S.M (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa, Kano: Benchamrk Publishers Limited.
Gusau, S.M (2011) Adabin Hausa a Sauqaqe. Kano. Century Reseachr and Publishing Limited.
Gusau, S.M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano Benchmark: Publishers Limited.
Illo, S.S. (1980). Waqoqin Niqa Kundin Shedar Malinta ta Qasa (NCE). Sakkwato: Kwalejin Illimi ta Tarayya.
Yakubu M. M. (2001) Adabin Hausa A.B.U. Press Ltd.
Zarruk, R.M. da wasu (1986) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa don Qananan Makarantun Sakandare Littafi na Xaya. Ibadan University, Press.
Mutanen da aka yi Hira da su
Hajiya Umamatu Gaida Ranar 2- ga watan 1 – 2017 da karfe 4 na yamma.
Hajiya Amina Kaka, jaen bypass Kano.

TASIRIN WAQA A YAU: TSOKACI DAGA WASU WAQOQIN GASA NA RANAR MAWAQAN HAUSA NA SHEKARAR 2017-2018.




            DAGA
                     A. S. BELLO 
          (08033551751)
                 SASHEN HAUSA
KWALEJIN ILIMI TA TARAYYA DA KE ZARIYA



TAKARDAR DA AKA GABATAR A WAJEN TARON RANAR MAWAQAN HAUSA A XAKIN TARO NA N.U.T HOTEL, MAGADISHU LAYOUT,       KADUNA.



1.0 Gabatarwa
Wannan maqalar ta zavo wasu waqoqi daga cikin waqoqin gasar ranar mawaqan Hausa na 2017-2018 a qalla guda goma daga cikin guda talatin da tara da suka shiga gasar. An yi nazarin jigoginsu musamman ta yadda suka shafi yanayi da tsarin zaman Hausawa a wannan zamani. An yi haka ne, domin a fito da fasahar da bajinta tare da taskace saqonnin da waqoqin suke son isar wa ga jama'a. Kar a manta  "waqa maganar hikima ce da ake rerawa ba faxa kurum ba wadda ke da wani saqo da ke qunshe cikin wasu kalmomi zavavvu, tsararru kuma zaunannu. (Yahaya (1984:2-3). Shi kuwa Xangambo (2007) ya ce ya kamata mu tuna cewa akwai waqoqi iri biyu: rubutacciyar waqa da waqar baka wato waqar makaxa. Shin me ce ce waqa? Sau da yawa mutane sukan yi wannan tambaya muhawara ta harqe. Ko da yake ba nufin wannan takarda ba ne a kawo wannan mahawara, a nan, waqa wani saqo ne da aka gina shi kan tsararriyar qa'ida ta baiti, xango, rerawa, kari (bahari) amsa-amo (qafiya) da sauran qa'idojn da suka shafi daidaita kalmomi, zavensu da amfani da su, cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba. Gusau (2003) ya nuna cewar waqa tana zuwa ne a sigar gunduwowin zantuka waxanda ake kira baitoci ko xiyoyi. Kuma ake rerawa da wani irin sautin murya ta musamman.
Ke nan waqa tana buqatar tsarawa da hikima da rerawa da saqo da zavavvun kalmomi tare da zamansu ko direwa. Wannan yana nuna mana cewa waqa daban take da zancen baka na yau da gobe, kuma tana xauke da wani saqo da take son isar wa ga al'ummar da aka tsara waqar dominta.
Ita kuwa kalmar tasiri za a iya ganin ma'anarta daga Qamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2007) inda ya ce tasiri yana nufin muhimmanci ko dangantaka ko qarfi. A nan, za mu iya cewa   waqoqin da suka shiga gasar ranar mawaqan Hausa Foundation sun yi tasiri a cikin al'ummar Hausawa a dai-dai lokacin da ake cikin wani yanayi a qasar nan da ake buqatar waqa ta fito ta taka rawar da ta saba na jan hankali al'umma na yin hani ko kuma a yi a kan al'amuran da suka shafi rayuwar al'umma. Don haka, wannan maqala tana kallon waqa a matsayin makaranta ce mai zaman kanta.
2.0 Bigiren Maqalar
Wannan maqalar ta taiqaita nazari ne a kan wasu zavavvun waqoqin mawaqan da suka shiga gasa a cikin taron ranar mawaqan Hausa na wannan shekara 2017/2018. Mawaqa 39 ne suka shiga wannan gasa, an zavo guda goma daga cikin su domin su wakilci sauran domin babu lokaci da za a yi nazarinsu baki xaya. An gina wannan nazari ne ta yin sharhi a kan jigogin da suke saqale a cikin waxannan waqoqin mawaqa, jigon cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da safarar mata da ilimi da dogoro da kai da darajar harshen Hausa da siyasa da illar abokan banza da mutuwar aure da kuma uwa uba tarbiyya. Daga cikin waxanda aka yi nazarin jigon waqoqin nasu akwai mawaqi Muftahu Umar da Shamsu Hamza da Zayyan Abubakar da Muhd Hassan Qaraye da Abdullahi. H da Sunusi D.Pambeguwa da Abdullahi Abubakar da Sunusi Dan Malam da Aisha Humaira Jos da kuma Xan Juma Hassan. An xauki kowanne mawaqi an yi sharhin jigon waqarsa domin a ga irin gudunmmowar da kowannensu ya ba da a cikin al'aummar Hausawa.
3.0 Sharhin Wasu Jigogin Waqoqin Gasa Na Ranar Mawaqan Hausa 
Bari mu fara da kallon yadda masana suka ba bayyana ma'anar jigo a mahangar nazarin waqa. Yahya (1997) ya ce jigo shi ne saqo ko manufa ko bayani ko ruhin da waqa ta kunsa wanda kuma shi ne abin da waqar ke son isarwa ga mai saurare ko kuma karatu ko nazari. Amma shi kuma Umar (1984) ya ce jigo kalma ce da manazarta adabin Hausa suka yarda su riqa amfani da ita wajen ambaton saqon da waqa ke xauke da shi. Waqa tana iya xaukar saqonni da dama. Marubuta waqoqin Hausa sun yarda cewa za a iya samun babban jigo da qananan jigogi a waqa xaya, wato ta duban jigo, za mu iya fahimtar inda waqa sa gaba. A nan za mu xauki waqar kowanne mawaqi a fito da jigonta tare da yi mata warwara.
3.0.1 Jigon Cin Hanci da Rashawa
Sanin kowane a Nijeriya cin hanci da rashawa, ya yi mana katutu a kusan dukkan al'amuran rayuwarmu. Ina ganin shi ya sa a har kullum shugaban qasa Muhammadu Buhari yakan yi qararawar cikin harshen Ingilishi da cewa "if  we didn't kill corruption, corruption will kill us". Wato idan mu 'yan qasa ba mu gaggauta kawar da cin hanci da rashawa ba, to, lallai cin hanci da rashawa na iya kawar da mu. Xaya daga cikin mawaqan nan Muftahu Muhammadu ya ce a cikin waqarsa ta cin hanci ya fito qarara yana nuni da cewa:
Naga hani da gwamnati take yi, don hana ba da rashawa,
Anti corruption commissions da takkafa don dai binne rashawa,
Hukumomin hani da ba da cin hanci domin karya rasshawa
ICPC naggano daa EFCC na gwanar rawa
Illa ci gami da ba da hanci tassaka ayyi danniya 
Naga halin Bribery Nepotism da kan hana cancanta gurin zama
Naga halin Bribery corruption na rushe gidan zama
Na ga baqar balahira ta zub da jini a cikin qasar zama
Na ga abin da yazzamo rashin kunya rashawa da tazzama
Hanyar bi ka kankaro haki naka domin bi da danniya
Waxannan baituka sun fito da babban jigon waqar, a inda aka nuna mana yadda cin hanci da rashawa takan gurgunta ci gaban tattalin arziqin qasa da ta al'umma. Illar cin hancin ne ma ta sa gwamnati ta kafa hukumomin hana fasa qori da cin dukiyar qasa da yi mata ta'annati ta EFCC da ICPC. Dukkan mu nan shaidu ne, kuma mun ga yadda waxannan hukumomi suke shiga da fita tsakanin ma'aikatun gwamnati da hukumomin daban-daban ana qwato dukiyoyin talakawa.
Marubucin ya karkasa nau'o'in cin hanci da rashawa kaso-kaso. Y ace akwai cin hanci na xauki xora a siyasa da cin hanci a tsakanin iyalai da cin hancin rashin kunya da cin hancin danniya da cin hancin fashi da cin hancin izza da cin hancin tsaro da cin hancin likita da cin hancin gidan kaso da cin hancin ilimi da cin hancin promotion da cin hancin na masinja da na maigida da cin hancin 'yan kasuwa (Algus) da cin hancin shige da fice (kwastam).
Don haka, mawaqin yana ganin mafita a nan ita ce, kowa ya yi haquri da haqqinai to zai zama abin ado duniya da lahira. Sannan ya ce sarki Allah wanda ya yi mutum da Aljan yazzaunar da mu cikin qasa xaya, ya hana cin hanci da rashawa, kamar yadda ya zo a cikin harshen abu Batulu Yahhana cin hanci bugun qasa.
3.0.2 Matsalar Tsaro
Amma shi kuma Mawaqi Shamsu Hamza a cikin wasu baitukan waqar tasa da ya yi a kan matsalar tsaro yana mai cewa:
Ga Shamsu a yau da batun tsaro 
Matsalar nan da aka qirqiro
Ko ko in ce wacce ta bijjiro
Ta yi qamari ta yunquro
Ta dabaibaye hanyar ci gaba.
A nan mawaqin ya fito da jigon waqarsa varo-varo kamar yadda ya ce, ya zo zai yi magana a kan batun tsaro, wanda aka qirqiro ko ta bijjiro. Daga jin wannan baitin ka san mawaqin yana jan hankalinmu ne a kan batun rashin tsaro da ya addabi jahohin yamma maso gabas na qasar nan da suka yi fama da rashin kwanciyar hankali na qungiyar Jama'atul ahlil sunna lil da'awatul wal jihad wacce aka fi sani da boko haram. Wanda yake rashin tsaron yankunan jihohin gabashin qasar nan ta yi qamari har ta dabaibaye hanyoyin ci gaba da rashin kwanciyar hankali da rashin zaman lafiya a yankin Borno da Yobe da Adamawa.
Mawaqin ya zayyano yadda matsalar tsaro da rarraba har ta yi rassa da dama a cikin qasar nan, domin ya nuna cewa shi kan sa bai san adadin su ba, amma ya tavo kaxan daga cikin kamar; rikicin gari-gari na qabilanci da na addini da sace-sace a qauyuka da birane da matsalar tsaro na 'yan daba da 'yan fashi da makami da na bangar siyasa da matsalar garkuwa da mutane da fasa qwauri da safarar kayan maye da rikicin Fulani da manoma da fasa bututun mai da nuna bambancin vangarenci da zaman banza da jahilci da talauci da jami'ai da kotuna. A qarshe kuma sai ya kawo hanyoyin da za iya bi domin a magance matsalar rashin tsaro a cikin baitukan kamar haka:
Mu shigar da rooton tsegumi
Ga hukuma ko da Hikimi
Ko ko mai laifi qasurgumi
Wasu cutarwa tamkar guba.
Ya qara ba da wata shawara a kan yadda za a samar da kyakkyawan tsaro a Nijeriya kamar haka:
                          Mui ta istigifari addu'a
Mui gumurzun koyon sana'a
Mu kiyayi baranda da barra'a
Mu bi doka oda sharri'a
Mu kiyayi haram ko ko riba.
Babbar mafitar da ya qara ba da wa ita ce ta neman ilimi, cewar duk wanda yake da ilimi ya kuma yi aiki da shi to lallai kam za a samu tsaro dawamammiya a Nijeriya, ga abin da ya ce:
Wanda yai ilimi kuwa tuntuni
Babu aiki zai yi tuna-tuni.
3.0.3 Jigon Safarar Mata
Ita ma wannan wata babbar matsala ce da ta addabi al'ummar Nijeriya har ma da Afrika baki xaya. Akan samu wasu mutane marasa imani waxanda sukan xauki mata yara da manya domin a kai su qasashen turai da birananmu na gida ana bautar da su, wani lokaci in an yi rashin sa'a sukan halaka. Mawaqi Zayyan Abubakar (Extra mai waqa) ya gina a waqar tasa a kan batun safarar mata, kamar yarda ya nuna a babban jigon waqar kamar haka:
A kan safara ta 'yan mata na zo zan nuna kukana
Al'umma sun yi ko oho to yazan cimma fata na
Ana safara ta 'yan mata kamar safarar tsirin gona
Abin ya sani na zautu ya zarce duk tunani na.
Marubucin ya ci gaba da kawo yadda al'ummar Hausawa da suke karkara, sukan saki 'ya'yansu mata tsakar rana zuwa birni domin aikin wanke-wanke, da zarar an je sai kuma a sha bam-bam sai ka tsince su a otel ko gidan dandi ka ga an ci amana. Ga abin da yake cewa a kan sakamakon matan:
A ba su waya da shaddodi da hoda dan suyo gayu 
Su ruxa maza da sun vullo turare na biyar sayu
Sai ai ta shiga da komowa kamar mai samfarin laya
Zaton kowa suna birni ashe sun je gidan gayu.
Ya qara da cewa wasu yaran matan Hausawa sun yi sallama da gida a kan sun tafi karatu qasashen waje sai kuma reshe ya juye da mujiya ga abin da yake cewa:
Scholarship ga 'yan mata ni nace mai ban haushi
A xauki xiya a kai turai cikin daxi a rarrashi
A kai su qasa ta alfarma su buxe ido su sha laushi
Karatu ya yi bankwana an bar dangi cikin haushi
Shi ma wannan mawaqin ya bayar da mafita ga matsalar safarar mata da ta addabi al'ummarmu. Inda ya yi kira ga hukumomi su zage dantse wajen daqile safarar mata, sannan a koma ga Allah a yi ta du'a'i tare da kira ga iyaye su bai wa ilimin mata fifiko, sannan daga qarshe sai a yi musu aure.
3.0.4 Jigon Ilimi
To ilimi dai gishir ne na zaman duniya da ma lahira, in babu kai babu miya. Ilimi shi ne yakan sanya mutum ya san yadda zai bautawa mahaliccinsa da sauran hanyoyin neman biyan buqatun rayuwa. Marubucin waqar Mahi yana mai cewa:
In ba ilimi sunan tafiyarka makauniya 
Ko da a ce kuwa kana gani da idaniya
In ba illimi ka zamto ba ka da moriya
Wahala a kanka ka shirya, qauye da ma alqarya
Qashin illimi shi ke sa wa yaro ya zamto xiya ka mui gyarawa.
A nan marubucin ya fito qarara ya nuna mana illar rashin ilimi a tsarin nema, in ba ka da shi ilimin, to za ka yi makauniyar tafiyar duniya da lahira. Domin rashin ilmin yakan hana a moreka a ilmance to tarbiyance. Ya ce amma idan kana da ilimi to ga abin da zai biyo baya.
Kai za ka sanya iyayenka su yi dariya
Sannan ya ce amfanin ilimi, yana yawo ne a duk al'amuran rayuwarmu ba ki xaya a dubi waxannan xangwaye:
Komai idan za ka yi sa ilimi bai xaya
Aiki na gwamnati ne ko kasuwa ka iya
In ba ilimi ai a yi asarar dukiya
Mu dage a kan ilimiyya, shi za ya sa mu a hanya
In mun yi ilmi ma walawa komai xaxas za mui yawa
A nan mawaqin ya nuna mana komai za ka yi ka yi shi a ilmance, kuma ko da harkar kasuwanci ne, idan kana da ilimi za a fi samun ribarta. Balle kuma uwa uba aikin gwamnati daman shi bai samuwa sai da ilmin. Idan kana da ilimi duka lamuranka ana sa ran za su tafi cikin tsari daki-daki, domin ba za a dinga tafiyar da su hargitsatsa-butsatsa ba.
3.0.5 Jigon Dogaro Da Kai
Sanin kowa ne addininmu da al'adarmu ba su yarda da zaman banza ba. Sun wajabta mana neman na kai da kuma hani da yin bara ko raraka. Mutuwar zuciya tana xaya daga cikin ababen da suka yi katutu a zuciyar wasu mutane a cikin al'ummarmu, domin haka mawaqi Abdullahi H. ya yi wannan waqa tasa a kan dogaro da kai a dai-dai wannan gava, wato karaya ta zo dai-dai da zama. Ga ma jigon waqar ta sa kamar haka:
In ba kai boko ba nemi sanda don riqewa
Kai ma mai ilimin nemi sana'a dan ka haxawa
Wanda bai da abin yi shi ya fi kowa yin kokawa 
Ba tudun dafawa
Ko abinci yake so lami ne don ba nama ba kifi.
Wannan baitin yana jan hankalin al'umma cewa ba sai lallai wanda ya yi boko ne zai iya zama mai arziqi ba, in ma ba ka yi bokon ba akwai sana'o'i da dama suna jiranka, kamar wannan sana'a ta waqa na xaya daga ciki. Hatta mai ilmin boko, shi ma ana kira a gare shi da ya nemi wata sana'a ya gwama da aikin nasa. Don haka, zaman banza da mutuwar zuciya a cikin al'ummar Hausawa ba ta gurbi daga bakin mawaqi Abdullahi.
3.0.6 Jigon Siyasar Qasa
Siyasa? yanzu a cikinta muke, kuma ita take mulkarmu a qasar nan. Don haka, shi ma wannan wani babban jigo ne da yake buqatar a sake duban sa   a matsayin madogara da ake amfani da ita wajen tafiyar da harkokin mulkin jama'a tun daga qasa har sama. Mawaqi Abdullahi Abubakar (Auta wazirin waqa) ya yi qoqarin gina waqar tasa a kan yarda ake tafiyar da mulkin siyasar Nijeriya a gurgunce, wato bayan an kaxa quri'ar zave an zavi shuwagabanni amma kwalliyar zaven ba ta biya kuxin sabulu. Wato 'yan siyasa ba sa cika alqawuran da sukan yi wa talakawa bayan sun hau mulki. Ga abin da ya ce:
Ku bar qarya to a siyasa ba shi riqe talakan qasa
Alqawari ku zam cikawa ga burin talakan qasa
Ku bar cin hanci a tsakaninku haka kan gurvata qasa
Wai shin duniya ku ke so ko ko talakan qasa
Mawaqin ya ci gaba da yin tunatarwa ga 'yan siyasa a kan cewa, su sani fa haqqin talaka yana kan su, don haka ya zama dole su ba su haqqinsu ta cika alqawaran da suka xauka, domin komai rana, komai zafi haka nan sukan fito su zave ku, don haka me zai hana su cika masu alqawaran da suka xauka wanda kuma sanadiyyar alqawarin ne ya sa suka zave su.
3.0.7 Jigon Zamantakewa Na Abokantaka
Shi ma mawaqi Sunusi Xan Malam ya gina baitukan waqarsa ne a kan abokan banza, musamman abokai marasa tarbiyya sukan waxanda sukan sauya tunanin abokansu na kirki su zama na banza. Ga abin da ya ce:
Da cikina yai taf ya xauka sai sharhole
Ba abin da nake so sai dai insha in qwale
Sai ka ganin gayu mun fito yawo sharhole
Duniya mai daxi muka yi ta da mugun tsalle
Mawaqin ya qara da nuna cewa sannu a hankali daga shaye-shaye sai batun neman mata ya ratsa lamuran rayuwa kamar haka:
In ka ganni da jummai kuma gobe ka ganni da Larai
Bin gidajen banza ban zaga gidaje na qwarai
Kullum zancena burina in fita turai
In haxu da Ester da su Mary chan ga sarai.
A nan lamarin rayuwa sun fara qamari kenan ana neman halaka, domin a xango na biyu na wannan baitin an nuna cewa abokai sun kai shi har ya fara bin gidajen banza, a maimakon ya dinga bin gidajen 'yan uwa yana sada zumunci domin ya samu lada. Marubucin ya yi amfani da wata fasaha na samarwa kai mafita daga wannan matsalar ta illar abokan banza. A inda ya sake jero wasu baituka da suka magance wannan matsalar da ta afku ta hanyar gamo abokan kirki waxanda aka shayar da su ruwan tarbiyya, sun zo masa da gyara kuma ya bi, Allah ya karvi addu'arsa, kuma ya gyaru tsaf. Kamar dai yadda muka karanta a cikin wasu hadisai na manzon Allah (SAW) inda za ka ga mutum yana aikata, ayyukan assha, sai kuma Allah ya shirye shi ya daidaitu bisa shiriyar Allah, ya dawo kan hanya madaidaiciya, ga abin da Sunusi ya ce: 
To a kwana a tashi Allah mai raya matacce
Wataran na dawo ya zo zan kwanta barci
Sai ga wani Malam ya kira ni yana wani zance
Ambatar sunana naji tsoro har zan kauce

Da zuwansa na gano da abokina ne shi ma
Ya taho shi gurina na tsaya muka gaisa ma

Abokin kirki maimakon da ya ma kore ni
Kowa ya qi ni duk inda na je a tsare ni
'yan uwa dangi da maqwabta suka guje ni
Shi sai ya ja ani a jikinsa ya qi ya barni
Ya saka ni a hanya sai ya ce in tashi in tuba
Na faxawa aboki ai ni ban san komai ba
Ka faxa mini kalma wacce za na faxa in tuba
A nan abokin nasa ya yi sandiyyar shiriyarsa kuma har ya tuba, aka tafi wurin iyayensa suka yafe masa. A nan, mawaqin ya nuna mana yadda abokai suka kai waccan mutum suka baro shi, sannan kuma aka samu wani abokin kirki ya zo ya taka rawar da ta yi sanadiyyar shiriyarsa.
3.0.8 Jigon Mutuwar Aure
Aure dai yana daga cikin wasu matakan rayuwar xan adam, bayan Ibada ce ta raya sunnar manzon Allah (S.A.W). Amma kuma duk da haka kullum sai a yi ta samu tasgaro da cikas a cikinsa daga ma'auratan lokaci zuwa lokaci. A bisa dalilai mabambanta, a wasu lokutan idan zaman aure bai yi daxi ba sai a yi ta kai ruwa rana, ana ta fama da tashin-tashina, idan auren na zumunci ya gamu da mutuwarsa, zumunci yakan yanke ya zama qiyayya idan kuma na soyayya ne aka yi ya zo ya vaci, shi kuma ya koma ya zama na gaabaa ko qiyayya.
Don haka, shi aure idan an yi shi an ta cin karo da togas, to ana iya yin gyara kuma in an yi sa'a sai a zauna lafiya. A bisa wannan dalili Aisha Humaira ta tsara waqarta a kan matsalolin mutuwar aure, sannan ta ba da mafita a cikin waqar tata. Ga kaxan daga cikin abin da take faxa:
Mun shiga uku 'yan uwa mun bani mun kasa mu danne son zuciya.
Mun shagalta da son buqatar ta kai ba mazan ba, ba ga matan ba
Aure  mutuwa yake amma ba mu san matsalar ina take ba
Daga nan sai ta fara jero matsalolin da sukan haifar da mutuwar aure, amma sai ta fara da fito da laifin mata tukunna, kamar haka:
Matsalar cecekuce da maigida
                         Kunya da sanin haqqin namiji a nan aka san shi a gun 'ya mace
Sai rashin kunya da tsabar musu da mazanmu suke da fama da shi
Yi na yi, bari na bari kayi ki yake zama duk wanda yake gudun abin faxa kar ya yi
Matar auren da ba ta bin mijin, gun Allah ba ta yin matsayi 
                        Sannan gidan mijin yin natsuwa ba za ta same shi ba.
A nan ta nuna cewar mata sukan jawa kan su yawancin matsalolin da suke jawo mutuwar aure. Amma duk da haka idan aka bi ta varawo sai a bi na mabi sawu. Aisha Humaira ba ta bar mazan ba, domin sai da ta jero matsalolin da mazan su ma a cikin zaman aure wanda ya kan yi sanadiyyar rabuwar aure, kamar haka:
Mugun hali da danne haqqi ga maza akwai shi zan yekuwa
Da yawa halin maza ne, mace mai qima ta zam karuwa
Da an ci biredi sai a yaga ledar qarshe ma a watsa ruwa
Laifi da ta yi masa tana Budurwa zai rama ba zai barta ba
Haka nan wasu ga matan amma hankali na can waje
Magariba ta yi su yi kwalliya, in ka yi zance za mu je.
Wannan hali ya sa aure mutuwa saboda rashin gaskiya, daga vangaren maza, wato mazan da matan duka a cire son zuciya a tsaya a yi aure na ibada tsakani da Allah. Namiji ya daraja matarsa, ita kuma mata da yi wa mijinta biyayyar da ya kamata, sai a zauna lafiya. Wasu mazan ba sa fitarwa da matansu haqqinsu na aure yadda ya dace, sannan shi kuma yana so lallai sai ta biya masa ta sa buqatar, alhalin bai wa kan sa adalci ba, biyayya dagareta zai yi wuya, wai abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Wannan waqar wa'azi ne aka yi wa duka ma'aurata gaba xaya kowa ya shiga tataitayinsa. In an ce ba san matsalar abubuwan da suke haifar da mutuwar aure ba, to gas hi Aisha Humaira ta lissafo su, sannan kuma ta ba da mafita.
3.0.9 Jigon Tarbiyya
Tarbiyya na daga cikin ginshiqin da sukan gina mutum ya zama na kirki ko kuma akasin haka. Shi dai mawaqi Danjuma Hassan (Shalelen Bauchi) ya gina jigon waqarsa a kan amfanin tarbiyya wajen nema tare da yin juriya da haquri a bisa wata manufa don cimma wani buri da xan Adam yake son ya sami wata biyan buqata. Ya ce idan da hali ma, ana iya haxawa da magiya tare da haqurin bibiyar abin da ake nema, da zarar ka cimma nasara bayan ka ci wahalar nema, sai tauraruwarka ta haska. Kuma daga ranar da aka ga ka zama gwani to shi ken an sai kuma a fara vata ka saboda ka zama gwani. Don haka, ya ce wannan hali ne iri na xan adam idan yau ya yabe ka gobe kuma zai ya zage ka. Ga abin da shalele ya ce:
Kafin a gane ka iya dole ka dinga bibiya
Har ka haxa da magiya ranar da an fahimce
Ka iya a lokacin ake ma tururuwa.
Don haka, shi yana mai jan hankali ga mawaqa su kasance masu tarbiyya, kuma kar su bari zagin da ake musu ya kasha msu gwuiwa, sannan yana gargaxi ga mawaqan da sukan gina jigon waqoqinsu bisa vata tarbiyya.
3.0.10 Jigon Zaman Lafiya
Shi ma wani mawaqi da ya cancanci a xaga masa tuta shi ne Sunusi Pambeguwa wanda ya gina waqarsa a kan wajabtar al'ummomin da Nijeriya da ake ganin sun bambanta da lallai lokaci ya zo da ya kamata a zauna lafiya.
Mu zauna lafiya ya mu al'ummah, don sai da shi duk qasa zatai qarfi, in babu shi ci gabanmu da gyara, qasa guda muke kowa-da-kowa.
Yana jan hankali al'umma cewa sai da zaman lafiya qasa za ta yi qarfin arziqi don haka tun da Allah ya yi mu a cikin qasa guda sai a huqura a hakan. Jigon waqarsa ta fito a wannan baitin da ke biye:
Ada qasarmu wasu basu barci rashin zaman lafiya sun ga qunci,
Jahar Plateau a da taji taci kasuwar Taminos tayo maraichi,
Zangon Kataf ta Kaduna da yammaci da yaqi ya tashi ranar babu barci,
Wasu garinsu bari sun yi Bauchi manya da yara sun tarwatsewa.


4.0 Kammalawa
Babu tantama in aka ce wannan gasa taskace ta qirqira da nuna bajintar da fasaha da wa'azantarwa da gargaxi da wayar da kai da kuma fito da hikimomin da Allah ya yi wa matasan Hausawa a wannan qarni a fagen waqa to ai babu laifi kam.Don hak a, ina mai kira ga shuwagabanin wannan qungiya da su ci-gaba da ba wa waxannan matasa goyan bayan da ta kamata ta yadda wata rana su ma za su zama gwarzaye a fagen waqa kamar su, musamman idan a dubi yadda ake ta qoqarin karkata hankalin mawaqan su dinga gina waqoqin nasu a kan jigon alfanu ba na hululu ba.






MANAZARTA
Bunza, A.M. (2006). Gadon Fexe Al'ada. Lagos: Tawal Nigeria Limited.
Xangambo, A. (2007). Xaurayar Gadon Fexe Waqa. Zaria: Amana Publishers.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waqa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S.M. (2008). Waqoqin Baka A qasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S. M. (1999). Tarbiyya A Idon Bahaushe. In Hausa Studies. Usman Danfodiyo University Sokoto. Vol.I No. I.
Gusau, S. M. (2005) Mawaxa Da Makaxan Hausa. Kano: Benchmark Publishers.
Umar, M.B. (1985). Dangantakar Adabi Da Al'adun Gargajiya. Zariya: Hausa Publication Centre. Mangwaran Babajo.
Yahaya I. Y. Da Wani. (1984). Jagoran Nazarin Hausa. Zariya: Gaskiya Cooporation Limited.