DAGA
A. S. BELLO
(08033551751)
SASHEN HAUSA
KWALEJIN ILIMI TA TARAYYA DA KE ZARIYA
TAKARDAR DA AKA GABATAR A WAJEN TARON RANAR MAWAQAN HAUSA A XAKIN TARO NA N.U.T HOTEL, MAGADISHU LAYOUT, KADUNA.
1.0 Gabatarwa
Wannan maqalar ta zavo wasu waqoqi daga cikin waqoqin gasar ranar mawaqan Hausa na 2017-2018 a qalla guda goma daga cikin guda talatin da tara da suka shiga gasar. An yi nazarin jigoginsu musamman ta yadda suka shafi yanayi da tsarin zaman Hausawa a wannan zamani. An yi haka ne, domin a fito da fasahar da bajinta tare da taskace saqonnin da waqoqin suke son isar wa ga jama'a. Kar a manta "waqa maganar hikima ce da ake rerawa ba faxa kurum ba wadda ke da wani saqo da ke qunshe cikin wasu kalmomi zavavvu, tsararru kuma zaunannu. (Yahaya (1984:2-3). Shi kuwa Xangambo (2007) ya ce ya kamata mu tuna cewa akwai waqoqi iri biyu: rubutacciyar waqa da waqar baka wato waqar makaxa. Shin me ce ce waqa? Sau da yawa mutane sukan yi wannan tambaya muhawara ta harqe. Ko da yake ba nufin wannan takarda ba ne a kawo wannan mahawara, a nan, waqa wani saqo ne da aka gina shi kan tsararriyar qa'ida ta baiti, xango, rerawa, kari (bahari) amsa-amo (qafiya) da sauran qa'idojn da suka shafi daidaita kalmomi, zavensu da amfani da su, cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba. Gusau (2003) ya nuna cewar waqa tana zuwa ne a sigar gunduwowin zantuka waxanda ake kira baitoci ko xiyoyi. Kuma ake rerawa da wani irin sautin murya ta musamman.
Ke nan waqa tana buqatar tsarawa da hikima da rerawa da saqo da zavavvun kalmomi tare da zamansu ko direwa. Wannan yana nuna mana cewa waqa daban take da zancen baka na yau da gobe, kuma tana xauke da wani saqo da take son isar wa ga al'ummar da aka tsara waqar dominta.
Ita kuwa kalmar tasiri za a iya ganin ma'anarta daga Qamusun Hausa na Jami'ar Bayero (2007) inda ya ce tasiri yana nufin muhimmanci ko dangantaka ko qarfi. A nan, za mu iya cewa waqoqin da suka shiga gasar ranar mawaqan Hausa Foundation sun yi tasiri a cikin al'ummar Hausawa a dai-dai lokacin da ake cikin wani yanayi a qasar nan da ake buqatar waqa ta fito ta taka rawar da ta saba na jan hankali al'umma na yin hani ko kuma a yi a kan al'amuran da suka shafi rayuwar al'umma. Don haka, wannan maqala tana kallon waqa a matsayin makaranta ce mai zaman kanta.
2.0 Bigiren Maqalar
Wannan maqalar ta taiqaita nazari ne a kan wasu zavavvun waqoqin mawaqan da suka shiga gasa a cikin taron ranar mawaqan Hausa na wannan shekara 2017/2018. Mawaqa 39 ne suka shiga wannan gasa, an zavo guda goma daga cikin su domin su wakilci sauran domin babu lokaci da za a yi nazarinsu baki xaya. An gina wannan nazari ne ta yin sharhi a kan jigogin da suke saqale a cikin waxannan waqoqin mawaqa, jigon cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da safarar mata da ilimi da dogoro da kai da darajar harshen Hausa da siyasa da illar abokan banza da mutuwar aure da kuma uwa uba tarbiyya. Daga cikin waxanda aka yi nazarin jigon waqoqin nasu akwai mawaqi Muftahu Umar da Shamsu Hamza da Zayyan Abubakar da Muhd Hassan Qaraye da Abdullahi. H da Sunusi D.Pambeguwa da Abdullahi Abubakar da Sunusi Dan Malam da Aisha Humaira Jos da kuma Xan Juma Hassan. An xauki kowanne mawaqi an yi sharhin jigon waqarsa domin a ga irin gudunmmowar da kowannensu ya ba da a cikin al'aummar Hausawa.
3.0 Sharhin Wasu Jigogin Waqoqin Gasa Na Ranar Mawaqan Hausa
Bari mu fara da kallon yadda masana suka ba bayyana ma'anar jigo a mahangar nazarin waqa. Yahya (1997) ya ce jigo shi ne saqo ko manufa ko bayani ko ruhin da waqa ta kunsa wanda kuma shi ne abin da waqar ke son isarwa ga mai saurare ko kuma karatu ko nazari. Amma shi kuma Umar (1984) ya ce jigo kalma ce da manazarta adabin Hausa suka yarda su riqa amfani da ita wajen ambaton saqon da waqa ke xauke da shi. Waqa tana iya xaukar saqonni da dama. Marubuta waqoqin Hausa sun yarda cewa za a iya samun babban jigo da qananan jigogi a waqa xaya, wato ta duban jigo, za mu iya fahimtar inda waqa sa gaba. A nan za mu xauki waqar kowanne mawaqi a fito da jigonta tare da yi mata warwara.
3.0.1 Jigon Cin Hanci da Rashawa
Sanin kowane a Nijeriya cin hanci da rashawa, ya yi mana katutu a kusan dukkan al'amuran rayuwarmu. Ina ganin shi ya sa a har kullum shugaban qasa Muhammadu Buhari yakan yi qararawar cikin harshen Ingilishi da cewa "if we didn't kill corruption, corruption will kill us". Wato idan mu 'yan qasa ba mu gaggauta kawar da cin hanci da rashawa ba, to, lallai cin hanci da rashawa na iya kawar da mu. Xaya daga cikin mawaqan nan Muftahu Muhammadu ya ce a cikin waqarsa ta cin hanci ya fito qarara yana nuni da cewa:
Naga hani da gwamnati take yi, don hana ba da rashawa,
Anti corruption commissions da takkafa don dai binne rashawa,
Hukumomin hani da ba da cin hanci domin karya rasshawa
ICPC naggano daa EFCC na gwanar rawa
Illa ci gami da ba da hanci tassaka ayyi danniya
Naga halin Bribery Nepotism da kan hana cancanta gurin zama
Naga halin Bribery corruption na rushe gidan zama
Na ga baqar balahira ta zub da jini a cikin qasar zama
Na ga abin da yazzamo rashin kunya rashawa da tazzama
Hanyar bi ka kankaro haki naka domin bi da danniya
Waxannan baituka sun fito da babban jigon waqar, a inda aka nuna mana yadda cin hanci da rashawa takan gurgunta ci gaban tattalin arziqin qasa da ta al'umma. Illar cin hancin ne ma ta sa gwamnati ta kafa hukumomin hana fasa qori da cin dukiyar qasa da yi mata ta'annati ta EFCC da ICPC. Dukkan mu nan shaidu ne, kuma mun ga yadda waxannan hukumomi suke shiga da fita tsakanin ma'aikatun gwamnati da hukumomin daban-daban ana qwato dukiyoyin talakawa.
Marubucin ya karkasa nau'o'in cin hanci da rashawa kaso-kaso. Y ace akwai cin hanci na xauki xora a siyasa da cin hanci a tsakanin iyalai da cin hancin rashin kunya da cin hancin danniya da cin hancin fashi da cin hancin izza da cin hancin tsaro da cin hancin likita da cin hancin gidan kaso da cin hancin ilimi da cin hancin promotion da cin hancin na masinja da na maigida da cin hancin 'yan kasuwa (Algus) da cin hancin shige da fice (kwastam).
Don haka, mawaqin yana ganin mafita a nan ita ce, kowa ya yi haquri da haqqinai to zai zama abin ado duniya da lahira. Sannan ya ce sarki Allah wanda ya yi mutum da Aljan yazzaunar da mu cikin qasa xaya, ya hana cin hanci da rashawa, kamar yadda ya zo a cikin harshen abu Batulu Yahhana cin hanci bugun qasa.
3.0.2 Matsalar Tsaro
Amma shi kuma Mawaqi Shamsu Hamza a cikin wasu baitukan waqar tasa da ya yi a kan matsalar tsaro yana mai cewa:
Ga Shamsu a yau da batun tsaro
Matsalar nan da aka qirqiro
Ko ko in ce wacce ta bijjiro
Ta yi qamari ta yunquro
Ta dabaibaye hanyar ci gaba.
A nan mawaqin ya fito da jigon waqarsa varo-varo kamar yadda ya ce, ya zo zai yi magana a kan batun tsaro, wanda aka qirqiro ko ta bijjiro. Daga jin wannan baitin ka san mawaqin yana jan hankalinmu ne a kan batun rashin tsaro da ya addabi jahohin yamma maso gabas na qasar nan da suka yi fama da rashin kwanciyar hankali na qungiyar Jama'atul ahlil sunna lil da'awatul wal jihad wacce aka fi sani da boko haram. Wanda yake rashin tsaron yankunan jihohin gabashin qasar nan ta yi qamari har ta dabaibaye hanyoyin ci gaba da rashin kwanciyar hankali da rashin zaman lafiya a yankin Borno da Yobe da Adamawa.
Mawaqin ya zayyano yadda matsalar tsaro da rarraba har ta yi rassa da dama a cikin qasar nan, domin ya nuna cewa shi kan sa bai san adadin su ba, amma ya tavo kaxan daga cikin kamar; rikicin gari-gari na qabilanci da na addini da sace-sace a qauyuka da birane da matsalar tsaro na 'yan daba da 'yan fashi da makami da na bangar siyasa da matsalar garkuwa da mutane da fasa qwauri da safarar kayan maye da rikicin Fulani da manoma da fasa bututun mai da nuna bambancin vangarenci da zaman banza da jahilci da talauci da jami'ai da kotuna. A qarshe kuma sai ya kawo hanyoyin da za iya bi domin a magance matsalar rashin tsaro a cikin baitukan kamar haka:
Mu shigar da rooton tsegumi
Ga hukuma ko da Hikimi
Ko ko mai laifi qasurgumi
Wasu cutarwa tamkar guba.
Ya qara ba da wata shawara a kan yadda za a samar da kyakkyawan tsaro a Nijeriya kamar haka:
Mui ta istigifari addu'a
Mui gumurzun koyon sana'a
Mu kiyayi baranda da barra'a
Mu bi doka oda sharri'a
Mu kiyayi haram ko ko riba.
Babbar mafitar da ya qara ba da wa ita ce ta neman ilimi, cewar duk wanda yake da ilimi ya kuma yi aiki da shi to lallai kam za a samu tsaro dawamammiya a Nijeriya, ga abin da ya ce:
Wanda yai ilimi kuwa tuntuni
Babu aiki zai yi tuna-tuni.
3.0.3 Jigon Safarar Mata
Ita ma wannan wata babbar matsala ce da ta addabi al'ummar Nijeriya har ma da Afrika baki xaya. Akan samu wasu mutane marasa imani waxanda sukan xauki mata yara da manya domin a kai su qasashen turai da birananmu na gida ana bautar da su, wani lokaci in an yi rashin sa'a sukan halaka. Mawaqi Zayyan Abubakar (Extra mai waqa) ya gina a waqar tasa a kan batun safarar mata, kamar yarda ya nuna a babban jigon waqar kamar haka:
A kan safara ta 'yan mata na zo zan nuna kukana
Al'umma sun yi ko oho to yazan cimma fata na
Ana safara ta 'yan mata kamar safarar tsirin gona
Abin ya sani na zautu ya zarce duk tunani na.
Marubucin ya ci gaba da kawo yadda al'ummar Hausawa da suke karkara, sukan saki 'ya'yansu mata tsakar rana zuwa birni domin aikin wanke-wanke, da zarar an je sai kuma a sha bam-bam sai ka tsince su a otel ko gidan dandi ka ga an ci amana. Ga abin da yake cewa a kan sakamakon matan:
A ba su waya da shaddodi da hoda dan suyo gayu
Su ruxa maza da sun vullo turare na biyar sayu
Sai ai ta shiga da komowa kamar mai samfarin laya
Zaton kowa suna birni ashe sun je gidan gayu.
Ya qara da cewa wasu yaran matan Hausawa sun yi sallama da gida a kan sun tafi karatu qasashen waje sai kuma reshe ya juye da mujiya ga abin da yake cewa:
Scholarship ga 'yan mata ni nace mai ban haushi
A xauki xiya a kai turai cikin daxi a rarrashi
A kai su qasa ta alfarma su buxe ido su sha laushi
Karatu ya yi bankwana an bar dangi cikin haushi
Shi ma wannan mawaqin ya bayar da mafita ga matsalar safarar mata da ta addabi al'ummarmu. Inda ya yi kira ga hukumomi su zage dantse wajen daqile safarar mata, sannan a koma ga Allah a yi ta du'a'i tare da kira ga iyaye su bai wa ilimin mata fifiko, sannan daga qarshe sai a yi musu aure.
3.0.4 Jigon Ilimi
To ilimi dai gishir ne na zaman duniya da ma lahira, in babu kai babu miya. Ilimi shi ne yakan sanya mutum ya san yadda zai bautawa mahaliccinsa da sauran hanyoyin neman biyan buqatun rayuwa. Marubucin waqar Mahi yana mai cewa:
In ba ilimi sunan tafiyarka makauniya
Ko da a ce kuwa kana gani da idaniya
In ba illimi ka zamto ba ka da moriya
Wahala a kanka ka shirya, qauye da ma alqarya
Qashin illimi shi ke sa wa yaro ya zamto xiya ka mui gyarawa.
A nan marubucin ya fito qarara ya nuna mana illar rashin ilimi a tsarin nema, in ba ka da shi ilimin, to za ka yi makauniyar tafiyar duniya da lahira. Domin rashin ilmin yakan hana a moreka a ilmance to tarbiyance. Ya ce amma idan kana da ilimi to ga abin da zai biyo baya.
Kai za ka sanya iyayenka su yi dariya
Sannan ya ce amfanin ilimi, yana yawo ne a duk al'amuran rayuwarmu ba ki xaya a dubi waxannan xangwaye:
Komai idan za ka yi sa ilimi bai xaya
Aiki na gwamnati ne ko kasuwa ka iya
In ba ilimi ai a yi asarar dukiya
Mu dage a kan ilimiyya, shi za ya sa mu a hanya
In mun yi ilmi ma walawa komai xaxas za mui yawa
A nan mawaqin ya nuna mana komai za ka yi ka yi shi a ilmance, kuma ko da harkar kasuwanci ne, idan kana da ilimi za a fi samun ribarta. Balle kuma uwa uba aikin gwamnati daman shi bai samuwa sai da ilmin. Idan kana da ilimi duka lamuranka ana sa ran za su tafi cikin tsari daki-daki, domin ba za a dinga tafiyar da su hargitsatsa-butsatsa ba.
3.0.5 Jigon Dogaro Da Kai
Sanin kowa ne addininmu da al'adarmu ba su yarda da zaman banza ba. Sun wajabta mana neman na kai da kuma hani da yin bara ko raraka. Mutuwar zuciya tana xaya daga cikin ababen da suka yi katutu a zuciyar wasu mutane a cikin al'ummarmu, domin haka mawaqi Abdullahi H. ya yi wannan waqa tasa a kan dogaro da kai a dai-dai wannan gava, wato karaya ta zo dai-dai da zama. Ga ma jigon waqar ta sa kamar haka:
In ba kai boko ba nemi sanda don riqewa
Kai ma mai ilimin nemi sana'a dan ka haxawa
Wanda bai da abin yi shi ya fi kowa yin kokawa
Ba tudun dafawa
Ko abinci yake so lami ne don ba nama ba kifi.
Wannan baitin yana jan hankalin al'umma cewa ba sai lallai wanda ya yi boko ne zai iya zama mai arziqi ba, in ma ba ka yi bokon ba akwai sana'o'i da dama suna jiranka, kamar wannan sana'a ta waqa na xaya daga ciki. Hatta mai ilmin boko, shi ma ana kira a gare shi da ya nemi wata sana'a ya gwama da aikin nasa. Don haka, zaman banza da mutuwar zuciya a cikin al'ummar Hausawa ba ta gurbi daga bakin mawaqi Abdullahi.
3.0.6 Jigon Siyasar Qasa
Siyasa? yanzu a cikinta muke, kuma ita take mulkarmu a qasar nan. Don haka, shi ma wannan wani babban jigo ne da yake buqatar a sake duban sa a matsayin madogara da ake amfani da ita wajen tafiyar da harkokin mulkin jama'a tun daga qasa har sama. Mawaqi Abdullahi Abubakar (Auta wazirin waqa) ya yi qoqarin gina waqar tasa a kan yarda ake tafiyar da mulkin siyasar Nijeriya a gurgunce, wato bayan an kaxa quri'ar zave an zavi shuwagabanni amma kwalliyar zaven ba ta biya kuxin sabulu. Wato 'yan siyasa ba sa cika alqawuran da sukan yi wa talakawa bayan sun hau mulki. Ga abin da ya ce:
Ku bar qarya to a siyasa ba shi riqe talakan qasa
Alqawari ku zam cikawa ga burin talakan qasa
Ku bar cin hanci a tsakaninku haka kan gurvata qasa
Wai shin duniya ku ke so ko ko talakan qasa
Mawaqin ya ci gaba da yin tunatarwa ga 'yan siyasa a kan cewa, su sani fa haqqin talaka yana kan su, don haka ya zama dole su ba su haqqinsu ta cika alqawaran da suka xauka, domin komai rana, komai zafi haka nan sukan fito su zave ku, don haka me zai hana su cika masu alqawaran da suka xauka wanda kuma sanadiyyar alqawarin ne ya sa suka zave su.
3.0.7 Jigon Zamantakewa Na Abokantaka
Shi ma mawaqi Sunusi Xan Malam ya gina baitukan waqarsa ne a kan abokan banza, musamman abokai marasa tarbiyya sukan waxanda sukan sauya tunanin abokansu na kirki su zama na banza. Ga abin da ya ce:
Da cikina yai taf ya xauka sai sharhole
Ba abin da nake so sai dai insha in qwale
Sai ka ganin gayu mun fito yawo sharhole
Duniya mai daxi muka yi ta da mugun tsalle
Mawaqin ya qara da nuna cewa sannu a hankali daga shaye-shaye sai batun neman mata ya ratsa lamuran rayuwa kamar haka:
In ka ganni da jummai kuma gobe ka ganni da Larai
Bin gidajen banza ban zaga gidaje na qwarai
Kullum zancena burina in fita turai
In haxu da Ester da su Mary chan ga sarai.
A nan lamarin rayuwa sun fara qamari kenan ana neman halaka, domin a xango na biyu na wannan baitin an nuna cewa abokai sun kai shi har ya fara bin gidajen banza, a maimakon ya dinga bin gidajen 'yan uwa yana sada zumunci domin ya samu lada. Marubucin ya yi amfani da wata fasaha na samarwa kai mafita daga wannan matsalar ta illar abokan banza. A inda ya sake jero wasu baituka da suka magance wannan matsalar da ta afku ta hanyar gamo abokan kirki waxanda aka shayar da su ruwan tarbiyya, sun zo masa da gyara kuma ya bi, Allah ya karvi addu'arsa, kuma ya gyaru tsaf. Kamar dai yadda muka karanta a cikin wasu hadisai na manzon Allah (SAW) inda za ka ga mutum yana aikata, ayyukan assha, sai kuma Allah ya shirye shi ya daidaitu bisa shiriyar Allah, ya dawo kan hanya madaidaiciya, ga abin da Sunusi ya ce:
To a kwana a tashi Allah mai raya matacce
Wataran na dawo ya zo zan kwanta barci
Sai ga wani Malam ya kira ni yana wani zance
Ambatar sunana naji tsoro har zan kauce
Da zuwansa na gano da abokina ne shi ma
Ya taho shi gurina na tsaya muka gaisa ma
Abokin kirki maimakon da ya ma kore ni
Kowa ya qi ni duk inda na je a tsare ni
'yan uwa dangi da maqwabta suka guje ni
Shi sai ya ja ani a jikinsa ya qi ya barni
Ya saka ni a hanya sai ya ce in tashi in tuba
Na faxawa aboki ai ni ban san komai ba
Ka faxa mini kalma wacce za na faxa in tuba
A nan abokin nasa ya yi sandiyyar shiriyarsa kuma har ya tuba, aka tafi wurin iyayensa suka yafe masa. A nan, mawaqin ya nuna mana yadda abokai suka kai waccan mutum suka baro shi, sannan kuma aka samu wani abokin kirki ya zo ya taka rawar da ta yi sanadiyyar shiriyarsa.
3.0.8 Jigon Mutuwar Aure
Aure dai yana daga cikin wasu matakan rayuwar xan adam, bayan Ibada ce ta raya sunnar manzon Allah (S.A.W). Amma kuma duk da haka kullum sai a yi ta samu tasgaro da cikas a cikinsa daga ma'auratan lokaci zuwa lokaci. A bisa dalilai mabambanta, a wasu lokutan idan zaman aure bai yi daxi ba sai a yi ta kai ruwa rana, ana ta fama da tashin-tashina, idan auren na zumunci ya gamu da mutuwarsa, zumunci yakan yanke ya zama qiyayya idan kuma na soyayya ne aka yi ya zo ya vaci, shi kuma ya koma ya zama na gaabaa ko qiyayya.
Don haka, shi aure idan an yi shi an ta cin karo da togas, to ana iya yin gyara kuma in an yi sa'a sai a zauna lafiya. A bisa wannan dalili Aisha Humaira ta tsara waqarta a kan matsalolin mutuwar aure, sannan ta ba da mafita a cikin waqar tata. Ga kaxan daga cikin abin da take faxa:
Mun shiga uku 'yan uwa mun bani mun kasa mu danne son zuciya.
Mun shagalta da son buqatar ta kai ba mazan ba, ba ga matan ba
Aure mutuwa yake amma ba mu san matsalar ina take ba
Daga nan sai ta fara jero matsalolin da sukan haifar da mutuwar aure, amma sai ta fara da fito da laifin mata tukunna, kamar haka:
Matsalar cecekuce da maigida
Kunya da sanin haqqin namiji a nan aka san shi a gun 'ya mace
Sai rashin kunya da tsabar musu da mazanmu suke da fama da shi
Yi na yi, bari na bari kayi ki yake zama duk wanda yake gudun abin faxa kar ya yi
Matar auren da ba ta bin mijin, gun Allah ba ta yin matsayi
Sannan gidan mijin yin natsuwa ba za ta same shi ba.
A nan ta nuna cewar mata sukan jawa kan su yawancin matsalolin da suke jawo mutuwar aure. Amma duk da haka idan aka bi ta varawo sai a bi na mabi sawu. Aisha Humaira ba ta bar mazan ba, domin sai da ta jero matsalolin da mazan su ma a cikin zaman aure wanda ya kan yi sanadiyyar rabuwar aure, kamar haka:
Mugun hali da danne haqqi ga maza akwai shi zan yekuwa
Da yawa halin maza ne, mace mai qima ta zam karuwa
Da an ci biredi sai a yaga ledar qarshe ma a watsa ruwa
Laifi da ta yi masa tana Budurwa zai rama ba zai barta ba
Haka nan wasu ga matan amma hankali na can waje
Magariba ta yi su yi kwalliya, in ka yi zance za mu je.
Wannan hali ya sa aure mutuwa saboda rashin gaskiya, daga vangaren maza, wato mazan da matan duka a cire son zuciya a tsaya a yi aure na ibada tsakani da Allah. Namiji ya daraja matarsa, ita kuma mata da yi wa mijinta biyayyar da ya kamata, sai a zauna lafiya. Wasu mazan ba sa fitarwa da matansu haqqinsu na aure yadda ya dace, sannan shi kuma yana so lallai sai ta biya masa ta sa buqatar, alhalin bai wa kan sa adalci ba, biyayya dagareta zai yi wuya, wai abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Wannan waqar wa'azi ne aka yi wa duka ma'aurata gaba xaya kowa ya shiga tataitayinsa. In an ce ba san matsalar abubuwan da suke haifar da mutuwar aure ba, to gas hi Aisha Humaira ta lissafo su, sannan kuma ta ba da mafita.
3.0.9 Jigon Tarbiyya
Tarbiyya na daga cikin ginshiqin da sukan gina mutum ya zama na kirki ko kuma akasin haka. Shi dai mawaqi Danjuma Hassan (Shalelen Bauchi) ya gina jigon waqarsa a kan amfanin tarbiyya wajen nema tare da yin juriya da haquri a bisa wata manufa don cimma wani buri da xan Adam yake son ya sami wata biyan buqata. Ya ce idan da hali ma, ana iya haxawa da magiya tare da haqurin bibiyar abin da ake nema, da zarar ka cimma nasara bayan ka ci wahalar nema, sai tauraruwarka ta haska. Kuma daga ranar da aka ga ka zama gwani to shi ken an sai kuma a fara vata ka saboda ka zama gwani. Don haka, ya ce wannan hali ne iri na xan adam idan yau ya yabe ka gobe kuma zai ya zage ka. Ga abin da shalele ya ce:
Kafin a gane ka iya dole ka dinga bibiya
Har ka haxa da magiya ranar da an fahimce
Ka iya a lokacin ake ma tururuwa.
Don haka, shi yana mai jan hankali ga mawaqa su kasance masu tarbiyya, kuma kar su bari zagin da ake musu ya kasha msu gwuiwa, sannan yana gargaxi ga mawaqan da sukan gina jigon waqoqinsu bisa vata tarbiyya.
3.0.10 Jigon Zaman Lafiya
Shi ma wani mawaqi da ya cancanci a xaga masa tuta shi ne Sunusi Pambeguwa wanda ya gina waqarsa a kan wajabtar al'ummomin da Nijeriya da ake ganin sun bambanta da lallai lokaci ya zo da ya kamata a zauna lafiya.
Mu zauna lafiya ya mu al'ummah, don sai da shi duk qasa zatai qarfi, in babu shi ci gabanmu da gyara, qasa guda muke kowa-da-kowa.
Yana jan hankali al'umma cewa sai da zaman lafiya qasa za ta yi qarfin arziqi don haka tun da Allah ya yi mu a cikin qasa guda sai a huqura a hakan. Jigon waqarsa ta fito a wannan baitin da ke biye:
Ada qasarmu wasu basu barci rashin zaman lafiya sun ga qunci,
Jahar Plateau a da taji taci kasuwar Taminos tayo maraichi,
Zangon Kataf ta Kaduna da yammaci da yaqi ya tashi ranar babu barci,
Wasu garinsu bari sun yi Bauchi manya da yara sun tarwatsewa.
4.0 Kammalawa
Babu tantama in aka ce wannan gasa taskace ta qirqira da nuna bajintar da fasaha da wa'azantarwa da gargaxi da wayar da kai da kuma fito da hikimomin da Allah ya yi wa matasan Hausawa a wannan qarni a fagen waqa to ai babu laifi kam.Don hak a, ina mai kira ga shuwagabanin wannan qungiya da su ci-gaba da ba wa waxannan matasa goyan bayan da ta kamata ta yadda wata rana su ma za su zama gwarzaye a fagen waqa kamar su, musamman idan a dubi yadda ake ta qoqarin karkata hankalin mawaqan su dinga gina waqoqin nasu a kan jigon alfanu ba na hululu ba.
MANAZARTA
Bunza, A.M. (2006). Gadon Fexe Al'ada. Lagos: Tawal Nigeria Limited.
Xangambo, A. (2007). Xaurayar Gadon Fexe Waqa. Zaria: Amana Publishers.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waqa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S.M. (2008). Waqoqin Baka A qasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S. M. (1999). Tarbiyya A Idon Bahaushe. In Hausa Studies. Usman Danfodiyo University Sokoto. Vol.I No. I.
Gusau, S. M. (2005) Mawaxa Da Makaxan Hausa. Kano: Benchmark Publishers.
Umar, M.B. (1985). Dangantakar Adabi Da Al'adun Gargajiya. Zariya: Hausa Publication Centre. Mangwaran Babajo.
Yahaya I. Y. Da Wani. (1984). Jagoran Nazarin Hausa. Zariya: Gaskiya Cooporation Limited.
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.