TATTAUNAWA TSAKANIN JARIDAR SARAUNIYA DA SHUGABAN HUKUMAR BAYAR DA KATIN SHEDAR ZAMA DAN KASA TA JAHAR KANO - INJINIYA MUHAMMAD AUWAL SANUSI
Tawagar ma'aikatan Jaridar Sarauniya karkashin jagoranci Editan labarai Malam Rabiu Muhammad Abu Hidaya da shugaban sashen fassara Yasir Ibrahim Kalla da kuma Sanah Shahada sun yi tattaki har ofishin shugaban hukumar bayar da katin shedar zama ɗan kasa na Jihar Kano, Injiniya Muhammad Auwal Sanusi, a ofishinsa da ke Tal'udu kusa da shataletalen Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano a ranar 17 ga watan Agusta, 2018 domin tattaunawa da shi game da mahimmancin katin ɗan kasa ga al'ummar kasa da kuma neman karin bayani game da wasu 'yan matsaloli da mutane ke fuskanta yayin neman katin ɗan kasar.
SARAUNIYA
Da farko za mu so jin takaitaccen tarihin rayuwarka da yadda aka yi gwagwarmaya har aka kawo wannan matsayi?
Ni dai sunana Muhammad Auwal Sunusi, haifaffan Jahar Kano, karamar hukumar Dala, unguwar Yalwa. An haifeni a shekara 02-06-1965. Na yi makarantar firamare da sakandare dina duka a Kano.
Na je Kaduna Polytechnic inda na samu shedar karatun Diploma da HND a ɓangaren ilimin (Chemical Engineering). Sannan na yi karatu a Abubakar Tafawa Balewa University, Bauchi, inda na samu shedar PGD ɓangaren ilmin aikin tafiyar da hukuma ko ma'aikata (management). Na yi karatu a Jami'ar Fasaha ta Yola, inda na samu shedar PGD a ilmin (Public Administration), sannan na sake dawowa Jami'ar Bayaro na samu shedar PGD a ilimin (Mechanical Engineering).
Na yi aiki a matatar mai ta Kaduna (NNPC) tsahon shekaru biyu. Bayan na gama Bautar Kasa, na koma yin aiki da ma'aikatar yin sabulu da omo a jihar Jos. Daga nan na sake komawa bangaren mai karkashin kungiyar Uni petrol kafin komawarta OANDO.
Na taba gwagwarmayar siyasa inda na nemi takarar ɗan Majalissar Tarayya mai wakiltar Karamar Hikumar Dala. Amma cikin ikon Ibangiji ban samu nasara ba.
A shekarar 2013 na samu aiki a wannan hukuma ta National Identification management commission. Bayan jajircewa da kokari, Allah ya sa yanzu ni ne a matsayin shugaban wannan hukumar ta Jihar Kano.
SARAUNIYA
Shi wanna ofishi na National Identification Management Center(NIMC) ɗin ya za a kira shi kai tsaye yadda mutane za su fahimta?
Wannan shi ake kira Hukumar Rijista da Samar da Katin Dan Kasa.
SARAUNIYA
Wanne muhimmanci katin ɗan kasa yake da shi ga al'ummar kasa?
Katin ɗan kasa yana da matukar muhimmanci. Mutanen da suke shiga kasashen makotanmu musamman Nijar za su faɗa maka muhimmancin katin ɗan kasa. Da shi kasa za ta san su waye mutanenta. Haka ma baki da suke shigowa, zamu gane su waye su ke shigowa.
Bayan wannan ma akwai sha'anin tsaro. Idan aka yi abu na laifi za a gane su waye suka yi. Sannan ta hanyar ne gwamnati za ta gane adadin alm'ummar dake cikin kasa. Hakan zai taimaka wa gwamnati gurin yin kasafin kuɗi (budget).
Gurin gano masu aikata laifi. Misali akwai waɗanda su ke haɗa hannayen jari da wasu. Daga baya sai su wayi gari su neme su su rasa. Amma ta hanyar katin ɗan kasa tsaf za a iya gano su, ana duba lambar katinsa ta dan kasa za a san waye.
Gurin ɗaukar aikin soja, ɗan sanda da sauran ayyuka, sai mutum ya bada shedar ɗan kasa za a ɗauke shi aikin.
Sannan hukumar kasar Saudiyya ma ta yarda da cewar da shi za ta tantance maniyyatanmu. Sun ce a wannan shekarar mara shedar ba zai shiga kasarsu ba. Ko da ka cika ka'ida sai kana da lambar ɗan kasa.
Shi wannan kati yana karkashin wata kungiya ta duniya wato (International Civil Aviation Organisation). Duk hukumar da ya kasance tana da wannan hakkin tana da wannan bayanin. Duk kasar da ka je aka tambayeka kai dan ina ne, sai ka ba da wannan katin ko lambar, to sun san kai waye kuma ka shigo kasarsu.
SARAUNIYA
Ka yi bayani a kan tantance 'yan kasa da sanin adadinsu, ya alakarku take da Hukumar Kidaya ta Kasa?
Su hukumar kidaya suna rijistar yaran da aka haifa da kuma waɗanda suka rasu, mu kuma muna yi wa rayayyu rijista ne.
SARAUNIYA
Waɗanne nasarori ku ke ganin kun cimma a aikin nan?
Nasarori da yawa sun fara bayyana, saboda a yanzu bankuna sun fi gamsuwa da lambar ko katin ɗan kasa. Sannan yaran da aka ɗiba aikin soja da ɗan sanda an tabbatar da cewa yan kasa ne ta hanyar shedar. Gashi ma hukumar Saudiyya sun tabbatar da cewa idan suka ganka da lamba ko katin ɗan kasa sun san kai ɗan Nijeriya ne, saɓanin baya da idan aka ga kowanne bakar fata to dan Nijeriya ne. Yanzu wannan ya kau. Sannan mun fara kai matakin da za a gane adadin 'yan kasa, yaro da babba. Sannan kana aiki ko ba ka aiki.
Nan gaba zaɓe zai zama kana daga ɗakinka za ka yi zaɓe da katinka na ɗan kasa.
SARAUNIYA
Ta ya ku ke gane wannan ɗan kasa ne ko ba dan kasa ba tunda kowa zuwa yake ya ce ya zo ai masa katin ɗan kasa?
Mutane da yawa a baya an musu katin amma ba su samu ba, kuma an yi babu tantancewa, amma a wannan an yi shiri na musamman an ɗora abin a kan ka'ida.
Yanzu ka karɓi katin alhali kai ba ɗan kasa bane zai yi wahala, domin idan za a yi maka sai ka zo da ɗaya daga cikin waɗannan: Katin zaɓe, takardar haihuwa, tsohon katin ɗan kasa, takardar shedar wurin zama na asali, shedar amincewar tuki wanda amfaninta bai kare ba da kuma fasfo na shiga kasashe. Mu a nan Jihar Kano, saboda halin mutanenmu, koda mutum bai da waɗannan abubuwan mun nemi alfarmar sarakunan gargajiya. Za su iya kawo mana shaidar mutum ɗan kasa ne a rubuce mu karba da sa hannunsu.
To koda mutum ya tsalleke duka waɗannan, in ya zo nan akwai jami'an Hukumar Shige da Fice da ke tare da mu. Su ma za su tantance mutum.
SARAUNIYA
Ya kuke gabatar da ayyukanku a sauran gurare, kamar sauran kananan hukumomi da kauyuka?
An fara aikin nan a Jihar Kano a watan Disamba 2012 a wannan babban ofishin kawai. Wadanda suka farga da kuma masu tafiye-tafiye ne suka fi yi saboda kalubalen da suke samu a kan katin.
A wannan lokacin asubanci ake yi a nan ana bin layi saboda akwai adadin mutanen da za a yiwa a rana. Da tafiya tai tafiya sai a shekarar 2013 aka bude ofisoshi 2 a kowacce sanatoriya(yankunan jiha). Sai ya zama ofisoshinmu sun zama bakwai. Zuwa karshen shekarar 2014 ofisoshinmu suka kai guda 27. Kawo yau muna da ofisoshi 68. Akwai a kowacce karamar hukuma da muhimman gurare.
Kuma akwai yiyuwar a kara wasu duba da yawan jama'a kuma alkaluman wadanda aka yiwa bai taka kara ya karya ba.
Muna yaba wa gwamnatin Jihar Kano domin a shekara 2014 ta bai wa cibiyoyinmu 50 na'urar tauraron dan Adam da na'ura mai amfani da hasken rana domin saukaka mana aiki.
SARAUNIYA
Shin a ganinka kun yi wa rabin mutanen Kano wannan rijista, kuma kananan yara za a iya musu wannan katin?
Batun yawan wadanda aka yiwa cikin mutanen Jahar Kano wadanda sun kai kusan miliyan ashirin amma har yanzu ba a yi wa mutanen da su ka kai miliyan daya da rabi ba har zuwa yanzu. To ka ga akwai damuwa, akwai tashin hankali sannan akwai neman mutane su tashi daga barci tun kafin abin ya zo yana cutar da mu. Sai 'yan kudu sun riga sun gama karbar nasu sun fara cin moriyarsa a zo ana cewa ai 'yan kudu aka bai wa dama. Muma nan an bamu damar, ba mu yi amfani da ita ba ne. Mu tashi mu farka tun yanzu don Allah!
Game da maganar yara kuma; wannan kati babu maganar babba ko yaro. In dai yaro zai iya zama mu dauki hotonsa da tambarin yatsan sa, to za a masa. Sai dai bambanci tsakanin yaran da suke kasa da shekaru 16 da babba. Shi yaro ana bukatar takardar haihuwarsa, sannan ya zama daya daga cikin iyayensa sun yi rijista. Za a yi amfani da na iyayensa a masa rijistar. Idan sun kai shekaru 16 sai su zo da shi a sake daukan hotonsu da na yatsunsu da kuma bayanansu, sai ya zamanto suna zaman kansu. Amma lambar da aka basu ba za ta sauya ba.
SARAUNIYA
Mutane suna ta korafi game da rashin fitowar katin dindindin da wuri, shin me ka ke gani ya kawo wannan tsaiko na rashin fitarsa tsawon shekaru?
Gaskiya ba haka aka so ba! Wannan hukumar tana iya bakin kokarinta. Kamar yadda na fada cewa ingancin wannan kati daidai yake da kowanne kati na kowacce kasa.
A lokacin da aka fara yin rijista ba lokacin ne aka fara yin katin ba. Sai ya kasance rijistar ta taru kuma a waje daya tal a ke yin kati, wato Abuja. Amma ana bada takardar wucin-gadi (slip) mai ɗauke lambar da ake bukata kafin a baka katin dindindin.
Akwai mutane yanzu haka sama da dari takwas da aka yiwa ba su zo sun karbi katinsu ba. Mun neme su da su zo su karba amma ba su zo ba.
Da mutane sun san kudin da ake kashewa wajen yin wannan katin da sun bawa abin nan muhimmanci sosai da sosai.
SARAUNIYA
Idan katin mutum ya bata, ya ya zai yi a sake masa?
Ba ma kati ba ko slip ka batar sai ka kawo rantsuwar kotu da shedar 'yan sanda. Sannan ka biya Naira dari biyar a banki na asusun gwamnatin tarayya. Sai mu baka takarda ka cike. Kada mutum ya ga an mashi cikin sauki ya je ya jefar da shi. Sai ya sha wahala matuka sannan a sake mishi wani.
A yanzu an fitar da tsarin da za ka iya duba lambarka idan ka yi rijistar kamar dai yadda kake duba lambar BVN ta waya. Lambobin su ne *346#. In ka tura kan kowanne kamfanin waya zai turo maka da lambarka matukar layin da shi ka yi rijista.
Idan layin wayarka ya bata, ko ka yi sauyin adireshi, ko sauyin suna, ko kwanan watan haihuwa, duka idan kana so ka sauya za ka kawo mana nan ka cike takarda; sai a sauya maka.
SARAUNIYA
Shin ta ya za a magance yin kati sama da daya kamar yadda wasu suke yi a katinan zabe?
Ba a bari mutum ya yi kati sau biyu. Muna da na'u'rori da za su nuna ka taba yin wani. Koda zanen yatsunka ne ya yi kama da na wani sai an ware an tantance kai ne ko ba kai ba ne.
Idan ka taba yi sannan ka sake, akwai doka na daurin wata 6 ko biyan tarar dubu dari ko ma a hada maka duka.
SARAUNIYA
Wanne kira ka ke da shi ga mutane akan su zo su yi wannan katin dan kasar?
Kira na ga mutane shi ne kada mutum ya bari a bar shi a baya, ya zama wajibi a amsa kira. Mutum ya taimaki iyalinsa, ya taimaki jaharsa, ya taimaki gwamnatin tarayya, domin abun ya shafi kowa da kowa. Ba abu ne da ya shafi gwamnati ita kadai ba.
Kuma a nan gaba kadan komai za ka yi sai da wannan kati, sannan ina kira ga mutane cewa su kasance masu bayar da bayanan gaskiya yayin yin wannan kati domin gudun samun matsala a gaba.
Alhamdulillah Godiya nake da wannan ziyara da kuka kawo min daga Jaridar SARAUNIYA. Allah ya dafa muku ya mai da ku gida lafiya.
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.