Tattaunawa ta musamman da Masani kan kiwon Kifi a zamanance Malam Hassan Ibrahim game da yadda ake kiwon kifi da tanade-tanaden kalubalen da ke cikin harkar.
Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya
Da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Malam Hassan: to assalamu alaikum jama'a, da farko dai sunana Hassan Ibrahim na yi karatuna na fimare a magwan Firamare daga nan na wuce sakandiren GSSS Kawaji amma a Kwalejin Rumfa na karasa sakandirena bayan nan kuma sai na shiga makarantar koyon aikin noma ta Audu Bako da ke Dambatta a kano bayan na kammala sai na wuce A.B.U Zariya na yi karatun babbar Difiloma akan aikin Noma(HND) sai kuma na shiga aiki koyarwa a sakandiren Maza ta Kimiyya da fasaha da ke Lauta a Gumel jihar Jigawa, ban jima ina koyarwa ba sai na bar su na dawo kwalejin Ilimi ta tarayya (F.C.E) kano wanda a yanzu haka a nan nake aiki.
Kamar in na fahimceka da kyau a cikin ilimin da kai kafi kwarewa akan abinda ya shafi noma da kiwo a zamanance haka ne ko?
Malam Hassan: haka ne.
Yauwa abinda na ke so mu yi magana a kai shi ne harkar kifi da kiwonsa a zamanance,(Fisheries) idan mutum yana so ya fara sana'ar kifi wasu abubuwa ne yakamata ya tanada don fuskantar harkar?
Malam Hassan: to da farko idan mutum zai fara sana'ar kiwon kifi ko nomansa yana da kyau a fara samun filin(Land) da zai yi wannan harka domin wannan fili shi ne mafi muhimmanci a ko wani sha'ani na harkar noma walau na kifi ko na noman iri, bayan samun filin sai kuma jari(Capital) da ma'aikatan gudanarwa(Labour) to shi wannan fili da za'a yi kiwon kifin ya kasu kashi uku kamar haka:
1-Concrete Font(Dan karamin kududdufin da za'a gina da bulo)
2-Azalt font(ramin kasa wanda ba'a zuba siminti a ciki ba) a kuma tabbatar kasar ba mai tsotse ruwa ba ce dan kada a wahalar da kifayen
3-Plastic font(Tanki na musamman domin kiwon kifi)
akwai kuma wuraren kiwon kifi na musamman (Captured areas) shi kuma yawanci gwamnati ke hurumin yin wannan kiwon shine manya koguna da kududdufai.
Manona: duk wannan jawaban da ka yi sai na lura kamar na masu karfi ne shin idan talaka wanda bai da ikon bin wadancan hanyoyi da ka fada ya zai yi a bashi masu sauki?
Malam Hassan: na'am! To ga mai karamin karfi zai iya fara kiwon kifinsa ko a gida amma ya tabbatar da cewa akwai wadataccen ruwa a gidan saboda shi kiwon kifi sai da ruwa domin kifin yana son canjin ruwa akai-akai a kalla duk kwana biyu ko uku a canja masa ruwa ya danganta da kyan ruwan da kuma yawan kifayen, idan suna da yawa za su dinga kashi a ruwan ka ga zai dinga sauri baci kenan.
Manona: ga mai fara yin wannan sana'a shin akwai wata ka'ida da zai bi domin fara wannan sana'a?
Malam Hassan: to ga mai fara wannan sana'a zai iya farawa da kifaye 50 ko 100 ba'a son mutum idan bai kware ba ya kwaso su da yawa, to in sha Allah idan ya fara da wadannan ya kuma kiyaye canja musu ruwa da kuma basu abinci akan kari zai ji dadin kiwon na su.
Manoma: da wani yakamata a dinga ba su abinci?
Malam Hassan: sau biyu a rana ko sau uku da safe da rana da kuma yamma, amma dai kifi an fi so a bashi abinci da sanyin safiya da kuma la'asar irin rana ta yi sanyi sosai.
Sannan wajen canja masa ruwa ba'a son lokaci guda a canja masa ruwa wannan yana illatar da kifi sosai, ana so a lokacin da ake zubar da tsohon ruwan a dinga zuba sabo, saboda canjin yanayi(Tamparature) na kifin, ba'a son sai an zubar da tsohon tsaf sannan a zuba sabo, ba mamaki tsohon ruwan ya fi sabon dumi dan haka ake so a lokacin da ake zubar da tsohon a dinga zuba sabon dan ya saje da yanayin da kifin ke ciki.
Manoma: akwai wata illa ne a tare da canja ruwan lokaci guda?
Malam salisu: kwarai kuwa akwai illa kasan shi kifi yanayinsa yana canjawa da ruwan daya tsinci kansa a ciki(Cold Blood Animal) idan ruwa mai zafi ne yanayin jikinsa yana komawa mai sanyi hakama idan mai zafi ne yanayinsa yakan koma mai zafi, dan haka ba'a son lokaci guda a sauya masa ruwa, sai dai a hankali a hankali.
Manoma: ta ya ya za'a iya canja ruwan kifin ba tare da an zubar da tsohon ba?
Malam Hassan:(dariya) ai duk wanda zai fara wannan sana'a akwai dan tanki da aka tanada domin fara wannan sana'a shi kuma wannan tanki a jikinsa akwai hanyoyin fitar da ruwa da kuma shigarsa(Outlet da Inlet).
Manoma: ga wanda zai fara wannan sana'a shin akwai wasu nau'in kifiye da ake so ya fara da su?
Malam Hassan:eh akwai amma ba su wuce kala biyu ba, akwai MARI akwai kuma TARWADA kusan danginsu daya (Family) amma akwai dan bambanci ita Mari ta fi Tarwada girma domin tana girma sosai domin idan ta girma zata iya kaiwa kamar cinyar mutum, ita ma Tarwada tana girma amma dai bata kai Mari ba, to wadannan sune nau'ikan kifayen da ake so mutum ya kiwata domin suna da juriya da saurin girma da kuma riba.
Manoma: akwai nau'ikan kifaye da yawa a duniya shin ko za mu yi sanin hakikanin yawansu a duniya da kuma dalilin da yasa aka zabi wadannan jinsi biyu domin kiwonsu?
Malam Hassan: to a lal hakika kifayen da suke duniya suna da yawa, ka ga ana samu a koguna ana samu fadamu ana samu a rafi da kududdufai da kuma teku. Duka wadannan abubuwan dana lissafa maka a kwai nau'ikan kifayen da ake samu a kowannensu, a kalla kifayen da mu ke da su a duniya wadanda kididdiga ta ba mu damar sani sun kai kimanin 600 amma shahararru wadanda aka fi sani a kasar hausa akwai:
Tarwada.
Karfasa.
Mari.
Qawara, da sauransu.
Manona: bari mu dan dawo baya kadan shin akwai wasu kwanaki da aka ware wadanda za'a soma kiwata kifayen da kuma adadin kwanakin da za'a fitar dasu a siyar a kasuwa?
Malam Hassan: eh to yawanci an fi so idan za'a soma kiwon kifin a soma da wanda tsayinsa bai wuce girman dan yatsa ba(Finger ling) ko kuma (Post Finger ling) su kuma sun fi na farko girma akwai kuma Jumbo shi Jumbo babba ne sosai ya dai danganta da karfi da mutum ke dashi amma dai yawanci an fi so a zuba (Finger ling ko Juba nil) domin su sun yi dan kwari ba za'a yi asarar sosai ba, amma in suka cika kankanta to wajen rainon nasu wasu za su mutu da yawa to idan aka zuba wadannan kifaye daga ranar da aka zuba su idan akwai kulawa ta sosai wata biyar zuwa shida sun isa a kwashe su a siyar ko a ci.
Manoma: akwai wasu magunguna da ake son a dinga basu ko kuma wata ka'ida da za'a bi don ingantuwar kiwonsu?
Malam Hassan: to shi dai kifi bai da wata matsala a kiwonsa sosai matukar an bi wadancan ka'idojin dana fada a baya na canja masa ruwa da bashi abinci akan ka'ida shi kiwon ba kamar na kaji bane bai da wasu cututtuka da yawa, amma ana so idan an zuba ruwan akwai wani magani na (anti biotic)da ake zubawa a ruwan wanda ko akwai wasu kwayoyin cututtuka shi wannan(anti biotic) zai kashe su haka kuma ko da wasu daga cikin kifayen wasu sun kamu za su warke.
Akwai kuma wani maganin da ake kira(booster) shi kuma ana zuba musu a cikin abincinsu a basu yana taimaka musu wajen saurin girma.
Manoma: Mun Gode.
Malam Hassan: Ni ma na gode.
Inasan infara kiwon Kifi amma bansan ta yadda Zamfara ba, please ina neman shawaran kwararru kamanku.
ReplyDeleteMy contact
08032312538
08020977776