Daga Rabiu Muhammad Abu Hidaya
Kimanin watanni biyu kenan ana takaddamar rikicin dakatar da yar wasan Hausa jaruma Rahma sadau a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood wadda ta samo asali daga lafazin da Rahman ta yi na cewa wai Adam Zango ya neme ta da fasikanci ita kuma taki sakamakon haka shi kuma ya cire ta daga fim dinsa da suke dauka tare, sai dai kuma bayan wani dan bincike na wucin gadi da wani kwamiti ya yi wai ya gano cewa karya Rahma take yi wa Adamu don haka kwamitin karkashin Kungiyar MOPPAN ya dakatar da ita.
Sai dai kuma wani abin lura a nan shi ne anya wannan kwamiti ko wannan kungiya sun yi zuzzurfan tunani kafin su dakatar da Rahma din kuwa?
Lalle idan mu ka yi duba da yadda masana'antar take ciki a halin yanzu za mu iya cewa ba wannan ne hukuncin da kungiyar yakamata a ce ta yankewa jarumar ba, duba da cewa akwai dokoki da yawa wadanda za a iya amfani da su wajen yi mata hukunci don ladabtarwa irin su. tara, gargadi ko jan kunne.
Sannan za mu yi cewa wajen yanke hukuncin an yi tuya an manta da albasa dalili kuwa shi ne kamata ya yi idan za a dakatar ita Rahma din a dakatar da ita tare da Adamun ko yaronsa mai suna Ali Atwork wanda shi ma ya shiga rigimar inda ya ciwa Jarumar mutunci amma sai ba a yi haka ba, aka yankewa Rahma hukunci ita daya, wani karin abin mamaki ga wannan kwamiti shi ne wasu masu ruwa da tsaki a harkar ta shirin Fim kuma shugabanni irin shugaban kungiyar Arewa Fim makers Baba Karami sun nuna damuwarsu a kan yadda aka dakatar jarumar ba tare da saninsu ba, a saboda haka ne suke cewa su bada yawunsu aka yanke wannan hukunci ba don haka su a gurinsu Rahma ba dakatacciya ba ce.
Har ila yau wasu daga cikin Daraktoci sun yi kunnen uwar shegu da wannan hukunci domin sun ci gaba da saka wannan jaruma a fina-finansu wanda ake ganin mai gidanta a harkar wato Ali Nuhu shi ne ya soma karya wannan doka da aka sanya ta hana sanya jarumar a fim har tsawon wata shida bisa dalilinsa na cewa ya riga ya aika da takarda ga waccan kwamiti don bashi damar karasa fim din da suka fara dauka da ita.
Mahangar Arewa ta hanga ta hango cewa matukar masana'antar ta Kannywood idan bata yi taka tsan-tsan ba lalle wannan rikici zai iya haifar musu da marar idanu da gagarumin koma baya a harkar musamman yadda kawunansu ya rabu a wannan hukunci da aka yanke, domin wasu na ganin cewa shin Rahman ce kadai me laifi za a yankewa hukunci? Ai akwai jarumai irinta da suka aikata laifi kamar Fati Shu'uma, Ali Nuhu, Artwork da kuma shi Adamun, don haka matukar ana so a yi hukuncin da kowa zai ji an so a kamanta to tilas a koma baya don warware lauje cikin nadi,
har ila yau wasu na ganin Hukumar tace Fina-finai da Dabi'i ta jihar Kano karkashin Dahiru Ahmad Beli ta taka muhimmiyar rawa wajen sake kunna wutar gaba a tsakanin yan fim din ya yin da ta goyi bayan kungiya daya ta kuma kwayewa daya zane ta hanyar tabbatar da hukuncin da waccan kwamiti yayi na dakatar da jarumar wanda shi kuma daya bangaren na AFMAN da sauran daraktoci suke ganin sam hukumar bata yi abin da ya dace ba kasancewarta hukumar da suke bai wa girma don haka kamata ya yi idan har za a yanke irin wannan hukunci to a dinga tuntubarsu ba a dinga yanke hukunci ba da saninsu ba, wannan tamkar mulkin mallaka ne wanda kuma su ba za su taba yarda da hakan ba.
To yanzu dai ta tabbata hukumar tace Fina-finai da Dabi'i tare da Kungiyar MOPPAN karkashin jagorancin Isma'ila Na'abba Afakallah suna nan a kan bakansu na sai jaruma Rahma Sadau ta yi wata shida sannan za a ci gaba da ganinta a fina-finai kuma yanzu muna iya cewa ta ci wata biyu saura hudu, yayinda kuma a gefe daya kungiyar AFMAN karkashin jagorancin Baba Karami da wasu daraktoci suke ganin wannan hukunci da waccan kwamiti da hukumar tamkar wasan yara ne.
To ko ya lamarin zai kare mu je zuwa "Wai mahaukaci ya hau kura".
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.