Tare da Abu Hidaya
Bayan mun gama ganawa da gwamnan Aderbisanat sai kuma muka waiwayi inda motarmu take da zuwanmu muka tambaya an kammala komai aka tabbatar mana da cewa komi ya kammala,
daga nan muka azawa mota giya muka yiwa garin Tanout tsinke da nufin idan mun je mu tsaya mu kwana a can da safe mu wuce Damagaram.
Ashe da sauran rina akaba ko kilo mita biyar ba muyi ba mota ta koma gidan jiya wato daukar zafi, wannan abin ba karamin bata min rai ya yi, abinda ya fara zo min rai shine kada Yan Tawayen da ake magana suna yiwa mutane fashi a hanya su cimma mana, domin an ce dare suke bi suna mutane yiwa mutane fashi,
a cikin wannan hali ne muka tsaya muka karawa motarmu ruwa muka sake daukar hanya amma kafin wata yar tafiya kadan sai Motar ta sake daukar zafi ruwan ya kone mun yi duk iya yin mu dan mu gano inda matsalar take amma ina abinku da abinda ba aikinka ba wannan yace matsalar birki ce wannan yace matsalar robar da ke kai ruwa ligireto ce ta lalace kai haka dai mu kayi ta kame-kame, wata dabara data fado mana itace tunda motar idan ta yi zafi tamfirecan tana saurin sauka to mu dena tsayawa idan ta yi zafin sai direba ya kashe motar a tafi a hankali(slow) kafin karfinta ya kare ta yi sanyi sai kuma ya kara tadata mu cigaba da tafiya a haka muka ci zango mai nisa a tafiyar, mun kusa dab da wani dan kauye Mai suna Abu zak sai motar ta mutu gaba daya taki ma tashi,
na duba gabas na duba yamma babu komai sai dajin Allah,
muna nan tsaye muna tunanin mafita sai kuma muka fara jiyo ihun buzaye daga can nesa haba ai tuni idona ya raina fata kuma gashi jejin babu wasu bishiyu balle ka ruga ka buya.
Ni dai addu'a kawai nake ina jiran tsammanin abinda ka biyo baya, sannu a hankali sai buzayen nan suka iso garemu ashe masu kai amarya ne,
wani abin dariya amaryar bisa jaki take sai kuma wasu tarin samari ko wannen su dauke da takobi dukkanninsu bisa rakuma a haka suka wuce mu suna ta ihu.
Mun isa garin silika wajen karfe goma sha daya na dare, duk mun jigata da yake garin na Bugaje ne a dudduke muka shiga Dakunan su, kasancewar dakunansu irin kananan nan ne, gaskiya Bugajen sun mana kirki domin haka suka yi ta dawainiya damu, a wannan dare aka dafa mana shayi tare wani nau'in abincinsu da ban taba ganin kalarsa ba da yake garin akwai nama dama ba'a maganarsa....
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.