LABARIN DAN JARIDA
Bana mantawa da wata ranar lahadi ina wajen taro sai wayata ta fara kara cikin hanzari na sanya hannuna cikin aljihu na dauko wayar, lambar ba suna.
A kunnena na kara tare da fadin hello muryar mace naji bayan mun gaisa sai take bayyana min wai mai bibiyar shafina ce a jaridar da nake rubutu tana min fatan alkhairi da kuma jinjina game da yadda nake fadar gaskiya a rubutuna, na mata godiya tare da tambayar sunanta? ta fada min sunanta Aisha muka yi sallama na mayar da wayata aljihu. Na cigaba da sabgata ba tare da tunanin komai ba domin kusan kullum sai na karbi waya makamanciyar wannan daga masoyana ma'abota karanta shafina a jarida.
Washe gari da safe ina shirin tafiya ofis sai ta sake kirana muka gaisa kamar jiya, amma wannan karon yanayin maganar ya dan tsawaita domin har tambayoyi tayi min.
Tun daga wannan rana kusan kullum sai mun yi waya da Aisha.
Gaskiya yarinyar tana da hankali da kuma iya magana wannan ne dalilin daya sa nake bata lokacina idan ta kira, a hankali har takai nima ina kiranta mu dade muna hira.
So shu'umi kwanci tashi kwana nesa sai soyayya mai karfi ta kullu tsakaninmu da Aisha a kalla yau mun shafe kimanin wata biyar muna soyayya, amma tsawon wannan lokaci ban taba zuwa gidansu ba kasancewar muna da yar tazara tsakaninmu tana kaduna ni ina kano.
Mun shaku kwarai da juna kuma muna tsananin son juna idan bama waya to zaka samu daya yana rubutawa daya sakon text a waya, a wannan halin Aisha zata min cake ko wani abinci ta je tasha ta baiwa direban da zai zo kano ya kawo min.
Watarana wani babban aminina zai tafi kaduna sai na bashi adireshin gidansu ya je su gaisa, daga nan ni kuma sai na gaya mata ga wani abokina nan zai zo gurinta su gaisa in zai yi yu ina so ta bashi hotonta ya taho min dashi? Ta ce ba damuwa.
Bayan kwana biyu sai abokina ya kawo min hotunanta, gaskiyar magana a lokacin dana ga hotunan bata yi min ba, amma sai na tuna ai ita bata ganni ba amma ta sadaukar da lokacinta gareni dan haka sai tausayi ya yi aiki na samawa sonta gurbi na dindin ta karfi da yaji a zuciyata, a haka muka cigaba da gudanar da soyayyarmu mai armashi da juna.
Duk da cewa ban taba zuwa gidansu amma na san kusan kowa a danginta domin takan bani labarin wasu wasu kuma takan hada mu a waya mu gaisa, kamar Mahaifiyarta da kanenta.
Ana tsaka da wannan sha'ani ina ta shirya-shiryen zuwa garinsu Aisha katsam sai ta kirani a waya tace kada nazo na bari zata zo ranar Juma'a hakan kuwa aka yi na zauna cikin jiran tsammanin ranar da zata zo.
Ranar juma'a da yamma sai ga Aisha a garin kano sai dai ranar an samu akasi a lokacin aikin ya yi min yawa bamu samu haduwa ba amma abokina shi ya kaita gidan data sauka.
Bamu hadu da Aisha ba sai washe gari Asabar a ranar da idanuna suka yi tozali da ita sai na ji sabon sonta ya sake shiga raina, ranar kamar mu hadiye juna tsabar saukin juna mun tattauna sosai game da yadda rayuwarmu zata kasance bayan aure da kuma irin tanadin da zamu yiwa rayuwar ya'yanmu.
Washe gari lahadi da sassafe Aisha ta koma garinsu tunda Aisha ta tafi sai naji kamar ta tafi da wani bangare na jikina.
Tafiyarta tazo da wani bakon al'amari domin tunda Aisha ta koma gida sai ta dena daga min waya sai in kirata wajen sau ishirin amma da kyar zata daga sau daya idan na samu ta daga sai tace min wai ina karar mata da chaji.
Wannan abin ba karamin daure min kai ya yi ba.
Idan na mata text message sam bata bani amsa, da tsanani ya kai tsanani sai na shirya na tafi gidansu na samu na ganta na kuma nemi ta sanar dani laifin da na yi mata sai tace ban mata laifin komai ba kawai dai ita maganar soyayya ni da ita yanzu babu.
Post a Comment
0 comments
Dear readers, after reading the Content please ask for advice and to provide constructive feedback Please Write Relevant Comment with Polite Language.Your comments inspired me to continue blogging. Your opinion much more valuable to me. Thank you.